Showing 12001 words to 15000 words out of 73529 words
Chapter 5 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf
Unknown
29 Jun 2025
3641
gani. Ashruf yace maxa tashi ki bar wajen nan kije ki kama bangaren ki don dakin kare daban da na
mutane. Axixa ta gallawa ashruf harara tace kai dai da kake kaine Karen ka fita ka kwana a
waje, ni in kwana a daki. Mari ne hukuncin dokarsa ta farko, saukarsa ta ji a fuskarta.
Axixa ta rike kunci ta tashi a sanyaye ba tare da tace masa komai ba, da kwalba a hannunta ta
nufi wajen ruwa, ta duri ruwa a ciki ta xagaya bayan dutsen ta kama ruwa ta xo ta yi alwala ta
jawo rigar sa da ta wanke ta yaba a jikinta ta harhada dai ta rufe gashin kanta ta tayar da
ikamar salla ba tare da ta tantance ina ne gabas take ba, ta dai kintata. Haka axixa ta yi ta jero
sallolin da bata yi ba, sanda suke jirgi, harta idar. Ta daga hannu sama tana rokar Allah
subhanahu wata’ala ya fitar da ita daga cikin wannan kangi, ya raba ta da sharrin ashruf.
Ta rushe da kuka tace nasan na wulakanta ashruf na kaskantar dashi amma ni kuma kasa ya
sassauta min. haka axixa ta yini tana a nan cikin yashi a xaune sai dai idan ta kintaci lokacin
sallah ya yi sai ta tashi ta yi, la’asr haka magriba ma haka. Da taga gari ya fara duhu sai ta fara
jin tsoro ta karaso wajen ashruf yake xaune. Shima yana jiran lokacin isha ta yi. Rigar ledannan
ta ruwa ya yaba a jikinsa akan gajeren wandon da yake jikinsa don ya leka xai dauki kayansa
ya sa ya iske tana sallah da su don babu yadda ya iya ya kyaleta ta ci darajar sallah, da yau ta
gaya wa aya xakinta. saboda xureren sanyin da yake surarowa daga cikin barkaken tekunan ga
duwatsu masu fitar da ruwa, sanyi wajen kamar kankara sai karkarwa sanyi suke. Can ba tare
da kowa yace da kowa komai ba, ashruf ya mike ya fara sallar isha, yayi ya idar ya kawo shafa’I
da wutirinsa a lokacin itama axixa tana yin sallar isha tana cikin yin shafa’I da wutiri ne taga
ashruf yana hade kujerarsa da sauran karikacen sa yana mikawa cikin daki. Axixa tayi ta sauri
kar ashruf ya shige ya barta, sai kuwa taga mutumin da gaske yake shigewarsa xaiyi ya dauki
fitila. Axixa ta mike a guje tace jirani kar ka barni, ashruf yayi mata banxa ya shige daki ya
banko kofa da karfi. Axixa ta rusa ihu mai firgitarwa tace yanxu anan dajin xaka shige ka barni?
Cikin sanyin nan kuma gashi ina jin tsoro. Wayyo ina ‘yan uwana ne yau, ina dady na? kuxo ku
ganni a cikin wannan hali. Ta fada jikin kofar tana kuka.
Ta ji ashruf bai ce komai ba. ta tashi a fusace ta ringa fisgar kyaren kofar nan amma ina ta
kasa budewa. Ta ce kai matsiyaci marar imani, dan talaka da bai iya samun waje ba, ka bude
min kofa. Ashruf ya turo kofa ya bude, axixa ta ji dadi a ranta, ta dauka ya bude mata ne don ta
shiga. Bata Ankara ba sai jin mari tayi tas! A kuncinta. Ya ce doka ta ta farko kenan kuma ba
xan bude miki ba tunda ke ba muharramata bace. Yaya xa’ayi ni da ke mu kwana a daki daya?
Ko kina so ki kwana a shimfida ta ne?
axixa ta fusata tace Allah Ya kiyaye in hada jiki ko shimfida da alade. Ya sake miko hannu xai
mare ta ta goce, yaja kofarsa ya kulle, ta fada a jikin kofar a tattakure tana ta sharbar kuka tana
sake jin sabon imani a xuciyarta, tayi tunanin ashe masu gadi haka suke ji take wulakantasu, ya
xamanto ko a barandarta suka xauna sai ta kore su. Ta tuna fulanin daji da suke cikin daji duk
sanyi duk damuna.haka ta kasance. Ta ringa ganin kamar wani abu ne mai fararen kaya yake
tunkarota. Sai ta rufe ido ta kankame tayi ta karanto addu’o’in da suka xo bakinta, harta fara
gyangyadi harma dai ta bingire da a bakin kofa tayi ta barci saboda gajiyar da tayi. Bata farka
ba saida taji ashruf na bude kofa, ya hankadata can gefe tayi firgigit ta tashi xaune taga ashruf
ne ashe yake bude kofa, ya jefa mata kwalba yace ruwa nake so karki wuce sakon ASHIRIN
DA HUDU .
Axixa ta dauki kwalba ta nufi wajen wani dutse ta taro masa ruwan ta kawo. Ya kalleta yace ba
kice ba. tace nagode master daka aike ni. Asruf ya yi murmushin jin dadi ya xaga bayan daki ya
kama ruwa yayi alwala. Da ya shige daki sai ta dauki kwalbar ta je ta ciko ta d la ruwa, itama ta
xagaya baya ta kama ruwa, ta xo ta yi alwala ta yi sallah anan kofar daki. Tana ganin ashruf ya
fito da gajeren wando da kwari da baka ya nufi cikin ruwa. Axixa ta xo bakin ruwa ta tsaya tana
kallonsa tana tunanin yau kuma wane irin aiki xai sa ta kafin ta ci kifin nan. Can ta ganshi da
wani gundumemen kifi mai girman gaske. Ya xo ya wuceta, tana biye dashi a baya har suka je
bakin kofar daki, wajen murhu. Ya harareta yace ba ki san dokata ta uku bane?
Me nace miki?
Axixa tace, babu itacen da xan hura wuta, ashruf yace kije ki tsinto a can. Ya nuna mata wani
waje. Ya ce da busassun itace. Axixa tace, duk jikin su kaya, ni kuma ba xan soke hannuna ba.
ashruf ya daka mata tsawa yace maxa ta je ta yiyo itacen a minti ASHIRIN DA HUDU kafin ya
kwada mata mari. Axixa ta nufi wajen itacen tana hawaye. Ta sha wuya ainun kafin ta iya karyo
itatuwan nan.
.
Comment da sharhi su suke kara mani karfin guiwar yimuku nagode
[8/28, 9:46 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[8/28, 9:48 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU
*4*
.
.
Nan duk ta caccake hnnunta. Ta tuna kauyawa matan da take gani da himilin itace sun karyo,
kuma su xo su dafa abinci, yau itama gata ta gamu da irin wannan rayuwa. ta kawo ta jifge a
gaban ashruf wanda yake a kishingide a nan kan kujera yana jiran dawowarta, yace ta dauki
kifin nan ta je wajen ruwa ta wanke shi tas, ta ciccire bawo-bawon bayan. Da kyar axixa ta
kinkimi kifin nan ta wanki ta xo ta hura wuta ta dora. Ya ce ta dauki kwalbarsa ta je ta ciko masa,
ta dauka da sauri ta ciko. Ta dawo, ta xauna, ashruf yace tashi ai ba ki gama ba. axixa ta mike
tsaye tana kallon ashruf xuciyarta cike da tsanar sa, yace ina so ki dan taka mun rawa ina
kallonki ina kallon kifina yana gasuwa. Axixa ta yi shiru ba tace komai ba tana dai tsaye. Ashruf
yace kina bata min lokaci ki yi min rawa malama. Axixa tace, ashruf baka isa ka wulakanta niba,
kar ka ga tun jiya kake marina kana sani aiki duk don ka ga ina yi shi ne xaka ce in yi maka
rawa ko, to ko xa ka kashe ni ba xan yi maka rawa ba. kai har mutumin da ka isa ka yi min
Magana ne balle ma ka dake ni. To ina mai sanar da kai ashruf jaki ko alade sai sun fika daraja
ka kuskura muka fita daga wajen nan, idan ba ikon Allah ba da ya rubuto min kaddara, da ko
akan tamarma daya xa mu xauna ne? balle daki daya ka kulle kofa dan rashin imani da rashin
ilimi ka bar ni a waje kana ciki harda cewa ko shimfidar ka nake so in kwana,? Allah Ya yi min
sutura ai, ni in hada hannu da kai balle jiki ai gara na kwana da alade ko jaki.
Ashruf ya mike a fusace ya kai mata mari sai ta goce, ta kwada masa mari, ya fusata ya kai
hannu xai rarumota, ta sa kafa ta dake shi a ciki ta xura da gudu tana cewa na fi so ka kasheni
a dajin nan daga kai sai ni ko gawata ma ka jefa a ruwa kar iyaye na su ga gawar.
Ashruf ma na bin ta guje yana cewa tun da mutuwar kike so ki tsaya mana, ya kike gudu?
Kuma yau ba xa ki hada jiki da alade ba da nixa ki hada yau, sai na nuna miki karshen iskanci.
Suka yi ta tsere a cikin yashi tulus, can ashruf ya sa kafa ya fyade ta ta fadi fuk! Ya damke ta
yace da ki hada jiki da ni gara ki hada da alade ko? to yau xa ki gani. Axixa na dukansa tana
xagi, tana ihu. Ashruf ya fisge mata kaya da damban tsiya tun tana kokarin fixgewa ta gudu, ta ji
ya shaketa da wannan karfaffan hannayen nan nasa. Tun tana da karfin ihu harta kasa ihu, ya
danneta yagama biyan bukatar sa da ita sannan ya dagata. (KALU INNA LILLAHI WA’INNA
ILAIHI RAJI’UN)
Abin tausayi axixa cikin jini dan yayi mata jina-jina, ya yi tafiyarsa ya nufi wajen murhu ya
manta da kifin da yake gasuwa, wanda tuni ya xama gawayi ya kone kurmus. Ya kashe wutar
ya shigewar sa daki, axixa na nan kwance ta kasa kuka ta kasa ihu. Addu’a kawai take Allah Ya
dauki ranta a inda take karta kara sakan daya don bata da amfani a duniya kwata-kwata. Can
bayan rana ta kwalle xafin rana yana dukanta, ta kokarta da kyar ta mike, ta sassaka kayanta
tana rarrafawa harta karaso kofar dakin ta leka cikin dakin bata ga ashruf ba. ta leka bayan
dakin baya nan, ta xaga bayan dutsinan nan duk babu ashruf . ta rusa kuka tace, daman ya
kawoni nan don ya yi lalata da ni ya gudu, ya bar ni a dajin nan? Ta yi kuka harta godewa Allah.
ga yunwa ga kishirwa don rabonta da abinci tun na jiya da safe, wata yunwar ce kuma ta
addabeta ga uwa uba tsananin bakin cikin abinda ashruf yayi mata, xuciyarta na kuna gashi duk
ya ji mata ciwo, sai radadi. Axixa bata taba ji gara ace tana kabarinta da rayuwar duniya ba sai
yau.
Ta ce a ranta ta san har abada ta yiwa farin cikin rayuwa bankwana ta san ba ita babu wani
sabon jin dadin duniya. Tun daga inda Allah Ya kawota. Da kyar ta mike ta sake tube kayanta ta
shiga ruwan daya ke bulbulowa a jikin wani dutse, ta yi niyyar yin wankan janaba, ta wanke ko
ina. Ta gama ta dauro alwala, sannan ta xo ta saka kayanta, tana ta leke-leke dai ko ta hango
ashruf amma bata ganshi ba. ta shiga daki, ta xauna ta takure babu abinda take sai tunani da
hawaye ta tuna abubuwa da yawa wanda take jin sa wai, wai a gari, yau gashi duk sun faru a
kanta. Ta kintaci axahar ta yi ta tashi, ta yi sallah, ta idar ta koma ta xauna, yunwa da kishirwa
sun addabe ta ta dauko wannan kwalbar da suke shan ruwa ta lallabo a hankali don kamar ta
fadi take ji, saboda jiri. Taje wajen dutsen ta tari ruwa, ta yi ta modar ruwan nan ta ciko ta
shanye ta sake cikowa ta shanye, har sau uku sannan ta koma daki ta xauna. Ta ji cikinta nata
murdawa don bata ci komai ba, ta modi ruwa. Abu dai kamar wasa cikinta ya ci gaba da ciwo,
sai aman ruwa tayi ta kwara amai a tsakiyar dakin nan, kamar xata mutu, abin tausayi. Ta ji
kamar daga sama an ce sannu. Ita ai a xatonta nesa ce ta xo kusa ko mutua ce ta xo an xo
daukar ranta. Ta daga kai a hankali ta kalli dogon mutumin da yake tsaye a bakin kofa, sai taga
ashruf tsaye rike da wani gasashen kifi a kan kwali a hannunsa.
Ta sunkuyar da kai ba tare da ta amsa ba, hawaye na xuba daga idanunta. Ya karaso inda
take, ya ajiye kifin a gefenta ya dauki kwalba ya fita. Can da aka jima sai gashi ya ciko kwalbar
nan da ruwa, ya xo ya ajiye a kusa da kifin, ya debo yashi ya xuba akan aman nan da ta
sharara, ya dauko tsintsiya da wani kwali ya kwashe, ya fita ya xubar. Sama da minti goma
axixa taga ashruf bai dawo ba, ta mike da kyar ta leka waje taga baya nan, ta fito sosai ta yi ta
lellekawa ko ina bata ga ashruf ba. ta dawo ta xauna a gaban kifinta, amma kanta ya daure tana
tantama ma ko kifin ba ita ya kawowa ba, karta ci ya xo ya mareta, ko ba nata bane. Can wata
xuciyar tace ke naki ne. ke ya kawo wa gashi harda ruwa ya debo miki. Sai ta tsayar da
shawara kawai ta ce kifin nata ne. ta fara gutsirar kifin nan tana wulka loma kamar ta hada da
yatsanta ta hadiye. Axixa ta yi ta cin kifin nan ba kakkautawa saida ta ji, ta yin at! Ta kora ruwa.
Ta tura sauran kifi gefe, sannan ta tashi ta yi sallar la’asar, ta ci gaba da laximi tana tunanin
duniya. Ta ji tunda take da ashruf bata taba jin ta tsaneshi ba irin ta yau, tsana mai tsanani akan
abinda yayi mata. Kuma bai taba yi mata abinda taga ya taimaketa taji dadin taimakon da yayi
mata ba irin nayau, don ya bata abinci ta ci a lokacinda take tsananin bukatarsa. Haka dai axixa
tayi ta tunani, ita tada, da ta yanxu. Halinda take ciki ta daga hannu ta roki Ubangijinta
madaukakin Sarki ya sawwake ya yassare mata ya fitar da ita daga wannan kangi da take ciki.
Har duhu ya fara ketowa wato magariba tayi, taje ta kama ruwa, ta dauro alwala. Nan ma tayi ta
leke-leke ko xata hango ashruf amma bata ganshi ba, ta shiga daki ta yi sallar magariba da aka
jima ta tashi tayi sallar isha’I, ta yi shafa’I da wutiri ta xauna tana jiran ashruf ya xo ya kwanta
waje in xai kwanta. Don haka ne ma yau ta yi shigar sanyi sosai fiye da jiya don ta sha wuyar
sanyi jiya. Ta loda tsummokarai a jikinta wai ita idan an kwanta a waje ta samu saukin sanyin.
Ta yi ta sauraron xuwan ashruf shiru bai xo ba, harta fara gyangaydi a xaune, ta yi kamar xa ta
fadi ta bude ido taga bbu kowa, har dai ta mike ta laluba saboda dakin duhu ta leka waje da ke
da hasken wuta ta hanhanga babu ashruf babu motsinsa. Ta yi tunani da tambayoyi a ranta ina
ashruf kuma yayi? Ko me yake nufi da yake tafiyarsa wani waje? Kar dai ya hada baki da wasu
ya tafi ya bar ni su xo su kasheni, ko kuma su saceni ma kwata-kwata.
Ta ji jikinta na karkarwa wani tsoro mai tsanani ya lullube ta fiye da na sanda ta kwana a waje
ma. Ta jawo kyauren kofar dakin ta rufe gam, ta sa tsumma ta daure ta rufe windon dakin, ta bi
ta tottofa addu’o’I a kowace kusurwa. Ta jawo sauran kifinta da ta rage da rana ta ci, don yunwa
kuma ta kara kamata ta kora ruwa, ta laluba ta hau gado. Ai sai ta ji gadon nan kamar wanda
aka saka masa katifar auduga don laushi, kan ka ce kwabo barci mai dadi ya saceta, ga dumi ta
kudindine da tsummokarai, dumin rus. Rabonta da ta ji dadin barci irn na wannan ranar tun da
ta baro jirginsu, yau kwana uku kenan. Babu yunwa ba kishirwa, babu sanyi ai ita ko a maparki
ma bata tuna ma a cikin kungurmin daji nan take ba. ta dauka a gida take, duk gabobinta ciwo
suke ga ayyukan da ta ringa yi bata saba ba, ga kuma murkushewar da ashruf yayi mata,
cinyoyinta sai sara mata suke don xugin radadin ciwo ta yi ta mika tana juyi cikin barci. Bata ma
san gari yawaye ba, har rana ta fito ral ta kawalle. Can ta yi juyi xata koma barci, sai taga haske
ya gauraye dakin, tayi firgigit ta farka, ta tashi xaune sai taga ashe har gari yawaye, bata sani
ba, tayi salati ta yunkura xata mike sai ta ji ta kasa saboda ciwon da jikinta yake yi mata. Ta
sake cije baki ta yunkura, ina ta kasa duk jikinta yayi tsami, sai ta fashe da kuka, kuka mai
tsanani tana cewa ashruf ka cuce ni ka cuci rayuwata, ka yi min fyade ka ruguxa min rayuwata.
Tayi kuka harta gaji. Sannan ta sulalo ta sauko gada kan gado, tana rarrafe ta karaso jikin kofa,
ta kama ta mike tsaye, ta kwance tsumman da ta daura kofar ta ture kofar ta leko, bata ga kowa
ba. ta fito waje bata ga kowa ba, ta waiga ko ina sai ta hango wani abu an kife da kwali a bakin
kofar dakin, ta karasa wajen ta bude sai taga gasashen kifine da gasassun tsuntsaye guda biyu.
Sai kamshi, ga maiko nasha-nasha ya tsatso a jikin tsuntsayen, a wannan karon har da gishiri a
gefe. Abin ya bawa axixa mamaki, musamman ma gishirin nan da ta gani, da tsuntsayen. Ta
kinkima xuciyarta cike da farin ciki ta mike daki ta fito ta kama ruwa da kyar ta tsugunna da kyar
ta mike tayi alwala, ta shiga daki ta yi sallah. Bayan ta idar ta yi addu’o’inta, ta jawo gasassun
tsuntsayen nan da kifin nan tana dangwala gishiri, ba lami shataf din da suka saba sinkimar
kifinsu a haka ba, gashi yau ta sami canjin gasassun tsuntsaye . Ta ci ta koshi, harta rage ta
ture gefe guda, ta rufe ta sha ruwa, ta koma