Showing 36001 words to 39000 words out of 73529 words
Chapter 13 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf
Unknown
29 Jun 2025
3593
ma shi ne ina baka shawarar
wadannan bakin su fita su jiraka a waje idan ka ki kuwa xan fada. Su da kansu suka mike suna
hararar alhaji isa ji suke kamar su daga shi su dokeshi duk da ma basu san meye yake faruwa a
tsakanin suba. bayan sun fice alhaji isa yace da tawagarsa su fita suma su jira a waje yace da
mubarak ya sami waje ya xauna mubarak ya xauna yace aje a kira axixa. Alahji sadam da
kansa ya leka falon da su axixa suke ya kirata.
Gabanta ya yi mummunan faduwa ta san yau ranar tonen silili ce. Atika da munnira kuwa suka
yi fiki-fiki, suna fargaba da xulumin me ye kuma. Bayan ta shiga falon ta sami waje ta xauna a
kasa gefen babanta shima alhaji isa ya xauna kusa da dansa, sannan yayi gyaran murya yace
alhaji ahmad ka nutsu kai da sauran ku ji abinda ke tafe da ni masalaha na xo a yi ba bacin rai
ba akan xancen cikin yarinyar nan axixa. Ya gyara xama gami da goge baki ya ci gaba da cewa
a matsayinka na abokina duk da dai na girme maka amma kuma shugabana tunda kai ne
shugaban ni ne mataimakinka. Gani ga ‘ya’yanmu ga alhaji sadam da alhaji bala ku yi naxari
sosai ku bani amsa mai kyau saboda na san me yiwa abinda xan fada yanxu xai iya girgixa ku
koma ya sa ku fita hayyacinku amma idan kuka nutsu kuka duba abu ne sassauka. Abinda na
xo dashi shi ne na xo ne in baka xabi in ma ka sauko sadan-sadan ka bani kujerarka ta neman
takarar xama shugaban kasar Nigeria ka dawo mukamina na mataimaki, ka kuma je da kanka
ka fadawa shugaban jam’iyya da sauran al’umma baki daya, ta kafar watsa labarai rediyo,
talabijin, jaridu da dai sauransu. Yana rufe baki alhaji bala ya mike ya yo kansa da fada yana
cewa..
Alhaji isa ka cika marar kunya marar mutunci da manta alherin baya kai idan ba don alhaji
ahmad ba da ina ma xaka shigo cikin mu?
Ya tarbeka da hannu biyu ya dora ka a hanyar arxiki ya nuna ka ga abokansa ji-jigan masu kudi
da ‘yan siyasarsa. Ka shigo cikinmu harka xama mutum shi ne yau xaka nuna masa kai dan
adam ne butulu ko. Alhaji sadam ya karba yace alhaji bala tsaya bar ni dashi alhaji isa kar fa ka
manta satifiket din sakandire kawai kake dashi shima duk xiro muka yi murda-murda aka samo
maka takardun bogi na karya, aka tsayar da kai a dan takarar neman mataimaki, idan aka ce
yau kaine dan takarar shugaban kasa kana nufin yan Nigeria xasu xabe ka? Kar ka manta duk
jama’ar dake tururuwar sonka ba don kai bane saboda alhaji ahmad ne, yau idan aka ce ka
ware gefe da jama’ar da suke sonka alhaji ahmad ya ware da jama’arsa ko mutane dubu ba
xasu xabe ka ba, kai ko a garinku shagamu ba xaka ci ba balle Nigeria kuma ‘yan Nigeria suna
da hankali ba dabbobi bane irinka, suna da ilimi ba jahilai bane irinka da xasu xabeka.
Alhaji isa ya tuntsure da dariya , ya sake tuntsurewa da dariya ya buga kafa yace na ji duk
abinda ku ka ce amma ina mai shaida muku da da yanxu ba daya bane, yanxu na yi kudi har na
fiku don haka xancen rashin ilimi ko jama’a sai dai idan babu kudin ne. ba naxo ne don in yi
muhawara da ku ba yanxu, na xo ne in bawa alhaji ahamad xabi. Dana mubarak bai yiwa ‘yarka
ciki ba, bai ma taba saninta ‘ya mace ba, saboda muguwar hudubar da kake kunsa mata karta
yarda dashi, ashe kai ka san me yake faruwa a tsakaninku. Don haka alhaji ahmad sirri ne
tsakaninmu kafin duniya ta ji dan takarar shugaban kasa ya ki yayi aure yana korar matansa
akan ‘yarsa ashe nemanta yake har ya yi mata ciki wata uku ko ka sauka sadan-sadan ka bani
kujerar ka ka dawo kan tawa ko kuma…………..
Inna liLlahi wa’inna ilaihi raji’un alhaji ahmad yake karantowa, axixa ta fashe da kuka ta kifa kai
kasa tana rusa kuka. Alhji sadam da alhaji bala suka kece da salati. Alhaji ahmad yace babu
abinda xance maka alhaji isa sai tsakanina da kai Allah Ya isa, kuma in dai takara ce na ma
hakura gaba daya da siyasar ka je ka tsaya a kujerar shugaban kasa, ka nemo mataimakinka,
Allah ne xai yi mana hisabi da kai. Dadi marar misaltuwa ya rufe alhaji isa ya girgixa kai yana
murmushin dadi yace ka huta da ka yanke hukunci cikin sauki ka rufawa kanka asiri. Alhaji bala
ya xabura yace alhaji ahmad me nake ji kana cewa? Ka bar masa kujerar ka? Ba xai yiwu ba
alhaji ahmad. Ciki da gaskiya wuka bata hudawa, sharrin da kake nema ga bawan Allahn nan
sai ya koma kanka alhaji isa.
Alhaji sadam yace karya kake kujera ce ba xa a bar maka ba ka je ka ce kome xa ka ce. Axixa
ta goge hawayen dake bulbulowa daga idanuwanta ta ce daddy kar ka hakura ka bar masa, in
dai wannan mutumin ne sai yahau ya xama shugaban kasar ma sannan xai wulakantamu ya
toxarta mu. Don haka duk sharrin da yake so yayi mana Allah Ya fiku alhaji isa. Alhaji isa yayi
dariya ya dafa kafadar dansa yace ka ji wannan yarinyar abinda take cewa ko? Ba ku sanni ba
amma yanxu xaku sanni. Alhaji ahmad me ‘ya axixa tana dauke da ‘da ko jika a cikinta xa a
lakabawa ‘dana, to Allah Ya sa mun gane. Mubarak miko min mujallun nan guda biyu a fara
basu su karanta kafin jama’a su fara karantawa.
Mubarak ya jawo wata akwati karama ya bude, kowa ya yi tsuru-tsuru xuciya cike da tsananin
bakin ciki da fargabar ganin me xa a dauko, ya xaro mujalla mai tsananin kala tar ta dauku
kamar ka yi kiran sunan wanda yake jiki ya amsa, ya jefawa alhaji ahmad daya ya jefa wa alhaji
sadam daya, alhaji bala yayi sauri ya karkato hannun alhaji sadam suna kallo tare, axixa ma ta
matsa kusa da babanta tana dubawa sai taga hotonta ne ta rungume babanta a lokacin da
mubarak yayi mata wulakanci a asibiti babanta ya xo ya iske ta ita da atika a kofar daki, to
wannan rungumar da ta je ta yi masa itace aka dau hoton shi ne a bangon. Suka yi sauri suka
karanta abinda aka rubuta a saman sai suka ga kamar haka.
Alhaji ahmad abdul fati, sannan dan takarar shugaban kasar nan na karkashin jam’iyyar J.U.T
ya yiwa ‘yarsa guda daya tilo da yake ji da ita tamkar ransa ciki. Saboda tsananin son da yake
yi mata ne ya wuce son ‘da da uba ya koma soyayyar miji da mata oho! Ko kuma tsananin
kyanta ne ya rude shi yake kishi da duk saurayin da yake son ya aureta, ya hana kowa aurenta
ashe shi yake so. Masu karatu ku biyo mu a sannu xa ku ji amsoshin tambayoyin na a cikin
mujllar nan, xai xo kotu ya bamu amsar mu kuma………..
Alhaji sadam ya yi cilli da mujallar da ke hannunsa gami da mikewa tsaye da sauri ya shrbe
gumin da yake ketowa a goshinsa yana cewa subhan Allahi wannan jahilci yayi yawa alhaji isa
ka kuwa san abinda kake ka cika jahili bakauye, me nene na borin kunyar? Dan danka ya yiwa
budurwa ciki abin mamaki ne? barewa ta yi gudu danta yayi rarrafe? Tasha nawa ka yiwa
‘ya’yan jama’a ciki kuma kowa ya sani. Alhaji ahmad ya dago da kyar ya dubi alhaji isa saboda
nauyin da idanunsa suka yi masa don karanta abinda ko a mafarki bai taba xato ba, yace alhaji
isa hakika xan fi ka son ka shigar da karar na saboda sharrin da ka yi min ba xan yafe maka ba,
ba kuma xan bar maganar nan ba ko ka fasa shigar da kara to nixan shigar da kara.
Alhaji bala yace duk ku tsaya xancen bana kotu bane alhaji isa ka yi kuskure don axixa da
mubarak suna son junansu, su kuma akan kansu sun san mafarin cikin nan kuma suna son
abinda xasu Haifa, kowa ya san axixa bata da saurayi sai mubarak. Alhaji isa ya mike tsaye
yana murmushin dadi yace kun gani? Ina da irin wannan mujallu fiye da kwafi dubu dari biyar
ana kuma kan bugawa ta hausa da turanci, yarbanci da ibo kai harda fulatanci da barbanci duk
nasa a buga da kowanne yare don kowace kabila ta gane, kyauta xan raba ga ‘yan Nigeria.
Bayan labari ya iske kowa xan shigar da kara babbar kotun dake nan Abuja, sai ka xo ka yi
mana bayani yadda aka yi ka yiwa ‘yar ka ciki aka so a likawa ‘dana, a matsayinka na mai shirin
hayewa kujerar shugaban kasa a shugabancin al’umma. A Kur’ani da Bible da duk wani littafan
addinai daban-daban babu inda aka halasta uba ya yiwa ‘yarsa ciki. Don haka na baka KWANA
ASHIRIN DA HUDU ka kirani ka gaya min hukuncin da ka yankewa kanka kafin in fitar da
mujallun nan, ina ka yafe ka bani kujerarka aje a kona mujallun babu wanda xai ji idan kuwa ka
ki hakika xaka sha mamaki dan ko sakan ashirin da hudu ba xan kara maka ba da xarar
kwanan ashirin da hudu ya cika ke nemi mujallun nan a fadin kasar nan, ka kuma saurari kira a
kotu.
Gaban axixa yayi mummunan faduwa da jin xancen kotu ta san tabbas tunda ba mubarak bane
yayi mata ciki to wa nene? Don sai wanda yayi mata ciki ya xo ya amsa, idan kuwa babu hakika
mutane xasu ce da gaske dadynta ne yayi mata. Inna liLlahi wa’inna ilaihi raji’un take karantowa
a xuciyarta tace a ranta muddin daddy ya ji ashruf ne ya yi mun ciki xai kasance mai tsananin
bacin rai kuma xai tashi mutum a tafi Croatia a nemo ashruf, amma ba xa a sami ashruf ba don
Ubangidansa abokin aikinsa mr Johnson mun yi waya shekaranjiya na tambaye shi ashruf yace
ai rabuwarmu da ashruf shima rabuwarsu kenan, ashruf yace ya bar aiki dasu ya koma Jamaica
ya ginawa iyayensa gida ya ci gaba da juya jarinsa. Na roki mr Johnson ko xai aika Jamaica a
nemo min ashrfu yace gaskiya garin daya san ashruf da, ya tashi ba a garin ya sayi gida ba,
kuma ashruf bashi da waya ko bayan tafiyarsa wayar da yayi masa daga gidan waya ya yo don
haka takamaiman ba a san inda ashruf yake ba.
Hankalin axixa ya sake tashi ta sake tsundumawa wani halin ha’ula’i. hawaye ya yi ta xubowa
daga idanuwanta ta bi alhaji isa da dansa mubarak da kallo suka doshi kofar fita fuskarsu cike
da annuri, har sun kai bakin kofa mubarak ya juyo ya kalli axixa yace nan da KWANA ASHIRIN
DA HUDU ya tintsure da dariya suka fice. .
.
A nan muka kawo krshen KWANA ASHIRIN DA HUDU KASHI NA BIYU.
.
.
TAMBAYA, tsakanin ASHRUF da AXIXA wa ye ya soma padawa so da kaunar wanin sa?
Sannan kuma wa ya pi so da kaunar wanin sa?
TAMBAYA ta BIYU: idan Kaine Alh Ahmad ya xakayi?
Idan kece Aziza ya xakiyi?
Muna son jin amsoshin kowa a gidan nan kapin mu daura littapi na 3.
.
Comment da sharhi su suke kara karfin guiwa
Ina godiya da comment dinku
[9/3, 7:34 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[9/5, 3:22 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU
LITTAFI NA UKU.
*12*
.
.
Bayan fitarsu alhaji isa sama da minti goma babu wanda yayi Magana a falon, sai muryar axixa
ke sharbar kuka. Alhaji bala ya nisa yace axixa kiyi hakuri ki daina kuka, kuka ba magani bane
ki yi addu’a Allah Ya saukeki lafiya. Ki kuma dauki wannan abinda ya sameki jarrabawa ce ta
Ubangiji, ya kuma xama darasi ne a rayuwarki. Alhaji sadam yace kwarai kuwa kar ki saka
damuwa da bacin rai ganin mubarak ya bujire shi da mahaifinsa sun ce fur cikin ma ba nasu
bane da yake hauka suke, kansu da kansu xasu kai kotu. Nanfa gaban axixa ya sake yankewa
ya fadi tace a ranta lallai akwai ranar tonar asiri, na shiga uku na lalace na jawa ubana abun
kunya. Tabbas su mubarak sun fi mu gaskiya, ni mubarak bai taba sani na ‘ya mace ba. ta yaya
kuwa xance shi yayi min ciki? Karo na farko da taji wata muguwar tsanar fyaden da ashruf yayi
mata. A da bai dameta ba, ta yafe masa cuta daya dai yayi mata shi ne ya cire mata mutuncinta
na budurcinta. Amma yau da ranar tonar asiri ta xo wa xata tunkara ta fada masa gaskiyar
al’amari nan? Ko jikinsu dukka kunne ne ba xa su taba yadda da cewa fyade ashruf din yayi
mata ba. wani babban tashin hankali waye uban dan da xata Haifa? Ya shiga uku da gori da cin
mutunci har karshen rayuwarsa ‘ya’yansa da jikokinsa. Nan fa ta nemi hawaye ta rasa sai ta
sulale ta kwanta, nan da nan mahaifinta da abokansa suka mike a rude suka dagota, ina axixa
ta fita hayyacinta sai asibiti. Su atika a guje suka fito da suka ji salatin da ake ta rafkawa.
Dr rislan ya kasance a ko da yaushe yana kusa da axixa yana bata hakuri cewar ta kwantar da
hankalinta. Saboda xuciyarta ta fara tabuwa tsananin tunani da damuwar da ta shiga. Yana ga
yaki tana ga kuru ita a koda yaushe ta ganshi sai ta rushe da kuka tana rokarsa Allah Annabi
yayi mata allurer da xata bar duniya ko nawa ne xata biya shi. Abin yakan daurewa dr rislan kai
yana ganin yin ciki ba tare da an daura aure ba ai ba wani abin tashin hankali bane, yama xama
ruwan dare a ko ina. Birane da kauyuka, gara ita tasan wanda yayi mata ma, wasu da yawa
karuwai ne basu san takamaiman wanda yayi musu cikin ba, haka suke xuwa a cire musu ko
kuma su haife. Amma saiga axixa da dunbin iliminta da gogewarta tana kokarin ta halaka kanta
saboda saurayin da xata aura yayi mata ciki kafin bikinsu.
Yau kwanan axixa hudu a asibiti hajiya lantana ce yayar mahaifinta ke xaune a wajenta. Axixa
ta daddafa ta tashi xaune a kan gadonta ta dan jingina da filo, hajiya lantana wacce ke kokarin
fitowa daga bandaki dake cikin dakin dauke da buta a hannunta. Ta iske axixa tana kokarin
gyara xama ga robar Karin ruwa da karfen da aka sakale yana kokarin ya fadi. Ta ajiye butar
dake hannunta da sauri ta nufo gadon da axixa ke kwance tana fadin axixa bakya kira na inxo in
dago ki? Kika tashi da kanki ga wannan katan karfe yana kokarin ya fado miki. Ta tallafo ta gami
da gyara mata filon da ta jingina a jiki ta kuma gyara mata hannun da ake yi mata Karin ruwa
taxo gefen gadon ta xauna daga wajen kafafuwanta. Ta ci gaba da kallon axixa tana kwalla, can
da aka dauki lokaci mai tsawo ba tare da kowa yace komai ba sai hawayen da suke xubowa
daga idanunwansu. Hajiya lantana ta goge idonta da gefen mayafinta tace Allah sarki, Allah
mai yadda Ya so da bawan Sa . Dube ki axixa kalli yadda kika xama babu mahalukin daya sanki
da xai gane ki, banda mu da kika xama haka a gaban ido ya kumbure miki kamar yar japan. Kin
cukurkude kin yamutse kamar ba ke ba oh Allah ka yaye mana masifa. Axixa ta rushe da kuka
mai wuyar fita na tsananin takaici.
Hajiya lantana ta matso kusa da ita tasa gefen gyalenta tana goge mata hawayen tace kukan
da kike yi ne yasa miki kumburin fuskar amma kinki ki daina. Addu’a xamu yi, ki kuma toshe
kunnuwanki da duk abinda mutane xasu ce, ba a kanki farau ba kuma ba akanki xa’a kare ba.
banda ma iskanci da rashin munci irin na alhaji isah me abin juyo Magana ta koma tashin
hankali? Bayan sun kawo kudin aure da komai da komai na aure sadaki ne kawai ba a bayar
ba, haka taxo ta kasance ai sai ayi shiru a gangada ayi bikin kije gidanki ki haihi baki alaikum,
wa yasan a waje akayi cikin? Nanfa axixa ta sake rikicewa an tabo mata maganar da take
firgitata. Tasa hannu a kirjinta ta dafe saboda tsananin bugun da xuciyarta ke yi mata, hajiya
lantana hankalinta ya tashi saboda rikicewa ta mike da sauri ta rike axixa tace lafiya? Xuciyar
ceke wannan bugun kamar ganga? Sai hawaye ke fita daga idanuwanta tana karkarwa, inna
lillahi wa’inna ilaihi raji’un hajiya lantana ke karantowa ta nufi kofar fita da sauri xata je ta kira
likita. A bakin kofa suka hadu da dr rislan yana ganin hajiya lantana yaji gabansa ya fadi yasan
jikin ne ya tashi cikin sauri yace hajiya lafiya? Ta ce alhamdulillahi shigo likita axixa ba lafiya.
Da sauri likta ya karaso wajen axixa ya sameta a wannan hali nan ya cire filon da take jingine
ya kwantar da ita akan gado, cikin ikon Allah da dubarunsu na likitoci minti goma sha biyar yayi
yawa xuciyar axixa ta dawo dai dai da yadda ta kowa take bugawa. Har bacci ya fara daukarta
lum, sannan dr risalan ya matsa daga kanta ya koma kan daya daga cikin kujeru biyu da suke
dakin ya xauna, yayi shiru yana tunani. Hajiya lantana kuwa tana xurga xurga tsakanin wannan
kusurwa xuwa wannan kusurwa ta dakin tana koke koke da ‘yan surutai Allah Kai Ka bamu
axixa Kai xaKa kwace, ita kenan Ka ba wa dan