Showing 18001 words to 21000 words out of 73529 words

Chapter 7 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3606

gishirin anan ne?
su duka suka tintsire da dariya, ashruf yace bishiyar gishiri kuma daman gishiri bishiya ce? Ai a
cikin ruwa nake samu, shi gishiri ai ruwa ne ko wane taku mai girma akwai dandanon gishiri da

xaki ji ruwan ma yana yi, to idan kika debo ruwan kika yi ta dafawa har ruwan yakone, to sai ki
ga gishiri a kasan. A nan na sami gishiri da yawa muke tsakura muke cin abinci. Axixa tace to
na tuna mun yi a chemistry. Ta ce sauko mu ci. Ashruf yace ai ni tunda sassafe na karya
wannan naki ne duka kiyi ta ci. Axixa tace ni ya min yawa. Ashruf yace ki ci ki rage na rana da
na dare kuma xan gasa. Ya mike ya fice ba tare daya ce mata komai ba. shiru bai dawo ba,
harta gama cin abincinta bai dawo ba. ta fito ta leka ko ina baya nan. Sai ta shiga tunani tana
cewa ina wannan yayi kuma? Kamar aljan a ganshi kuma a rasa shi. Ta hau kan kujera ta
xauna tana waige waige ko daga ina xata ga bullowarsa? Sai can ta hangoshi da himilin itace a
kafadarsa, ta tareshi da sauri ta kama masa suka sauke. Ya yi wani gwauron numfashi gami da
ajiyar xuciya.

Ta kalle shi ta yi murmushi tace, sannu da kokari. Ashruf yace yauwa. Suka dunguma xuwa
gindin wata bishiya mai sanyi don rana ta fara takewa suka xauna. Axixa na xaune kan kujera
ashruf na xaune a kasa kan yashi nan fa suka fara taba hira. Axixa ta kalli ashruf tace ashruf ba
ni labari . Yayi murmushi yace labari yana wajenku mai girma axixa. Axixa ta lumshe ido tace
labarin rayuwarka da masoyiyarka ta kasarku. Ashruf ya tunstire da dariya harda buga kafa a
kasa, tace ai dariya ma naba ka?
Ashruf yace muguwar dariya ma, ina kika taba ganin talaka da soyayya?
Ta ce talaka baya soyayya?
Ya ce ni dai bana yi, duk inda kika ganni aike na je yi in samu na cin abinci. Ta ce wato kai ne
ina xaka? Aiki ina ka fito aiki. Ashruf yace kwarai kuwa. Ta ce yanxu ko da wasa babu wata
daka taba gani a duniya ka ji kana sonta tun farkon rayuwarka har yau?
Ya ce na taba yi kuma ban taba yi ba. ta Harare shi ta ce, me kenan kake nupi?
Ya ce ke dai ban taba yi ba. axixa ta tsuke fuska ta mike a fusace tace bari ma in bar maka
wajen nan tunda baka so muyi hira.

Ya mike da sauri ya tari gabanta yana cewa yi hakuri ki dawo ki xauna xan fada miki. Irin dan
jan lokacin nan nake kada hirar ta mu ta kare da wuri. Ya bata dariya sai ta tustire da dariya
tace, to xan dawo bari dai in sha ruwa, cikin sauri yace koma ki xauna in je in debo miki. Ta
koma ta xauna amma sai ta xauna a kasa, ta mike kafa. Tun da ga nesa yake cewa ya kika
xauna a kasa? Ya karaso ya mika mata ruwa a kwalba tace thank you, ta karba ta sha shi dai
yana tsaye a kanta, ta ce xauna akan kujerar ba komai na fi son xaman kasar. Bayan ya xauna
ta kalleshi ta yi musrmushi tace na fa gode.
Ashruf yace ni fa bana son yawan godiarnan da kike yi min ai aiki nane. Can dan da aka jima
ba tare da kowa ya cewa kowa komai ba, axixa ta nisa tace nikuwa ashruf ina da tambaya ko xa
ka bani amsa? ashruf ya tsareta da wadannan kwaxa-kwaxan idanuwansa yace, me xai hana in
baki amsa uwargidana axixa. Ta yi dan murmushi ta sunkuyar da kai kasa tana dan xane-xane
da tsinke a kasa ta dago tace ashruf wai don Allah me ya sa mutum yake jin ya tsani mutum
ne?
ahsruf yace ban gane tambayar ba. axixa tace xaka ga wani lokaci idan xama ko tafiya ta hada
ku da wani mutum sai ka ga jinin ku bai hadu dashi ba, kawai ka tsaneshi shima ya tsane ka.
Ashruf yace ba yadda xa a yi mutum ya tsani mutum haka kawai sai dai idan da dalili, kin ga na
farko watakila daya yana yiwa dayan mummunan hali yana uxxura masa baya kyautata masa

don haka sai tsana ta shigo.

Ta yi shiru tana dan tunani can ta nisa tace haka ne, to me kuma yake sawa, daga baya mutum
ya ji yana son mutumin daya tsana?
Ashruf yace kyautatawa ce kuma take sa soyayya. Ta ce mu a can kasar mu a yarenmu na
hausa, hausawa suna cewa kiyayya bata xama soyayya, wai babu yadda xa a yi kana kin
mutum daga baya kuma ka xo ka ce kana sonsa. Ashruf yace in dai hausawa ne ba haka suka
ce ba, hausawa sun ce soyayya bata xama kiyayya sai dai kiyayya ta xamo soyayya. Axixa ta
xaxxaro ido tace ashruf ina ka san hausawa balle ka san me suka ce?
Ashruf yace kika sani ko ni bahaushe ne?
tace babu abinda ya hada ka da hausa ko xo baka sani ba. ashruf yayi ‘yar siririyar dariya yace
axixa kenan, ba don in kin yi yaranki na hausa ba bakinki ciwo yake da daga yau mun daina
Magana da turanci da hausa xamu dinga yi. Ta ce waye yace maka haka?
Ya ce axixa ce ta ke fadawa Mubarak daya ce ku dinga yarenku kar mu ji in xaku yi maganarmu
kika ce ba xa ki bata bakinki ba, keda turanci kika saba Magana dashi xa ki ci gaba. Ta yi shiru
ta sunkuyar da kai kasa tace, wannan ya wuce. Ya kalleta yace tun daxu kike tambaya ta
labarina, me ya sa kike so ki ji labarina ne? tace haka kawai ashruf ba don komai ba sai don mutumin da kake tare dashi xaka so ka san ko
shi wa nene. Ko ba haka ba? ashruf ya nisa ya yi musrmushi ya kalleta, kallo ido da ido yace
kina so ki ji labari na ko? To xa ki sha labari yanxu kuwa amma fa sai kin yi hakuri saboda
labarina yana cike da abin ban tausayi mai tsanani don duk rashin imanin mutum ya ji labarin
nan xai tausaya min, ba kuma kullum nake so in dinga tuna abinda suka faru baya ba, saboda
bacin rai.
Axixa ta dafe kirji tace ashruf iyayenka ne suka rasu?
Ya ce ina da uwa ina da uba duk suna nan . axixa tace na dauka ma sun rasu ne tun kana
karami. Ya ce ai ba sai yaro ya rasa mahaifansa bane maraya ko marar gata ke dai gyara xama
ki sha labari ashruf ya kaikaice cikin harshen hausa wanda axixa ta ji kamar a mafarki yana ta
kwaranyo yaran hausa kamar jakin kano. Don tun haduwarta dashi ko xo bai taba fada da
hausa ba sai gashi yau hausa harda Karin Magana.

LABARIN ASHRUF
Ya ce sunana Ashruf El-mustapha (ja) sunan mahaifina ne el mustapa(ja) saboda mahaifina fari
ne tas shi yasa ake kiransa ja, mahaifiyata kuwa sunanta Fatima. Allah Ya yiwa mahaifina arxiki
tun yana matashi bai yi auren fari ba, ya gada a wajen mahaifinsa ne. wanda ya rasu ya bar shi
shi kadai, kasancewarsa kwararren dan kasuwa mai ilimi yakan je kasashe daban-daban domin
kasuwancinsa kamar kasar larabawa, turawa har ma da china. Wata rana ya baro garin
mahaifarsa wato jahar katsina, wani garine a Nigeria shi dan asalin babban birnin garin ne, ya
tafi Libya don wasu harkokinsa sai ya hadu da Fatima wato mahaifiyata tana yarinya matashiya
bata wuce shekaru goma sha hudu ba. ya nuna yana sonta, to kasancewarsa bakar fata dan
wata kasa sai suka hanashi aurenta da kyar dai da Allah Ya yi matarsa ce ya aure ta abin ya
xama abin surutu. Balarabiya ta auri bakar fata . ya taho da ita Nigeria gida duk danginsa suka
ganta bayan xuwansu Nigeria da kamar wata bakwai mahaifina ya ga dai kasuwancinsa ya fi ci
a kasar turawa wato America, ga mahassada sundame shi, sai yakaura shi da amaryar sa xuwa

America , gaba daya da xama a babban birnin wato Washington, a nan ne Allah Y basu
haihuwa suka haifi xubaida yayata kenan bayan an haifeta, da shekaru uku sai aka haife ni. Mu
biyu muka taso a gaban iyayen mu masu matukar son junansu, xaman lafiya da kwanciyar
hankali ga wadata an yi mana tarbiyya a bisa shari’ar musulunci, an kuma ba mu ilimin islama
da na boko, tun muna ‘yan kanana kuma komai uba yake sayowa ‘ya’yansa na jin dadin yaro
duk mahaifinmu ya dau nauyin komai kika sani.

In muka gani muke so na ci ko na sawa, ko na wasan yaro mahaifinmu da mahaifiyarmu xasu
bamu. Wata rana da yamma muna xaxxaune a farfajiyar gidan ni da yaya xubaida muna hawa
keke, momi kuma tana xaune akan wata kujera tana karanta Alkur’ani sai ga daddy mu ya
dawo, muka tafi da gudu muka taryeshi a bakin motarsa, direban sa ma ya fito daga motar sai
muka ga wani mutum shima ya fito daga motar bakikirin dashi gajere mai jajayen idanu don
lokacin shekarata bakwai, ina kallon horror film, amma saida mutumin nan ya bani tsoro, muka
kankame daddy muna jin tsoron wannan bakon. Dady y ace mu daina jin tsoronsa sabon direba
ne aka kawo masa ofis daxu, dan uwansa ne dan Nigeria, saboda shi taufik tsohon direban sa
tafiya xai yi kasarsu dan Malaysia ne, shi ne aka samo masa wannan xai dinga kai mu
makaranta da sauran aike-aiken gida. A matsayin mahaifiyarmu mai tsananin addini da gudun
xargin mutum akan abin da bai yi ba saida ta ji wannan bakin direban bai kwanta mata ba ta ce
a sallameshi kawai bata sonsa. Amma dadynmu yace siffarsa ce a haka bashi da fara’a, amma
yana da hankali.

Kuma yana bukatar a taimaka masa kasancewar bako a wannan kasa, bai san kowa ba, bashi
da komai, tunda ya iya tuki mu ringa nuna masa gari a hankali xai san ko ina. Aka bar shi a
gidanmu aka bashi dakinsa a boys quarters yake xaune, yace sunansa yakubu(takaka) don
haka takaka muke ce masa musamman daddy ya iya kiran takaka kamar shi ya rada masa
sunan. Muna nan da takaka yana tukamu sai muka ga ashe mutum ne mai kirkin gaske yana da
hankali don haka har cikin gida dady yake kiransa, ya bashi kudi su kirga tare ya kai masa
banki, duk huldodin kasuwancinsa yana aiken takaka ko ina da takardunsa da komai, takaka ya
san kansu.

Bayan xuwan takaka da shekaru biyu, wata rana daddy yace tunda mun yi hutu mu xo muje
wani gari da ake kira texas anan America ne mu xuyarci abokinsa. Wani bature, suna yawan
xuwa gidanmu shi da iyalansa mu ba ma xuwa. Muka gama shirinmu tsaf da sassafe muka fita
muka nufi gari a can muka yini bamu bar taxas ba saida la’asar likis don haka har dare ya fara
yi mana a hanya kamar magariba haka muna tafiya sai muka ga takaka ya tafi gefen hanya
sosai yana dan shiga daji daidai da wani katon rami ya tsaya, ya kashe mota abu ya bawa
daddy mamaki, yana xaune a gaban motar, yana karatun jarida, sai ya ajiye jaridar yace da
takaka lafiya ka xo nan bakin rami ka tsaya?
Takaka yace fitsari ne yayi bala’in matsa ta. Daddy yace ai kanka tsaya xaka gaya mana ba
kawai ina karatu ba kan in dago in ga ka xo nan ka tsaya ban da abinka kuma tsayawa ko daga
can gefen titi ne ma ai ya isa a tsaya ba sai ka xo nan daf da rami ba ka tsaya. Ka je ka yi da
sauri ka xo mu tafi.

Takaka ya fia yana dan xuge-xugen taxuge sai muka ga yana fitowa yana kallon wani gefe.
Ashe ya hada baki ne da wani mai tirela idan ya ga fitarsa ya taho da gudu ya daki motarmu
mu gangara shi kenan mu mutu, can gida kuma ashe ya gama kammala takardun daddy na
kudaden sa da kamfanoninsa da yake da hannun jari takardun gidaje da motoci duk ya kwashe
idan ya kashe mu sai ya kwashe kudi ya gudu. Ai kuwa hakan aka yi da mai tirela ya hankada
motarmu cikin wannan gundumemen ramin mai girman gaske, ga xurfi. Suka yi tafiyar su, gashi
dare ne babu wanda ya ganmu. Ashruf ya sharbe hawaye ya ci gaba da cewa a haka muka
kasance har gari yawaye wasu sun cika a cikinmu wasu sun jirkinta.
Axixa ta goge hawayen dake xubo mata tace, waye ya rasu a cikin ku?
Ashruf yace ‘yar uwata yayata xubaida ko motsawa bata yi ba motar ta danne mata wuya yayi
kwatsa=-kwatsa mahaifiyata kuwa wurgi aka yi da ita gefe ta buga kanta da wani dutse ta yi
doguwar suma da a sati ma bata farka ba, dady kuwa a lokacin kafarsa ta hagu ta fincike ita
daban shi daban. Axixa ta rafsa salati tana fadin wannan rashin imani da yawa yake. Waye ya
fito daku?
Ya ce kwananmu biyu anan sai ga ‘yan wata jami’a ‘yan geography masu bincike binciken
yanayin kasa, Allah Ya kawo su nan, to a nan fa suka ganmu cikin wannan mawuyacin hali, ni
kadai ne ido na biyu ko kwarxane ban yi ba, ina ta xagaya su ina tattabasu shiru, daddy ne ma
ya farfado idan na kira sunansa yakan amsa amma yaya xubaida da mommy ko motsi basa yi.
Nan da nan suka kwashe mu sai asibitin wani kauye don mun yi nisa da garin da muka je. Mun
kuma yi nisa da Washington . aka bawa mommy gado ita da daddy don an aunata tana da rai,
yaya xubaida kuwa harta fara kumbura ta rasu kin san turawa basu binneta ba sun dai saka
mata chemicals don ta daina warin har sai iyayenmu sun farfado sun ga gawar ‘yar su sannan a
binne ta.

Ni dai lafiyata kalau daya daga cikin likitocin ya dauke ni ya kaini gidansa, muna xuwa asibitin
in ga iyayena mu koma har dai daddy ya farfado sosai ana hira dashi. Mommy kuwa ta farfado
amma bata Magana sai kallo, wai ashe kwakwalwarta ta tabu, sun yi sun yi ina babu yadda xa a
yi ta yi hankali. Daddy kuwa sai keken guragu aka bashi, babu kafa daya ta cuxge. Daga karshe
bayan daddy ya ga gawar yaya xubaida sai ya yi mata addu’a yace su binne ta.

Momy kuwa sai kallon gawar take batace komai ba aka binne yaya xubaida. Bayan asibiti sun
gama damu suka fara tambayar daddy yaya?
Me ya faru?
Ya ce shi dai ya san ya taho texas shi da direbansa da iyalansa, sai direban ya xo ya tsaya a
daidai wajen da aka ganmu yace xai yi fitsari, to bayan ya fita ne sai muka ji yayi fito ni dai ban
juya ba saida na hango wata katuwar tirela ta nufomu a guje bamu Ankara ba sai ji muka yi
anan ta kulikulin kubura damu har haka ta faru.
Duk suka tausaya mana kuma kowa ma yana xargin babu tantama da hadin bakin direba
takaka wajen faruwar wannan al’amarin, gashi sama da satinmu uku a asibiti bamu ganshi ba.
nan dai suka kwashemu muka nufi gidanmu, abin mamaki takaka ya hada komai ya sayar hatta
gidanmu ya sayarwa wani dan uwansa dan damfara wani bature, ya ringa dauko lauyoyi da
shaidun cewa gidansa ne ya saya ga takardun gidan. Kudi a banki babu, kamfanoni babu,

takardu gashi a lokacin kai be waye ba babu dokoki da ake bi a kwatarwa mai gaskiya hakkinsa
musamman bakar fata a can bamu da hujjar da xamu ce kayanmu ne ko ba mu muka sayar ba,
kiri kiri komai namu ya gagare mu. Daga karshe wani makwabcinmu ne dan kasar jamaika shi
ya taimaka mana da muhalli, ya kuma je wajen manyan gwamnati ya fadi halin da muke ciki,
ake taimaka wa mommy da magani da take sha take samun barci, don barcin ne saukinta idan
bata sha maganin ba babu barci sai ta yi ta kuka tana kiran yaya xubaida ko takaka tana
kokarin ta fita da gudu amma idan tasha maganin lafiyar ta lau sai dai babu Magana sai kallo.

Muna nan dai a gidan bawan Allah nan dan jamaika mai suna david ba musulmi bane ina xuwa
makaranta duk da dai ba tamu tada bace mai tsada ta yaku bayi ce. Ina aji biyar na firamare
david da iyalansa suka fara shirye shiryen komawa kasarsu jamaika kasancewar ya yi ritaya,
hankalinmu yayi mummunan tashi saboda babu inda xamu je mu ci abinci mu kuma xauna. Don
a lokacin ma gwamnati ta daina biyawa mahaifiyata kudin magani shi David din ne yake saya
mata. Uncle david ya bawa mahaifina shawarar ya koma kasarsu mana sai mahaifina yace ba
xai iya komawa Nigeria ba don xai wulakanta ya toxarta fiye da yadda yake a nan, yace shi
daman mahaifansa sun rasu bashi da wa babu kani ko kanwa sai ‘yan uwan uwa da uba. Ya ce
hassada da bakin cikin da suke nuna masa shine ummul aba’isin barinsa garin.

Ya ce yanxu daya xama haka idan ya je dariya xasu yi masa ba xa kuma su taimaka mana ba
karshen ta mu yi bara, mahaifiyata kuwa da wannan ciwon nata karshe sai dai ta baxama dawa
tunda babu maganin da take samu tana sha. Ya ce can libiya kuwa idan ta koma shi ma babu
mai kula da ita don daman mahaifiyarta ta rasu tuntuni, mahaifinta ma ya rasu tana cikin jinyar
nan bata da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login