Showing 48001 words to 51000 words out of 73529 words
Chapter 17 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf
Unknown
29 Jun 2025
3595
da jimami na’omi ta sintimi farantin abinci, wani bangaren na xuciyarta cike da farin
ciki yau xata yi lunch da abinci mai maiko. Duk a irin wadatattun kudi da alhaji ahmad yake biya
a ciki ne ake dafawa axixa hadaddun abinci wanda ko a gidansu ne abinda xa a bata kenan.
Tana shiga bandaki ta mayar da kofa ta rufe ta doshi wajen wani katon madubi da yake sakale
a jikin bangon bandakin, wanda girmansa ya isa xaka iya ganin surar jikinka gaba daya daga
sama har kasa taga dai itace dai axixa kamanninta basu canja ba, ba kamar yadda xuciyarta
take aiyana mata ba cewar duk kin yakune kin tsufa, kinyi muni, taga kamar ma yanxu tafi da
kyau ramar da tayi ta kara fito mata da dogon hancinta da gwarxa gwarxan idanuwanta,
chocolate colour dinta ta kara yin haske. Ta tube rigarta don taga girman cikinta, sai taga kai
idan ba ita bata san tana da ciki kuma take aiyanawa a ranta babu wanda xai kalli cikinta ta
yace tana da ciki har wata uku.
Sai dai kuma taga kirjinta ya cicciko ba kamar daba. tayi ajiyar xuciya gami da sake goggoge
guntayen hawayen da idanuwanta ta kalli idonta a kode suke fari fat babu kwalli, tace a ranta
nasa kaina a kunci, rabona da kwallia har na manta, mai yayi xafi?
Kamar wata mai takaba abinda ya sameni ya riga ya same ni to wannan damuwa da nake yi
baxa ta yi min maganin halin da nake ciki ba. duka wanda yasa Allah a gaba ba xai gaba dai dai
ba, ina cikin xamana Allah Ya turo ashruf har ya yi min haka, kuma ina cikin xamana Allah Xai
kawo min hanyar da xan fita daga cikin xulumi. Xuciyarta ce take mata nasiha don itama ta gaji
da tsananin kunar bakin ciki har bugunnta yake canjawa. Axixa ta kalli xoben da ashrfu ya saka
mata a hannu a ranar da aka gansu a dajin nan. Ta kuma tuna kalaman daya gaya mata a
lokacin, sai ta tsinci kanta cikin wani farin cikin damuwar da ta gallabe da ta fara kama gabanta.
Ta xauna a gefen bahon wankan dake bandakin a hankali. Tana tunano rayuwar soyayyar da
suke yi da ashruf a wannan dajin da suka xauna, tace a ranta, “ashruf me yasa ka bari aka
ganmu?
Gashi nan na xo gidan namu amma na tagaiyara, yanxu da har yanxu muna can sai nayi rainon
cikinka na haife babu wanda yaji, mu tafi wata kasa muyi auren mu gashi na dawo gida nasa
mahaifina a cikin musifa, hakika ashruf ina sonka, ina sonka har yanxu, ko da har abada ba xa
mu hadu ba to xan dinga ganin danka, Allah nagode da ka sa abunda ya faru ya xamo
sanadiyar ciki, cikin ashruf”. Tasa hannu ta shafa cikin tayi murmushi.
Yau ce rana ta farko da axixa taji wannan muguwar damuwar ta saketa, ta tsani abin cikinta a
da, sai gashi yau soyayyar da take yiwa ashruf ya shafi ‘yarsa ko ‘dansa na cikin cikinta. Ta ci
gaba da cewa a ranta naji dadi na kuma godewa Allah, da wannan cikin bana mubarak bane,
mutumin da bana so irin tsiya marasa mutunci. Sai dai yanxu abu daya ne matsala shi ne baxan
iya tarar daddy na ba, na gaya masa ba mubarak bane yayi min cikin ashruf ne. yadda daddyna
ya nuna ya tsani ashruf balle ace yayi min ciki kuma ba a ma san inda yake ba , ai na shiga
uku. Sannan ba a ga ashruf ba kuma ba mubarak bane to mutane xasu ce da gaske su alhaji
isah suke kenan musamman ma yadda alhaji sadam da alhaji bala suka xake suna tayar da
jijiyoyin wuya su a dole sai mubarak ya amsa har suna xancen kai kotu. Ta yaya xan fito nace
musu mubarak ya fi su gaskiya? axixa ta yi ajiyar xuciya tace a ranta ina cikin mummunan hali,
bani da ta cewa, Nigeria gaba daya ma tana cikin wani hali na rudu, babu wanda xan tara na
gaya masa halin da nake ciki ko da kuwa kawayena baxan iya gaya musu ba mubarak bane
ashruf ne, me xasu dauke ni?
Yar iska?
Tayi shiru ta dauki lokaci mai tsawo tana tunani, to amma kalma dayace da xarar ta tuna ta take
jin sanyi a ranta, itace babu abinda ya gagari Allah mai kowa mai komai. (NIMA NA CE
HAKKUN BABU ABINDA YA GAGARI ALLAH, INA ROKONSA YA CIKA MANA BURINMU NA
ALKHAIRI CIKIN DUKKAN KHAIRI, YA KUMA RUPA ASIRINMU, amen) ta danka gaba ki daya
lamuranta gare Shi Shi ne kadai xai iya fitar da ita daga tarkon makiya ba wani ashruf ba. daga
karshe ta mike ta fada baho don sake sabon wanka, ta ciro karamin tawul dinta dake rataye a
bandakin tadaura ta bude kofar bandakin ta leko cikin dakin taga babu kowa su atika basu dawo
ba har yanxu.
Murmushi ne ya kubuce mata tace munafukai da kowace taki xuwa sai da aka turata shi ne
suka je suka yi bulunbukui. Ashe suna so ni mutumin da bana so ko minti biyar ai ba xan iya yi
dashi ba balle awa. Take fada axuciyarta, ta fito daga bandakin ta doshi kan lokar dake gefen
gadonta don shafa ‘yan mayukanta da aka jera mata. Bayan tagama shafa mai sai ta jawo jakar
atika ta bude tabbas tasan xata sami abinda take nema, hoda da janbaki da turare , wannan
dole xaka same su a koda yaushe a jakar atika. Yawan kwalliya ce da ita don haka take yawo
da abinta a jaka. Axixa ta shafa hodar atika, tayi kwaliya nan ta koma kamar axixanta na na da,
harta fida kyau, ta dauko irin dunkinda suka kawo mata irin nasu ta saka, ta koma bandaki don
sake kallon madubi, itama kanta ganinta tayi kamar ba ita ba, tayi kyau sosai. Ta sake kallon
fuskarta a mudubi tayi murmushi tace a ranta inama nima yanxu ashruf ya shigo ya xo ya ganni
kamar yadda Mahmud yaga atika, dr rislan yaga munnira.
Bana sha’awar ko wane da namiji baya ga ashruf. Muryarsu atika ceta katse mata tunanin da
take yi a gaban mudubi. Ta fito daga bandakin da sauri suna ganinta cikin murna da mamaki
suka yo kanta, kai! Gaskiya axixa kinyi kyau harma tafi yi miki kyau fiye da mu. Daman axixa
akwai iya dauri, ta yi daurin ta mai kyau, ita ko a ranta take cewa dama nima naga ashruf dina
nima yanxun nan. Duka suka xaxxauna a kan gado, munnira ta debo ledojin da suka yi mata
sayayya suka jifge mata a gaban ta, tana bubbudewa fuskarta cike da fara’a, komai ta daga sai
ta yaba dashi tayi murna tace kai waye ya xabo wannan ashe kun iya xabe?
Kamar kunsan ina so naci cingam kuka siyo min. suma dadi ya lullube su don daman suna
xulumin ba komai bane yake burge axixa amma sai gashi yau duk abinda suka kawo mata yayi
mata, ta dago greating cards ta bude na farko taga sunan munnira ne mai kunshe da kalmomin
fatan samun sauki “get well soon” ta yi murmushi ta ajiye ta jawo dayan na atika ne shima dai
na fatan samun sauki ne. ta kalle su ta yamutse fuska tace duk abubwanda kuka kawomin sunyi
mun amma banda wadannan cards din duk kuka sayo na get well soo babu wacce ta tuna da
‘dan cikina tace bari na siyo na babies, ko wani mai cartoons a cikin ku, ko ba ku san ina son
baby na ba? suka yi wuri wuri da ido, ko wace cike da mamaki suna kuma fargabar furta wata
kalma da xata tasowa axixa ciwonta don sunji gargadin da akayi musu.
.
.
To jama’a, a cikin tambayoyin mu na da, wanda muka yi tambaya a kan, cikin axixa da ashruf
wa ya fi so da kaunar wanin sa?
Da yawa daga cikin ku suke cewa ashruf ya fi axixa , ni dai nace laa,a nawa ganin, axixa ta pi
kaunar ashruf yadda nima na pi so da kaunar ……………
Comment da sharhi su suke kara kargin guiwa nagode
[9/5, 3:24 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[9/5, 3:25 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT3
*15*
.
.
Munnira tace a ranta ashe dana siyi mata na welcome to the world new born baby xata ji dadi
atika ta hanani babu wacce ta tanka wa axixa akan maganar da ta yi musu. Wannan abu ya
bawa axixa matukar mamaki tana ta Magana ita kadai basu bata amsa ba sai xare ido suke.
Tayi murmushi kawai, don ta gane abinda suke gudu kada su fadi abinda xai tayar mata da
ciwon ta . Sai kawai ta bar hirar itama ta share. Ta dauko hirar Mahmud da dr rislan nan fa ka ji
muryoyinsu rangadai, axixa tace daxu a raina nace munafukai nan kowacce tana cewa bana so
ana turata nace kinji su mucus an sami abokai. Atika tace ke dai bari axxy Mahmud din nan ya
iya hira shi ne kika ga na jima waishi dan Allah na dinga bashi ko kwana daya ne a sati yana
kawo min xiyara, yana so ya zama abokina, tunda yasan yaxo late yasan wani ya rigashi don
babu yadda xa’a yi kyakkyawa kamata na rasa wanda ya mace min.
Axixa ta yi dariya tace Mahmud kam ya yi gaskiya sadik ya riga shi atika tace wane Sadiq? Ai
munyi baram baram. Kifkifta idon da munnira ta ke yiwa atika shi ne ya tunatar da ita gargadin
da mahaifinta yayi musu. Atika tace a ranta ai kuwa Baba yayi gaskiya daya ce min me shegen
surutu gashi har na manta na fara xuba axixa bata lura da kifta idon da munnira tayiwa atika ba
sai taji kawai atika ta yi shiru, da ta dauko hira, axixa ta gyara xama tace meye ke kuwa xai sa
kuyi baram baram da sadik. Shi da baya son bacin ranki? Atika ta kasa bawa axixa wannan
amsa, munnira ceta yi caraf tace karyar atika ce, babu abinda ya hadasu da sadik yanxu muka
rabu dasu, har mubarak dinma.
Axixa tayi wani kagaggen murmushi da kyar tace yau saura kwana goma sha biyar su mubarak
su fitar da mujallarsu ko? Ragas kake ji a xuciyar atika da munnira, munnira ta nisa tace axxy
wato ke duk sasantawar da akayi tsakanin daddyn mubarak da daddyn ki baki sani ba? . atika
ta gyra xama tace ai alhaji isah da kansa yaje ya sami daddynki ya bashi hakuri suka ce sunsan
sunyi kuskure abubuwan da suka fada, mujallu kuwa duk an kone su xance ya wuce. Munnira
ta kara da cewa ai shi ne yanxu mubarak ya xo yake ce mana yaya xaiyi ya xo wajenki yana jin
kunyarki, mu tayashi baki hakuri yasan ya yi kuskure, ya kuma yarda ciki nasa ne. axixa ta
kyalkyale da dariya ta sake kallon fuskokinsu ta sake tuntsirewa da dariya harda kwalla takeyi
dan dariya, farin ciki ya kama su munnira wato su gasu masu iya tsara maganar kwantar da
hankali. A tunaninsu axixa ta tsaru da tsarin da suka yi mata, gashi har hankalinta ya kwanta
axixa ta lafa da dariya tace ina jinku wato yanxu xance ya wuce mubarak da mahaifinsa sun ce
dai cikin nasu ne dai ko? Atika ta yi murmushin dadi tace kwarai kuwa axixa tace to yaushe ne
bikinmu don nafi so na haifar masa dansa a gidan sa? Munnira tace to ai duk sai kin samu sauki
ne naji an fara tsara yadda xa a yi bikinku wai sai kin warware.
Axixa ta sake tunstirewa da dariya ta ce makaryata. Yaushe kuka kware da karya ban sani ba?
suka tsaya cirko cirko can atika tace au baki yarda ba? yaushe muka taba yi miki karya?
Axixa tace yau dai kun fara daga jin wannan kalamai naku kakaf abinda xaku xo min dashi ne,
kawai don hankalina ya kwanta, to na gane ku karya ne har abada alhaji isah da mubarak ba xa
su taba amincewa da cikin ba, mubarak kuma yanxu ya sami sabuwar budurwarsa sumayya
tajuddeen Emanuel ‘yar gidan gwamnan lagos radau kake jin bugun faduwar gaba a tare dasu
atika, suka yi tsit basu da ta cewa. Ta ci gaba da cewa tunda alhaji isah ya furta sai ya fitar da
mujallun nan harda sa rana kuwa, gashi yau saura kwana goma sha, babu wani xancen sulhu,
axixa ta daddaka musu dundu a kai tace kawayena ku saki jikinku muyi hira kunji ni ku sake,
babu wata Magana da xata gigita ni, don haka muyi labarin gskiya da gaskiya. ta sake yin
dariya, ta sake tambayarsu, suka biye mata suna yiwa kansu da kansu dariya, atika tace
shegiya axixa wato kin gane mu shi ne don kanki kika ci gaba da bugun cikinmu ko? Wallahi
karya bata da dadi musamman idan aka kamaka. Munnira tace ai shi yasa ake cewa ramin
karya kurarre ne. mu kam yau an kama mu, yanxu dan Allah wane munafiki ne har ya xo ya
baki labarin mubarak da sumayya? Axixa tace mubarak ne ya fada min a waya, atika tace
wannan mubarak din ya cika marar mutunci nifa shi yasa kika ga muna jin tsoron Mahmud
sa’ad da yaketa binmu daxu na dauka ire iren su mubarak ne.
Axixa ta yi tsaki ta kau da kai t ace meye kuwa mubarak xai iya yi muku ko ni da muka yi haka
dashi ya isa ya hana ni yawo a garin Abuja, ai da shi da ubansa duk basu isa ba, su din me?
Don haka kuje duk inda kuke so babu abinda ya isa yayi muku. To ku meye ma ya hadaku
dashi? Ba ni yake fada don haka bai shafe ku ba. ga abokansa samarin ku dole xaku
haduwa, kuyi gaisawar mutunci, ni wallahi bana so ku dauki gaba da mubarak a kaina. Atika ta
tabe baki tace in gaya miki gaskiya mun bata dasu sadik, mubarak ya xugasu sunxo munyi
baram baram. Atika ta kwashe labarin yadda suka yi da sadik kakaf ta gayawa aixa kamar dai
yadda ta bawa munnira labari a mota.
Axix tayi murmushi tace amma atika akwai ki da wulakanci wato beran gidanmu ya fi sadik
matsayi a wajenki kenan lallai dole sadik yaji haushi duk irin son day a nuna miki. Munnira ta yi
dariya tace to ai atika da sauki tayiwa sadik, ni kuwa jiya jiyanan juma’a muka yi rashin mutunci
dashi ibarahim ya fada min inda xaki xaki san mutum daya ne ya turo su, kuma shi kadai ya xo
min babu dan rakiya. Ana saukowa daga masallacin juma’a sai gashi a gidanmu na fito ina
wasa da willi dog Karen gidanmu. Kinsan masifaffen kare ne, yana ganin Ibrahim kamar ya san
da abinda ya xo dashi sai yahau gurani Ibrahim yana so yayi masa haushi na tura shi cikin
gidansa na kulle. Na kalli ibarahim na dan masa murmushi sai naga yayi fuska ya bata rai, nace
mu shiga cikin gida yanda muka saba hira, sai yace no, nanma ya isa. Na xo ne na ganki xan
wuce gida yanxu daga masallacin juma’a nake, nace to nagode da ka xo ka ganni, sai yace ni
kuwa daman ina so nayi miki wata Magana akan abubuwan da yake faruwa tsakanin axixa da
mubarak bana so ki shiga maganar nan dai dana ga maganar tasa babu layi kawai dinbin son
kai ne, da kuma mubarak ya aiko shi, na taka masa birki domin ya fito fili ne yace wai na rabu
da axixa , kawai na kira masa willi dog ya bi Ibrahim a guje sai ga ibarhim a cikin ruwan
sweeming pool din nan willi ma ya fada ya bishi. Ni kuwa me xan yi banda dariya na kwallawa
kannena kira suka yo waje sai kyakyacewa muke, sallau mai gadi ne ya bani haushi hard a
tahowa a guje ya rike willi dog, ya fito tsamo tsamo daga ruwa abin kunya, axixa da atika suka
kwashe da dariya suka yi dariya har cikinsu yayi ciwo. Munnira tace aini sai ranar nasan kare
ashe yana da matukar amfani ai willi dog yayi min komai daya raraka Ibrahim.
Wannan maganar da munnira ta fada ta likewa axixa a rai da tace kare ashe yana da amfani
axixa tace a ranta, hakika yana da amfani don na wulakanta ashruf har na xamar dashi kare
saboda shi ne wulakantacciyar dabbb , daga karshe shi ya koyamin abinda ni bil adama ban
sani ba, gashi kuma ya jefa ni cikin tashin hankali da rudani bani kadai ba harda iyayena da duk
sauran al’ummar kasar nan masoyanmu, Nigeria xata shiga rudani shi yasa xata rikice kwata
kwata duk a dalilin mutumin da na dauke shi a matsayin kare, sai nan da nan ta canja yayin da
suka lura wani tunanin bacin rai ne ya rufe axixa, dariyar da take yi ta tsaya cak ranta yabaci
lallai kare yana da amfani axixa ta fada a bayyane ba tare da ta san tunanin da take yi a
xuciyarta ne ya fito fili ba. atika tace axixa meye? Ta dago ta kalle su taga sun daina hirar da
suke yi sun tsaya suna kallonta. Ta yi murmushi tace me kuka gani?
Munnira tace ji muka yi kina maimaita abinda nace ashe kare yana da amfani, sai muka ji kince
lallai kare yana da amfani. Axixa ta yi shiru don ta dauka a xuciyarta ta fada ashe sunji, sanna
tace a'a karan ne ya burge ni da yayiwa ibarahim haka shi ne nace lallai kare yana da amfani.
Ta gyara xama don su ci gaba da hirarsu itama axixa ta basu labarin yadda