Showing 63001 words to 66000 words out of 73529 words

Chapter 22 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3590

sauran abokansu suka ga Aziza da Ashruf a lokacin
sun ako su Alhaji Sadam wajen motocinsu zasu tafi gida, wannan ya nuna musu shaidar cewar
soyayyarsy tana nan rangadadau. Alhaji Ahmed ya ji dadi amma Elmustapha ya fishi jin dadi
ganin Aziza da Ashruf. Da ta gaishesu sai ta yi wuf ta fada cikin gida sai ta yi daki aguje ta iske
Anti Sharifa a zaune a kan gado tana kallon CNN News ta fada kan gado tayi tsalle. Anti sharifa
ta ce “ Ashruf ya zo ko ?” Aziza ta rungumeta ta ce “ Anti ya aka yi kika sa ni shi ne kawai
abinda zaisa ki wannan murna”
Ranar da Atnti sharifa tas cika sati uku sa zu wa a ranar kuma Aziza ta fara shiya wani abu ba
tare da ta barei kowa ya gane ba. Daman ta suyowa Anti sharifa sabuwar waya (handset) da
sabon lay I ta bata, sannana taje ta dauki wayar babanta ba tare da ya sani ba da misalin karfe
uku na rana ta shiga bandaki ta dinga turowa Anti sharfa wasu messages masu firgitarwa, ko
kuma ince masu ban mamaki. Do farko ta turo mata da wani message kamar haka:
Assalamu alaikum
Sharifa ko zaki yarda ki zama abokiyar rayuwata ma’ana ki maye dakin marigaiya?”
Anti sharifa na karantawa sai taji gabanta ya fadio waye wannan? Kai karya idonta yake nuna
mata yaya Ahmed ba zai rubuto mata wannan sako ba. Bata garna mamaki ba sai wani ya sake
shigowa kamar haka :
Sharifa babu wata mace da na ganta a duniya tuna bayan rasuwar fatima na ji ina so ta maye
dakin marigaiya sai ke ki yarda da ni sharifa ki rungume yarta marainiya.
Da farko tayi tunanin to anya kuwa ba Aziza bace take turo mata wadannan text din ba kuwa
amma ai kuma ga Aziza a bandaki tana wanka. Ga wayarta kuma a caji a kan talabijin. Tabbas
Alhaji Ahmed ne da kansa kenana. Kafin Azizar ta fito sai ta turo na karshe tas ce.
You mean so much to me sharifa I love you.
Aziza ta nade wayar a hular leder da ta saka a kanta do kada gashinta ya jike ta fito daga
bandaki. Cikin wannan hali Aziza ta iske Anti Sharifa tana karanta message na karshe tana gani
Aziza sai tayi sauri ta rufe wayar ta yi shiru. Aziza na shafa mai tana satar kallon Anti sharifa
can ta ce “Antina lafiya?” Tace “Kalau Aziza kamar yadda Mamarsu kakar Aziza take kiranta.

Can Anti Sarifa ta nisa tace “Aziza gaya min lambar dadyn ki ina so nayi storing a wayata”.
Aziza ta ce “Land line ko handset”. Tace “Nasan Landline handset dinsa dai”. Aziza ta karkace
ta fado lambobi, anti Sharifa na rubutawa, taga sak lambarce akayi mata wadannan messages.
Sai ta sake nutsewa cikin tunani da mamakin wannan al’ajabi. Kafin Aziza ta gama shafa mai
sai Alhaji Sadam ya bugowa Alhaji Ahmed waya ga waya kuma a tufke a gashin Aziza ga Anti
Sharifa kuma a kwance tana kallon Aziza wacce ke gaban mudubi tana rangada wa Ashruf
kwalliya sunyi waya da shi yace su hadu a lambu da yamma. Allah ya sa ta kashe ringing tone
din a vibration wayar take. Aziza ta bala in tsorata jin wani abu garr a kanta saura kiris ta fige
hular wayar ta fado sai ta tuna kada Anti Sharifa ta gane. Aziza ta fita a guje, Anti Sharifa ta bita
tana kia “Aziza meye lafiya?” Tace “Kalau Anti Sharifa ina zuwa”. Taje ta lallaba ta ajiyewa
Dadinta wayarsa falon da ta dauko daman a caji ya saka ta.
Da daddare Aziza ta sami dadynta a falonsa tayi sallama ta shiga ya ce “Azzyn daddy lafiya?”
Ta ce “Lafiya Dad nazo ne in taya ka hira yau”.
Ya ce “Ina sane dake dan Antinki tazo ki ka guje ni sai na aika ma sannan na ke ganinki”. Ta ce
“Dady ba haka bane kasan marayan da bai taba sanin dadin uwaba ya sameta ran tasaka”. Sai
ya ji tausayin Aziza ya kamashi da taga haka sai ta rushe da kuka, yaji hankalinsa ya tashi ya
fara goge mata hawaye yana lallashi. Da kyar tayi shiru can suna hira ta ce “Dady bana so Anti
Sharifa ta barni saboda kowacce yarinya idan tayi aure mahaifiyarta take samu ta fada mata
matsalarta amma banda ni dan haka nace ba zan barta ta tafi ba”. Yace “yi hakuri Aziza nine
mummy nine daddy ki fadamin duk abinda yake damunki kinji ko? Da da Anti Sharifa bata nan
ba ni kike samu ba? Ta ce “Dady ai wasu matsalar ta mata ce kawai”. Yayi murmushi ya ce
“Haka ne Aziza to zan taya ki rokar Anti Sharifa ta zauna tare da mu nima idan ina ganinta tana
tunomin da marigayiya kamarsu daya”. Dadi ya kama Aziza jin ya fara soso mata wajen da yake
yi mata kaikayi ta ce. “Dadyu rannan a wajen birhtday partyn ka kace ka kusa kayi aure kafin
zabenku dady wacece matar?” Ya yi dariya ya ce “Wasa nake babu wata wacce zan aura”.
Aziza ta yi murmushi ta gyara zama ta ce “Dady na kenan”. Yace “Yaya akayi ne Aziza?” Tace
“Babu” Yace “Karya kike bakinki akwai magana” Su duka suka kyalkyale da dariya. Ta ce “Dady
akwai magana gyara zama in baka labari ko kuma ince shawara. Daman Anti Sharifa nayi maka
sha’awar ka aureta hankalinka zaifi kwanciya Allah Dady tana sona kamar yadda mummyna
take so na da”. Yayi shiru yana kada kai sai gaban Aziza ya fara faduwa tana tsoron amsar da
zai ba ta, can ya dago yakalleta ya yi murmushi ya ce “Banda abinki Aziza me Sharifa zata
yidani nayi mata tsufa Sharifa sai yaro ba irina ba”. Ta kyalkyale da dariya ta ce “Dady baka yi
mata tsufa ba ka bani wuka ka bani nama in dai da amince, amincewarta kake nema an gama”.
Yace “Jeki na baki wuka na baki nama dama suya duk na baki”. Yace “Jeki na baki wuka na ya
lullubeta ta rungume shi ta fita tana murna. Ya bita da kallo yana murmushi yace “allah sarki”.
Daga dukkan alamu Alhaji Ahmed yaji dadi da wannan hadi na ‘yarsa ta kuwa yi masa zabin
mata ta gari, ladabi biyayya, addini ga kyawu dandashi.
A sati guda Aziza ta hada kakkarfar soyayya tsakanin mahaifainta da kanwar mhaifiyarta. Tun
tana daukar wayoyinsu tana turowa daya text ta koma ta dauki wayar dayan tayi reply. Takai ta
kao har da hannaunsu suke dauka su rubutawa juna text din soyayya. Daga bayan ma sai suka
fara magana a waya, suka ma daina magana a waya harma suke haduwa a falo ko a lambu
suna tattaunawa. Dadi ya lullube zuciyar Aziza ganin abinda take mafarki ya fars zamowa
gaskiya.

[9/12, 5:33 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[9/12, 5:35 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT4
*29*
Ranar da kwana ashirin da hudu ta cika su Alhaji Ahmed suka raka Elmustapha k out don ci
gaba da shari’arsa da Alhaji Isa (Takaka). Shari’arsa Alhamdulillahi anci nasara kotu kuma tayi
matukar dokari wajen lissafa adadin dukiyar Alhaji Elmustapha dake wajen takaka aka bashi
abinsa miliyon niaron ne kudin aka kuma tarkato masar takardun kudaden hannun jarin da har
yanzu wasu takardun sunayensa ne jiki. Kotu ta yanke wasu miliyoyin kudi da Takaka zai biya
na diyya da yayi sanadiyar mutuwar zabaida yayar sannan gta ce zata yanke masa hukunci
akan sanadiya da yayi musu wajen nakasasu kuma ya jefa su cikin kuncin rayuwa Nana gaba
za ayi Shari’a akan kisan gillar da yasa aka yiwa minister sai a hada a hujunta shi. Dadi marar
misali a wajen Elmustapha da dansa Ashruf da sauran masoyansu sunyi musu muma kwarai da
gaske. Yanzu Ashruf da mahaifinsa basu da wani buri illa suga Hajiya Fatima mohafiyar Ashruf
ta ji sauki don har yanzu tanaa kwance a asibitin tana shan magani alhamdulillahi a kullum kara
samun sauki take yi. Watanin Anti Sharifa biyu a gidan su Aziz tace zata tafi gida garinsu Guru
ta sanarwa da magabatangta. Alhaji Ahmed ya yi moata alkawarin cewa nan da sati biyu zai
aiko da magabatansa don neman aurenta. Abin arziki da direba ya hada mata suka tafi hard a
Aziza yar rakiya. Ashruf bai so aziza tafi guru bat a barshi. Amma ta bashi tabbacin cewa ko
kwana biyar ba za ta yi ba zata dawo. Cafdijan you Guru tana da manyan baki. Azizar ce ko
sharifa? Dukkaninsu sun zama wata sabon gani garin an dade ba a gansu ba. Tswofaffin I yaye
da kakanni sai koke koken dadi ake. Hakika Aziza ta saduda da rayuwa tunda ka ganta a kauye
har zata yi kwana uku da ta tsani talata da talauci ko zama bagta yi idan tajie amma sai ga
Aziza a dakin kiasa anyi rufi da ciyawa katangar kara tana taya wata tsohuwar dimame da safe3
a murhun duwatsu uku. Rayuwa kenan.
Ranar litinin da misalign goma na safe jam’iyar nana mai matukar farin jinni wajen’ yan Nigeria
wato J.U.T suke yin wani gagarumin taro don yin sahawarar wanda ya kamata a tsayar a
matsayin dan takarar mataimakin shugaba kasa a madadin Alhaji Isa Elyakub, cancanta ta
nuna Alhaji Isa Elyakub. Wannan abu ya yi wa jama ‘a dadi musamman dan takarar shugaba
kasar Alhaji Ahmed abdulfathi da babban abokinsa Alhaji Bala tuwona maina kenan. Bayan
‘yan uwansa da abokan arziki cewa aure zaiyi kowa ya yi mamaki ya kuma taya shi murna
musa mman day a fadi wacce zai aura. Kowa yaji dadi musamman don Aziza. Ya tura
magabatansa sun kai kudin aure, kudin gaisuwar uwar uwa da uba da sauran kudaden da
hausawa suke fara kaiwa na al’ada. Aziza da mahaifinta, ashruf da mahaiginsa suka nemi biza
do fita kasashe gurda uku, dubai, America da saudiya don yin ummara. A dubai kuwa kayan
aure (lefe) Aziza zata taya mahaiginta zazzaba don zabarwa antinta kaya masu kyau. Sannan
su wuce America can kuma saboda kafar toba mai kyau kamar ta mutane alhaji ahmed ya dauki
nauyi da kudinsa za a yiwa alhaji elmustapha don ya mike tsaye yayi tafiya a dama da shi a
harkar rayuwa kamar kowa. Ashruf duma don yayi jinyar mahaifinsa a asibiti don zasu dan
daddatse wasu wurare a jikin kar don a samu a sa ta robar ta daidaita ta zauna daram.
Waatansu daya da rabi a can. Daga dawowarsu sai aka fara rangada bikin alhaji ahmed da
amaryarsa anti sahrifa. Duk da dai bayan daurin aure Alhaji Ahmed ya yarda anyi recptin. Aziza
ta so ta shirya parties iri daban daba Alhaji Ahmed ya ki yace su ba yara bane. Da kyar ya

yarda suka je wajen wata dinner da ta hada musu a Sharaton Abuja. Dinner tayi tsari tayi kyau
sosai manya, samari da ‘yanmata sun hallara. Ango da amarya sun sha ado sunyi kyau sosai.
Daga karshe aka kai amarya kayataccen gidanta wanda kusan komai na gidan sai da aka canja
shi komai sabo dal dal. Ga angwanci ga sayisa zabe ya karato duk sun hadu sun hautsinewa Alhaji Ahmed amma
abokansa suka ce sun hutarshi da yawon kanfen da sauran kacaniya da ‘yan siyasa duk zasu
tsaya masa yaje ya huta gajiyar biki shi da amaryarsa. Ko dar Alhaji Ahmed bai ji ba saboda ya
san Alhaji Sadam zai tsaya masa komai. Saboda ya saba babatu dama, ga Alhaji Elmustapha
da dansa Ashruf da jikinsu, bakinsu da dukiyarsu tsakani da Allah kanfen suke taya su. Lungu
da sako, garuruwa babu inda Alhaji Elmustapha da Ashruf ba su shiga ba sunawa Alhaji Ahmed
kanfen dake sunsan illar talauci sunfi kowa sanin me zasu ce wa talaka ya gamsu da Alhaji
ahmed zaiyi masa aiki ya rabashi da wannan matsanaciyar rayuwar nan da ‘yake ciki. Saura
wata daya zabe don haka kowa ya yi wujiga wujiga duk ‘yan mazan gidan basa nan. Aziza sai
ta yi kwana uku bata ga Ashruf ba yana can ya lula garuruwa suna kanfen. Sai dai suyi magana
a way Ashruf na bata hakuri a koda yaushe saboda Aziza ta shiga damuwa wai bata ganshi ba
kwana biyu. Siyasar Nigeria akwai rikici babu shige da fitar da ‘yan adawa basu yi ba donsu
kushe Alhaji Ahmed ga ‘yan Nigeria don karsu zabeshi amma Allah shi ne shaidar mutum Allah
ya san Alhaji Ahmed ya san niyyar sa ta ya yiwa talakawa aiki tsakaninsa da Allah.
RANAR ZABE
Ranar asabar Cincirindon jama’a suna ta firfitowa domin jefa kuri’arsu ga dan takarar shugaban
kasar da suke so. Nigeria kakaf dinta mata da maza suyi kokari sun firfito kwansu da
kwarkwatarsu don jefa kuri’a, burane da kauyuka. Gidansu Aziza kakaf dinsu kowa ya fito ya
shiga gari don jefa kuri’a. alhaji Ahmed kuwa yau kwanansa biyu bai tako gida ba suna can
siyasa ta rincabe ana addu’o’I sunnan ana fadakar da jama’ar Nigeria akan kada su bi son
zuciya saboda ‘yan kudaden da ake basu don su yi zaben tumun dare su tsaya su yi tunani don
su zabi dan takara na gari wanda zai amfani al’umma gada daya sannan su bawa Allah zabi ya
zabar musu shugaba na gari. Allah Ubangiji (S.W.T) ya duba zukatan al’ummar Nigeria ya karbi
addu’o’insu ya zabar musu shugaban kasa na gari. Sai karfe uku na daren wannan rana asbar
sannan babban jami’in zabe ya sanar da sunan wanda ya lashe zaben shugaban kasa shi ne
Dr. Alhaji Ahmed Abdulfathi da mutaimakinsa Injiniya Sadam Tahir. Su Alhaji Ahmed sunji dadi
da wannan sa’a Allah ya basu suka lashe zaben amma ‘yan Nigeria sun fi su jin dadi da Allah
‘ya zabar musu shuwagabanni na gari masu kishin ‘yan kasarsu da tsoron Allah. Labari har
kunnen Alhaji Isa Elyakub wanda ke gidan yari inda aka ajiyeshi kafin a yanke masa hukunci.
Take ya hau shessheka zuciyarsa ta samu matsala saboda tsananin mummunan labarin a
wajensa cewar Alhaji Ahmed shi ne shugaban kasa Alhaji Sadam mataimakinsa. Rabe rabe aka
maikashi ga likitocinsu na daurarru don ceto ransa saboda fuk ya fadi kasa da jin labari Alhaji
Ahmed ya lashe zabe. Bayan an kammala hada hadar zabe ranar litinin ta sama kenan aka kira
Alhaji Ahmed da mataimakinsa Alhaji Sadam za a rantsar da su. Ashruf da mahaifinsa suma
sun tafi wajen bikin rantsawar, Anti Sharifa ma da su Maman Atika dakkansu sun tafi. Aziza ce
kadai ta rage a gida itama ta shirya tsaf zata biya ta gidansu Mannira da Atika ta tafi da su
kamar yadda suka shirya, sai taji wayar babban falon dadynta tana kara ta tafi da sauri ta daga
kan wayar sai taji muryar wani mutum ne yace “Nan gidan mai girma shugaban kasa ne?” Ta ce
“Eh nan ne lafiya?” Yace “Lafiya kalau likita ne daga nan asibitin masu larurar kwakwalwa ne

game da marar lafiyar da kuka kawo mana ne”. Gaban Aziza ya yanke ya fadi gudun karfa wani
abu ne ya faru ga mahaifiyar Ashruf saboda burin Ashruf yanzu shine yaga lafiyar mahaifiyarsa
kawai haka mahaifinsa ma. Tace “lafiya?” Likitan yayi ‘yar siririyar dariya yace “Ba wata matsala
ba ce daman illa ma abin farin ciki”. Aziza ta yi ajiyar zuciya ta ce “Alhamdulillahi Doctor yaya
aka yi?” Yace “Fatima Elmustapha Allah ya bata sauki mun gwargwada ta mun lura ta samu
waraka daga wannan larura ta tabin hankali da take fama da shi. Yanzu ma munsao tayi hakuri
ta zauna a wajenmu zuwa sati guda saboda munsan yanzu shi kansa mai girma shugaban kasa
yana gwagwarmayar zaben nan sannan mu dawo da ita gida ta tilasta ta ce ita tana son ganin
mai gidanta da Ashruf tun jiya take tayar da hankalinta. Kinsan mai larura irin wannan bai kamta
ba kuma a dinga ja mata rai a hanata tazo taga iyalinta kada tayi tananin ko rasuwa ma suka yi
ake boye mata zata iya sake rikicewa. Idan da halin wani nata ya zo asibitin yanzu zai iya zuwa
don ya dauketa”. Farin ciki ya rufe Aziza tace “Doctor babu matsala ni sunana Aziza Ahmed
Abdulfathi ganinan yanzunnan zanzo in dauketa”. Da sauri ta zari gyalenta da mukullan
motarta ta nufi wajen mota. Gidansu Munnira ta fara zuwa dake Wuse zone six ta dauketa suka
wuce zuwa asibitin dake yafi kusa da wuse. Suna isa suka shiga ofishin babban likita anan suka
sami Hajiya Fatima tana zaune a kujerar dake kusa da teburin likita yana mata wasu tambayoyi
da zai kara taimaka masa wajen sanin inda kwakwalwarta ta dosa kuma wanne magani zai
rubuta mata taci gada da sha. Bayan su Aziza sun gaishe da likita sai suka karasa gaban Hajiya
Fatima suka durkusa suka gaisheta wacce tun shigowarsu take tayi musu mursushi. Ta mika
musu hannu suka gaisa ta shafawa Aziza kumatu ta ce “Ke ‘yar budurwa mai kyau”. Ta shafawa
Munnira kumatu ta ce “Ke ‘yar fara. Likita ya ce “To Aziza ga wannan takarda magunguna ne na
rubuta mata kada a dinga yawan bata mata rai ko kuma a dinga gaya mata abubuwan tashin
hankali amma ragas ta sami sauki mun gwargwadata sosai munga hankalinta ya dawo jikinta”.
Hajiya Fatima ta juya ta kalli likita tace “Sune zasu tafi da ni?” Yace “Eh su ne ku tafi shike nan”.
Tace “Kace min nan Nigeria ne ina zasu kaini? Kace Ashruf da babansa zasu zo, ina suke?”
Aziza ta yi murmushi tace “Mummy can zan kaiki wajensu yanzu sun fita unguwa ne shi yasa,
da aka yi waya basanan sai ni kadai gidanmu daya da su Ashruf din ai”. Tace “Mafi mishikala”.
Babu matsala kenan ta mike tsaye suka fita bayan ta yiwa likita godiya da addu’o’I dake
malama ce makaranciyar alkur’ani mai tsarki, suka nufi gida. A bangaren Anti Sharifa ta ajiyeta
ta nuna mata bandaki don tayi wanka ta nunnuna mata mayukan shafawa kala kala da
turarurruka da sauran kayan kwalliya ta ciro mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login