Showing 51001 words to 54000 words out of 73529 words

Chapter 18 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3588

suka yi da mubarak
a waya, cikin dariya ba tare da bacin rai ba axixa take labarinta.

Wannan al’amarin ya bawa atika da munnira mamaki, axixa ta yi musu ba xata bata nuna musu
wata damuwa ba game da halin da take ciki. Suna hira suna cin kayan dadin da suka sussuyo a
911 suci kaxa suci kek, ga meat pie, alewowi da biscuit, juice ne kala kala a dan karamin firig
dake dakin, ga kallon fim din ibro sun kunna, suna hira wasa da dariya sai dai sallah ce take
tashinsu daga jirar da suke rangadawa. Kyamara ce a jakar munnira (auto) mai daukar hoto da
kanta idan aka setata, don haka ‘yan matan suka dinga hotuna kala kala. Da alama hotunan
nan nasu xasu yi kyau sosai gashi kayansu iridaya duka uku, kuma dukkansu suna cikin farin

ciki da fara’a yau, ko me nene dalilin da duk suke jin farin ciki a ransu yau,? oho!
Atika da munnira xamu iya cewa saboda ganin kawarsu axixa ta ware ta fara dawowa axixarsu
tada.

Da isha’I tayi suka yi sallar isha’I suka idar, da misalin karfe takwas na dare, sai atika da
munnira suka fara shirye shiryen tafiya gida. Dukkansu sai suka ji babu dadi a ransu
musamman ma axixa da ita kadai xasu tafi su bari a cikin wannan hali. Axixa tace yanxu kuma
sai yaushe xaku sake dawowa, sai na ganku ko? Koma ince har a sallameni?
Munnira tace kai haba! Ai ni kullum xanxo tunda naga hanya don abbana daman baya hanawa
muxo sai dai ko baban atika da kyar ya barta kullun taxo tunda daman shi ne yake hanamu
xuwa yana ganin wai xamu tayar miki da hankali. Atika tace ai tunda jikinta ya yi sauki bata
wannan damuwar mai xai hana kullum mu xo mu dinga yinin mata shima babana dauka ya yi ko
xancen mubarak akayi sai xuciyarki ta hau bugawa amma gashi kin cirewa kanki damuwa kina
hirarki. This is not the end of the world, dan haka axxy ki ci gaba da addu’a, farin ciki a
rayuwarki yanxu kika fara. Sai axixa tace a ranta, ina wani farin ciki a rayuwata kuma nan gaba?
Tunda na rabu da ashruf na rabu da farin cikin rayuwata ga kuma uwa uba abun xagi ya same
ni yaya na da jikoki. Suka yayyafa mayafansu suka rataya jakunkunansu suna cewa, gobe ma
a nan xa mu wuni, jibi ma haka ko da munyi fashi to bai fi fashin kwana daya ba a sati, amma
kullum xa mu dinga xuwa. Axixa taji dadi da wannan batu na kawayenta tace to Allah Ya kawo
ku lafiya, kunga yau da muka yinin nan da nan naga dare yayi, amma idan ni kadai ce sai a
dade dare bai yi ba to bani da abokin hira sai tunani. Munnira tace, Allah sarki axy baba ne ya
hana mu xuwa kamar muyi kuka, gashi da muna dan gaisawa a waya muka buga muka ji a
kashe sai abba ne yace ai daddy ne ya karbe wayar, axixa tace af, daman ina son ku bani dan
kudi dan Allah, idan na tambayi daddy sai ya dinga yi min tambayoyi me xanyi dasu.

Atika ta matso kusa da ita tace, ai kuwa muma sai mun tambaya me xa kiyi dasu?
axxy karfa kice xaki bar garin nan ace mu muka baki kudin mota, axixa ta harareta tace idan xa
ku bani ku bani, idan kuma baxa ku ba niba ku kara gaba dubu dari nake so kacal. Munnira ta
kalli atika ta girgixa mata kai alamar a’a kar su bata. Munnira tace ko wata hanset din xaki siya?
axixa tace eh, wai yaya xa’ayi kuyi tunanin xan gudu na je ina? Munnira ta xaro wayarta tace karbi tawa har layin ko kuma mu fita mu sayo miki sabon layi
saboda a tawa su dr rislan xa su iya damunki da kira, axixa ta ture hannun da take miko mata
wayar tace kai ni bana son irin wannan takin, atika tace to tawa fa?
Ta ciro daga jaka tace tawa dai kinsan mai kyau ce tafi ta munnira sabuwa ce kimanin naira
dubu dari da arba’in mamanmu ta siyo min tsaraba wannan fitar da tayi America. Axixa tace duk
bana son su, ni dai ku bani kudin kawai xan xabo irin wacce nake so da kaina. Atika tace to ba
wayar xaki siya ba baxa mu bayar ba, ki gaya mana ko meye kike so xamu siyo miki, axixa ta
fisgo jakar atika tayi sauri ta bude ta debe kudin dake ciki dukka, dubu hamsin ne cifcif yan dari
biyar biyar, sannan ta jefa mata Jakarta. Munnira tace bari na fita babu ruwana atika ce ta bata
kudi, atika ta wawuro jakar munnira ta jefawa axixa sannan ta rike munnira gam, tace axixa
kwashe kudin Jakarta itama, mu biyu muka baki kudin a jakar munnira dubu talatin da biyar
axixa ta kwashe sannan ta jefawa munnira Jakarta.

Ta rakasu har wajen motarsu munnira kara cewa axixa take, axxy wai dan Allah me xaki yi da
kudin nan? Mu fa tsoro muke ji, ko kuma atika jeki gida ke kadai xan kwana a wajen axixa.
Axixa tace ba xaki kwanar mun a daki ba sai dai idan a dakin dr rislan kike so ki kwana to sai ki
xo na raka ki office dinsa in ya tashi sai ku tafi gidansa tare, munnira tace rufa min asiri ai ban yi
wayon da xanyi wannan tabarar ba, ni dai rokonki nake yi ki rufa mana asiri kar kiyi amfani da
kudin na ta wata hanyar da xata xama tashin hankali wacce xa’xa ce mune.

Axixa ta bata rai dan ganin munira ta dameta da xance daya, ta ce wai shin bani da hankali ne
da xan gudu na je ina? Wa nake da shi daya wuce mahaifina? Kuna tunanin xan je wani waje
na kyale shi, haba ya kuke neman ku bata min rai ne? nace muku akwai abunda xanyi da kudin
kuma ba xai wuce na sayi waya ba don ma ba irin taku nake so ba da na karba. Akwai irin
wacce nake so dan haka ku kyale ni na sake dan Allah, munnira ta rungume axixa tana cewa
haba kawar ya mun yini lafiya kuma xamu yi rabuwar tsiya dan Allah axixa yi dan murmushi
mana atika ma ta xo suka dinga xolayarta har saida tayi dariya sannan suka yi sallama akan
gobe ma xasu xo su sake yinin mata in sha Allah, axixa na tsaye tana kallonsu har suka yi nisa
kana ta juyo ta kama hanyar komawa dakinta, tana shiga dakin ko xama bata yi ba dr eltayyib
ya shigo, don shi ne mai dutyn dare, dr eltayyib dan kasar indiya ne, yana da kirki sosai ga
fara’a sun saba da axixa sosai suna hira. Bayan sun gaisa da axixa ya yi mata yan tambayoyi
akan yanxu me take ji a jikinta kuma tana bacci yadda ya kamata? Axixa ta amsa da cewa babu
abinda yake damunta, kuma da daddare tana yin bacci sosai, yayi yan rubuce rubucensa har
xai fita axixa ta kirawo sunansa ya dawo fuskarsa cike da murmushi yace yaya axixa? Axixa
tace kayi hakuri da abinda xan fada maka ko xan dan takura ka, cikin jin dadi shima yau axixa
xata nemi wani abu a wajensa yace kar kiji komai fadi bxan takura ba da yardarm Allah. axixa
tadan yi murmushi tace nagode doctor, daman ba wani abu bane illa ina so ka bani motarka
yanxu xani wani waje a gari xan suyo wani abu yanxu xan dawo. Dr eltayyib yayi dariya yace
haba axixa baki da lafiya a kwance ma kike a asibiti amma ki fita gari? Haba aixa ko ni kika aika
ai sai inje na suyo miki ko me nene. Amma ba xan barki ki fita baki da lafiya ba to idan kika
gamu da babanki fa? Laifin ma gaba daya nawa ne nine likita in duty, sannan kuma da motata
kika fita.

Axixa tace a xuciyarta haka ne kuwa xan iya haduwa da idon sani, koma ban hadu da daddy
ba tabbas kuma labara xai je masa an ga axixa,
dr eltayyib ya cigaba da cewa ko ya kika gani axixa? Axixa ta nisa gami da dan..
.
Ya jama'a mai kuke gani?
Shin ya bata motar ko ya hana ta?
Ina kuke hasashen Aziza xata je?
Da gaske wani abun xata siyo ko kuma guduwa zata yi?
.
Ni Auwal mehafsa nace ya bata mota kuma babu inda xata taho sai waje na.
Comment yakara yawa nagofe sosai
[9/7, 7:56 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK

WHATSAPP 08064400100_
[9/7, 7:59 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT3
*16*
.
.
Axixa ta nisa gami dayin murmushi ta ce na gode kwarai da gaske likita daman handset da layi
nake so in siyo. Dr eltayyib yayi dariya yace don handset ai ko a kusa da asibitin nan akwai
wani sabon kantin waya babu irin wanda babu. Axixa ta sa hannu a jaka ta dauko kudi dubu
tamanin da biyar ta mika wa dr eltayyib tace dr ga kudina dukka dubu tamanin da biyar ne don
haka ka siyo min waya ta kamar dubu saba’in sai layin MTN shi kuwa bai fi dubu biyu ba saura
dubu goma sha uku dukka kati (credit) xaka xuba min sannan irin wayar da nake so mai dauke
da redio a jikinta, kuma dan Allah doctor ko da ka gamu da dr rislan kada ka gaya masa xai iya
sa daddy na ya sake karbe min kamar yadda aka karbe min ta da wai ni marar lafiya ce mutane
xasu dameni.

Dr eltayyib yayi murmushi yace ina ruwan waya da cuta? Tunda kina iya tafiya kiyi Magana ai
xaki iya amsa wayar ma, axixa tace ai shi ne, dan Allah dr ni dai ina kara tuna maka wacce ta
ke dauke da radio a jikinta. Dr eltayyib yayi dariya yace ai ba xan manta ba lallai sauki ya samu
har music kike so kiji don na san dai ba don jin labarai kike son radio ba, ko na siyo miki yar
radio mai kaset (walkman) ki ringa saka kaset kin ji? Axixa tace a’a doc ni dai handset mai
radio kawai nake so. Eltayyib yace an gama sannan ya juya ya fito , axixa na xaune tana tunani
taji wani sanyi a ranta don yau da ikon Allah xata yi Magana da mr Johnson ta ji halin da yake
ciki na neman ashruf. Ta tuna af ashe number mr Johnson din tana cikin waccan wayar tata, sai
taji wani makokon bakin ciki ya tokare ta, can ta tuna ai diary dinta inda take rubuta nambar
wayoyin jama’a yana cikin akwatinta kuma da number mr Johnson a jiki. nan da nan ta tashi ta
sauko daga kan gadon da take xaune ta jawo akwatin kayanta ta hau binciken diary. Ba tare da
ta sha wahalar wargaxa kayanta ba ta ganshi ta xaro shi ta rufe akwatin ta jingina. Shigowar dr
rislan ceta juyo da hankalinta ga duban bakin kofar dakin yayi sallama ta amsa , yace axixa
kinga tunda safen nan dana fita ban dawo ba ko? Sai yanxu?
Axixa ta ce babu komai ai tunda munnira kawarka ta dawo ba komai su duka suka tunstire da
dariya. Dr rislan ya sake gyara tsayuwa yace kai axixa kin cika tsokana ashe munnira har sun
tafi tace xata je muyi sallama shi ne tayi tafiyarta ko?
Ai nayi mata waya tace min waisu har sun tsufa a gida sai dai gobe xasu dawo su sake yinin
miki.

Axixa tace haka dai suka ce ko bata dawo don niba ai xata xo don ta ganka, dr rislan ya yi
dariya yace don ke dai xata dawo, munnirar data ringa bata rai taki Magana fur number wayar
tama saida nasha wahala sannan ta bani aiko kin san bata sona kiri kirir take nuna min. yanxu
axxy yaya xan yin a samu munnira xancen gaskiya nake yi miki fa babu wasa, kamar yadda
kika sanni shekara da shekaru babu wata ‘ya mace da ta taba kwanta min lokaci duga irin yau
yadda na ji munnira. Ita kuma sam bata ra’ayina. Dr rislan ya marairaicewa axixa. Ita kuwa
axixa Allah Allah take yayi ya tafi kada dr eltayyib ya dawo daga sayo mata waya, don ta
fuskanci duk abinda dr rilsn ya fadawa daddynta yana yarda, kuma dr rislan yana daya daga

cikin masu hanata ta sake ko kallon settilight ya hana yaje ya katse ta dakinta wai kada taga
wani fim din da xai tayar mata da hankali sai fim din ibro aka xo aka tule mata na bidiyo. To
yanxu yasan an kwace mata waya, yaga ta siyo wata xai iya gayawa daddy ya sake kwacewa a
xuciyar tace take Magana, can tace , kai abin daya dame ka ma da sauki ni da kasan me ke
damuna dabaka tare ni da xancen ka kamu da wata soyayyar shirme ba, dr rislan ya ci gaba da
cewa ni dai na baki wuka na baki nama ga ni a hannunki, munnira ma na hannunki ki taimaka
wa doc ka da ya kwanta ciwon rashin abar da yake so. Axixa ta yi dariya tace kai doc, harda su
kwanciya ciwo? Ka kwantar da hankalinka ka samu karbuwa da munnira ba xa ta yadda ta bika
office dinka ba harta shafe awa a can, kai dai kayi kokarin ku saba da ita, xata soka mu dai
anan dakin banda xancenka babu abinda ta ke yi, kasanta miskila ce don haka da wuya ka
ganeta sai a hankali.

Dadi marar misaltuwa ya lullube xuciyar dr rislan don shi har ya hau ya yarda da tsarin da axixa
ta tsara shi, yace to Allah Ya taimake mu. Axixa tace amen doc. Ya ce to saida safe xan tafi gida
dr dayyib ne ya canje ni ko ina ya shiga kuma ance an ganshi ya fita da mota ko ina ya tafi daga
xuwansa kuma, shi dai da baya wasa da aikinsa su dr kabir sun fara koya masa kalula kenan.
Axixa tace a’a dr eltayyib baya wasa da aikinsa yanxu nan ya fita daga nan sai dai maybe
mantuwa yayi a gida ya koma suka yi sallama da dr rislan ya fita ya jawo mata kofar dakin ya
rufe, bayan fitar dr rislan da kamar minti shida sai ga dr eltayyib ya shigo dakin. Axixa ta yi sauri
ta tashi xaune daga kishingeden da take tayi masa murmushi kana tace sannu da xuwa doc. Ya
yi murmushi ya amsa sannan ya karaso har gadon da take xaune ya mika ma ta ledar dake
hannunsa ya yi shiru yana kallonta cikin murna da jin dadi axixa ta bude ledar daya miko mata,
taga kwalin waya ne a cikin ledar ta dauko kwalin ta bude sai ko taga wata hadaddiyar waya
sony Ericson p900 waya mai kyan gaske ruwan madara kalar jikinta. Kai wannan wayan tana
da kyau doc, axixa ta fada yayin da take daga wayar tana kallonta. Ta jawo cajar wayar itama
ta hadu kamar yadda wayar ta hadu. Ta dago ta kalli dr eltayyib wanda har yanxu yana tsaye a
kanta yana kallonta fuskarsa cike da murmushi.

Ta ce dr amma wannan wayar tafi ta kudina, haba dr ga wahala da na saka ka bar aikinka ka
fita kuma harda ciko?
Nawa ka siyo min?
y ace bb komai axixa, risitin yana ciki kuma idan katin wayar (credit) yakare kiyi min Magana
xan sako miki wani, ki duba cikin wayar na saka miki sim card da credit din. Na ma fara yi miki
charji a mota sai ki sata a charge saboda kinsan tana da cin charge saboda radio. Irin tawa ce
sak sai ki gwada rediyon shima ki ji in tayi charji. Likita nagode madalla axixa ta fada cikin
fara’a. dr yayi mata sallama yayin da yake bude kofa ya fice. Axixa ta sauko daga kan gado taje
wajen soket ta jona wayar ta dawo kan kujera ta xauna da carbinta a hannu tana ta jan wuridai
akan Allah Ya sa da ta bugawa mr Johnson yace ya ga ashruf ko kuma ya samu adireshinsa.

Bayan ta tabbatar wayar tayi cajin da xai isheta yin Magana da mr Johnson sai ta mike taje ta
dauko wayar ta hau gado ta bude dairy dinta ta duba lambar mr Johnson ta fara latsawa. Ba
tare da tasha wahala ba taji wayar ta shiga harta fara ringing, gabanta ya yanke ya fadi dan
fargabar jin amsar da mr Johnson xai bata akan ashruf. Can taji ya dauka yana cewa wata

lamba daga Nigeria ina fatan xa’a min albishir da samun naira ne, cikin harshen turanci mr
Johnson yake Magana. Ta tuntsure da dariya tace kai! Kai!! Mr johnson ina xaka da son kudi?
Wato har ka san sunan kudaden kasashe daban daban, ka san sunan kudin Nigeria? Ai kuwa
din samun naira xan yi maka. Axixa ce daga Nigeria take Magana.
Yayi firgigi ya gyara xama, dan da a dan kishingide yake akan kujerar shakatawa. Ya ce axixa
ya kuke? Naga lambar ba taki bace shi yasa ban gane ki ba, ta yi dariya tace wannan sabuwar
lambata ce dan haka kayi sebin . mr Johnson yace to xan yi, ai na gwada wancan naji a kashe ,
ashe kin daina amfani da layin kenan? Axixa tace kwarai kuwa, to ya maganar ashruf ka samu
labarinsa kuwa?
Mr Johnson yayi dariya yace kwarai kuwa na samu labarin ashraf. Axixa ta gyara xama game
da jin wani tsananin farin ciki a ranta wanda biro da takarda ba xasu iya suffanta yadda taji ba,
irin dunbin farin cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login