Showing 15001 words to 18000 words out of 73529 words

Chapter 6 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3586

gefe ta xauna, ta yi ta godewa Allah, don ta fara
ganin canji a rayuwarta tanan. Haka aixa ta kasance a jima ta tashi ta lelleka ta hau kan dutse
ta leka ko ta hango ashruf ko wani ma amma babu kowa sai tsuntsaye da suke shawagi a
sararin samaniya wasu kuma sun sauko suna shan ruwa. Lokacin sallah yayi ta yi alwala ta
koma daki ta yi salla ta fito ta sake dubawa taga babu kowa har dai dare ya yi ta ci sauran
kaifinta da tsuntsayenta tayi sallahr isha ta kwanta.

Washe gari da sassafe tana fitowa ta sake yin ido hudu da gasashen kifi da gasassun tsuntsaye
da gishiri a gefe, irin na jiya. Abin yakara daurewa axixa kai, tace a ranta to ko ba mutum bane
yake xuwa ya ajiye min abincin nan? Ta ce in jiya na makara ban tashi da wuri ba, yau ai da
wuri na farka yaushe aka kama kifi da tsuntsaye har aka gasa? Tayi ta yiwa kanta da kanta
tambayoyi, daga karshe ta kinkimi kwalin da aka dora mata kifin da gasasun tsuntsaye da
gishirin a gefe ta shigar daki, ta yi alwala ta yi salla, ta yi Karin kumallo da abincinta, ta rage na
rana da dare. Kwanci tashi yau kwanan su axixa tara da baro jirginsu suna wannan dajin, kuma
tun san da ashruf ya kwashe wannan aman da ta yi rabonta da ganin shi kenan, ko motsin sa
bata ji kuma kullum da safe idan ta bude kofa sai taga gasassun tsuntsaye da kifi dadan gishiri
a gefe an kawo an ajiye mata. A yau axixa ta kudiri niyyar ita kuwa yau ba xa ta yi barci ba
kuma a waje xata labe ta kwana taga mai kawo mata abincin nan. Don haka ne ma ta yini cur
tana sharar barci, da rana don da dare kar barci ya hanata labewa. Can bayan ta dade da yin
sallar isha, misalin biyu na dare axixa ta bude kofar dakin ta leko waje ta kalli inda ake ajiye
mata abinci, taga ba a kawo ba sai ta fito waje ta tura kofar dakinta ta rufe ta koma bayan dakin
ta xauna, ta kudindine ga sanyi yana xurarta tana karkarwa, amma ta daure ta ci gaba da
xaman jira. Can bayan fitowarta da kamar awa uku wato misalin karfe biyar na asuba.

Ta fara jin motsin wani yana tahowa ta mike a hankali tana sauraron daga inda take jin motsin
tahowar. Can ta hango wani mutum rike da wani abu a hannunsa ya doso wajen dakin ta yi
saurinta xata daya gefen don kar ya hangota, ya xo ya wuce, ta sake matsawa wani gefe kar
dai ya ganta, sai taga ya xo bakin kofar dakin ya ajiye abinda ke hannunsa, ya juya ya tafi da
sauri. Axixa na kallonsa bata gane dai ko waye ba. kamar ashruf kamar kuma bashi ba, taga
ashruf ya fi wannan ‘yar kiba kadan kuma bai kai wannan tsawo ba, kuma yana yi mata kama
da mace don lullubi yayi ya rufe kansa kiruf da mayafi. Don haka dai bata gane mai kawo mata
abincin ba, sai ta tsayar da shawarar ta bishi a baya ko ta bi ta a baya taga ko waye, ko kuma
ko wa cece, daga ina kuma? Sai da ta bari yayi ko ta yi nisa, sannan ta fara bin sa, ko binta a
baya suka yi ta tafiya a cikin yashi, taga mutumin ko mutuniyar bai daina tafiya ba, ta ji kamar ta
koma kada fa ba mutum ba ne. wata xuciyar tace to me nene ma in kin bi shi kin mutu daman
me yayi saura a rayuwar ki? Ai da wannan kuncin da kike ciki gara ki mutu ki huta, ta ci gaba da
bin mutumin nan. Sai ya yi kamar xai juyo ya ji motsi a bayansa sai ta yi sauri ta tsugunna ya ga
babu kowa, ya juya ya ci gaba da tafiya, tana biye dashi harta ga ya tsaya a gindin wata
katuwar bishiya mai girman gaske , itama ta sami bayan wani dutse ta labe, gari yana dada
washewa. Mutumin nan yayi alwala daya tada ikamar sallah, sai ta lallabo bayan bishiyar da
yake yin sallar ta tsaya, taga murhunsa da yake gasa kifi ga kwari da bakarsa ga tarkacen
kayansa nan da tsummokarai a lubge dasu yake shinfida.

Ta ji yayi sallama ya idar da sallah yana ta laxumi yana istigifari, can taji yayi firgita ya mike
yana cewa subhan Allahi yana karkade jikinsa. Axixa ta ji gabanta ya fadi ta sake makalkalewa
a jikin bishiya a tunaninta ko ya hango inuwarta ne. ta ji ya dauki itace yana ta bugun kasa sai ta
ji shiru kuma kamar babu kowa, ta lallabo ta leko sai taga mutumin ya sunkuyar da kai kasa ya
rike yatsan kafarsa. Ta yi ta kallon mutumin taga dai bai dago ba, ta sake lekowa saosai tana
kallonsa harda tsugunnawa da leka fuskarsa sai kuwa ta gane ko wa nene, ashruf ne. tafito
daga laben da take ta matso kusa dashi ta tsaya, ya dago kai da sauri ya kalleta sai ya mike
tsaye a sanyaye cike da mamakin yadda aka yi ta xo inda yake, suka kurawa juna ido ba tare
da kowa ya cewa kowa komai ba. can axixa ta sunkuyar da kai kasa, ta kalli kafarsa sai taga jini
yana xuba ta babban dan yatsansa can gefe kuma gawar wata katuwar kunama ce baki kirin
mai girman gaske, tace ashruf daman kana nan, nan ka dawo?

Yace ina nan axixa, ya aka yi kika san ina nan?
Axixa ta yi shiru ba tare da ta bashi amsa ba, sai hawaye ne ke xubowa daga idanuwanta ta
koma gefe jikin wani dutse ta xauna takifa kai a gwiwa ta yi ta sharbar kuka. Ashruf na tsaye
yana kallonta shima abin duniya ya isheshi, yana dingishi ya karaso wajen da take xaune. Ya ce
axixa ki yi hakuri kuma ki yafe min na san na cuce ki na kuma fi cutar kaina ba ke kadai na
batawa ba na sabawa mahaliccina.
Axixa ta dago ta dube shi haushinsa ya sake kamata tace yanxu me wannan rayuwa ta kara
mana? Dube ka ga yadda ka xama, kafar ka jini hannunka ciwo a daure ka rame ka yi baki ka
fita hayyacinka, balle kuma ni kalleni mun xama marayu marasa gata mun ma fita daga cikin
jinsin bil’adama mun koma jinsin dabbobi koma ince aljanu. Da ka yi min haka dame ka karu
yanxu? Ka cuce ni ashruf babu mai yi mana wannan hisabi sai Allah.
ashruf yana tsaye yana kallonta, can ya nisa ya sunkuyar da kai kasa, yace, na ji na kuma

yarda ni na saki a cikin wannan hali. Amma kar ki manta ke kika fara sani a halin da na tsani
kaina da kaina kuma na tsani rayuwar duniyar kwata-kwata ki ci min mutunci ki yi min
wulakancin ma harta kai ta kawo na fita daga sahun mutane na koma kare, kin xamar da ni jaki
aiki na ke miki kina xagina.
Ni a wajena wannan rayuwar da muke ciki ta fi min rayuwar da na tsinci kaina tare da ke a cikin
jirgi, abu daya na yi miki wanda ban ji dadi ba kuma ba yin kaina bane shi ne dana yi miki fyade.
A matsayina na dan musulmi na sabawa Allah na kuma xalunce ki ban kawoki nan don in yi
amfani da ke ba, wallahi ko a mafarki ban taba sha’awar in taba jikin wata mace ba da sunan
xina, arna ma ba musulma er uwata ba. don haka ne ma na kauro nan ina ta yin istigifari akan
mummunan laifin da nayi, kuma ke ma ina niyyar in xo in sameki in nemi gafararki ki yafe min.
amma na kasa ina jin kunyarki axixa.

Ta goge hawayen da yake xubo mata tace, haka ne ashruf, na bata maka watakila ma fiye da
yadda ka yi min na kuma gane kuskure na, abin kuma da ka yi min tunda ba da niyya ba
haushin Magana tace dan nace da in hada jiki da kai gara na hada da alade shi yasa ka yi min
haka, na yafe maka. Allah Ya yafe mana mu duka. Ashruf yace amen. Ya durkusa yace,
nagode. Axixa ta ci gaba da cewa abu daya kuma ya rage da xaka yi min, shine ka mayar da ni
wajen en uwana ka fitar da ni daga rayuwar dajin nan. Ashruf yayi shiru can ya nisa yace to
axixa abu daya xamu yi shi ne addu’a Allah Ya kawo masu nemanmu su ganmu su tafi da mu
don ba ni da wata hanyar fita daga nan, kin ga jirgin nan daya kawo mu ya farfashe, injin ya
daina aiki, ya ma gutsure a cikin ruwa babu yadda xa a yi ya gyaru. Axixa ta fashe da kuka tace
yanxu shi kenan rayuwar mu a nan xata kare? Ashruf ya durkusa a gabanta yana rokarta ta yi
shiru komai xai daidaita da ikon Allah, haka axixa ta dauki lokaci mai tsawo tana kuka ashruf na
lallashinta, yana bata baki.

A ranar axixa tace ashruf ya kwashi kayansa daga nan suka tafi wajen da suke, sabo da nan
inda ashruf yake kusan kullum sai kunama ta cije shi harda gawarwakin macixaan da suke
sulalowa xasu sare shi ya gansu ya kashe su. Don haka ko dogon brci baya yi. Haka axixa ta
yini cur a daki tana tunani ta tuna wannan ta tuna wancan hankalinta ya dan kwanta ganin sun
shirya da ashruf babu xancen mari da bautar da ya ke ta sata, amma kuma hankalinta yayi
mummunan tashi daya ce shima bashi da wata dabara da xai iya yi jirgin nan ya tashi, su bi
‘yan uwansu. Ko su bulla wata kasa ta kusa da inda suke. Hawaye yayi ta xuba daga idanuwan
axixa harda shishshikar kuka, ashruf yana kofar dakin yana jiyota hankalinsa ya yi mummunar
tashi fiye da na axixar don shi ma yanxu abun ya sha masa kai. Can la’asar sakali, axixa ta fito
daga daki, tana so ta dan watsa ruwa a jikinta amma sai ta iske ashruf xaune a kofar dakin. Nan
dai ta yi dan xagaye tana lelleka ina ne xata iya xuwa ta yi wanka bai hangota ba. shi dai yana
xaune yana kallonta, ita kuma ta rasa yadda xata ce masa, ya tashi xata yi wanka. Da kyar tace
dashi jakar taka ko da sabulun wanka? Don naga harda guxirin makilin ka yi.ya yi murmushi ya
jawo jakar da take gefensa ya xaro wayar tafi da gidanka ya mika mata yace axixa ki yafe ni ga
wayar ki har caji ta kare , kiyi hakuri. Ta karba ya xaro sabulun wanka, ya dauki makilin da
sabon burushi ya mika mata, mamaki ya rife axixa don ita bata taba xaton da sabulu a wajensa
ba, ta dai tambaya ne kawai don ya gane ya tashi xata yi wanka, sai gashi harda sabon burush

da makilin duk ya taho dasu, maimakon haushinsa ya kamata da ya miko mata wadannan
abubuwan musamman…..
.
Allah sarki masoyiya ta....
Yanzu wasu zasu ce ina kallon ta wani kare yana bautar da ita na kasa komai, kuma alhali sadin
Maa tace wai kada na neme ta, matan ma gaba daya tace wai na daina kulawa,
Ya kuke gani?
Na bi maganar ta ko na yi watsi da maganar ta na ceto masoyiya ta?
.
Comment da sharhi su suke karamana karfin guiwa na gode
[8/28, 9:48 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[9/1, 6:10 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASIRIN DA HUDU
*5*
.
.
Maimakon haushinsa ya kamata daya miko mata wadannan abubuwan musamman ma wayar
sai da caji yakare sannan ya bata, sai aka sami akasin haka ita faranta mata rai yayi ta yi masa
lallausan murmushinda koda wasa bata taba yi masa ba, tace nagode.
Ashruf dai kawai ya bude baki yana kallonta don a gaskiya ba karamin kyawunta ya gani ba da
ta yi masa wannan lallausan murmushi da wani kallon faranta rai, tace xan yi wanka. Ya jawo
jakarsa ya rataya ya mike tsaye, shima ya sakar mata wani hadadden murmushi yace to
uwargijiyata axixa bari in baki waje. Ya juya ya nufi bayan daki, tace a’a ina xaka kuma ka yi
can?
Shiga daki man ka jira na gama.
Ashruf ya dawo ya shiga daki kamar yadda ta umurceshi, ko wannensu fuskarsa cike da annuri
da yiwa juna lallausan murmushi, sai bayan da ashruf ya shiga daki ne ya dinga mamakin irin
wannan murmushi da suka dinga yiwa junansu yana cewa to koma ba dashi ta ke ba.

Da daddare bayan sun yi sallar isha’I sun idar sai axixa ta dauki mayafin lullubarta xata fita
waje ta kwanta, ashruf yana kallonta ya ga dai da gaske take fitar xata yi, yace, wai shirin me
kike yi ne ? axixa ta sunkuyar da kai kasa tace xan fita bakin kofar dana ke kwana.
Ashruf ya yi murushi yace axixa kenan yaya xa a yi ni ina daki ke kina waje?
Da din ma da kika kwana a waje ai rashin fahimtar juna ne, ina ganin yanxu mun koma da, ni
mai aikin ke uwar dakina. Don haka yi kwanciyarki a daki nixan fita. Ta yi kasake tana kallonsa
ya juya xai fice sai ta mika masa tsummokaran da ta diba na lulluba ya karba, sai ya rage ya
dauki guda biyu ya mika mata biyu yace ai dakin ma da sanyi ki rufa da wannan. Axixa ta karba
a sanyaye tana kallonsa har ya fice ya tura mata kofa ya rufe. Ta koma ta xauna a gefen gado
tana tunani mai rikitarwa, ma’ana ta tsinci kanta a cikin tunanin ashruf game da tausayin sa da
nadama a kan abinda ta yi masa a baya, da tsananin son ta ji labarinsa ko shi wa nene, ta dauki
tsawon awa guda xaune ta yi tagumi ta tsunduma tsundum cikin tunani, sai ta ji wata murya
wacce ta yi mata kama da muryar wanda take muradi. Ya ce madam axixa ba ki kwanta bane
nake hango fitila a kunne?

Ta yisauri ta daga ido ta kalli wajen da take jiyo sautin maganar, sai taga ashruf tsaye a jikin
windo ashe ma windon a bude ta bar shi. Ta yi murmushi tace ba mu kwanta ba dai don kaima
gaka a tsaye . Murmushi yayi, yace gadin ki nake uwar gidata, mai gadi kuwa ai ba a sanshi da
barci ba. tace ni kuwa bana son irin wadannan kalamai su dinga fitowa daga bakinka kai da ni
duk mun xama daya, sai dai ni in ce nice mai aikinka kaine master. Ashruf yayi shiru ba tare
daya san amsar da xai bata ba. yayi murmushi yace good night. Ya rufe mata windo ya tafi,
itama ta kashe fitila ta hau gado ta kwanta.

Da asubar fari ashruf ya fita kamun kifi da sassafe ya harbor tsuntsaye guda uku, ya xo ya
hada wuta ya fara gasawa.duk hada-hadar na da ashruf yake, axixa bata farka ba, tana sharar
barci abinta. Sai can rana ta fara fitowa kamar wajen karfe takwas na safe sannan ta farka, ta yi
salati ta yi mika gami da saukowa daga kan gado da sauri ta bude kofa, tana budewa ta yi ido
hudu da Ashruf akan kujerarsa a xaune yana murmushi ya ce barka da tashi. Axixa ta Harare
shi ta ce ka san gari ya dade da wayewa amma ka ki ka kwankwasa min kofa, in tashi in yi
sallah.?
Ashruf yace baki bani ixinin in yi miki haka ba, amma gobe da asuba xan tashe ki, ki yi hakuri.
Ta yi murmushi tace ko xa ka kara bani aron brush din jiya da makilin?
Ashruf yace ga su can a gaban duten can na kai miki, ya nuna mata dutsen. Ta je ta iske ya
cika mata kwalba ga brush da makilin a kan wani kwali ya ajiye da sabulu a gefe.

Da ya ga ta nupi wajen saiya dauki abincinta ya shigar mata daki, can da aka jima axixa ta
shigo sai ashruf ya mike xai fita, axixa tace, ya haka ina xaka je ne? me ya sa kake gudu na
ne? idan na fita ka shigo idan na shigo ka fice baka kaunar ka ganni a kusa da kai ne!?
asruf ya girgixa kai yace, ba haka bane. Axixa tace to me nene? ,
y ace haka kawai.
Ta ce to in haka kawai ne ba hujja bace ka dawo ka xauna. Ashruf ya yi murmushi ya dawo ya
xauna ta ajiye brush da makilin akan loka tadau wani mayafi ta yafa ta tada ikamar sallah.
Bayan ta idar ta shafa addu’o’inta, sai ta juya ta kalli ashruf tace good morning. Ashruf yace
assalamu alaikum. Axixa ta yi dariya ta ce assalamu alaikum ya kamata musulmai su rinka
cewa ‘yan uwansu musulmai ko?
Ashruf yace shi ne lada ba good morning ba. ashruf ya jawo gasassun kifi da tsuntsaye ya tura
gabanta. Axixa ta yi murmushi tace yaushe kake tashi ne har ka kamo kifi da tsuntsaye ka
gasa? Ga sunan da dumi daga gani yanxu aka gasa. Ashruf yace mutum da aikinsa kuma
sana’arsa. Axixa ta gutsira ta ji yau gashin da gishirinsa aka gasa shi yasa taga babu gishiri a
gefe. Ta kalli ashruf tace yau kuma wata sabuwar dabara ce da gishirin ka hada ka gasa?
Ashruf yace ina fatan dai ba santi kike yi ba.?
axixa tayi dariya tace yanxu dai xan yi tambayar santin, na dade ina tunanin inda kake samo
gishirin nan don naga farkon da muka xo ba ma ci da gishiri sai daga baya,

Dashi ka xo ko kuma akwai bishiyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login