Showing 54001 words to 57000 words out of 73529 words
Chapter 19 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf
Unknown
29 Jun 2025
3592
daya lullube mata xuciya. Ta nisa tace ai dole ne na jinjina maka mr
Johnson na sanka a kwai cika aiki, bani labarin dan gidana. Mr johson ya tsuke baki yayin da
xuciyar sa take yi masa tuni cewar a kyauta xaka bata labarin? Banga ta ajiye maka makudan
kudi a gefe ba, ko a kyauta xaka nemo mata ashraf din? Ko kai tsuntsu ne ba kudin jirgi xaka
biya ka je ba? ya katse tunanin da yake yi yace mai girma axixa anga ashruf a America a wata
babbar kasuwa dake Washington amma bani na ganshi ba. daya daga cikin ma’aikatanmu suka
hadu, axixa taji wani dum a xuciyarta farin cikin daya lullubeta ya fara ribas. Ta ce mr Johnson
kayi min dalla dalla na gane. Ina ashraf din yake yanxu?
Mr Johnson yace gaskiya takamaimai bansan inda ashraf yake ba, kuma shi wanda ya hadu
gaisawa suka yi kawai suka taba yar hira suka rabu. Ashraf din yace masa sarar kaya ya xo yi
xai koma Jamaica. Ya tambayi lambar wayata dan ya daina samuna a wancan tsohon layin
nawa, ma’aikacin namu yace bai san number taba.
Kinga babu wata hanya da xansan inda ashraf yake yanxu, kinga idan nace yana Washington
nayi karya tunda sare sare yake xuwa yi bama America kawai ba har sauran kasashe yana
kaiwa Jamaica, sannan a Jamaica baya garin da na sani, sannan number waya ta daya sanni
da ita da yanxu ba da ita nake amfani ba, shi kuma bai bayar da tasa ba don haka axixa sai dai
ince miki banga ashraf ba.
Hawaye mai wuyar fita ne ya ketowa axixa, ta rike kai ta runtse ido ji take daman ba a halicce
taba, ta tsani xmanta a duniya gara ace tana kwance a kabarinta da jin wannan bayani da mr
Johnson yace, yace ya naji kin yi shiru ne axixa wai dan Allah na tambaye ki? Neman ashraf din
me kike yi ne? ko ya yi miki wata yar damfara ce kinsan shi talaka ya iya butulci ka jawoshi
jikinka ya cuce ka, bayan dimbin kudin da mahaifinki ya bashi bai gode ba saida ya kwashe
muku wani abu ne ko kuma…………..
axixa ta daka tsawa a cikin fushi tace ya isa haka mr Johnson, wannan duk bai shafeka ba, ba
dole ne ka ji me yasa nake neman ashraf ba, kai ka fini sanin ashraf tunda kake da ashraf ya
taba yi maka sata ko damfara?
Haba mr Johnson karka dinga manta alheri mana.
Bana neman ashraf don wani mugun abu da ya yi kin sai don alheri, ni dai ka nemo min ashraf
in har xaka iya ni kuma xan biyaka ko nawa kake so muddin kayi alkwarin gano inda yake. Ba
sai ka kawo shi Nigeria ba kawai kana ganinsa ka bugomin waya muyii Magana dashi shike nan
ka ci kudinka. Kafin ka tafi nemansa xan turo maka da rabin kudin, idan ka nemoshi sai na cika
maka cikon kudinka. Ya kyalkyale da dariyar dadi ya mike tsaye yana xaxxagayawa dake a
bakin ruwa yake a kasarsu Croatia yace mai girma axixa kinyi Magana dama kece baki yi saurin
cemin ga masu laushi ba, masu laushi sune dollars. Da tuni baki ga ashraf ba. aida a ranar da
wanda yaga ashraf din nan yace min yaga ashraf a waje kaxa da a lokacin xanyi sauri na je
America dan idan nasa police din da suke da duty a kasuwar a ranar sunsan waye ya shiga
kasuwar daga ina yake ina xaije, da na nemo miki ashraf tuni.
Haushin mr Johnson ya kamata ya sake lullube xuciyarta tace a ranta wannan ina ga ko ruwan
gidansa uwarsa ta sha sai ta biya shi, bashi da mutunci akan kudi nanfa tafara jin muryar mr
Johnson tangarai, yaji batun kudi. Ya ce mai girma axixa xan nemo miki ashraf a kan kudi dallar
dubu dari sai ki turomin da rabi dalar dubu hamsin kenan ta account dina xanyi miki sending
text din account number, ni kuma xan bar duk abinda nake yi na nemo miki ashraf. Xanje
Jamaica tsohon gidansu kinga baxan rasa ko mutum daya da xai san wane gari suka koma ba
da adireshinsu, ko number wayar su ko?
Axixa tace a ranta da ka san da haka kaki xuwa sai yanxu da ka ji kudi. Shi dai mr Johnson
kintato kudin yayi ya gayawa axixa don idan ta nemi ragi ya rage mata saisu daidaita yadda
yake tunanin xai samu, amma ga mamakin sa sai yaji ta yarda. Axixa tace mr Johnson na
yadda xan baka dollar dubu dari ka nemo min ashraf amma kada ka wuce kwana goma xuwa
goma sha uku daga yau, sannan kayi min sanding account nuber taka ni kuma ranar litinin dake
yau asabar babu aiki litinin xan turo maka da rabin kaje ka nemo min ashraf , kana ganinsa ka
kirani a waya ka bani ashraf muyi Magana shi kenan ka cika aikinka, cikon kuma xan turo maka.
Dariya yake kyalkyalewa dadi yayi masa yawa har ya kasa Magana, axixa ta kashe wayarta
cikin sanyin jiki ta sulale ta kwanta kan gadonta tana mai tasanin jin takaici, yayin da kuka ya
kece mata mai dauke da tsananin tausayi ya kecewa axixa babu abinda take ji a ranta sai
tsananin bakin ciki da tsanar ci gaba da rayuwa a duniya . Wayar tace tayi ringin cikin mamaki
waye yasan numberta har aka fara kiranta, kasancewar ta duba taga ba mr Johnson bane
number MTN ceta Nigeria , sai ta latsa cikin sanyin murya tace hello. A harshen turanci taji ance
ah axixa har kin yi bacci ne? ta yi shiru bata bada amsa ba don bata san ko waye ba, bata gane
muryar ba balle number. Ya sake cewa na kira ki ne don naji ko wayar da layin suna yi sosai
babu matsala? Axixa batace komai ba dai tana sauraron mai Magana yayi dariya yace axixa
kinki Magana lafiyarki kalau kuwa? Dr eltayyib ne ke Magana, ta yi wata doguwar ajiyar xuciya
kana tace doc kai ne? ban gane ka ba na yi mamakin waye yake kirana bayan yanxun nan na
sayi layin ni kuma bansan numberka ba, waya tana lafiya kalau nagode doc saida safe. Ta yi
sauri ta katse wayar ba tare da ta barshi ya sake cewa wani abu ba, ta kifa kai taci gaba da rusa
kukanta, can taji wayar ta sake yin kara kadan ta jawo wayar ta duba sai taga text message ne
ya shigo, ta bude inbox don ta karanta cike da mamakin kuma waye yayi mata message taga
wasu zakakan kalmomin soyayya ne daga kasar ya rubuta sunansa dr eltayyib. Taja wani
dogon tsaki gami da kashe wayar kwata kwata ma. Ta duro daga kan gado taje ta saka wayar a
caji tasa mukulli ta datse kofar dakin, tasa rigar baccinta ta kashe fitilar sai abinda ya dameta a
ranta cikin bargon nan nata xugi da radadin bakin ciki ya sake dawo mata damuwa da takaici
fiye da na da suka dawoma xuciyarta tace bana mantawa da mahaliccina, Allah KaiKa halicce
ni Ka jefani a cikin halin da nake ciki, Kai ne kuma xaKa fitar dani, Allah nagode maKa, Allah
Kaine abin godiya. Yayin da ta fara jin duk wata damuwa tana gushewa daga xuciyrta, domin
kuka ba xaiyi mata magani ba, Allah(SWT) Shi ne babban maganin duk wata masifa da bala’i.
Allah sarki, axixa da tunanin ashraf ta kwanta don haka da mafarkin sa ta kwana, mafarki mai
dadi wanda ya sata farka da farin ciki matukar farin ciki kuwa taji ana kiran sallar assalatu. Tayi
salati ta mike don yin sallar asuba, bayan ta idar ne ta xauna tana laxumi da yan addu’o’inta,
yanxu addu’ar axixa bata wuce ta roki abu uku xuwa hudu, na farko tayiwa mahaifiyarta da ta
rasu addu’ar nema mata gafara a wajen mahaliccinta da sauran musulman da suka rigamu
gidan gaskiya. na biyu kuma ta nemawa mahaifinta samun Karin lafiya da Karin arxiki da kuma
Ubangiji Ya bashi nasara akan duk abinda ya sa a gaba na alheri ya dora shi akan makiyansa
masu son suga bayansa ya saya ci gaba da kyawawan halayensa su bishi har kabarinsa. Sai
kuma wannan mawuyancin hali da take ciki Allah Ya yassare mata ya fitar da ita daga tashin
hankalin nan da take ciki na bangarorin nan guda biyu, na daya sharrin da alhaji isah yake
shirin ya jefasu a ciki da kuma yadda xata tari mahaifinta tace ashraf ne yayi mata ciki ba
mubarak ba. tasan wannan Magana ba karamar batawa mahaifinta rai xai yi ba.
Basu da ta cewa kuma a kotu tunda bamu da gaskiya, tunda babu wanda ya san ashraf don
haka cewa xa a yi karya ake yiwa ashraf sai dai in uba ne ya yiwa yarsa ciki da gaske ne kenan
xancen alhaji isah, axixa tace a ranta dole nayi shiru mu tayin shari’a da mubarak akan rashin
gaskiya kenan, idan ashraf bai xo ba, ba xan taba cewa ba mubarak ba ne. haka axixa ta
kasance ta yi kuka tayi addu’a har gari yayi haske tangarai. Ta shiga bandaki tayi wanka tayi
brush taxo ta shirya tsaf ta ci kwalliyarta.ta bude mukullin kofar dakin don likitoci da nurses xasu
fara xagaye don duba mararsa lafiya. Ta koma kan gado ta jinginar da kanta a jikin filo taci gaba
da tunanin kywawawan mafarkin abin kaunarta ashraf da ta kwana tana yi a daren jiya. Ashraf
ne sosai ta gani suna waje mai kyau suna hirar soyayya. Hakika wannan mafarki ba karamin
fami yayiwa axixa a xuciyar taba, ya sake taso mata da dankareriyar soyayyar da take yiwa
ashraf a ranta ta ji dama su hadu mana kamar yadda ta ganshi a mafarki suna tare a yanxu da
take tsananin nemansa.
Xuciyarta tace gaskiya mutum ba a bin wulakantawa ba ne ko yaya ya ke Allah ne Ya halicce
shi,kuma kowa da baiwar da Allah Ya yi masa, mai kudi da talaka duk daya ne a wajen
mahaliccinsa, sai dai wanda Ya fi tsoron Allah shi yafi matsayi ranar gobe kiyama.
Na wulakanta ashraf don na tsani talaka ina ganin talaka shi ya so ya zama talaka ni a haukata
don bansan talauci ba, ban taba dandana shi ba, sai da Allah Ya nuna min ishara nayi kwana
ashirin da hudu a cikin rayuwar talauci na dandana.
Yau ga shi dan talaka da da dallar dubu dari ina neman sa na rasa shi, ashraf yau ya fi min kudi
wuyar samu. Da kudin nawa na rasa ashraf din dana ke kiransa da wulakantacciyar dabba, yau
shi ya jefa ni da mahaifi na cikin damuwa, saboda talaka guda daya wanda da ban dauke shi
mutum ba, na yi kuskure nayi kuskure! Nayi nadama, na koyi darasi a duniya yanzu babu wani
mutum baya ga mahaifina wanda nake so da tsananin kauna a raina irin ashraf talaka likis na
mace a sonsa, wannan duk ishara ce Allah Ya nuna min. Ba a wasa da ikon Allah, Allah natuba
ni ba komai ba ce illa kaskantacciyar baiwarKa bani da komai ba ni da kowa bansan komai ba
kuma sai abinda Ka sanar da ni ya Allah aziza tana fadi a zuci Wani lokaci a bayyane tana
hawaye tana yiwa Allah kirari saboda Ya nuna ikonSa akanta, ya nuna mulkin Sa a kanta, Ya
nuna isarSa a kan ta, don ita bata isa ba, babu mulkin nan babu takama duk sun kare. Haka
aziza ta kasance cikin nadama cikin addu'a wani wani lokaci ta yi kuka.
Ranar litinin tayiwa atika waya ta ce taje dakinta cikin durowarta ta dauko mata cek dinta na
bankunan da take ajiyar kudadenta. Tayi mata gargadi kada tabari kada ta bari kowa ya sani
musamman mahaifinta. Idan zasu zo su taho mata da shi, don kusan kullum sai atika da
munnira sunzo sun yinin mata. Bayan sun zo tayi musu wayo ta sulale ta ce musu tana zuwa, ta
tafi ta hau taxi taje banki tayi cuku cuku taturawa Mr Johnson wadannan makudan kudi har
dalar dubu hamsin rabin kudin da suka yi za a tura masa, sannan tadawo asibiti suka ci gaba da
hirarsu dasu atika ba tare da sunsan ina taje ba.
Kwanci tashi yau saura kwana biyu daga CIKIN KWANA ASHIRIN DA HUDU da Alhaji isah ya
daukar wa Alhaji Ahmad ya bashi kujerarsa ko ya fitar da mujallun nan, kuma kirmisisi har yau
Alhaji isah bai ji sako daga wajen Alhaji Ahmad ba. Wannan abu ya bawa Alhaji Isah mamaki
don shi a tunaninsa Alhaji Ahmad xai tsorata yayi sauri ya janye ya bar masa, amma yaga ko
gexau. Ransa ya baci sosai ya sake lasar takobinsa kuwa sai ya yi masa rashin mutumci da sai
dai kowa ya rasa a tsakanin su sai ya masa cin mutumcinmutumci Idan kwana ashirin da hudun
nan ta cika be ji komai da ga bakin Alhaji Ahmad ba. Mujallu Kuwa ana ta ci gaba da bubbuga
su da yare daban daban don kowacce kabila ta gane sakon da ake son a isar. Hankalin aziza
ya sake tashi ita kadai take jin abinda yake damunta azuciyarta. Kullum kunnenta a sauraron
radio dake wayarta ko taji yo abinda ke gudana a kasar amma har yau bata ji wani labari ba da
ya dibanci rigimarsu da Alhaji Isah, kullum cikin dare sai tayiwa Mr Johnson waya amma bata
samunsa, ko taji a kashe, ko kuma tayi ta ringing ba a dauka ba. Hankalin aziza ya kara tashi
tace a ranta me Mr Johnson yake shirin yi min ne? Na bashi rabin kudi har yau bamu yi
magana ba na ji ko kudin ya sameshi ko bai same shi ba ma, yana Jamaica koma a gida yayi
kwanciyarsa akan kudin yaki zuwa oho. Gashi saura kwana biyu cif a fitar da mujallun nan sai
shiga kotu kuma.
A kotu mune ba mu da gaskiya domin Mubarak bai yi min ciki ba ashraf ne, na rasa ashraf din
kuma. Ta rushe da kuka, tayi ta huta ta ci gaba aikin ke nan ga babu mai lallashin ta don ita
kadai take kebewa ba tare da kowa ya ganta ba. Dadinta ma, bata mantawa da mahaliccin ta
Bata gajiya da yin addu'a, don komai yayi tsanani maganin sa Allah, kuma addu'a ita ce babbar
makamin mumini, salihan bayi basa bin yan tsubbu da bokaye idan masifa ta same su daga
hannu sama suke suna neman sauki a wajen Ubangijin su.
KWANA ASHIRIN DA HUDU.
kwana ashirin da hudu ta cika, da misalin karfe bakwai na safe..........
.
.
.
To en uwa, da patar ba muna karanta littapin bane kawai domin nishadantar wa kawai, mu dage
mu ilmantu daga darasin da ke cikin sa, Allah Ya sa mu dace.
Aamiin.
.
Sannan ku ba Aziza shawara ya xatayi?
Comment dinku yana burgeni
[9/12, 5:32 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT4
*27*
Abinci kala kala aka shiryawa baiki, amma Hajiya Fatima mahaifiyar Ashruf kinci tayi saboda
taga wasu bakin mutane magana taki ta amsa. Mijinta sai bayani yake cewar bata magana ai
sai dai wani lokaci idan abin ya tashi take kiran sunan Zubaida ko Takaka ta ce ina suke? Sai da
aka kaisu taa babu kowa sai ita sai mijinta ya lallabata sannan ta zauna ta ci abinci. Ya sa ta
tayi wanka ta zo ta kwanta yini tayi tana bacci saboda kwana sukayi a zauce a jirgi.
Washegari ranar juma’a kenan ta:I karfe tara na safe jama’a suke tururuwar zuwa kotu don
kawai aga Alhaji Isa saboda za a fito da shi zuwa kotu daga wajen ‘yan sandan da yaka a tsare
dan yin shari’a da su Ashruf Tururuwar jama’a daga wasu garuruwan ma zuwa ake. Su Alhaji
Sadam sun hallara kakaf dinsu a gidan Alh. Ahmad tun karfe tara, tara da rabi suka dunguma
cikin motocinsu zuwa babbar kotu. Su Alhaji Ahmed sunyi matukar mamakin ganin dandazon
jama’ar da suka yo ca adan Alhaji Ahmed suna daga masa hunnu suna Allah ya kiyayeka sai
mai gaskiya, sai kayi shugaban kasa. Dakyar da sudin goshi
Yan sanda da bodyguards dinsa suka kareshi saboda jama’a kowa yana so ya yi hannu da shi
kafin su shiga Alhaji Elmustapha ya ce “Muddin suka shiga ciki da matarsa taga takaka tabbas
za ta rikice ta hana a ara aiwatar da shari’ar don haka ya ce ba ta rikice ta hana a fara aiwatar
da shari’ar don haka ya ce ba za su shiga ciki ba. Karfe goma da minti uku babban alkali mai
shari’a (Chief Judge) ya shigo shi da sauran mataimakansa masu shari’a kowa ya mike don
girmamwa sai da lkali mai shari’a ya zauna sannan kowa ya zauna. Allkali ya bawa
magatakarda izini ya karanta shari’a, magatakarda ya fara karanto abinda yasa mai kasa Alhaji
Elmustapha yake karar Alhaji Isa Elyakub. Shigowar Alhaji Isa ce tasa kowa ya waiga yana
kallon ikon Allah. Alhaji Isa ne sanye da wata riga ‘yar shara fara wacce wuya tasa tayi bakikirin
kamar wani tsohon mahaukaci. Ankwa ce a sakale a hannayensa da kafafuwansa. ‘Yan sanda
biyu ne suke biye da shi suka kaishi cikin dan kewayen da wandanda zasu fafata shari’a suke
tsayawa a gaban alkali. Alhaji Isa Elyakub ya kasance yau yana cikin wani hali na tsananin
bakin ciki da takaici, kamar yadda ya saba suka jama’a a irin wannan yanayi na kunci. Babu
haushin wanda yake ji sai Ashruf saboda shi ne ummul aba’isin tona masa asiri har ta Kaishi ga
sawa a kashe minister. Fada yake da zaga-zage tsakaninsa da Allah. Wanda wannan ma
babban laifi ne daya sabawa dok kotu, cewa yake ‘’karya ake min dukka sharri ne, waye
Ashuruf da zaice nine na kwashe kudin mahaifinsa shekaru ashirin da hudu shi kansa yaron
baifi shekara talatin ba yaushe