Showing 3001 words to 6000 words out of 73529 words

Chapter 2 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3581

komai dai da aka sani ana
samu a daki. Ga wani katafaren falo wanda ya kunshi komai da komai na kayan kallo da
kujerun alfarma da dardumai masu laushin takawa, ga dakin cin abinci shima daban yake a
tsakanin falo yake da kicin, inka shige cikin jirgin sai ka rantse ka ce a wani gidan kake
hadadde mai kyan gaske.

Idan ka hau sama wani katon fili ne budadde nan da kujerun shakatawa iri-iri kuma anan ne
xaka dinga ganin ruwa don wajen a bude yake kawai da karfe aka agaye filin. A nan xaka ji
wata iska mai sanyi da kamshin ruwa suna tashi na alfarma. Duk da wannan fadi da girma
sama da kasa na jirgin bai kare ba, akwai kuma can karkashin jirgin shima akwai wata na’ura da
xata kai ka can kasan jirgin misali idan suna so su yi wanka a ruwan akwai kataferen
xagayyayen wajen wanka wato (sweeming pool) da kuma wani bangare da ake jifge wasu

kananan jiregen ruwa masu kama da balo buga musu iska ake yi amma da akwai bangaren
injin da ake jonawa da gas suke amfani su kuma idan matafiyan suna son su xagayawa cikin
ruwa suke shiga suna xaxxagawa cikinsa ko in sun hango wani tsibiri ko wani gari a gefen ruwa
suna so su sauka su ga al’adar ‘yan garin ko kuma su ga yanayin wani abu to shi ne ake yin
ampani da wadannan kananan jirage. Suna da masifar gudu ainun don kallon wani abu suka
tsaya yi a wani gari da yake bakin ruwa kuma a jirgin ya wuce da kamar awa to a cikin dan
kankanin lokaci wadanda suke cikin dan karamin jirgin nan xasu iya xuwa su sami babban jirgin.
Babban jirgin shi baya tsayuwa a ko’ina sai kamar a wata kasar da take da tashar jirgin ruwa
kuma matafiyan sun ce suna so su tsaya a kasar da dai makamantan wannan.

Su axixa sun yi wajen awa biyu cikin jirgi da fara tafiya kuma su duka suna xaune ne a wannan
kataferen falon suna kallon talabijin. Axixa ta matsa kararrawa ma’ana mai aiki daya ya xo tana
son wani abu. Ashruf cikin sauri ya shigo cikin ladabi da fargaba yace, gani axixa ta yatsine
fuska tace babu mutum sai kai? Ashruf bai gane abinda take nufi ba, yace ai ni ne daman xan
dinga yi muku aike-aike na dauko muku duk abinda kuke so, sauran ai su suna kicin su suke
dafawa ni kuma xan dinga miko muku. Axixa tace ina nufin mutum nake kira ba kare ba, ahsruf
ya sunkuyar da kai ya ma rasa mai xai ce mata.

Kowa ya kurawa axixa ido yana kallo da alama babu wanda ya ji dadin abinda ta yiwa ashruf.
Amma saboda ita babu wanda ya isa da ita sai kowa ya yi shiru yana kallonta. Can ta nisa ta
kurbi lemo tace, to tun da sai kai kadai (guldo) sunan kare ne. guldo to ina so gasashsshen kifi
marar kaya da yawa a tsaga cikin a xuba albasa da tumatur da yaji a gasa a gudansa a kawo
min kar a wuce minti ashirin da hudu. Ashruf ya juya xai fice sai ya ji tana kira, irin kiran nan da
ake yiwa kare. Ashruf bai juyo ba sai ya ji ta daka masa tsawa tace, ba ka san kiranka nake yi
ba ma ko?
Ashruf ya juyo a fusace yace sunana ashruf kuma kiran kare na ji kina yi shi yasa ban juyo ba.
ashruf na rufe bakinsa sai ga mr Johnson a gabansa ya bata rai kai ka ce an aiko masa da
mala’ikan mutuwa ne, duk wannan wasa da dariyar ta mr Johnson ya dakawa ashruf tsawa
yace ya fice ya bashi waje. Ashruf ya fice cike da kunar xuci, ya nufi kicin a fusace, kuku nan
suka lura da ran ashruf a bace yake, mummunan baci kuwa sai suka shiga tambayarsa me ke
faruwa ko dai mutuniyar taka ce?
Dake duk wanda ya san ashruf ya san shi da gudun cin mutuncin axixa a wannan tafiya.

Ashruf yace bakar dagar nan ce take son ku gasa mata kifi cikin rawar jiki suka bude firij suka
dauko irin kifin daya fasalta musu suna gyarawa suna tambayar ashruf me ta yi maka kuma
ranka yabaci. Ashruf y ace ban taba yin kisa ba amma ina ganin daga kan makiyiyar nan tawa
xan fara in ya so idan na kasheta nima a kashe ni. Daya daga cikin kukun ya yi sauri ya taryi
maganar ashruf yace yi shiru ka daina fadar haka abokina bacin rai ne amma ai ba xa ka iya
kasheta ba kuma komai lokaci ne nan da ‘yan kwanaki ko wata xaku rabu watakila ma kai da ita
babu wanda xai kara ganin wani, koda yake suma bakar fata ne kaima haka watakila kasar ku
ma daya idan aka bi tarihi. Ashruf yace ita daga Nigeria take ni kuma daga jamaika nake babu
hadinmu. Yana rufe baki sai ga mr Johnson ya bugo kofa ya shigo yace kuwa da wa Allah Ya
hadani in bada kai ba, ya hau ashruf da fada fa,fa,fa kamar xai hadiye shi. Ashruf dai ya

sunkuyar da kai kasa yana sauraron kawai.

Mr Johnson ya ci gaba da cewa ba ka dauki duk abubuwan da na dinga gaya maka ba ko? To
a kan axixa xa ka iya rasa aikinka, don haka ka kiyaye! Cikin ladabi ashruf yace xan kiyaye mai
gidana, kuma don Allah ka yi hakuri ba xan sake ba. washegari da duku-duku ashruf ya dauki
komar kama kifinsa ya dulmiya cikin ruwa yana ta kokarin kama kifaye. Sai can ya yunkuro ya
fito dauke da kifi himili guda a cikin koma a kafadarsa ya hayo jirgi ya shigo cikin jirgin sai ko
suka yi ido hudu da axixa wacce ta harde akan wata kujerar shakatawa da kofin lemo a
hannunta da jarida tana karantawa a kusa da ita kuma abin kaunar ta ne, Mubarak yana kan
keken wasa jini yana tattakawa. Ashruf ya duka ya gaishesu, Mubarak ya amsa amma ban da
mutuniyar ko kallonsa bata yi ba. ashruf ya jawo daron da yake wanke kifi ya fara dauko kifayen
nan daga cikin koma yana datsasu tunda da ransu suna tsalle-tsalle, in ya datsa da wuka sai ya
jefa cikin daron wanda yake a cike da ruwa. Axixa ta yatsine fuska ta kalli Mubarak tace wannan
kuma mai ake yi ne?
daga ina ya samo kifi haka masu rai?

Mubarak yace ina nan tunda asuba naga ya fito ga sanyin asubar nan na tambayeshi yace
mun kifi xai kamo yake gaya min shi daman aikin sa don ya dinga kamo kifi ne kawai don haka
duk kifin da matafiya suke ci to sabon kamawa ne. axixa tace wadansu mutanen basu da
hankali kuma basa gudun wahala. Yanxu yaya xa a yi mutum ya fito tun da asuba ya shiga ruwa
ga sanyi ya kamo kifi kawai, nawa xa a biya shi? Mai xai samu? Mutane su suke jawa kansu
talauci da kansu saisu dorawa gwamnati ko kuma masu kudi alhali kuma su suke jawa kansu
talauci, ga dai wahalallen rigarsa a yage kansa duk a cukurkude yana tafe ciki a shamule kai ka
ce bai taba cin abinci ba, da ka gan shi ka ga talauci amma kuma kullum baya hutawa a bauta
yake.

Bai kuma sami kudin ba. Mubarak ya nisa cikin harshen hausa yace, axixa idan xamu yi
Magana irin wannan a gaban wadanan mutane to mu canja harshen hausa tunda basa jin
hausa amma idan da turanci ne suna ji saisu dauka ci musu mutunci muke yi. Axixa ta gallawa
Mubarak wata matsiyaciyar harara cikin harshen turanci tace da turanci na saba Magana kuma
da turanci xan ci gaba ba xan yi hausa ba in wahalar da kaina. Dan su ji daman nake fada.
Ashruf a durkushe yake kawai kamar yana gyaran kifi amma sauraronsu yake yi kawai, duk a
bubuwanda axixa ta ke yi masa na cin mutuncin bai taba jin ya tsaneta ba, sai dai ya tsani
halinta, ba kamar a wannan lokacin, yayi shiru yana tunani bai san sanda hawaye ya rinka
kwaranyowa daga idanuwan sa ba, ya tausayawa kansa da kansa yace, a ransa wannan bata
san Allah bane mai axurtawa? Kuma Shine mai talautawa, yace, da na san inda xani inyi kudi
lokaci daya ta hanyar halak daba xan xo ina ta wahalar da kai naba.

Can kamar a mafarki ya ji tana kira irin na karnuka ya ji tace guldo! Guldo kira nake fa.
Mubarak yace malam ahsrauf xo nan. Ashruf ya taso ya xo wajen Mubarak yace yes sir. Axixa
ta yi caraf tace yes ma because I’m the one calling you, I need something cool not cold. Ashruf
ya kurawa axixa ido yana cewa a xuciyarsa inama-inama badan gudun hukuma ba kuma ‘yan
nan kasar babu ruwansu da mai gaskiya mai kudi kawai da na shake yarinyar nan yau data

gayawa ‘yan garinsu.
Mubarak yace jeka mana ba Magana take yi maka ba, ka kura mata ido ko kuma ba xa ka je ba
ne?
ashruf ya nisa ya duka yace, sorry sir! Ya juya xai tafi, sai axixa tace guildo xo nan. Ashruf ya
dawo tace, ba xan iya shan abun hannunka ba, da yagaggiyar rigar nan taka mai karni a cikin
sakan ashirin da hudu nake so ka yi wanka ka canja kaya ka kuma kawomin abu mai sanyi in
sha.
Ashruf ya juya ya nufi dakinsu cikin sauri yayi wanka ya kuma canja kayan ya shiga kicin ya
dauko musu lemo da kofuna biyu ya kawo musu. Axixa ta kalleshi daga sama har kasa ta kuma
kalli agogo. Ta ce, nace sakon ashirin da hudu yanxu ka yi minti ashirin da hudu, ashruf ya
sunkuyar da kai kasa takaici marar misaltuwa suka lullube xuciyarsa yace I’m sorry, ya duka ya
ajiye musu lemon da kofuna akan tebur ya juya xai tafi. Axixa ta yi fito tace, guldo, ashruf ya
juyo ya dawo sai ta kurawa gaban rigarsa ido ta kece da dariya. Ashruf shima sai ya kalli inda
take kallo a kirjinsa tana dariya amma sai ya ya rasa abin dariya, rigarsa t-shirt far ace sol a
wanke to me abun dariya a jikinta kuma! Axixa ta yi ta dariyar har Mubarak ya dinga kallon ta
shima bai san abinda take yiwa dariya ba, amma kuma dariyar sai take bawa dariyar sa dariya,
axixa ta gama dariyarta tace guldo kana da ‘yaya ne?
ashruf yace eh, ina da ‘yaya. Axixa tace, shi yasa ka sayo riga mai hoton ‘yan aljanu wato
(catoons) kamar wani yaro to ko su ‘y’yanka ka soyowa ta yi musu yawa don kar ka yi asara
kake saka kayan ka?

Ashruf ya ji kamar ta daba masa wuka a ransa yayi shiru yana sauraronta tagama masa
iskancin da taga dama ta sallame shi ya wuce cike da takaici ya nufi dakinsu yana xuwa ya
sake tube wadannan wankakkun kaya ya sake sa yagaggu masu karni na aiki ya dawo ya ci
gaba da aikin wanke kifinsa. Axixa tace da Mubarak darling ka ga abinda nake gaya maka ko
shi talaka kullum a matsiyacinsa yake ya fi so a ringa ganinsa a cikin tsiya da talauci shi yasa
na tsani talakawa musamman wannan. Ta nuna ashruf ya juyo a fusace yana kallonta.

Axixa ta yi shiru tana tunani a ranta tace, wannan mutumin daya sami fili irin kallon nan da yake
min daya faffallamun mari koma ya shekeni don naga daga kallon da yake min ya ji haushi tace
amma sai dai ka mutu ni kuma daga yau xan sa kafar wando daya dashi

ina bakatar nadunga samun comment dari biyar a wannan kayataccen littafin domin somin
tabine nagani sainajiku naku a kullum maidebemiki kewa
Abdul Dboy
Bauchi state
[8/28, 9:41 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[8/28, 9:44 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU.
*2*
.
.

Hantsi sakaliya rana ta fara fitowa su atika da suke ta barci ciki ya fara kiran ciroma duk sun
tattashi. Bayan sun yi sallah, sun yi wanka sun yi brush sun tattaru a dakin cin abinci su axixa
ma sun shigo. Ashruf tuni ya fara aikin jera musu abinci iri-iri a kan tebur.
Bayan ya kawo musu komai da komai xai fita sai ya ji mutumiyar tasa ta mike da gudu tana
kakakin amai ta nufi shara ta tofar da abinda ta sa a bakinta, Mubarak da sauran duk sun mike
a hargitse suna tambayarta lafiya?
Bayan da axixa ta gama ‘yan tofe tofenta aka bata ruwa ta kuskure bakinta sai ta dawo ta xauna
tace da ashruf xo nan. Ashruf ya matso yace ga ni, axixa ta daka masa tsawa tace yau wane
irin kifi ka kamo mana marar dadi?
Ashruf yace a wajen dafawar sane suka cika gishiri! Axixa tace kifin ne kansa bashi da dadi ya
fara rubewa don haka a canjo min wasu. Ashruf ya kinkima ya nufi kicin. Mr Johnson da sauran
kuku suka xo suka kewaye kwanon kifin nan a cike da mamakin me ya sa aka dawo dashi?
Ko ci basu yi ba bayan irin shirya shi din da akayi, yayi dadi. Mr Johnson yace, ashruf lafiya?
Ashruf yace tace kifin babu dadi. Mr Johnson ya dauki cokali ya gutsira ya dandanan ya ji dadi,
dadin ma mai xakakwa don shi ya dade bai ji irin wannan dahuwa mai dadin wannan kifin ba.

Ashruf yace, ranka ya dade yaya ka ji kifin?
Mr Johnson ya nisa yace kifin kam da dadi don ko maki aka ce in bawa kifin nan xan bashi
sama da casa’in a cikin dari. Koda yake babu komai masu kudi ne komai suka maka ka yi
murmushi ka basu abinda suke so. Ka xamar da kanka tamkar wawa wanda baka san abinda
kake ba, don su bamu kudinsu mu kuma idan muka tashi karbar kudinsu sai mu yi ta karba su yi
ta miko mana su kuma kamar wawaye. Ashruf miko wani kwanon. Ashruf ya mikowa mr
Johnson wani kwano na tangaran mai kyan gaske, wanda ya fi na farkon kyau mr Johnson ya
juye kayatacciyar miyar kifin nan a ciki ya cewa ashruf ya dauko ya biyoshi dashi. Ashruf ya
kinkima yana biye da mr Johnson har dakin cin abinci inda su axixa suke. Axixa tana ta faman
yiwa Mubarak babbalin masifa wai yana xaune yana kallon irin abubuwan da ashruf yake yi
mata baya Magana shi kuwa yana ta lallashinta shi da abokansa su Ibrahim da kawayenta su
atika.

Su mr Johnson suka shigo, ya gaishe su sannan ya matsa kusa da axixa ya duka yace, mai
girma axixa ki yi hakuri kifin da yaran nan ashruf ya kawo muku bashi da kyau ashe. To gashi a
cikin gaggawa an yi sauri an dafa muku wani. Mr Johnson ya karbi kwanon kifi daga hannun
ashruf ya mika kan tebur a gaban axixa yana ta faman yi mata murmushin kwantar da hankali.
Axixa ta yatsuna fuska tace da mr Johnson bude mun in ga irin wannan din, mr Johnson cikin
rawar jiki ya bude sai ya ga axixa ta kawar da kai ta tashe hanci tace mr Johnson matsar min da
kifin nan daga gabana na gane irin na daxu ne. to in har ba xa ku iya ciyar da ni ba irin abinda
nake so xan ringa fita kasuwa bakin ruwa ina siyo abinda nake so ina dafawa. Mr Johnson yayi
sauri ya tari maganar da take yace haba madam axixa ki daina fadin haka yanxu ko daya daga
cikinmu kike so a dafa miki ba a dafa miki ba balle kifi?
Mr Johnson yayi murmushi yace to yanxu ranki ya dade me kike so cikin minti ashirin da hudu
adafa miki kiyi hakuri axixa mu da ku muke alfahari muna sonku amma mun fi son kudinku.
Ashruf babu abinda yake yi sai kallon mr Johnson yake wani yashe baki yana wani murmushi
waishi a dole ya xamar da kansa wawa saboda yana son kudinsu. Ashruf yace a ransa ina xan

iya yiwa wannan makiyiyar nan tawa wannan murmushi tana ci mun mutunci ai ina ganin xan
rasa aikina akan wannan yarinya. Maganar axixa ce ta farfado dashi daga tunanin da yake ya ji
tace wannan kifin da ya kawo mana ne bana son irin sa, irin wanda nake so yanxun nan ya
shiga ruwa ya kamo min kananan kifaye, jarirai ba iyaye ba. mr Johnson yayi murmushi yace,
an gama. Ashruf ka ji maxa-maxa ka je ka dauko komarka ka shiga ruwa yanxun nan ka kamo
kifaye kanana. Ashruf yace, to amma yanxu kamun irin wadannan kifi yana da wahala da dai da
asuba ne yanxu rana ta yi duk sun watse sun yi kasan ruwa. Mr Johnson ya ce ita kuma su take
so. Axixa ta karasa da cewa a yanxu kuma.

Ashruf ya wuce sumi-sumi a cikin sanyin jiki ya nufi wajen da yake ajiyar komarsa ya dauko
karamin jirgin da yake hawa ya tafi kamun kifin yahau ya tafi cike da takaici ga yunwa danko
karyawa bai yi ba.
Ashruf bai dawo ba saida la’asar sakaliya ya kuwa ciko daro da kifi irin wanda tace tana so ya
wanke su anan kan barandar jirgin ya dauko xai kai kicin sai ya ci karo da axixa ta fito daga
wani daki a guje da kofin lemo a hannunta tana dariya, cikin dakin kuma ga sautin kida nan da
alama ma dai rawa suke ko wani party, kuma gudun da ta yi ta yo waje watakila ita da darling
dinta ne ko kuma kawayenta ta tsokana ta yo waje saura kiris Ashruf

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login