Showing 45001 words to 48000 words out of 73529 words
Chapter 16 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf
Unknown
29 Jun 2025
3587
Atika ta ci gaba da cewa sai nan da nan
ya canja haushi ya kamashi yayi wani farat ya mike daga kan kujera daman a farfajiyar nicon
hlton muka hadu wajen ‘yan runfofin nan na hutawa yace haka kika ce ko? To naji daga yau na
janye soyayyar nima da nake yi miki kije da axixa ni xanje da mubarak mu xuba. Ko kallonsa
banyi bana yi watsi dashi na kau da kai ina wakar Jennifer lopex ta “if you have my love”.
Munnira ta mika mata hannu suka kashe tace atika kin burgeni, kina kan burgeni kuma ai nima
munyi haka da Ibrahim jiya jiyan nan ina jin mubarak ne ya turosu wato so yake ya xugesu su
rabu da mu dan shi sun rabu da axixa.
Kin san tsoransa suke juya su yake kamar waina, kamar yadda ubansa yake juya iyayensu
suma, ai gara keda sadik da soyayyar har yana miki xancen aure ke kika ki. Ni kuwa fada nake
fada da uwarsa ina xancen ta bari ya aure ni, atika ta juyo tana mata kallon mamaki gami da
bude bakin mamaki. Munnira tace wallahi fada ni da uwarsa sosai harda yaba Magana, na
tsaya nayi mata tatas dan nasan na rabu da Ibrahim nagama, tun kafin haka ta faru tsakanin
axixa da mubarak. Atika tace ban labari a dai dai lokacin ne suka karaso get din shiga babban
asibitin wato international hospital yayin da masu gadi suka bude musu get suka shige ciki.
Munnira tace a ranar birthday party daddyn axixa muka hadu da ita, kinsan ta je ita da
kawayenta en duniyar nan su hajiya rabi , na xo wucewa ina nemanku sai naji ance gata nan ,
itace munnira, na juyo da sauri don naga magulmata. Sai naga suruka tace naje da ‘yar kunyar
nan na duka na gaishe su, ke kinga dakyar suka amsa har maman Ibrahim dinfa sai daya daga
cikinsu tace surukan xamani ko durkusawa sosai ba a yi, sai maman Ibrahim din tace ina xan
yadda daman na kai dana wajen masu soyayyan ido kesashshe ai sai a xamar min dashi bawa,
wata motsatstsiya a ciki da wani bakin lebenta sai tace ko kai a raba ki da shi kwatakwata an ga
naira.
Raina yabaci, da har xan wuce na yi shiru sai nace kai bari na gyara musu daurin dan kwalin
kansu naga duk a karkace suka yi shi na juyo nace, Allah Sarki masu da, idan ma yace xan
aureshi to karya yake yi, don ibarahim bashi da abinda xan iya aurensa sai dai ma cane shi ne
xai kwasa ya kaiwa uwarsa, dan ‘yan kano to jidda masu bakin lebe ragowar taba. Kowa gaba
yake so ya ci, ba baya ba. napi ibarhim kudi sai dai na nemi wanda ya fini sai duk suka rike baki
wasu na salati, daurin dankwalin da suka turoshi gaba sai naga ana turashi baya. Na wuce ina
karkada mukullin mota ina juyawa, bayan da aka gama party ina fitowa na hango kungiyarsu
wasu tafka tafkan mata da kyar suke juyi a gabana, kawai na bangaje wasu na wuce, shi ne
babarsa take wani fadace fadacenta wai marar kunya ko girmanmu bata gani, ko kallonta banyi
bana wuce amma ibarhim yaki rabuwa da ni sai a kan axixa da mubarak muka rabu jiyan nan
atika tace Allah mutuniyar, yanxu haka kuka yi baki gaya min ba, lallai?
A daidai lokacin ne suka karaso wajen da ake tsayawa suka tsaya, sannan suka fito suka debo
ledojinsu, hannunsu bibbiyu cike da kaya suka doshi dakin da axixa take kwance. Security
dake wajan ta ruga da sauri ta karbi ledojin hannunsu tana yi musu sannu da xuwa. Xuciyarta
cike da farin ciki ta san yau ko ba komai xata samu ‘yr dubu biyar a wajen ‘yan matan nan, don
daman ta san masu xuwa duba axixa masu kyauta ne don kullum alhaji ahmad da abokan sa
sai sun bata kudi masu yawa idan suka xo, tana gaba suna biye da ita har cikin dakin. Axixa
suka gani xaune a kan gado sanye da doguwar riga da hijab carbi a hannunta. Munnira ce a
gaba ta karasa da sauri wajan axixa ta rungumeta su duka suna hawaye, atika ma da sauri ta
karaso ta rungume axixa. Suka ga axixa ta rame tayi wani fari fau, sai dara daran idanuwanta
ne suka sake fiffitowa, dogon hancinta ya sake fitowa ya yi dodar, suna kallonta xuciyarsu cike
da tausayinta babu wanda ya iya Magana a cikinsu sai axixa take hawaye. Shigowar wani
mutum ce tasa dukkansu ukun suka juya idanuwansu xuwa bakin kofar dakin,
Mahmud sa’ad ne, wannan saurayin da yake binsu tundaga 911. Yayi wuri wuri ya kasa cewa
komai sai kallon kallo suke yi shi da ‘yan matan ukun.
Munnira ita kam harta karkata rabin jikinta xuwa ga bandaki wai idan taga alamar ya nufosu da
mugun abu ta fada bandaki ta rufe. Mahamud sa’ad ya ji kamar a mafarki daya daga cikin ‘yan
matan uku ta kira sunansa, yayi furgigit ya kalleta gami da karasowa wajen gadon cike da
mamaki, ta yi murmushi tace Mahmud baka gane niba ko? Ya yi mata kallon kurilla ya yi ajiyar
xuciya yace ah axixa kece? Long time yaya kike? Atika da munira suka sauke numfashin daya
kasa durgowa waje don tashin hankali. Axixa ta nuna masa kujera tace ya xauna. Bayan ya
xauna ne suka sake gaisawa da axixa tace a’a na dauka wani ne ya gaya maka ina nan ka xo.
Mahmud ya yi doguwar ajiyar xuciya yace eh to tare da sisters dinki muke. Ya nuna su atika
wadanda har yanxu suke tsatstsaye suna kallonsu, suna tambayar kansu da kansu to wannan
ina axixa ta sanshi ya sansu ne a wajen axixa shi yasa yaketa binsu?
Axixa ta kalli atika ta kalli munnira taga kamar fuskarsu ta nuna sufa ba tare suke ba, basu
sanshi ba. tace atika ya dai kuke kallon kallo da Mahmud ashe tare kuke baku gaya min ba,
munnira tayi murmushi tace tare muke das hi amma ai bamu sanshi ba mu dai tun daga 911
yake binmu we don’t know why? Mahmud yayi ‘yar siririyar dariya ya kalli axixa yace axxy kamar yadda kika san ni da har yanxu
haka nake, I don’t hide my feelings and I said what is in my mind . naga kawarki ko sister ki
wannan ya nuna atika, naji ina son ta xama kawata atleast mu ringa gaisawa, atika ta galla
masa uwar harara, munnira da axixa suka kyalkyale da dariya. Kallo daya xaka yiwa Mahmud
xaka gane yana cikin wani hali na fargaba idan atika ta ki bashi hadin kai.
Yayi narai narai da ido kamar xai yi kuka, Magana yake tsakanin sa da Allah bada wasa ba,
axixa tace kar ka damu Mahmud atika sunanta and she is my best friend every thing will be
alright, just cool down and relax. Mahmud ya yi ajiyar xuciya yayin da wani jini mai sanyi ya fara
xagawa a cikin xuciyarsa. Axixa ta juya ta kalli atika ta bata rai tace ke atika ga yayana Mahmud
ki xama kawarsa yanxun nan. Dukansu suka tutsire da dariya har Mahmud din. Ya ce axixa har
yanxu kina nan da manyancenki din nan dana sanki dashi a da ko?
Atika tace, kece ma baba ko kuma ince mama, to mama axixa na ji.
Mahmud ya xare gilashin dake fuskarsa ya kura ido akan atika tana Magana sai kallonta yake yi
nan dai munnira ta kula da kallon Mahmud yayi yawa da yake yiwa atika, ta kamo hannun atika
ta tura ta waje tace Mahmud bita kuje ku gaisa muma musa so mu gana da ‘yar kawata.
Mahmud ya samu abinda yake so ya yi xumbur ya mike ya bi atika wacce take kokarin dawowa
dakin, Mahmud ya tarbe gabanta, munnira tayi sauri ta rufo kofar dakin, atika da Mahmud suna
tafe suna ‘yar hira har wajen motocinsu , munnira ta dawo ta xauna kan gado tana dariya tace,
Allah mutumin ya cika naci tun a hanya yake binmu yana yi mana Magana bamu kula shi ba,
ashe saida ya biyo mu ya xo ya kura mata ido harda cire gilashin idonsa, ina kika sanshi ne wai
ke?
Axixa tayi murmushi tace Mahmud sa’ad mujinyawa wani senior na ne a high school muna
shekarar farko su kuma suna ajin karshe, suka fita suka barmu, munyi mutunci da Mahmud
sosai sune masu tar mun fada idan na tsokano kinsan tun ina yarinya baki na baya shiru, ban
sake haduwa dashi ba sai a spain wata shekara da aka yi min aiki a wuya, shi kuma ya raka
dad dinsa ganin likita sai a talabijin nake dan ganinsa sometimes a wasu occations kinsan dan
gidan gwamnan bauci ne, gaskiya Mahmud yana da kirki ga nutsuwa akwai ilimi kuma. Munnira
tace af axixa ga kayanki a leda irin wannan shaddar ta jikinmu tare muka dinka, tashi ki cire
wannan doguwar rigar ta jikinki ki saka. Axixa tayi murmushin karfin hali tace haba munnira ina
ni ina wata kwalliya? Ku dai kuyi ‘yan mata wallahi tunda kuka shigo nake kallonku kunyi min
kyau kamar wasu’yan biyu. Dole Mahmud ya rikice da ganin atika, munnira tace to ke in kin
saka sai kin fi yin kyau fiye da mu. Axixa tace munnira kima daina bata bakinki babu wani farin
cikin danake ji a rayuwata balle nayi wani ado, nayi ma wa?
Munnira ta cire gyalen da ta yane jikinta tace da axixa shin xaki tashi ki sa ko sai na saka miki
da Karfi?
Kinga fa baki da lafiya banso na matseki ki tashi kisa axixa me ye bambancin ki a da da kuma
yanxu ki daina sawa ranki da banbanci, shi yasa kike damuwa mu duk daya muke ganinki kece
dai kike ganin wani iri, dan Allah kawata tashi ki saka kinga ba za mu ji dadi ba, musamman
atika da kanta taje ta sayo mana a wani kanti ta kai dinki tace lallai a dinka kafin yau asabar
saboda mu taho miki dasu ki saka. Kalar da kike so ce fa axixa karki sanyayar mana da gwiwa.
Sallamr dr rislan ceta katse axixa daga amsar da take shirin bawa munnira suka amsa masa
cikin fara’a. ya shigo bayan sun gaisa ya kalli axixa yace yaya jikin naki? Axixa tace
Alhamdulillah na ji sauki. Ya ce to Allah Ya kara sauki, ya dauko abun aune aunensu yace to
bari na auna BP dinki. Munnira daga kan gado ta koma kan kujera. Dr rislan ya daure mata
dantsan hannunta yasa a kunnensa yana matsa wani dan kullutun da yake hura iska a jikin
abinda ya daure hannun axixa, bayan yayi dan gwaje gwajensa ya ciccire mata sai yayi
murmushi yace yauwa axixa ko kefa? Sauki ya fara samuwa ya dauko magungunan daya
kamata tasha ya bata sannan ya juya ya kalli kujerar daya kamata ma’aikaciyar jinya daya mai
kula da ita tana xaune yace, a’a wa cece yau ya kamata ta xama tana nan?
Axixa tace mis na’omi ce, ta xo nace ta je can ofishinsu ta hutawarta, tunda niba abinda xata yi
min. komai ina iya yi da kaina, kuma ga kawayena nan sunxo xasu tayani hira yau har dare
kaga na’omi gara ta huta.
Dr rislan ya juya ya kalli munnira yace ok, kawayenki sunxo ashe amma kamar banga atika ba
kwata kwata, ko bata gari ne? axixa tace ah tare suka xo da atika tadan fita ne yanxu xata
dawo. Dr rislan yace itama wannan kamar na so na santa dan dai kunfi xuwa da atika ne. axixa
tace xaka santa mana sunanta munnira bala cikin fara’a yace oh munnira Bala ce ok dad dinki
ya bani sunanta a cikin sunayen wadanda xasu xo su dubaki. Munnira ta danyi murmushi ta
kawar da kai gefe alamar ta kagu ya yi fice ya basu waje, gashi sai kallonta yake yi yadda ta
tsani kallo maimakon ya fita sai ya je kusa da kujerar ta ya xauna akan dayann kujerar, kamar
yadda ya saba bayan ya dudduba axixa sai ya dan xauna su taba ‘yar hira sannan ya fita, haka
ko da xai shigo sau goma sai ya taba ‘yar hira da axixa don ya ji ko akwai wani abinda yake
damunta a rai yake sata damuwa a rai, ta sigar wayo da dabaru irin nasu na kwararrun likitoci
yayi bugun cikin axixa har ya gaji amma baiji tak ba akan abinda yake daga mata hankali har
take tunanin gara mutuwarta da irin rayuwar da ta ke ciki.
Bayan dr rislan ya xauna a kusa da munnira suna ‘yar hira da axixa amma yau yanayin hirarsu
ya bambanta da kullum sai axixa tayi ta Magana ita kadai dr rislan bai ji ba yana satar kallon
munnira. Axixa ta lura da hakan sai taji bakinta tayi shiru ta xuba musu ido kawai tana kallo.
Munnira ta lura kallon da dr rislan yake yi mata ya yi yawa sai ta yi dan siririn tsaki ta harareshi
ta mike ta nufo wajen axixa ta xauna akan gado kusa da ita tace, axixa muyi hirarmu kinji yaya
gari?
Axixa tayi murmushi tace gari ku xa a tambaya ke da dr rislan ni da nake a makale kamar wata
kaxa a akurki. Dr rislan yace gaskiya munnira ke xa a tambaya gari ke ce a gari don nima ina
nan asibiti tare da axixa idan kinga na fita to gida naje ina xuwa kuma bacci xanyi saboda na
gaji gani gwauro. Munnira ta yi shiru ta sakar musu hirar don dr rislan ya saka baki, ita tafi son
ya tashi ya fita ya barta da kawarta, har wani gyara xama yake yi. Can ya sake lakuto munnira
da hira yace hajiya munnira ko kina tsoron allura ne naga tun daxu kinki sakin jiki muyi hira?
Kuma ma baki cika rako axixa asibitin nan ba.
Munnira dai har yanxu taki ta tanka masa ba wai ko in yaga tayi shiru xai tashi ya fita. Axixa t
agama karanta dr rislan wannan yan shinshine shinshinen da yake yi tabbas kokarin kawo hira
yake wajen munnira yana son su saba daga karshe kuma soyayya ce batun. Ita ko taki fur, ko
me nene dalilin da taji bai kwanta mata ba?
dr rislan saurayi ne san kowacce budurwa kin wacce ta rasa ya hadu inji samari, yaro ne dogo
santalalle siriri mai kyan gaske. Kallo daya xaka yi masa kasan ya hada jini da farar fata,
mahaifinsa ne bahaushe, mahaifiyarsa kuwa ‘yar dubai ce, don haka ya dauko kamar
mahaifiyarsa, gashin kansa ne mai tauri irin namu na hausa, amma farin hancin duk irin na
larabawa ne.
Dr rislan ya mike tsaye kyakkywar fuskarsa cike da murmushi yace axixa bari na fita na barki
da kawarki ko ta sake naga bata son na xauna na taya ku hira, yanayi yana kallon munnira
wacce cikin rada tace da yafi m. dr rislan da axixa suka hada ido suka tuntsire da dariya domin
dukkansu sun lura da motsin bakinta sun gane abinda tace dr rislan yace kawarki cewa tayi
dama yafi na fita din, to babu inda xani idan kuwa kinga na fita sai dai in ke ce kika rakani har
office. Munnira tace doctor don Allah kaje ni har ciwon kai nake ji wallahi, axixa tace aiko kin
hadu da maganin ciwon kai tunda gaki ga dr rislan don haka ki tashi ki raka shi office dinsa ya
rubuta miki magani ki sha ki wrake doctor rislan yace yauwa axixa haka xa a yi, kafin munnira
tace wani abu axixa ta tashi taja hannunta ta tura waje tace haka kika yiwa atika daxu kema
kije. Munnira tace Allah axixa tausayinki nake don baki da karfi to bari na dauki gyale na. axixa
ta jawo gyalenta ce gashi nan ta wurga mata. Doctor rislan yace yauwa axixa yau ni kin gama
mun komai. Ya bi munnira suka fice axixa ta tura kofa ta rufe, sai ta tsinci kanta cikin
matsananciyar damuwa, ta kara tausayawa kanta da kanta.
Sha’awar munnira da atika ta kamata, ta gansu das gwanin sha’awa yanmata masu jini a jika
wadanda xabga xabgan samari suka mace a sonsu. Hakika na tashi daga aiki axixa ta fada a
bayyane yayin da hawaye ya fara bulbulowa daga idanuwanta akan kujera ta xauna ta sa
hannu biyu ta dafe goshinta hawaye yana xuba ratata akan cinyarta.wani gumi ya keto mata
yayin da ta fusge hijabin da ta kunsumawa kanta akan doguwar rigar da ta bunjuma. Haushi da
takaicin rayuwa ta isheta, hakika ashruf bai cika alkawari ba tunda gashi har yau bai neme ni
ba, koda yake tunda yaga ban amince na karbi xobensa ba, a matsayin sadaki nasan ya fitar da
rai akai na. wata kila ma ya dauka har anyi bikinmu da mubarak, shima me yiwa ya samu wata.
Axixa take tunani a ranta, hawaye ya ci gaba da shatatowa daga idanuwanta. Shigowar na’omi
ce tasa axixa ta tsagaita da kukan da take yi tadago idonta da kyar ta kalli na’omi wacce ta
sankare a tsaye da ture din abinci a hannunta . tace madam axixa kukan ne ya dawo haba
kyakkyawa dake kina damuwa ko akwai wani ciwo ne da yake damunki na kira likita?
Axixa ta girgixa kai alamar a’a tasa hijab dinta tana goge idonta na’omi ta ajiye farantin abinci a
gaban axixa ta dauki fulet da cokali tana kokarin bude flask din abincin ta xuba mata. Axixa ta
daga mata hannu alamar ta dakata da xuba abincin nan. Na’omi tayi kasake tana kallon axixa,
axixa ta nisa tace don’t worry na’omi bana jin cin abincin ne kwashe kawai ki mayar musu kicin
ko kuma kuje kuci. Ta mike ta shiga bandaki ba tare da ta jira amsa daga bakin na’omi ba. cikin
tausayawa