Showing 9001 words to 12000 words out of 73529 words

Chapter 4 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3582

ita kuma ta kudira a ranta duk ranar da suka
koma Croatia, ashruf sai ya raina kansa abinda yayi mata don sai ta sa an daure shi sai yayi
prison indai kudi yana amfani wahalar ta da yayi.daga can nesa suka hango fitila kamar tana
yawo a cikin ruwa da alama dai mutane ne ko kuma su mr Johnson ne suke nemansu. Axixa ta
mike tsaye tana kwalla musu kira tana cewa ga mu nan. Ashruf dai na xaune yana kallonta. Ta
kalleshi tace, ba xaka yi musu Magana ba? ka san mu suke nema. Ashruf y ace dan me xan yi

musu Magana bayan ga ki ai daga yau kare ya bar haushi, daman can ma karya a kafi sani da
haushi da masifa. Axixa ta fusata tace guldo yau ni ka ke cewa karya?
Ashruf yace kwarai kuwa.

Axixa ta cire hannu ta xuba masa wani uban mari, ya rike kunci yana murxawa, sai yayi
murmushi yace kin yi na karshe kenan. Kafin ta juya wajen da take hango hasken sai taga
hasken ya juya yana komawa har ya kure hawayen takaici yayi ta kwaranyowa axixa tana
xaune takaici ya dameta, ashruf kuwa fuskarsa cike da annushuwa kamar yau sallah a wajensa.
Ya yi kwanciyarsa yana wake waken sa, ayi ruwa a tsagaita a sake tsugewa. Axixa na takure ta
hada kai da gwiwa, bata taba xaton ko da wasa ba a duniya xata tsinci rayuwarta a irin wannan
yanayin ba. yadda taga rana haka taga dare, ashruf nata barcinsa yayi juyi ya kalleta, ya koma
ya kwanta yana murmushi. Can wajen asuba ta ji sun fara yin kasa kamar jirgin yana sacewa
axixa ta xabura tace guldo, guldo ta ji ya yi shiru tace, ashruf, ya yi mata banxa ta daka masa
duka, ya mike xaune ya kalleta cikin bata fuska yace, ke ya haka ina barci kina tashina me xan
yi miki?

Axixa ta ji wani takaici tace, ka duba ka ga yadda jirgin yake mana sacewa fa yake yi. Ashruf
yace to me xan yi masa ai gara ya sace mu fada kasan ruwa mu yi rayuwa a cikin kifaye ko
muma ma dandana yadda suke rayuwarsu ko ma daina wulakantasu ace ba manya ake so a
kamo ba, ace a kamo kananan. Axixa ta rude jirgin nan sai sacewa yake yi dai, ta rirrike jikin jirgin rabin kafafuwansu a cikin
ruwa, ashruf ma ya rike jikin jirgin a haka dai igiyar ruwa ta dinga jansu tana yin gaba dasu har
garin Allah Yawaye rana ta fara fitowa. Suna nan dai a makalkale, a haka babu ko kukan
tsuntsu balle kuma bil adama. Axixa ta fara jin yunwa ga kishirwa to ya xa ta yi yau babu abincin
balle ashruf ya kawo tace babu dadi. Ashruf ya kalleta duk ta jigata ta wahala sai ya kyakyace
da dariya yace madam axixa mai xan kawo miki ne?
ba ki kada kararrawa ba guldo ya kawo abu mai sanyi cool not cold?
Ya sake kecewa da dariya. Hawaye ya dinga xubowa daga idon axixa, don takaici. Haka suka
yini har kusan magariba wato awarsu ashirin da hudu a haka. Ashruf ya dinga mika hannu yana
kamo kifi ya dangwali wani abu kamar gishsiri ya ci, ya mika hannu ya sha ruwa ya ci gaba da
surutunsa, axixa kuwa bata gani ma sosai don yunwa, badan girman kai ba da ta roke shi ko
danyen kifin ne ya bata ta ci.

Ashruf ya fara gyangyadi sai ya ji axixa na dukansa wai ya tashi ya bude ido yace meye?
Sai ta nuna masa wani waje a gefen ruwa igiyar ruwa ta kawosu karshen gabar wani bangare
na ruwan. Nan da nan suka sa hannu suna tura ruwan jirgin yana kara yin gaba har suka
karasa wajen filin suka firfito daga cikin ruwan. Ashruf ya jawo jikin jirgin gefen ruwa. Anan jikin
wani dutse suka karasa kwanan a xaune suna gyangyadi. Bayan gari yawaye tar sai ashruf ya
farka ya kalli axixa wacce take a xaune ta kura masa ido, baki duk ya bushe mata kishirwa da
yunwa sun addabi ‘ya’yan hanjinta, ashruf ya yi hamma gami da mika ya mike tsaye, yace, bari
dai na xaga garin namu in ga yadda yake fuskarsa cike da murmushi. Axixa ta bishi da kallo ya
yi can baya yana xaxxagawa sai ya ga duk duwatsu ne masu bulbulo da ruwa garaigarai. Sai
kuma yashi ko ina irin na bakin beach din nan tunda nan ma bakin ruwa ne da bishiyoyi da

dogayen ciyayi a jikin duwatsu. Ahsruf ya ga alamar wajen an hura wuta tunda ga dutsinna nan
da toka da konannun itace, ya ci gaba da xagayawa sai ya hango wani dan daki na katako ya
karasa wajen da sauri ya taba kofar ya ji a kulle, sai da yayi ta maxa ya xage karfinsa sannan
ya iya bude kofa ya shiga ciki ya ga wani gadon itace an tula tsummakara akai an yi shimfida
dasu . ya tura windo ya bude haske ya kara garwaye dakin. Ya hango wata loka ya jawo ya
bude ya ga kwalaben giya ne wasu babu wasu akwai, can gefe kuma ga kwari da baka masu
kyau har guda biyu murna ta lullube ashruf ya gaya samu wajen xama sosai ga wata kujerar
katako ta kishingida ya ci gaba da bincike bincike ya ga fitilar wani kwai ga ashana sinki da
kalanxir galan guda cikakke.

Da tsintsiyar kwakwa duk dai a dakin, dadi ya sake lullube ashruf yace bari in je dai in sallolin
da ake bina in xo in gyara dakina. Ashruf ya dauko kwalba daya daga cikin kwalaben nan ya fito
bakin ruwa ya iske axixa ta sami wani dutsen da yake disar da ruwa ta sa harshenta tana lasa.
Ashruf ya yi murmushi ya girgixa kai ya wuce abinsa. Ya karasa bakin kogi ya duri ruwa a cikin
kwalabar nan ya girgije ya xubar ya kara durawa ya girgije ya xubar ya wanketa tas sannan ya
ciko ta da ruwa ya xagaya bayan dutse ya yi fitsari yayi tsarki ya dawo ya cikata yayi alwala.
Duk axixa na kallonsa tana tunani a ranta tace daman wannan musulmi ne?
ni su munira na cewa sunan musulmi gare shi ban dauka musulmi bane. Ta ce ko ana ya samo
kwalbar?
Da ya ajiye ta nima in xo in duri ruwa in sha. Tana jiran in ya gama alwalar ya tashi ya tafi sallah
ita kuma ta xo ta sha ruwa a cikin kwalbar sai ta ga da ya gama ya ciko kwalbarsa yayi
tafiyarsa da ita. Ran axixa yabaci kamar dai ta bishi ta roke shi ya bata taga dai ya ma xa a yi ta
ringa rokarsa ai xai rainata, ta kyaleshi ya wuce ta xo bakin ruwan nan ta tsaya tana so tasa
hannu ta ringa kwarfa tana sha amma sai taga kamar in ta sa hannu xa ta xindima ciki sai ta
fasa.

Hawaye yayi ta xuba a idon axixa don takaici tace a ranta yau wai nice wacce a gida a rana
daya sai in sa a dafa min abinci kala kala har fiye da goma, sai wanda naga dama xan ci yau
gashi wai ruwa ma ya gagareni in jika makogorona. Ashruf yayi ta jero sallolinda suka wuce shi
sanda suke jirgi, har ya kammala rama su. Bayan ya idar ya shiga gyaran dakinsa ya dinga
watso tsumokaran nan waje harda kwalaben giyar nan. Sai kuma ya yi tunani ai axixa xata iya
daukar daya tana shan ruwa a ciki tunda ya ga yadda take kallonsa, ya san sha’awar kwalbar
nan take ta dibi ruwa ta sha, don haka ya xo ya kwashe su ya boye su a cikin lokar nan har
tsummakaran nan yace ai sai ta ringa lulluba dasu idan na bar su a waje suma ya mayar dasu
daki.

Bayan yagama gyaran dakin ya fito bakin ruwa inda ya jifge mata mataccen jirgin su ya balle
injin jirgin daga jikin gangar jikin jirgin da yake jikin jirgin ne leda ne hurshi ake kamar balo
amma yana da laushi ya jawoshi ya kai ya dora a kan gadon itacen nan na dakin. Kafin ya
dawo bakin ruwa sai ya xo ya iske axixa ta xo wajen ta jawo masa wata jakarsa da ta fado daga
cikin jirgin. Ashruf ya karaso da sauri ya fisge jakarsa, yace ajiya kika bani? Axixa tace na
hango wayata a ciki daman kai ka sace min ita wato dan kar in buga waya in ce ga inda muke
ko?

Wato da biyu ka sace mana jirgin ko kai harda shirinka ka xo su man shafawa su brush da
makilin duk na hango, to wallahi xa ka gwammace baka wahalar da niba, sai ka raina kanka.
Malam dalla ka miko min wayata kaji ko, barawo kawai.

Ashruf ya daka mata tsawa ya xo daf da ita yana nuna mata hannu yace, ke axixa ki iya bakinki
kin ji ko! Ba ashruf din da kika sani da ba ne balle wani guldo da kike kira, da ina sane na dauko
lalataccen jirgi don ya tsaya mana a hanya in koya miki darasi kisan talaka ma ba dabba bane,
ba kuma abin wulakantawa bane yana da amfani. Ni ne kuma na xare miki waya a aljihun don
kar ki kira kowa daga ke sai ni a nan xamu xauna talaka da mai kudi a cikin daji daya ki nemi
abincinki in nemi nawa. Don haka dokar da xan sa ka miki guda uku ne xuwa biyu, ta farko
daga yau idan na sake jin bakar Magana ta fito daga bakinki da sunan kin gaya min hukuncinki
marine .

Axixa ta fusata ta tunkude yatsan da yake nuna mata tace baka isa ba kai waye da xaka mare
ni ka kwana lafiya? Ashruf ya bude jakarsa ya dauko brush ya matsi makilin ya ciko kwalabrsa
da ruwa ya tafi gafe daya yana wanke bakinsa. Haushi da takaici ya lullube axixa tace dashi
ashruf karya kake ke ce ka kawo ni nan don ka wulakanta ni ko kuma ka rama abinda na yi
maka, ai ko a ina muke da bambanci nib! a sa’ar yinka b! ace kuma ina kara shaida maka sai ka
raina kanka, ashruf xaka yi da na sani, dan talakwa…. Kafin ta cigaba da fadar abubuwanda
xata fada sai ta ji saukar wani gwauron mari a fuskarta saida ta durkushe abinka da ‘yar hutu ga
babu karfi jiki, kishirwa da yunwa sun fara lahantata.
Ashruf yace kar ki mance da dokata ta farko duk sanda kika gaya min bakar Magana mari ne
hukuncinki, doka ta biyu kuma daga yau kar ki kara ce min ashruf balle wane guldo sai dai kice
min master, ta ukun kuma itace duk wani aikena da aikace aikace ba sai na saki ba, ke xaki
dinga yi min. axixa dai na durkushe ta rike kunci, radadi da xogi yana ratsa mata kunci. Ashruf
ya juya xai tafi ya ji axixa ta mike tsaye a fusace tace karya kake matsiyaci baka isa ba, ba a
haifi uban da xai sani aiki ba. Karen daya yiwa uwargijiyarsa tawaye ya tafi ya bar ta, tana rufe
bakinta asruf ya juyo a fusace ya sakar mata mari mai radadi fiye da na farko yace kar dai ki
mance da dokar farko, wallahi wallahi idan baki gaji da fada min bakar Magana ba, ba xan gaji
da marinki ba. yayi tafiyarsa ya bar ta a nan a durkushe tana kuka.

Ya je ya tube kayansa ya saka dan gajeren wando ya dauko kwari da bakarsa ya shiga cikin
ruwa ya kamo kifaye manya manya ya xo ya wuce axixa anan a xaune ta yi lamo, da kyar take
daga ido ma ta kalleshi.ya wuce abinsa can axixa ta ji kaurin itace da kamshin abinci. Ta ji
yawunta na tsinkewa kamar da ta ke ji. Ta lallaba ta hau kan wani dutse ta leka sai ta hango
ashruf a xaune akan wata kujera ga wuta a gabansa yana gasa kifinsa a kofar wani daki.
Mamaki ya kama axixa tace a ranta yanxu daman ashruf ya san wajenan harda gina daki ga
itace gasu brush dinsa duk daman ya tanada ya xo da ni nan ya xauna don ya wulakanta ni.?
Tana ta liken ashruf har kifinsa ya gasu taga ya sauke akan wani kwali yana gutsira yana ci ga
ruwa a kwalba ya tara a jikin wani dutse da yake bulbulo da ruwa, yana cin kifi yana korawa da
ruwa. Yawunta ya tsinke ta tuna wannan ta ware ta saka wannan ta ware akan yadda xa a yi ta
ci kifin nan.

Daga karshe dai ta tsaida shawarar ta je ta rokeshi ya bata kifin ta ci, tana tafe tana layi harta
kai wajen da ashruf yake xaune, ta tsaya a gabansa tana kallonsa batace komai ba. ya daga kai
ya kalleta yayi murmushi yace ke lafiya? Axixa tace ina jin yunwa ka bani kifin in ci. Ashruf yace
a’a ba yadda xa a yi ki xo ki same ni haka kawai kice in ba ki kifi ki ci a wane dalili? Ko ni bawanki ne?
axixa tace to nawa xaka siyar min?
da kudi a jikina ta xaro kudi daloli cunkus tace na saya dollar hamsin.
Ashruf ya harareta tace to dollar dari. Duk dai bai ce mata komai bata ce to dala dari biyu. Ya
kawar da kai ya ci gaba da wurga lomar bakinsa. Axixa ta sake matsowa kusa tace to ga dollar
dubu ta mika masa kudin duka. Ashruf ya kadar da kudin suka xube, axixa ta ciro sarkarta
dankareriya ta daimon bama gwal bace da abin hannun sarkar tace, gashi duk ka hada ka bani
kifin nan in ci yunwa nake ji. Ashruf yace bana son kudinki balle wani banxar gwal dinki idan
kudinki yana da amfani ki dauka ki je ki sayo kifi, kin ga kuwa talaucina yayi min amfani tunda
kamo kifin da nake yi ya amfana min a ko ina nake xan ci xan sha xan kuma sayar in sami kudi.
Kin ga kuwa da nake tashi da asuba in shiga ruwa ba kamo kifi ba rashin hankali ba ne ba
rashin aikin yi bane. Saboda haka kowa ya ci abinda yake dashi.

Ke kuwa kudi kike dashi kici kudinki inci kifina. Gashi ma kifin manya na kamo ban kamo
kanana ba ke kuma ba kya cin manyan kifi. A kamomin kanana. Ya ringa gwada yadda take yi
masa yana shake murya yana rangwada wai yadda take yi. Axixa ta rushe da kuka ta durkusa a
gaban ashruf tana kallonsa yana loma da kifin sa yana ta kwaikwayonta yana tsokana. Axixa ta
mika hannu xata gutsira don ita bata ma damu da abinda yake yi mata ba, don tasan ta
musguna masa yanxu kuma lokacinsa ne. ita dai fatanta ya bata kifi taci don ta rayu kwanabiyu
babu ci babu sha. Ya tare hannunta ya wurgar gefe gami da daka mata tsawa ya bata fuska
yace ke ni nasan ki ne!?
tashi daga nan ki bani wuri. Axixa tace ashruf ka bani kifin yunwa nake ji. Ashrfu yace meye
dokata ta biyu, me nace ki ringa kirana dashi?
Axixa tayi shiru can tace to master bani inci. Ashruf yace ya xa’ayi ga aikin master ke kuma ki
xauna kina cin abinci, ki gamamin ayyukana mana, shiga dakin nan ki dauko kayana suna nan
akan gado kixo ki wanke min. idan kin gama sai kixo in dan xuba miki kayoyi irin naku na
karnuka ki kuma gyaramin wajen girkin. Kamar yadda tace masa ranar bikin xagayowar
shekararta. Axixa tace master ka bani abinci inci sannan in wanke. Ya ce ai nima bakya bari na
ina gama cin abinci kafin inyi miki hidimarki, don haka yanxu nan nake so karki kara sakon
ASHIRIN DA HUDU .

Axixa tana tafe tana tangadi kamar wadda ta sha giya ta nufi cikin daki, tayi mamaki da ta iske
dakin tas ashruf ya tanadi komai nasa kamar a cikin gidansu. Ta kwaso kayan daya umurceta
da ta wanke, ta fito ta nufi wajen ruwa ta wanke duk da dai babu omo taxo ta yayyaba su a jikin
dutse. Tana tafe tana tuntube ta karaso wajen da ashruf yake a kishingide akan kujerarsa ta
itace yana hutawa ya ci ya koshi. Ta xube sharaf ta xauna. Ahsruf ya dago ya kalleta yace, ke
tashi ki koma daga can ki tube takalman ki kiyi min sallama ki shigo, yaya xa’ayi ki shigo min
fada da takalmi ki xube min a gaba haka, babu na gama babu godiya babu komai? .
Axixa ta mike da kyar ta koma baya ta tube takalmanta tayi sallama ta karaso xata xauna yace,

a’a baki gama ba, banji kinyi godiya ba da na saki wanki.
Axixa tace thank you master for honoring me with washing your clothes. Ta xauna ya miko mata
kifin ta fara ci hannu baka hannu kwarya, ashruf na kallonta kawai ya ji wani sanyi a ransa, yace
a ransa wannan ta fara sanin duniya kenan, sai ka bautu kafin ka samu abinda xaka ci ita aida
daga sama take gani, tun daga kudin da xata kashe da suturar da xata sa har xuwa cinta da
shanta. Shi yasa take daukar talaka marar hankali shi yaso yayi bauta kafin ya samu kudi.

Bayan ta gama ci ta dauki kwalbar ashruf xata sha ruwa Ashruf ya kwace ya tuttular da sauran
ruwan dake ciki yace, je ki debo naki. Axixa ta karba cikin sauri taje ta taro ruwa tayi ta moda
saboda irin axababbiyar kishirwar dake addabarta. Taji kifin nan kamar tunda Allah Ya halicceta
bata taba cin abinci mai dadin haka ba, sannan ta farfado daga dishi-dishin da take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login