Showing 33001 words to 36000 words out of 73529 words

Chapter 12 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3597

falon
don yin alwalar magaruba, tana shiga ta ji an banko kofar bandaki da karfi sai ga axixa a guje ta
xo tana kwararo amai. Hanakalin atika ya tashi tana rike da ita amai sai xubowa yake har
‘ya’yan hanjinta motsawa suke, ta kyala amai, amai mai yawa, sannan atika ta bata ruwa ta
kuskure bakinta ta wanke fuskarta. Atika na rike da ita xuwa kan kujera ta kwantar da ita. Ta
koma bandaki, tayi alwala ta fito, ta fara sallah kenan ta ji axixa ta sake shiga bandaki a guje
tana kwarara amai. Babu yadda xata yi salla take. Tana idarwa ba tare da ta tsaya yin addu’ar
kirki ba ta tashi da gudu ta bi axixa bandaki. Ta iske ta a kwance a kasa tana kwararo amai
daga kwance. Atika ta hau kwakwaxo tana hawaye tana na shiga uku axixa kar ki mace mun
daga ni sai ke!

Ta dagota da kyar ta wanke mata fuska da baki ta sakalo kafadarta suka fito, bayan ta kwantar
da ita ta shiga cikin gida da sauri ta leka ko ina babu kowa. Ta shiga kicin sai ta iske ‘yan aiki
mata da kuma kuku su uku maxa. Ta ce idan daddy ya xo ku ce na tafi da axixa asibiti bata da
lafiya. Cikin rudani suka ce me ya same ta? Suma ma’aikatan gidan sun ga canji a wajen axixa
saboda yanxu tana kyautata musu babu abinda bata basu. Babu fada da kyara da kyama irinta
da, wasa da dariya ce a tsakanin su. Kuma duk sati tun dawowarta take musu rabon kudi duk
juma’a mai yawa kuwa wani lokaci har suturunta take bawa matan. Don haka suma tsanar da
suka yi mata da sun daina, har basa so ta fita, amma da addu’a suke ta yi tayi tafiya su huta.
Suka biyo atika yuu, har wajen axixa, suna ta yi mata sannu. Daya daga cikin masu aiki mai
suna amina tace an yiwa daddy waya ba a same shi ba?
atika tace af ni na rude ma na manta da wata aba waya. Ta dauko handset dinta ta buga ta ci

sa’a tana ringing kash amma ba a dauka ba, ta sake redialing tana ringing ba a dauka ba. ta ce
ba a dauka ba ina jin ya barta a mota ya shiga filin jirgi kin san sun tafi raka su mr henrry filin
jirgi xasu juya London yanxu tace da guda biyu daga cikin matan masu aiki ku tayani mu sata a
mota mu tafi asibiti da ita. Comment da sharhi su suke kara kwarin guiwa nayimuku posting inba
Comment to sai bayan kwana ashirin da hudu
[9/1, 6:17 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[9/3, 7:34 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT2
*11*
.
.
Ku tayani mu sata a mota mu tafi asibiti na nemi daddy a waya idan kuma ya xo gida ku gaya
masa mun tafi international hospital. Amina da Rebecca ne suka tallafo axixa xuwa bakin mota,
atika ta hau sama dakin axixa da gudu ta dauko dan karamin katin ganin likita. Ta fito ta iskesu
a bakin mota nan ma wani sabon amai axixa ta kyelaya. Bayan an goge mata bakinta da
fuskarta don hawaye ne keta xuba kiran Allah! Allah!! take sai daddynta kuma suka sakata a
bayan mota ta kwanta. Atika tace amina ta xo su je dan ita babbace. Rebecce kuma ta je ta
gyara duk inda ta yi amai. Sai international hospital. Basu wani bata lokaci ba suka wuce da ita
wajen likitanta, mai suna dr Rislan. Idan axixa ta je ko mutane nawa ne ke jiran ganinsa xai bar
su ya dubata tukunna, yana ganin axixa cikin wannan hali ya mike da sauri yace da matar daya
ke dubawa ta yi hakuri ta jira shi a waje ya gama da axixa tukunna. Bayan sun dorata kan
gadon duba marasa lafiya sai likita ya shiga yiwa atika tambayoyi wata ta amsa in ta sani wata
kuma axixa ta amsa da kyar.

Ya ce da atika xai so ya auna fitsarinta yanxu don ya ga me ke damunta takmaimai, ya basu
kwalba da bandaki a afishin atika na rike da ita suka shiga, ta yi fitsarin. Ta kawo masa, ya kira
daya daga cikin ma’aikatan asibitin yace maxa ta kai laboratory na asibitin yanxu a auna fitsarin
nan a kawo sakamako. Axixa kwance take cikinta na murda mata tace xata yi amai a kawo wata
wata roba ta kasa, ta sake cewa ga amai nan a matso da robar ta kasa don duk abinda ta ci ta
gama amayrwa babu komai a cikinta. Likita nata gwaje-gwajensa yana ‘yan tambayoyi ya matsa
cikinta yace da xafi?
Inda xafi tace eh, idan babu tace babu atika da amina mai aiki suna waje kan benci. Atika nata
gwargwada wayar daddyn axixa. Sai can ta ji an dauka bayan sun gaisa taji muryar bata daddy
bace tace, da wa nake Magana? Ya ce ni ne habu direban alhaji isah. Atika tace ina alhaji
ahmad din? Ya ce shi da alhaji isa tun daxu suka shiga cikin filin jirgi basu fito ba xasu ga tashin
wasu baki. Atika tace to idan sun fito ka ce atika kawar axixa ta kira cewar axixa bata da lafiya
muna international hospital.

Ya ce to Allah Ya sauwake. Tana cikin wayar ne taga nurse din da fitsarin da xa a auna taxo ta
wuce. Sai ta tashi ta bita ciki. Bayan ta bawa likita ta fita, sai likita ya bude sakamakon gwajin
ya duba ya koma ya xauna a sanyaye ya sake ya duba rasitin ya kuma duba takardar
sakamakon. Atika ta xo ta xauna a kujerar dake gaban teburin likitan tace. Dr rislan lafiya?

Me nene yake damun ta?
dr rislan ya dago ya kalli atika yace yaushe aka yi bikin axixa?
Atika tace saura wata goma ba a yi ba ma. Ya ce an daura aure?
Atika tace a’a ba a daura ba wani abu ne?

Dr rislan yace sakamako ya nuna axixa tana da juna biyu na wata uku. Yana rufe bakinsa axixa
na rikito daga kan gado ta mike ta dora hannu aka ta kwalla kara. Atika da dr rislan suka riketa.
Babu abinda axixa take gani sai jujjuyawar komai kafafunsa ya koma sama. Can ta sankare ta
mike ido ya kame mata numfashi ya tafi. Wa’iyyaxu biLllahi, atika ta fasa ihu kira take likita
dubata xata mutu. dr rislan ya danna kararawa, kan ka ce kwabo ofshin dr rislan ya cika da
kwararrun likitoci, a cikin masu shigowa kuwa harda alhaji ahmad da alhaji isa da alhaji sadam,
wato mahaifin atika sun shigo kenan suka ga likitoci a guje suma suka bisu, alhaji ahmad ya ga
tashin hankalin da bai taba gani ba ‘yarsa axixa ce a mimmike a sankare ido a kafe akan gado
an turata an yi dakin nemo numfashi da ita.

Rislan dasu alhaji isa sai hakuri suke bashi suna bashi Magana cewar bata mutu ba cuta kuma
ba mutuwa bace. Atika sharkab ta yi ta yi daidai tana rusar kuka. Amina na rirriketa, dr rislan
yace su shiga ofishinsa su xauna xai je ya ga halin da axixa take ciki. Bayan xamansu da kamar
awa daya da rabi, kowa yayi shiru yana karanto addu’ar da ta xo bakinsa, bude kofar dr rislan
ce tasa kowa ya dago, alhaji ahmad yayi xumbur ya mike yana tambayar likita yaya?
Dr rislan ya sa hankici ya goge gumin goshinsa yayi murmushi yace da alhaji ahmad ya xauna
yace ka kawantar da hankalinka axixa ta bude ido har tace ina daddy. Su duka suka ce
Alhamdulillah. Dr rislan ya xagaya kujerarsa ya xauna. Alhaji isa el yakub ya jawo kujerarsa
gaban teburin likita yace wai takamaimai me ke damun ‘yar mu? Likita ya ciro takardun da ya yi rubuce rubucen bayanan da axixa ta yi masa da kuma takardar
sakamakon gwajin da aka yi mata yace a bayanan da ta yi mana na abinda yake damunta ba
mu tabbatar da takmaimai abinda ke damunta ba saida muka yi mata gwaji na fitsari. To
sakamako ya nuna ‘yarku tana dauke da juna biyu na wata uku. Su duka suka hada baki CIKI!!!
Likita yace ciki to saboda girgixar da ta yi da bacin rai shine ya sa ta fita hayyacinta ta fadi a
sume.

Kuma bacin rai ya so ya yi mata yawa daman tana yawan tunani kuma ba a so yayi mata yawa
da juna biyu da yawan tunani don haka kar a sake a yi mata wata maganar da xata bata mata
rai, ko kuma a nuna mata ciki wani abu ne na tashin hankali, ku yi kokarin kwantar mata da
hankali gami da yi mata fatan Allah Ya sauketa lafiya. Don yanxu saura kiris hawan jini ya
kamata, kuma ban da Allah Ya kiyaye da cikin ya xube, amma yanxu ita lafiya abinda ke cikinta
ma lafiya. Alhaji isah el yakub ya sa hannu ya dakatar da likita yace kai rislan ya isa dan Allah
ka bar mu mu ji da abinda ke damunmu da wannan bayane bayane naka na banxa, wai ba dan
Allah Ya kiyaye ba da cikin ya xube, ya xube mana dan uban cikin cewa muka yi muna so, yara
sun ja mana abin kunya a wajen adawa, daman kiris ake jira.

Alhaji ahmad kuwa tunda ya rike kai ya sunkuyar da kai kasa bai sake cewa komai ba sai xufa
ke keto masa duk da fankar ofishin alhaji sadam kuwa babu wacce yake harara sai ‘yar sa atika

cewa yake saura ke duk sai an gwadaku dan ubanku. Daman nima hankalina bai kwanta da
barin ‘ya’ya mata ba balagaggu su tafi wasu kasashe da gardawan samari ace ba xa a yi
masha’a ba, xamani dai an ce haka ake yayi rayuwar hutu. Yanxu ina hutun yake?
Hutu ko tashin hankali, likita nata basu Magana yana basu hakuri, yace in kuna son ganinta
tana can wani daki nurse a waje ta rakaku don mun bata gado xamu ci gaba da kula da lafiyarta
sai ta huta sosai kar hayaniya ta sake saka mata wata damuwar a sanyaye suka fita wata
nurse ce ta rakasu dakin da axixa take kwance ana kara mata ruwa, suka yi mata sannu, ta
amsa da kyar, alhaji ahmad dai kallon ‘yarsa yake samun lafiyarta shi ne burinsa, cikin ma ya
dameshi amma ya san kome ya samu bawa kaddara ce daga Allah ya san ‘yarsa ya san halinta
shedan yana tare da kowa amma mutum ya xamanto koda yaushe yana fada da xuciyarsa a
duk lokacinda take kunsa masa sharri.

Bayan sun yi kamar minti goma sha biyar da shiga sai suka ce xasu tafi. Alhaji ahmad yace xai
aika a dauko yayarsa hajiya lantana dake kado estate gidan daya saya mata ita da ‘ya’yanta da
jikokinta, atika ta yi sauri tace daddy xan xauna da ita abar hajiya lantana ni da amina mai aiki
muka xo mun isa mu xauna da ita. Alhaji ahmad yace to madalla shi kenan. Haka suka shiga
motocinsu sanyi kalau babu mai Magana har unguwar life camp gidan alhaji ahmad suka shiga
kayataccen falon da yake xama da bakinsa. Tsawon minti ashirin babu wanda yace wani abu.
Alhaji isa el yakub ya nisa yace wai alhaji ahmad me nene abin yi? Na ji ka yi shiru sai ni da
alhaji sadam muke ta babatu. Alhaji ahmad yace alhaji isah mai xan ce da kaddarar Ubangiji?
Kaddara mai kyau da marar kyau ta sami musulmi sai ya runguma. Daman ‘da ko ‘ya amana ce
Allah (SWT) Yake bawa bayinsa kuma ranar gobe kiyama mutum yayi bayanin wacce irin
tarbiyya ya bawa dan da aka bashi, musamman ‘ya mace sai an sa ido amma saboda
al’adunmu sun yi baya, ba ma amfani da abinda Manxo (SAW) yace idan yarinya ta shekara
goma sha biyu a aurar da ita, mun dauki al’adun turawa yara suna da ‘yanci su yi abinda suka
ga dama ba a tsawatar musu, gashi nan yan ce ranar da nake dana sanin barin axixa ta kawo
xuwa yanxu ban aurar da ita ba, na dauka tana daukar gargadin da na ke yi mata. Inna liLlahi
wa’inna ilaihi raji’un. Alhaji isa yace har yanxu ban ji mafita ba alhaji ahmad yaya xamu yi da
cikin nan da dana ya yiwa ‘yarka?

Alhaji sadam yayi gyaran murya yace alhaji isa ai gaggawa daga shedan take ka bari a yi
naxari sosai sannan a fara xancen mafita, babu laifin axixa babu laifin mubarak, laifin ya fi a
garemu. Alhaji isa yace babu wani laifin,mu dan mun amince su fita su huta mun ce su siyo
ciki? Ai babu ja, dan iskan namiji sai ‘yar iskar mace. Don ni na san na yiwa dana tarbiyya. Dukkansu
suka bude baki don mamakin kalaman da suka fito daga bakin alhaji isa el yakub, kamar a
mafarki. Ya tashi ya kade rigarsa ya sa kai xai fice har ya kai bakin kofar fita ya juyo yace
wannan cikin a xubar idan bahaka ba xance babu ruwan ‘dana. Alhaji sadam y ace don ka san
cikin ba a jikin danka yakeba ko? A xo cirewa ta mutu ba asararka bace ai.
Ya ce oho ku kuka sani. Ya kada kai ya fice abinsa. Tashin hankali ya tabbata a xuciyar alhaji
ahmad a daren yau ji yake dama ba a halicce shi ba, baya kunyar me mutane xasu ce masa
kamar alhaji isa shi ‘yan adawa yake tunani.

Shi tsayuwa a gaban Ubangijinsa shi ya fi damunsa. Nan dai alhaji sadam yayi ta bashi baki
akan ya yi hakuri ya cire tunani ya kuma toshe kunnansa akan abinda alhaji isah xai ce
kasancewar sun sanshi butulu ne. daga karshe alhaji sadam yayi masa sallama yace saida
safe, ya tafi. Alhaji ahmad ya kasance ya kwanan a xaune yana tunani, yana kuma addu’o’I
Allah Ya rufa musu asiri Ya kiyaye gaba. A asibiti kuwa kwanan su atika suka yi basu runtsa ba,
axixa na ta faman fixge ruwan da ake kara mata wai sai ta fita ta bar kasar an rasa ta don abin
kunya xai xamewa mahaifinta, likitoci na rikota atika na yi da kyar dai aka yi mata allurer barci ta
samu ta yi barci sannan wajen asuba suma su atika suka samu suka kwanta hakarkarinsu saida
su axixa suka kwana biyu a asibiti sannan mubarak ya xo dubata shi da abokansa ibarahim da
sadik.

Bayan sun yi mata sannu sun ajiye kayan dubiya sun xaxxauna akan kujerun dake dakin, sai
atika tace mubarak kwana biyu ba mu ganka ba ko ka yi tafiya ne? ya yatsune fuska ya tabe
baki y ace no! ina nan a gari xuwan ne dai kawai ban xo ba. axixa ta ji gabanta ya fadi ras, tace
a ranta yau mubarak ne yake mun irin wannan yatsunar kamar Kashi? Ta ce to ni dai sai yadda Allah Ya yi dani. Suka mike suka ce xasu tafi mubarak ya xaro bandir
din ‘yan dari biyar biyar ya jefawa axixa kan gado yace gashi a siyawa baby kayan kara lafiya
tunda ku masu ciki ana so ku ringa cin kayan kara lafiya. Hawaye ne ke xuba daga idanuwan
axixa kawai , ta kasa Magana, atika ta fusata ta dauki kudin daya jehowa axixa ta biyoshi don a
lokacin har sun fita daga dakin ta seta keyarsa ta buga masa bandir din kudin tace mubarak
karya kake ka yiwa axixa irin wannan wulakancin kafin ka rike dubu hamsin axixa ta rike dubu
dari, to ko a kotu xa ka yi bayani don axixa bata da wani saurayi daya wuce ka dan iska kawai.
Ya kufula ya kawo mata mari abokansa suka rike shi, suka ja shi suka tafi.

Axixa na bakin kofar dakin tana kallonsu ta rushe da kuka. Nan atika ta tsaya tana lallashinta
muryar mahaifin axixa ce yace lafiya kuka fito?
Axixa ta tafi da sauri ta rungume babanta tana rusar kuka, alhaji ahmad yace ya isa mu shiga
daki. Bayan sun shiga daki ne yake tambayarta me yake faruwa. Atika ta xayyane masa duk
yadda suka yi da mubarak. Alhaji ahmad take ya ji wani daci ya cika makoshinsa don takaici.
Amma sai ya nuna musu su kwantar da hankalinsu wannan ba komai bane. Kwanan axixa
takwas a asibiti aka sallame ta. Ranar da aka sallameta ne da daddare axixa atika da munnira
suna wani falon da yake daga cikin gidan suna kallon wani American film mai suna SPECIES
suna ta kokarin kwantar mata da hankali su bata wannan labari na abin dariya tana dan
daurewa tana yi amma ba har xuci ba don xuciyarta cike take da takaici. Babanta kuma alhaji
ahmad yana falo tare da wasu ‘yan uwansa da suka xo duba lafiyar axixa daga yobe, garinsu
alhaji sadam da alhaji bala suma duk suna tare a falon ana ta hira ana kora lemo. Sai ga alhaji
isa el yakub da dansa mubarak da tawagarsa babu sallama babu kwankwasa kofa sun fado
musu falo budik! Kowa ya juyo yana kallonsu, alhaji sadam yace haba alhaji isah kai jahilin ina
ne? haka babu sallama ka fadowa mutane gida.

Alhaji isa yace sallamar me xan yi a gidan da ake aikata masha’a, ba abinda ya kawo ni bane,
ni abinda ya kawo ni shi ne in fada anan ko kuwa xa a matsa a bamu waje mu kebe dan sirri ne
amma alhaji sadam da alhaji bala ku xaku iya xama danku xama shaidu. Alhaji ahmad yace ko

me ka xo ka fada ka fada ka fita ka bamu waje. Alhaji isa yace niba xai shafe niba kai xai shafa
koma a gaban mutanen na fada amma adalcin da xan yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login