Showing 42001 words to 45000 words out of 73529 words

Chapter 15 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3598

na ke baki fa bawai rokarki nake yi ba… alhaji bala ya katse maganar da yake yi
a fusace y ace kai! Kai!! Mubarak dakata kada ka sake ka sake kirawo axixa a waya baka da
hujjar ka xabar mata abinda xata yi kana jina ko! Mubarak y ace shin da wa nake Magana na ji
dai ba muryar alhaji ahmad bace, alhaji bala y ace koma dai dawa kake Magana ba dole ne ka
sani ba, ka rabu da axixa ta huta bata jin dadi, duk wasu kwanankin da kuka dauka duk na
banxa ne babu wanda xaku iya tsoratarwa duk abunda xaku yi kuje kuyi, in Allah Ya yarda
kanku xai koma. Mubarak ya nisa y ace ok yanxu na fuskanci da wanda nake Magana, abban
munnira ina ganin kune fasagurbin kwai da kuke dumama wannan Magana kuke tursasawa,
kuke xuga alhaji ahmad kada ya sauka ya barwa daddyna.

Hakika shi ya fiku sanin gaskiyar al’amari kuna cutarsa ne xaku kaishi ku baro shi kuma. alhaji
bala ya daka tsawa y ace kai mubarak ka iya bakinka nib a da kai xanyi ba sai dai nayi da
ubanka marar kunya, banxa shashasha, dabba… alhaji ahmad ya taso ya fusge wayar daga
kunnen alhaji bala ya yi sauri ya kasha wayar ma kwata kwata ba tare day a bari mubarak ya
mayar da amsa ba, alhaji bala ya dawo kan kujerar da yake xaune ya xauna yana huci ga gumi
don tsabar fushin day a dira a xuciyar sa, ji yake inama mubarak a kusa das hi yake day a masa
habo don naushi xai skar masa a wannanbudadden hancin nasa irin na ubansa sai ya fashe .
alhaji ahmad y ace haba bala ina kai ina tsayawa da wannan yaron kana fadi in fada das hi, ai
ba sa’anka bane, to ko ubansa ma yanxu ka tsaya kuna fadi in fada kasancewar kasanshi bashi
da hankali mahaukata ne fa, alhaji ahmad ya karaso gadon da axixa ke kwance tana hawaye
har yanxu, ya dafa kanta y ace axixa ki daina kuka, kukan me kike akan mahaukacin yaron nan!

Ban gaya miki ba idan kinji irin wadannan abubuwan ki yi ta addu’a Allah Xai yaye miki, kiyi
shiru. Ya warwaro tissue yana goge mata hawaye. Alhaji bala yace ai wannan anyi ba’ayi ba ne,
an canja mata daki don kada mutane su dameta ashe kuma a waya xasu ringa damunta. Alhaji

ahmad y ace ai nima tunanina da nake yi ken an ina ganin da wayar xan tafi gida don ba xasu
kyaleta ta huta ba. ya kalli nurse din da take kula da ita y ace baiwar Allah mu xamu tafi idan
ruwan nan da aka saka ya kare ki cire mata ki kaita bandaki tayo alwala taxo tayi sallah gad an
karamin kur’aninta nan akn loka ki bata ta karanta ko ta daina jin yawan faduwar gaba da bacin
ran nan. Axixa ki dage da addu’a Allah Xai fitar dake daga duk wani makircin makiya, kinji ko!
Axixa ta gyada kai da kayr alamar taji, tausayinta ya lullube shi yaji kwalla ta cika masa
idanunwa, yaji tsana kan tsana fiye da tad a yake yiwa mubarak da babansa alhaji isah. Haka
suka yi sallama da axixa suka tafi suka barta a nan a kwance cikin halin damuwa musamman
ma wayarta da babanta ya tafi mata da iat. Tana shirin idan ta sake samun saukin jikinta ta sami
karfin yin Magana tana so tayi wa mr Johnson waya ta sake ji ko ya jiyo inda ashruf yake ya
nemo mata shi kafin nan kan kwana ashirin da hudu da aka dibar musu ta cika, to gashi yanxu
daddynta ya tafi da wayar tata. Hawaye ya sake kece mata hard a sheshekar kuka, Halima ce
ma’aikaciyar dake kula da ita tasa tissue tana goge mata hawayen idanuwanta tana bata baki
akan tayi hakuri ta daina kuka.

Xuciyar Halima cike da mamakin ko me ya sa axixa take kuka! Dunbin dukiyar babanta, da
iliminta, ga kyau ga gata ita kuwa me xai dameta a duniya! Halima take tambayar xuciyarta.
Hakika kowa da abinda yake damunsa wani rashin kudi ya dameshi wani ko kudin ya dameshi
inji wani mawaki.
Bayan dawowar axixa wannan sabon sashe cikin taimakon Allah saboda yawan addu’o’in da
axixa ta dage tana yi ita da mahaifinta, cikin kula ta musamman da likitoci suke bata Allah Ya
sauwakewa axixa yawan damuwa ta daina jin bugun xuciyar nan da yake damunta. Don takan
tashi xaune kan gadonta tana kallon talabijin, an sayo mata kasissinan ibro iri-iri sababbi da
tsofaffi na da, tana kallo wani lokaci tayi murmushi wani lokaci kuma ta tsuntsure da dariya idan
yayi wata kwabar. Yau axixa kwananta tara a asibiti kwananta biyar kuma da dawowa wannan
sabon sashi. Amma sai yau da kyar da sudin goshi sannan alhaji sadam ya bar atika da
munnira xasu xo wajen axixa. Da yaki fur wai ba xa su xo su dameta ba. gani yake xasu iya
fada mata wasu maganganun akan abubuwan da alhaji isah da dansa suke yi a gari, sun fara
yadawa amma indirectly cewar alhaji ahmad xai sauka daga kan kujerar takarar shugaban kasa
ya bawa alhaji isah. Har alhaji isah duk ya fara sawa ana lillika fostocinsa duk da dai bai fito fili
ya fadi cewar shi dan takarar shigaban kasa bane yanxu amma yana cewa yana batawa alhaji
ahmad da abokansa rai alhaji sadam da alhaji bala, don bayan su biyun nan babu wanda
yasan abinda yake faruwa tsakanin alhaji isah da alhaji ahmad said a kuma a can bangaren
alhaji isah ya fara yadawa wasu kadan daga cikin abokansa cewar alhaji ahmad xai sauka ya
bar masa kujerarsa saboda wani abin kunya day a dunguma.

Don haka kafin alhaji sadam ya bar su atika su taho asibiti wajen axixa said a ya kirasu falonsa
ya ja musu kunne sosai y ace to yau asabar xan barku kuje ku yini a asibiti wajen axixa, ban
yarda ku saki baki ratata kuna hira ba balle ku yi subutar baki ku fadi wata Magana da xata sake
dagawa axixa hankali. Don yanxu jikinta da sauki hankalinta ya fara kwanciya ana hira da ita
radai da wasa da dariya, musamman ke atika kinfi munnira shegen surutu ko sunan mubarak
karku furta mata balle wasu abubuwanda yake yi, kinga rannan ina nan falo nake jiyo muryarki

kina bawa mamanki labara wai kinga mubarak a mr bigs shi da wata sumayya Emmanuel ‘yar
gidan gwamnan lagos ya rike hannunta suna siyan ice cream ina ruwanki! To ki iya bakinki karki
sake ki fadwa axixa. Atika t ace to in Allah Ya yarda ba xa mu fada mata maganar da xata tayar
mata da hankali ba. alhaji sadam y ace yauwa idan kuma ita ta tambaye ku wani abu game da
mubarak ko kuma mijallar nan da xasu fitar don alhaji ahmad ya gaya min har mafarki take taga
su mubarak a kotu, to sai ku ce mata ai yanxu xancen mujalla ko xancen kotu yak au an
daidaita da alhaji isah ya amince yanxu mubarak ne yayi cikin harma an kone mujallaun xance
ya wuce.. da dai sauran maganganun da xasu kwantar mata da hankali in Allah Ya yarda ma
har kwana ashrin da hudun ta cika su fitar da mujallaun suyi haukarsu su gama ba xata sani ba
tana asibitin a kulle. Daga karshe su atika suka yi gidya suka mike suka doshi wajen mota suka
shiga suka nufi asibiti dake daman sun gama shirin su tsaf xasu tafi ya kirasu yayi musu
wannan gargadi.

Atika sadam c eta ke tukawa wata tsadaddiyar motar da mahaifinta ya bata a matsayin kyauta
ta kammla jami’a da suka yi. Munnira na gefenta suna tafe suna hira suna tuntsira dariya. Atika
ta kalli munnira t ace wai baba ni yake cewa na fiki shegen surutu lallai baba nai sanki ba, ina
na kai rabinki ma a surutu, sai dai y ace kinf I ni wayon ladabin karya idan kinga manya ki rika
sum sum da kai da kyar kike magna, ni da axixa ne ‘yan gaste gates munnira ta kyalkyale da
dariya t ace kamar kin sani amma fa kwannan nan abbana ya gano hali nay a ce munnira
munafuka ce mai ladabin karya. A haka dai suka ci gaba da hira ta makaranta hard a ta gida
har suka isa shop suka yi siyayyar kati ta get well soon da kayan kwalama masu yawa, nan
cikin ma’aikatan shop din suka taimaka musu da kwashe kayan. Akujerun baya suka xuba
kayan sannan suka yi musy Allah Ya kiyaye hanya.

Gaskiya en matan nan biyu sun bawa mutanen dake wajen matukar sha’awa, samari da
alhaxai da masu kudin inyamurai da suke shige da fice a wajen wato chief, babu wanda ransa
bai biya da son ‘yan matan nan a xuciyarsa ba, musamman ma irin shigar da suka yi, kayansu
iri daya, mayafansu ne da takalman su kawai suka banbanta, suna tafe suna hira har suka
shiga mota, jama’a na kallonsu, wasu suna satar kallonsu wasu a kiri kiri suke bawa idanunsu
hakkinsu.

Mahnud sa’ad mijinyawa dan gidan gwamnan baushi state ne yana daya daga cikin masu
kallon kuru kuru, babu abi8nda xuciyarsa take sai dukan uku-uku tke domin shi har yaga matar
da yake so, ya dade yana mafarkin irinta ta xama matarsa gasu nan ‘yan maa gwanin kyau
wannan na cewa munnira ce tafi wancan na cewa atika tafi kyau, amma babu wanda yayi karya
kuma idan mahawara xa a fafata akn wacce tafi kyau atika ko munnira bana jinx a a iya kayar
da kowa a duk bangarorin biyu, atika tad an fi mannira tsaho duk da dai su duka dogaye ne
marasa kiba, kyawawa.

Yanxu a cikin ‘yan matan nan biyu idan aka ce ka xaba wa xaka xaba! Imran ya tambayi
abokinsa Mahmud sa’ad da basher. Basher y ace farar, imran y ace a’a a ganina bakar ta fi
kyau, dube su sosai kafin su shiga mota. Mahmud sa’ad wanda har yanxu yake xaune a
bangaren direba dake shi ne wanda yake tuka motar bai ce komai ba yana kallon atika wacce

tun da yayi toxali da ita ya bawa xuciyarsa shawarar ga abokiyar rayuwarsa. Shigowarsu kenan
suka tsaya a kusa da motar su atika ko kiftawa basu yi ba daga cikin motar suka hango ‘yan
matan nan suna fito shi ne suka yi lamo a mota suka ki fitowa suna kallonsu ta cikin gilas din
motar su dake baki ne wulik (tinted) na waje baya ganin na ciki. Dai dai sanda atika take bude
kofar motarta xasu shiga imran da basher suka yi xuruf suka fito daga motarsu da sauri wai bari
su wuce ta gabansu sun san suma sun hadu dole ‘yan matan xasu yaba, Mahmud sa’ad yana
kallonsu suka fita suna tafe suna gyara riga (shirt) suka wuce ta gaban ‘yan matan nan, suka ga
ko gexau su da bola duk daya ne k inda suke ma ‘yan matan basu kalla ba, suka shiga motarsu.
Atika ta kunna mota inda taja wani dogon ribas har wajen get din tasa giyar gaba ta tayar da
kan motar sannan ta hau titi dodar ta bude wuta tana keta gudu a titi. Imran da basher ya suka
jiyo suna kallonsu har suka kure, sannan basher ya bugi imran da bayan hannunsa y ace dalla
malam ga irin tan an n ace muyi musu Magana kace wai mu wuce ta gabansu xasu dasu aiga
irinta nan sun kufce mana, kai ba kyau ba, nib a fasali ba, ya xa a yi su wani dasa! Ai na so mu
tsara su suga muma akwai dollars a bokina sais u sauraremu.

Imaran y ace mun yiwa kanmu wallahi amma ai na rike nambar motar tasu (ATI ONE) aka
rubuta a irin wuraren nan na ‘yan hutu ina sa ran wataran xamu sake haduwa. Kafin imran ya
rufe bakinsa Mahmud sa’ad ne ya ja wani dogon ribas ya fita a guje. Wait wait! Suke fadi amma
ina ya taka tad a karfi ta fisgeshi aguje yake don kada su atika sub ace masa, imran ya kalli
basher y ace shegen nan fan a san ‘yan matan nan xai bi, gara ma nayiwa usman direba waya
ya kawo min motata nan idan bah aka ba sai dai mu kwana a nan don na san Mahmud ya
manta da mu tunda yabi ‘yan matan nan bama xai sake tunawa da yabar wasu a 911(nine
eleven) ba sai ya ganmu xai hau salati y ace ya manta. Atika gudu take sharawa tsakaninta da
Allah kasancewar ta sami titi makeke marar cunkoson motoci ko gargada. Haka xalika shima
Mahmud biye yake da ita a guje, atika tana lura da hadaddiyar bakar jif din dake binta gaf da
gaf ta madubi. Ta ce da munnira kai munnira nifa wannan bakar jif din dake bina banfa yadda
da ita ba, kinsan garin nan ba lafiya karfa shegun nan ne suke binmu da wani mugun abu.
Munnira ta juya da sauri tana liken motar dake bin su t ace wai suwa kike xargi!

Su mubarak ai munfi karfin su da ikon Allah sharrinsu ya koma kansu, tsaya su wuce in ymu
mu bisu baya. Atika tasa siginal alamar xata tsaya kana tayi slow ta fara gangarawa gefen titi,
ta samu waje ta tsaya cak. Abin mamaki sai wannan bakar motar da take binsu itama tayi gaba
dasu kadan ta gangara gefen hanya ta tsaya, wannan abu ya karatsorota ‘yan matan nan biyu
suka kuma sake gaskatwa su wannan motar take bi, suna xaune a mota suna kallon motar a
gabansu xuciyarsu cike da fargaba, kwakwalwarsu cike da xulumin yaya xasu yi, sai suka ga an
bude kofar gaba ta bangaren direba, wani santalelen saurayi ne mai gwarxa-gwarxan ido ‘dan
kyakkyawa ya fito daga motar, (NI KUMA NACE KOMAI KYANSA BAI KAI BOSS INA BA) ya
fito ya tunkaro su atika. Cikin fargaba da rudani munnira t ace da atika, atika yi sauri ki danna
mana lock din motar atika ta danna kofofin motar dukka hudun suka datse, ya karaso daidai
wundon atika yana mata Magana ta gilas dake duk gilashin motar a dage suke daman saboda
na’urar sanyin da suka kunna a motar wato A.C ya sake matsowa ya sunkuyo yana Magana,
amma babu kalma daya da ta shiga kunnuwansu basa jin abinda yake fada, yasa hannunsa ya
kwankwasa gilas din da wani xoben da yake jikin babban dan yatsansa yana ci gaba da

Magana, munnira da atika sai xare ido suke yi a tsoroce suke musamman ganin hannunsa daya
a aljihunsa yake, suna fargabar ko wata ‘yan bindiga ce . atika ina ga mu ruga a guje mu bar
mutumin nan bashi da gaskiya haka kawai daga ganinmu a mota ka ringa binmu mun tsaya
shima ya tsaya to me xai ce mana! Ko kin san shi ne a wani wajen atika t ace kin jiki, ina xan
san wannan halittar ke baki sanshi, bakya ganinsa kamar ma bad an…
.
.
Comment dinkufa yaragu ko littafin babu dadi mucanza wani ina neman shawararku
[9/5, 3:23 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[9/5, 3:24 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT3
*14*

.
Ba kya ganinsa kamar ma ba dan Nigeria ba, kamar wani black American, ko wani dan south
Africa koma wani dan Somalia ne oho, kuma da yadda akayi bashi kadai bane a wannan bakar
motar don tun a 911 na ganta a kusa da mu har wasu samari guda biyu suka fito daga ciki.
Munnira tace ah to wannan mu suke bi dan Allah tada motar mu gudu rabu dashi, sai wani
murmushi yake yi na mugunta, duk ire-irensu mubarak ne ‘yan iskan lagos ne kinsan yanxu
mubarak sune da lagos saboda sumayya Emmanuel, muje muje atika karki sake kallonsa ma.
Atika ta kunna mota da sauri yayain da ta fussga a guje tabar shi a nan a tsaye. A guje take
tukin har saida ta daina hango shi sannan tayi ajiyar xuciya. Ta ce munnira kina ganin xamu ci
gaba da yawo a cikin Abuja haka mu kadai, nifa su mubarak sun fara bani tsoro kinsan me ya
faru? Munnira tace a’a sai kin fada. Atika ta sauke numfashin daya tunkaro hancinta ta juya
tadan kalli munnira sannan ta mayar da idanuwanta ga kallon gabanta tace kinsan ada sadik
gulma yake yi irin baya bin bayan axixa baya kuma bin mubarak, to yanxu da gulmar ta kare
masa shi ne ya fito sarari yana cemin wai gaskiya axixa bata kyauta ba, me nene da me nene
wasu surutan banxa dai harda cewa in har ina so dangantakar mu da soyayyarmu ta ci gaba
dole ne naja baya da axixa don ba xai yiwu yana hulda da mubarak ba yaxo yana yi da axixa
domin idan ina tare da axixa xasu ringa haduwa, munnira ta danyi kara don mamaki yayin da
wani ashar ya kubuce mata tace A’uxubillahi har ina danna asher yanxu haka sadik yace miki?
Mamaki xai kashe munnira atika ta kyalkyale da dariya, nace masa kai yanxu sadik banda
abinka soyayyar ma da muke yi kara ce kawai, ba wai har xuciyata ba, babu inda xata je. Wato
kai a xatonka nayi nisan da bana jin kira akanka har wasu dokoki xaka sakamin kenan?

Na ce to kuwa da ka cire matsayin da ka kai kanka a wajena don kuwa Karen gidansu axixa
ma baxan rabu dashi ba balle axixar kanta. Xanfi jin ciwon rabuwa da beran gidan su axixa da
rabuwa da kai. Munnira ta kyalkyale da dariya tana tafawa saboda bala’in burgeta din da ta yi
wajen bashi amsar da ta dace da maganar daya fada.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login