Showing 57001 words to 60000 words out of 73529 words

Chapter 20 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3596

ya ganni sanda na turasu-a mota kuma yaya basu mutu ba?
Alkali mai shari’a yana ta buga guduma akan Alhaji Isa Elyakub yayi shiru amma yaki.
Alhaji ahmed ya kira elyakubu ya kira dan sanda day ya ce ya shiga wani daki da yeke wajen
kotun ya shigi da Alhaji Elmustapha. Waigawar nan da alhaji isa zaiyi sai ya hango alhaji

elmustapha ya tunkaroshi akan kekensa na guragu nan kaji bakin alhaji isa elyakubu ya mutu
rumus ya rasa ta cewa nan aka hau kallon kallo to fa!!! Alkali mai shari’a ya umarci Alhaji
Elmustapha ya fadi dalilin da yake darar Alhaji isa Elyakub da kansa don ya ji da kunnensa
Alhaji Elmustapha ya fara da bismilla sannan ya fara zuba dogon turanci kai ka ce bush ne
shugaban kasar America da kansa kasancewar zaman da ya yi America ya sa ya fi jin turanci
har kamar fiye da yaransa hausa. Ya yi dalla dalla yana fadar labarinsa yana fadar kwanan
watan da lokacin da kuma lambobin takardunsa na gidaje, na motoci da account number sa
turkashi! Alhaji isa ya rasa ta cewa alkali ya juya alkali alhaji isa ya ce ‘’to kaji fa abinda ya
fada’’. Alhaji isa ya yi tsaki ya kawar da kai ya ce ‘’duk karya yake min duk shirri ne makiyana
suka yi hayarsu don agan na tozarta ni ba nine takaka ba, idan kuma sunce nine waye
shaidarsu a sanda abin ya faru?”
Alhaji Elmustapha ya ce “bani da shaida sai allah, allah shi ne shaidata sannan matata wacce
nace tunda hatsarin ya faru take tabin hankali bau sunnan wanda take iya tunawa daga Zubaida
‘yarta da ta rasu sai takaka ita kadai ta isa shaida idan shi ne takaka zata nun shi”. Alkali mai
shari’a ya ce ‘’aje a shigo da ita’’. Dan sanda ya fita ya taho da ita. Hajiya fatima ta bawa duk
wani mai imani da yake zaune a kotun nan tausayi da daga gannin ta tasha wuta a rayuwarta.
Tazo gaban mijinta ta tsaya; alkali mai shari’a ya ce “ mallama ki fada mana cikakken sunnaki
sannan ki fada mana abinda kika sa ni game da alhaji isa elyajib’’ . ta yi shiru kamar bada ita
yake magana ba bata kalli inda yake ba balle ta saurari abinda yake cewa balle har ta bashi
amsa alhaji elmustapha ya ce ‘’ai bata gane magana kuma ita bata magana sai jifa jifa’’. Alhaji
elmustapha ya kama hannun matarsa ya jata har gaban Takaka cikin harwshen larabci ya ce
“Fatima waye wannan karon farko ta daga kai ta kalli Takaka”. Cikin harrshen turanci ya sake
cewa suka dau dan lkacin suna kallon juna. Yau ne rana ta farko da Fatima ta fara tuna wani
abu a kwakwalwarta don tunda suka yi hatsarin nan bata taba tuna wani abu a suka yi hatsarin
nan taba tata tuna wani abu a kwakwalwarta ba ita dai gata nan ce kawai. Ta rike kai sai jiri take
ji yayin da take kokain tuno wani abu da ta sa ni da. Ta sake dagowa ta kalli Takaka bakinta ya
hau karkarwa ha’waye ya dinga zubowa daga idanuwan tana nuna shi da hannu tana ja da
baya can ta kwalla ihu ta rirrike mijinta tana magana cikin harshen turanci ta ce “Malam boyeni,
boyeni”. Takaka ya sake zazzare mata jajayen idanuwan nana nasa babu abinda a tuna sai
lokacin da aka kawo shi farkon zuwansa gidansu haka ya dinga zare ido yana kallonsu wai shi
bakauye yazo yaga America.. Ta fara ihu tana cewa “Wannan ne, wanann ne”. Ta ci gaba da
kallon Takaka daga karshe ta tunano lokacin da Takaka ya kaisu bakin rami ya ajiyesu a cikin
mota ya ce zaije ya yi fitsari ya fito daga cikin motar ya tafi yana zuge zugen tazuge koda ya yi
fito sai ga wata katuwar tirela ta tunkarosu ta angaza motarsu suka fara wuwwuntsilawa. Sai ko
ta sake rafsa wani ihu ta fadi kasa tana cewa “Takaka ne ya turamu a rami ni da Zubaida ta yi ta
surutai tana kara mijinta ya gurgur da kekensa wajen da take kwance ya fara yi mata magana
ya rukota ya tasheta zaune sannan ta tsagaita da ihun da take. Tausayinta ya sa jama hawaye
musamman Aziza da kuka ta fashe don tausayin mahaifiya masoyinta. Nan take Allah (S.W.T)
ya ma tsa Alhaji Isa Elyakub da farko ya fara kyalkyalewa da dariya yayi ta dariya kamara tabab
sai ya fara fada da kansa abin kamar almara ya fadi duk abinda ya faru tsakaninsa da Alhaji
Elmustapha har yadda ya yi niyyar ya hallakar da su a tunaninsa ya dauka sun dade da mutawa
ya fadi dalla dalla hanyar da yabi ya kwashe takardun dukiyar Alhaji Elmustapha ya ce har
yanzu kanfanonin da Alhaji Elmustapha ya zuba hannayen jari yana nan yana karbar riba sai

dai wasu an canja sunayen. Daya bayan daya dinga fadar ribar da suke bashi a shekara. Na
America daban wani a kasar England wasu a Germany da France kuma da sunan Elmustapha
a takardun har yanzu.
Alhaji Elmustapha ya nem kotu da ta fitar masa da hakkinsa dan iyalansa na musifar da Alhaji
Isa Elyakub (Takaka) ya jefa su na niyyar halakar da su da ya yi sannan ya roki kotu data karbar
masa dukiyoyinsa da Takaka ya kwashe masa ya kara da cewa ayi lissafin ribar da bankuna da
kamfanonin da ya zuba hannayen jari suka bawa Takaka har tsawon shekaru ashirin da hudu
ya biya shi sannan ya bashi kudin motoci da gidaje da ya sayar shima ya biya kudin. Alkali mai
shari’a daga karshe ya yi na’am da wannan koke na Elmustapha ya yi masa alkawarin zasu
lissafa yadda wadannan kudade suke za a biya shi. Nan da kwana ashirin da hudu su dawo don
ci gaba da wannan shari’a. alkali ya tashi ya fita ‘yan sanda suka sa Alhaji Isa a gaba suka fita
da shi zuwa inda yake a tsare. Su alhaji ahmed ma suka nufi gida, Aziza da munira da atika
suan fitowa suka doshi motar da suka zo a ciki a motar aziza ce ke tukawa suna tafe suna hira
yau farin ciki ne a zuciyarsu ganin allah ya tonawa alhaji isa elyakub asiri. Musamman aziza tayi
matukar murna ganin ashrug dinta zai sami nutsuwan a zuciyarsa ga dukiyarsu zata dawo babu
wani abu dayake damun aziza a yanzu banda wata biza da ya rasa, kawai don tace idan ya tafi
kada ya dawo shi ne yaki dawowa.
Aziza bata tsaya a ko ina ba sai a gidan su atika. Atika ta ce dama a gidanku muka sauka mun
yi da mahmud sa’ad zaije can ya sameni. Dr. Rislan ma zaije can wajen munira’’ aziza ta ce
wato acan kuke labewa kuna zance ko ya saina gayawa su mama ince kunyi samiri ku na boye
musu’’. Atika ta ce ‘’dan allah aziza yi hakuri karki fadawa miji su aure zasu yi min’’.Aziza ta ce
kuma ke be auren yayan nawa zaki ba kenan?’’
Atika ta ce ‘’Ba haka ba ne, kin gane ina so in gama darantar guy din ne in san how much loves
me don ina sona auri miji mai tsananin sona fiye da yadda nake sonsa. Na lura da hakan
Mahmu na sona amma ina so in sake sanin hakan”. Munnira ta nisa ta ce “Ke kina ba da wata
hujja marar kan gado so ai da ya ne, ni abinda yasa bana so a gida a san Doctor Rislan shine
don in koyi zurfin ciki irin na Aziza sai soyayyarmu ta yi nisa ta nuna daf da mun gama shirin yin
aure sai ince Abba, Umma ga mijina sai suyi ta mamaki”. Su duka suka kyalkyale da dariya
Aziza ta ce “Ni dai Mama nake so in gani idan zaku tafi gidan mu ku dauki motarku. Tafi”.
Suka firfito daga motar suka nufi cikin gida, suna shiga ko zama basu yi ba sai ga Mama Atika
ta yi sallama ta shigo Aziza ta tafi ta rungumeta tana shagwaba kamar mai shirin fashewa da
kuka tana cewa “Mama gurinki fa nazo Allah Mama abin yana ta kara damuna”. Tayi muyarshi
ta shafa mata kai ta ce “Haba Aziza ‘yar Mama kada abin ya dameki zo muje daki ki gaya min”.
Atika da Munnira wadanda kansu ya daure basu gane kus kus din da Aziza take yi da Mama ba
suka yi wuf suma suka bisu cikin daki wai su ma sai sunji meye yake damun Aziza. Maman
Atika datse dakin taja hannaun Aziza zuwa kan gado suka zauna ta ce “Ya ya aka yi ne Aziza?”
Cikin shagwaba Aziza ta ce “Mama kinga Ashruf shiru yaki zuwa babansa ya ce wai biza ce bai
samu ba shi ya sa bai zo ba amma ni nasan ba haka bane don karya zo ya ganni ne kawai.
Dazu muna fitowa daga kotu ya bugowa dady na waya yana tambayar ya ya shari’ar ya ce a
bawa dadynsa suyi magana aka bashi ya ce a bawa Baba daga karshe ya ce a bawa abban
Munnira Allah Mama baice ina nake ba”. Tayi narai narai da ido zata yi kuka. Mama ta yi
murmushi ta ce “Haba Aziza kada kiyi kuka ki kwantar da hankalinki ki barni da case din zanyi
miki maganin matasalarki, da kinyi kuka a rashin Ashruf yanzu ma kiyi kuka ai abin zai yi miki

yawa. Ashruf ma yana sonki sosai tsoronki yake shi ya sa bai’ce ina kike ba tunda ga yadda
kuka rabu”. Atika ce take kwankwasa musu kofa Mama ta ce “Allah mai kwakwasa kofar nan
idan na bude zaki yi kuka”. Atika ta yi dariya ta ce “Mama ni ba labarinku zanji ba wayar Aziza
na kawo mata ta barta a falo dadynta ne yake so ya yi magana da ita”. Aziza ta mike da sauri ta
bude kofar ta karbi wayar. Dadynta ne ya ce “Hallo Azizyn dady kina ina?”
Ta langwabe kai ta ce “Ina gidan su Atika dad”.
Ya ce maza kizo kiga wani abin al’ajabi yanzun nan fa”. Ta yi tsalle ta ce Dady fadamin kafin in
zo”.
Ya ce “A’a sai kinzo zaki gani”. Ya kashe waya.
Ta zari dankwalinta da sauri ta ce da Maman Atika “Mama zan dawo da yamma dady ne ya ce
inzo yanzu”. Ta ce “To sai kinzo.” Aziza ta fita da sauri Atika da Munnira suma suka biyota
daman su haka suke so, suka duru a mota sai life camp inguwar su Aziza. Aziza da sauri ko
rufe mota bata yi ba ta fada cikin gida. A babban falo ta iske babanta a zaune da wata farar
mata mai kyawun gaske a gefe a zaune akan kujera. Aziza ta yi musu sallama ta tafi ta durkusa
a kusa da babanta ta ce “Dady gani nuna min abin al’ajabi”. Ya ce “Haba Aziza kamar wata ‘yar
karamar yarinya ki gaishe da bakuwa mana”. Aziza ta ce “Sannu ina yini”. Bakuwa ta yi
murmushi tace “Ban karbi gaisuwarki ba daga nan, zo nan mana Aziza”.
Aziza taji mamaki ya rufe ta ganin yadda matar take yi mata magana kamar ta santa. Ta taso
tazo ta zauna a kusa da matar ta mika mata hannu saka gaisa, matar ta girgiza kai alamar
tausayi ta ce “Allah sarki Aziza” Nan da nan kuma idanuwanta suka kawo hawaye. Aziza ta
sake shiga cikin duhu wacece wannan har take kokarin ta fashe mata da kuka? Alhaji Ahmed ya yi murmushi ya ce “Aziza sake kallon ta sosai zaki gane ta kinsanta fa”. Karon
farko Aziza ta yiwa matar nan kallon nutsuwa sosai ta kalleta sai kuwa ta tuno fuskar kanwar
mahaifiyarta ce uwa daya uba daya suke da mahaifyarta kamarsu daya sak da mahaifiyar
Aziza. “Aunty Sharifa sunanta. Rabon da Aziza ta sake ganita tun tana shekaru shida a lokacin
da mahaifiyarta ta rasu. A shekarar kuma aka yiwa Anti Sharifa aure a Lagos mijinta yake basu
shekara a Lagos ba aka turashi kasar Germany suka koma can da zama. Bayan shekaru biyar
da rasuwar Haijya Fatima mahaifiyar Aziza Allah Ya yiwa mahaifiyarsu rasuwa wato kakar Aziza
daman tuntuni mahaifinsu ya rasu. Anti Sharifa ta zo Nigeria a lokacin rasuwar amma Allah bai
yi sun hadu da Aziza a guru ba wajen rasuwar don su ‘yan guru ne. lokacin Aziza tana London
tana sakandire bata zo ba. Don haka Aziza tuni ta manta da yadda fusakar Anti Sharifa take
balle kuma ita Anti Sharifa ba zata gane Aziza ba. Amma me jini yasa kamarsu day kamar anti
sharifa kaki tayi na Aziza domin futik kamar su daya saboda Aziza da mahaifiyarta Hajiya
Fatima ta yi kama itama kuwa Anti Sharifa da yayarta tayi kama Hajiya Fatima soboda haka ne
suka yi kama daya. Da can su Aziza suna da lambar wayarta sukan yi waya amma daga baya
su Anti Shaifa suka tashi daga Germany zuwa India basu sake waya da su Aziza ba
kasancewar suma lambar da suka bata sun sake tunda suka dawo Abuja don da su Aziza a
Lagos suke suma. Shekara guda kenan da rasuwar mai gidan Anti Shairfa. Tayi waya mai
duguri garin su mijin tasanarwa iyayensa da ‘yan uwansa suka dunguma can aka bunneshi har
tafita daga takaba aka raba gado ‘yan uwansa suka dawo ita kuma ta kaura Saudia ta zauna a
can ta ci gaba da yin ibadunta a kasa mai tsarki saboda tsananin bakin cikin rayuwa. Taga me
zata zo gida Nigeria ta yi bayan bata da uwa balle uba, ga ‘yar uwarta Fatima wacce su biyu
mahaifansu suka haifa ta rasu, mininta mai ji da ita ya rasu basu da da ko daya. Tana Saudiya

ne sai ta fara tunanin ‘yar uwarta Aziza me zai hana ta zo ta ga Aziza ‘yarta ko saji dan sanyi
dukkaninsu. Shine ta zo Nigeria musamman don Aziza.
Cikin rawar murya Aziza ta ce “Aunty Sarifa ce?”
Sharifa ta fara zubar da hawaye ta ce “Aziza nice”. Sai suka rungume juna suka kankame
junansu saboda tsananin murna da jin dadi su duka kuka suke tamkar kwayar marigayiya. Alhaji
Ahmed ma ji yake tamkar a yau mai dakinsa ta rasu saboda ganin kanwarta ta juye sak
Fatimarsa kamarsu, kallonsu, maganarsu tafiyarsu duk iri daya. Allahu akbar hawaye ya ji taf a
cike a idanuwansa shima da yake zaune yana kallonsu sun rungume juna suna kaku. Alhaji
Ahmed ya yi karfin hali ya dinga lallashinsu sannan suka tsagaita da kukan. Daga karshe ya ce
da Aziza ta kaita daki da kayanta ta huta saboda tun safe tazo take zaman jiransu. Aziza da
Aunty Sharifa suka hau sama dakin Aziza a nan suka iske Munnaira da Atika suna ganin Aunty
Sharifa sai da gabansu ya yanke ya fadi saboda sunga kamarta da marigaiya Maman Aziza har
kamar ta baci, tun kafin Aziza ta gabatar da Aunty Sharifa ga kawayenta Munnira ta ce “Amma
wannan kanwar Mummy ce ko?” Aziza ta ce “Anty Sharifa ce wacca nake baku labarinta tuntuni
nace tana India wani lokaci har nace zanje India in nemeta dady ya hanani ai itace ta zo”. Su
duka suka ce “Oho Allah sarki” Cikin ladabi suka durkusa har kasa suka gaisheta. Aziza ta
gabatar kawayenta ga Antinta. Aziza ta nunawa Anti Sharifa bandaki don yin alwala azahar tayi.
Wayar Atika ce ta hau kara tana dauka taji muryar Mahmud Sa’ad ya iso ya ce ta fito. Tana
ajiyewa ta Munnira ma tayi kasa Dr. Rislan ne Cikin sauri suka fa da bandaki suka yi alwala
suka zo suka yi sallar azahar.
Suna idarwa suka fara dandasa kwalliya a fuska hoda, jagira wet lips da dai sauran kwalliye
kwalliye ta ‘yan mata. Wayar Munnita ta kara yin kara ta dauka ta duba Atika ta ce “To Doctor ya
gaji da jira kenan”.
Mannira ta ce “Aini banma san wannan lambar ba bari naji waye”.
Ta ce “Lafiya ban gane mai magana ba?”
Ya ce “Barista Hayat ne kin manta dazu a kotau kika bani lambarki.
ta ce ‘’oh barista ya ya aiki?’’ y ace ‘’da godiy, funnira kinsan ance kyan alkawari cikawa gani na
iso ina yajen get ‘a tsaye’’.
Ta ce ‘’to sannu da zuwa barista, ka shigo cikin get din hana barista ta tsaya daga wajen kamr
wani bako. Gamu an suwa yanzun nan’’. Suka ajiye waya. Aziza da atika haka hada ido suka
kyalkyale da dariya suka tafa. Aziza ta e ‘’munnira tsaya tsaya yaushe kika zama compus girl
har aike hada samari kala kala waye kuma barista?’’ Atika ta ce ‘’ke kince mata compus girl, player zaki ce hata lallai munnira har wani barista kika
samu shima kika tashi wannan lokacin ya zo don su hadu da dr. rislan. Yanzu haka zaki yiwa dr.
rislan? Munnira dai tsantsara hauri take a gaban mudubi sai murmushi take dawai. Da ta ama
daurin ta fara feshe duk jikinta da designers turaren da hake a shake akan mudubin masu
kamshi kala kala. Atika ta ye ‘’munnita meye haka? Sai kace wata amarya kike fesa ferare hark
ala kala ko kunya bakya ji kije gaban surayi ana kamshi bududu ai yasan shi kika fesawa ‘’.
Aziza t ace ke kuwa ta hada doctor da lauya ba dole ta kece raini ‘’.munnira dai sai kyalyyala
dariya take bat ace das u omnai ba ‘’atiku ta nisa ta ce ‘’bani waje kiga ni turare daya a ya
isheni in fesa saurayi dai ba miji ba, wai waye barista munnira kinga bana son neman maganan
da hada fada gaskiya zanyiwa Mahmud waya ince ya sameni a gida da ddare ba zan fita ba kar
inje a casu a gabana doctor da wuya ga daddy yana gida ya jiyo hayaniya ya leko yaga une

muka hada samari fada jeki ke kadai’’.
Munnira t ace ‘’dalla barista hayat ne fa ‘’. Atika ta ce me ya kawo shi in ba zance ba ‘’. Aziza ta
ce ‘’kai barista hayat yana da matukar kirki, ga tausayi, yana burgeni amma da zaki kulashi da
kin kyauta min ‘’. Munnira t

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login