Showing 39001 words to 42000 words out of 73529 words

Chapter 14 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3605

uwana ahmadu Allah Ka raya masa ita Allah Ka
dubeta Ka fito da gaskiya akan mugayen mutanen nan da suke kokarin su sheganta mata
abinda ke cikinta.

Mubarak ashe haka kake? Mun dauka kai na gari ne? ashe badon Allah kake son yarinyar nan
ba? ka lallaba ta kayi mata ciki, sannan ka guje ta? Kamar a mafarki axixa take jiyo surutan
hajiya lantana firgigit ta mike xaune tana mikewa ta tashi da axababben ciwon kai da
mummunan bugun xuciya dr rislan aguje ya taso ya riketa ya mayar da ita ya kwantar akan
gado. Hajiya lantana wacce tuni tadau kuka kai kace axixar ta cika, cikin sheshshekar kuka

axixa take cewa dr rislan ka taimake ni dr ka yi min allurer nan yanxu na bar duniya dan
xamana a duniya bakin ciki ne. baka ji abinda mubarak suke cewa ba? likita nata kokarin
lallashinta yana cewa xanyi miki allurer kwanta tukuna. A daidai lokacin ruwan da ake kara mata
yakare, dr risalan ya dauko wani sabo akan ‘yar karamar lokar dake gefen gadon ya xare na da
ya saka mata wannan, ya dauko wata allurer ya matsa a cikin ruwan allurer da xata sata tayi
bacci mai nauyi.kafin yagama ‘yan soke soken sa har bacci ya fara daukar ta surutan dake yi
tana Allah Ka dauki raina yau yana yin kasa kasa har tayi shiru luf bacci ya dauketa.

Dr rislan ya kalli lantana yace hajiya kiyi shiru ciwon ya lafa bakya ganin ta yi bacci kuyi dai
addu’a Allah Ya sawake mata, a naxarin da nayi da kuma abinda idona ya gane min ciwon nan
na axixa baya bukatar dan xaman jinya saboda akwai kalma guda daya da in an fadeta take
tayar mata da ciwon, koda yake xanyiwa Alhaji ahmad mahaifinta waya ko kuma idan ya xo
xamu yi maganar, ina ganin xamu canja mata sashe inda kwatakwata ma babu mai xuwa
wajenta balle ya fadi Kalmar da xata ringa bata mata rai sai mu ma’aikata kawai xamu ringa
kula da ita. Nan fa hajiya lantana ta hau dr rislan da fada tana cewa yaushe aka fara wannan
sabon tsari abar marar lafiya shi kadai babu ‘yan’uwa? Tun tashina idan an kwantar da mutum
da wani daga cikin en uwasa a wajensa, sai dai idan da gaske ne da aka ce likitocin yanxu su
suke karasa maras lafiya su cire masa kayan cikin. Dr rislan ya yi murmushi ya nufi kan kujerar
da yake xaune daya kwashi ‘yan kayayyakinsa na aune aune ya nufi kofar fita. Hajiya lantana
bata yi shiru ba, ta ci gaba da cewa yaro ina maka kallon mai gaskiya da imani karfa ka sake ka
bawa ahmadu wannan shawara ta dauke dan xaman jinya don ni ko da ya yarda babu inda xani
ina tare da axixa.

Dr rislan ya sake kecewa da dariya yace hajjaju kenan, mu ma likitoci burin mu muga marar
lafiya ya sami sauki. Kuma koda Allah Ya sa cutar ta mutuwa ce ya rasu a hannunmu wallahi
hajiya wani lokacin munfi ‘yan uwansa jin tashin hankali, balle axixa ki tambayeta ni ne likitansu
duk kasar nan shekara da shekaru. Ya sa kai ya fice yana murmushi. Hajiya lantana a tsaye
take ta sankare tana sake maimaita maganar dr rislan a ranta babu dan xaman jinya, babu dan
xaman jinya kamar yaya? Kashe ‘yar xasu yi. Bari ahmadun ya xo na ji abinda xai ce. Amma
babu yada xa a yi marar lafiya a barshi shi kadai ace kuma xasu barshi da rai basu karasa shi
ba sun cire wani waje nasa ba. haka kuwa akayi baban axixa na xuwa ofishin dr rislan ya wuce
kafin ya shiga dakin da axixa ke kwance. Dr rislan yace alhaji na lura akwai wata muguwar
muguwar Magana da axixa take tunawa ko kuma idan wani ya furta take jin tashin hankali har
budun xuciyarta yake canjawa ya bambanta dana kowa. Haka ne? alhaji ahmad yayi ajiyar
xuciya yace hakika likita nima na lura da hakan.

Dr rislan yace to ni dai abinda nake gani shi ne mai xai hana mu dauke axixa daga nan sashen
mu kaita bangaren da ba a yarda ‘yan dubiya su shiga ba kuma babu dan xaman jinya. Domin
‘yan dubiya da ‘yan xaman jinya suna kara creating problems a wannan rashin lafiyar tata.
Muna da ma’aikata masu kula da ita. Kai ko motsi tayi cikin dare akwai ma’aikaciya da take
xaune akan ta xata yi kararrawa likita ya xo. Haka xa a kula da tsaftar jikinta da ta makwancinta.
Cinta da shan ta da kuma uwa uba lafiyarta, ko yaya ka gani ranka ya dade?
Alhaji ahmad yace lallai haka xaifi dacewa da axixa ya xamo bata ganin kowa balle taji mugun

labari , don haka dr na baka wuka da nama, ga axixa duk wani taimako irin naku na likitoci ayi
mata rislan I trust you. Bana fargaba a aikinka no matter wat it will cost xan biya ni dai fatana
axixaa ta sami lafiya hankalinta ya kwanta, ta daina damuwa. Kuma baka ganin idan axixa taga
bata ganin kowa a cikin ‘yan uwanta da kawayenta ba xa ta shiga wani damuwa ba tayi xaton
kowa ya gujeta ne akan wannan larurar da ta same ta?

Dr rislan yace hakika xata damu idan aka ce kwata kwata babu wanda xaixo wajenta a cikin
‘yan uwanta, wasu kadan xasu iya xuwa kamar kai xaka iya xuwa a koda yaushe ka ke son
ganinta, sannan da wasu daka kula tana sansu a ranta masu hankalin da xasu kwantar mata da
hankali ba wadanda xasu kara hargitsa taba, yanxu xanso ka bani sunan irin mutanen da kake
ganin axixa xata so ta gansu don hankalinta ya kwanta. Xan rubuta sunansu na bawa security
dake gadin bangaren don idan wasu daban sun xo ta hana su shiga. Baya ga wadanda xaka
bamu sunansu babu wanda xa a bari ya ga axixa. Alhaji ahmad yace fara rubuta sunana da
abokaina alhaji sadam da alhaji bala, dr risaln ya yi ‘yar dariya ya dukar da kai yace ranka ya
dade banda ku aiku ba sai an rubuta sunan ku ba koda yaushe kuka xo xaku iya wucewa. Alhaji
ahmad yace to rubuta sunan kawayenta biyu atika sadam da munnira bala, sai kuma wata
karamar yarinya jikar hajiya lantana ce yaya ta axixa na sonta sosai sunanta Nilfa itama xa a
ringa kawo mata ita duk bayan kwana biyu.

Daga karshe kuma ka rubuta nafi’u sangali wani dan nijar ne a gidanmu yana bawa fulawa
ruwa shima mutuminta ne yana bata dariya sosai, ina ga a duk sanda na bushi iska xansa a
kawoshi ya dubata su danyi wasa da dariyarsu. Dr rislan ya rubuta sunayen da alhaji ahmad
yake xano masa. Bayan y agama rubutawa yace hakika axixa xata sami saukin tashin hankalin
da yake damunta, kuma baka ganin akwai wasu fina finai da kake ganin tafi so ta ringa gani
wanda yake sata nishadi da dariya, don xai yuwu idan aka kunna mata satilight xata iya ganin
wani film da xai yi kama da halin da take ciki hankalinta ya tashi koma tayi xaton ita ake
kwaikwayo kuma mai larura irin wannan abu kadan xa a yi sai ta tsargu ta dauka da ita ake .
don haka xamu so ta ringa kallon fina finan ban dariya wanda bai kunshi wani abu ba da xai yi
kama da halin da take ciki. Alhaji ahmad ya yi murmushi yace dr banda abinka ina marar lafiya
ina kallon kaset? Dr rislan yace alhaji xaka yi mamaki a kwana biyu kaga axixa daram a xaune
tana hira da kowa radai, domin har yanxu babu takamaiman wajen da yake yi mata ciwo a
jikinta tsabar damuwa ce da tunani ga tashin hankali shi ke damun axixa, da xarar duk
wadannan sun kau a ranta to axixa lafiyarta kalau sai dai xanso ko ta warke mu cigaba da riketa
a nan asibitin har sai ta huta sosai.

Alhaji ahmad yace babu damuwa xansa atika ta debo mata irin kasissinan data fi so a cikin
kaset dinta, amma ina ganin duk a cikin films tafi son na Ibro (Allah Ya jikansa da rahama,
amen.) don ko a hoto ta ganshi sai ta sha dariya, balle a film yana bata dariya matuka kuma
tana son film dinsa don bata ganin film din hausa sai idan da ibro, ina ganin ma idan ta
warware xan aiko da mota aje kano a dauko mata ibro ta ganshi ayi suprising dinta dashi. Dr
rislan yace kwarai kuwa xata ji dadi, amma fa alhaji nasan xaka sha fama da hajiyar da take
xaman jinyar axixa don naji tana cewa babu inda xata je ta bar axixa ita kadai wai likitoci suna
kashe mara lafiya idan ba dan xaman jinya. Alhaji ahmad ya kyalkyale da dariya yace bari naje

na sameta idan na yi mata bayani xata gane sai dai kuka ne yau xata sha rafsawa. Alhaji
ahmad ya mike tsaye yana cewa thank you so much doctor rislan ya mike da sauri don
girmamawa yace nima nagode alhaji, Allah Ya bata lafiya yayi sauri ya budewa alhaji ahmad
kofa ya fita nan da nan yaransa (bodyguard) da suke tsattsaye a bakin kofar ofishin suna jiransa
yana fitowa suka xagaye shi daya agabansa. Dukkansu suna sanye da bakar riga suit da bakin
wando, bakin takalmi da bakin gilashi. Suka nifi dakin da axixa take kwance.

Alhaji ahmad ne kadai ya shiga dukka a bakin kofa suka tsaya daya ne dai ya rakashi har ciki
da yaga ya xauna a gefen gado kusa da ‘yar sa sun fara Magana da ‘yar sa sai ya fito ya jawo
musu kofa ya rufe, cika aiki. Bayan ya gaida hajiya lantana ya tambayeta yaya mai jiki ta kwana
da jiki hajiya lantana tace jiki dai gashi nan ya lafa ya tashi abin dai sai addu’a. ta rushe da kuka
tace wadannan mutane sun cuce mu yanxu ahmadu mubarak din nan da mahaifinsa kasan
haka suke ka yadda da xaka dauki ‘yar taka kwaya daya jal ka basu mararsa mutunci? Axixa
wacce kamar a mafarki take jiyo sunan mubarak don shaker bacci take haikan. Amma jin sunan
abin da ta tsana ya farkar da ita sai hawaye ke kwaranyo mata. Ta kalli mahaifinta tace daddy
me su mubarak suka sake yi maka kuma? Alhaji ahmad ya juyo sosai ya fuskance ta yace axixa
babu abinda su mubarak suka yi min sunce ma a gaisheki.

Ta rushe da kuka tace daddy ya xa a yi suce a gaishe ni, bayan har sun kai kara kotu, na
gansu fa a kotun. Alhaji ahmad ya fuskanci a mafarki ta gansu saboda tsabar ta sa abin a ranta.
Da kyar ya bata baki da dabaru sannan ta daina xubar da hawayen dake xubowa daga
idanuwanta, ya lura da cewa hajiya lantana tana daya daga cikin masu furta maganar da take
kara tayarwa axixa hankali jikinta ya kara hargitsewa. Ba tare da alhaji ahmad yace da hajiya
lantana komai ba akan shawarar da suka yanke da dr rislan yace ta dauko kayanta su xo su
tafi. Ta tsaya xata tambaya me nene dalilin da xai ceta tafi tabar axixa ita kadai yace xasu yi
maganar a gida. Da kansa ya kinkimi Jakarta ya mikawa daya daga cikin yaransa ya rike yace
da ita hjiya yafa gyalenki ki xo mu tafi da sauri wasu manyan likitoci ne turawa daga kasar waje
xasu shigo su dubata basu so suga kowa a wajenta muje gida xan kara miki bayani yace da
axixa suna dawowa yanxun nan, suka dunguma suka fuce suka nufi wajen da suka ajiye
motocin da suka xo dasu, suka shiga suka tafi.

Axixa a kwance take tana kallonsu har suka fita suka jawo mata kofa suka rufe, ta mayar da
idonta ga kallon silin din dakin tana mai tsananin tunani akan abinda ya addabi rayuwarta, tasa
hannu ta shafa cikinta taji tauri tauri kuma har ya fara dagowa yana girma ba kamar daba ita da
cikinta yake a shamule kamar xai hade da doron bayanta, amma yanxu ya fara dan dagowa.
Taji takaici marar misaltuwa a ranta, tunanin yaya rayuwarta xata kasance nan gaba ashruf,
ashruf ta fada a ranta yayin da hawaye yayi mata kawanya tun daga idonta har bayan
kunnenta. Tace yaushe xan ganka ashruf? Ina xan ganka? Dama na ganka ashruf, ta rushe da
kuka mai tsanani yayin da xuciyarta ta sake rikicewa da wannan mugun bugun daya bambanta
dana sauran mutane. A daidai lokacin dr rislan da wasu ma’aikatan jinya su biyu (nurses) suka
sako kai cikin dakin. Axixa suka iske ita kadai cikin wannan halin yayin da suka karaso aguje
don taimaka ma xuciyarta ta sauko daga bugun da take .

Da kyar da kyar xuciyar axixa ta lafa, cikin sauri aka dorata a gadon turawa aka turata sashen
da ba a yarda kowa ya shiga dubiya ba daga marasa lafiya sai likitoci nurses da wasu ‘yan
tsirarai a cikin yan uwa. Nan ne kuma bangaren wadanda jikinsu yayi tsanani wasu ma basa
cikin hayyacinsu (intensice care unia ) don haka basa son a damesu, tsit xaka ji bangaren
kamar babu bil adama sai karar takalman likitoci da sauran ma’aikatan jinya suna takai kawo
akan mararsa lafiya. Awa ashirin da hudu likitoci suke a tsaye kan mara sa lafiya….
.
Comment da sharhi su suke kara karfin guiwar me posting comment kamar dubu Ashirin da
hudu
[9/5, 3:22 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[9/5, 3:23 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT3
*13*
.
.
Wannan ya canji wannan wancan ta canji wancan, saboda suna bukatar kulawa sosai, don
haka kudin da suke biya yafi na sauran bangarorin. Musamman bangaren da aka kai axixa,
bangare na masu kudi akan masu kudi, daban yake kawatacce a cikin likitocinma kwararrun
likitoci ne suke kula da ‘yan wadannan dakuna. Baya gad r rislan wanda yake daga cikin manya
manyan likitocin da ake ji dasu a wannan asibiti, wanda shi kadai ne bakar fata, duk sauran da
suke duba axixa turawa ne suna kula da ita fiye da kima.

A ranar da daddare alhaji ahmad da alhaji bala suka ga sabon dakin da aka kawo axixa, suna
xaune akan kujeru biyu da ked akin yayin da axixa ta ke kwance akan gado tayi lamo ana yi
mata Karin ruwa a hannunta na hagu. Idanunta sunyi luhu-luhu don kumburin kuka da bacci. Ta
rame kurket sai wani dashewa da ta yi, ta yi jajur sai kace marar jin a jiki. wayarta ce take kara
karkashin fulonta, gabanta ya yanke ya fadi ras domin karar ringing din data sakawa mubarak
ce tunda daban ta sa nasan. Tasa hannunta na dama a sanyaye tana laluben wayar,
ma’aikaciyar data ke kula da ita ta taso da sauri ta jawo mata wayar a karkashin fulo ta mika
mata ta karba ta dannan a sanyaye gami da yin shiru ba tare da t ace komi ba. tana sauraron
abinda take ji a cikin wayar.

Hallo, hallo yak eta fadi, ta yamutsa fuska t ace ina jinka yaya! Ya ce yauwa axixa ce ko, to
daman ba wani abu bane illa naji ance kin sake sumewa an kaiki asibiti shi ne xan baki shawara
da ki dinga suma a banxa ba gara ki roki daddy bay a hakura ya janye takarar nan ya barwa
daddy na, baki ganin yin haka kema samun saukin ki ne! yaya kika gani ina ganin tunda kece
kadai a wajen mahaifinki mai tsananin son abinda kike so ki shawarceshi. Mana ya bar bana mu
kuma mu kame bakinmu muyi shiru ba sai kowa yagi ba .daga karshe ina tare da sumayya
emma sabuwar masoyiyata yar gidan gwamnan legos wacce da xarar an gama hada hadar
xabe mun xama prexident xa a yi bikinmu. Su dukka wajen taji sun sheke da dariya muryar
mata da maxa ga disco na tashi a wajen da suke da alama dai a wani club din ‘yan iska suke.

Tashin hankali ya sake rufawa xuciyarta yayin da hawaye ya dinga xubowa daga idanuwanta,

kirjinta yah au dukan fat-fat bakinta yana karkarwa tana son tayi Magana ta kasa. Cafdijam yau
mbarak ne yake yabawa axixa irin wadannan bakaken maganganun haka! Hausawa sunce
duniya rawar ‘yan mata na gaba ya koma baya, axixa da don tsabar iya yaba Magana da ciwa
mutum mutunci sai nace itae misss world, amma yau ga mubarak din da ko musu baya iya yi
mata yau yana gaya mata ba dadi. Tana kokarin mayar masa da martini ta nemi Magana ta rasa
a bakinta sai karkarwa dab akin nata yakeyi. Hakika axixa babu lafiya bata data cewa sai
yadda akayi da ita, makami daya ne ya rage mata wanda xata iya amfani das hi wajen kare
kanta shi ne hawaye. Idan aka kuntata mata sai ta rushed a kuka, shi ne kadai sinadarin da
yake sanyaya mata da xuciyarta. Mahaifinta da abokin mahaifinta alhaji bala suka kula da halin
da axixa take ciki ga wayar kuma ta rike gam a kunnen ta kamar dole akace sai ta saurari
abinda mubarak yake fadi. Alhaji ahmad y ace axixa lafiya! Waye kuke waya dashi kike kuka
hankalinki kuma a tashe! Alhaji bala ya mike yaje ya fusgi wayar a hannunta ya saka a
kunnensa ba tare day a karanta ko sunan waye a jiki ba, yayi kasake yana sauraron abinda ake
fada a cikin wayar, kalma daya yaji ya fuskanci ko wanene yake Magana, mubarak isah ne
yake cewa axixa gashi yau saura kwana ashirin cif-cif a cikin kwanankin da muka debar muku
kafin mu fitar da mujallun na.

Kinga ashe kuwa da sauran lokacin da xaki shawarci mahaifinki, ya sake kyalkyalewa da dariya
y ace shawara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login