Showing 27001 words to 30000 words out of 88300 words

Chapter 10 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1589

yace ta zauna).

B'angaren Ameena na kuwa ta kammala karatunta cikin nasara, harta anshi resi d'in ta, Abdool kuwa an girma dan yanzu yakai shekara 5 yana nursery 2 a Emirate dake garin Argungu, gashi da k'ok'ari sosai sai dan Neman wayo da surutu har tsoro yakeba Ameena idan ya fad'i wata magana kamar wani Babba, Niko ya had'u da Asma'u aifa shikenan d'an biyemasa takeyi suyi tayi, itadai Ameena kallo kawai nata tana mamakin wannan shak'uwa dake tsakaninsu.....

Asma'u yayarta ta fara sanar ma soyayyarta da Abdulrahim, Ameena tayi farinciki da jin k'anwar tata ta had'u da *muradin ranta* (maman ussey), amma saida tayi Mata mitar k'in fad'a mata tun farkon soyayyar sai yanzu take gayamata, hak'uri ta bata tare da had'e hannayenta biyu guri d'aya.

Dukan wasa takai mata tare da Kama hannayenta ta maida ita kan bed "ki rage zurfin ciki kanwata kada ya cutar dake wata rana"

Tana dariya tace "yes Aunty ur wish...." Dariya sukayi baki d'aya dai shigowar Abdool shima ya dane gado tare da kamu rungume Asma'u tayi tare da jan guntun hancinsa tace..

"Clever boy kasan me akewa dariya ne hala?"

"Yes tunda Aunty da Mami na dariya nasan suna farinciki ne.." Nan dariyar sukayi gaba d'aya suna mamakin wayo irin na yaron...

Ameena nace taje ta sanar da Babban su game da maganar Asma'u, har da maganan zuwan su Ard'o dan Abdulrahim ya kirata ya gayamata suna zuwa cikin satin.

B'ata rai taga Baban nasu yayi yace ta kira Asma'u, jiki sanyaye ta fita, tare suka dawo.

Asma'u ya kira sunanta cikin kaushin murya, bai jira amsawarta ba yaci gaba da magana.

"Yayarki tazo min?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? da zancen yaron da kike so, yanzu abunda ya faru da 'yar uwarki bai zama izina gareki ba, har kike tunanin Auren 'yan jahar Sakkwato, to bama wannan ba na Riga mun gama magana da Malam Musa zamu had'aku Aure da d'an wajensa Mustapha" tunda ya fara magana Kanta na k'asa haka itama Ameena, harda hawayenta jin anyi mata fami akan ciwon ta.

Sannan yaci gaba "dan haka inaso ki kira wannan yaron ki gayamishi karma yazo da iyayensa dan an Riga anyi miki miji, kinji ko?" Kai ta girgiza masa alaman eh.

"Yawwa kuje Allah yayi muku Albarka" Ameen suka ansa sannan suka wuce, bayan fitarsu inna dake zaune tunda aka fara maganar bata ce komai ba.

"Amma Alhaji kana gani anyiwa yarinyar nan ad......." Katsesa yayi.

"Ya isa Habeeba wannan ba huruminki bane" shiru tayi da bakinta tare da fadin "Allah ya kyauta"...

K'arshen tashin Asma'u ta shiga, rabuwa da masoyi da rana tsaka siddin akwai wahala, sai dai ya zama wajibi gareta tabi umarnin babanta, Ameena da itama d'aure kawai take amma k'anwar tata ta bata tausayi tasan zafin rabuwa, dafata tayi tana tare da k'arfafa mata guiwa(dan uwa rabin jiki, Allah ya barmu da yan uwanmu).

Wayarta ta d'akko ta kirasa amma ina bata zuwa saboda matsalar network, ko ranar da ya kirata saida yaje kan titi dan basuda network cikin gari, haka taita kira tak'i shiga, tsawon kwanaki uku amma ba labari, ana hudun kuma tace bama zata kira ba.

Ard'o kuma duk bala'inda iya Hari yi yayi kamar bai san tanayi ba, Sam bai yarda da tarbiyar Saude ba, kuma bazaiyima danshi auren dole ba, haka suka shirya tsaf shida Malam Garba da k'annensa guda biyu sai Abdulrahim suka doshi hanyar Argungu ba tare da sanin Iya Hari ba, Abdulrahim yaso ya kira Asma'u ya gayamata sai kuma yace kawai bari ya bata surprise.

Basu sha wahala ba gurin gane gidan dan sunbi kwatancen da Asma'u tayi, har k'ofar gida suka isa da motar da yake ta Abdulrahim CE, sunyi sa'a sun samu Baba k'ofar gida tarba ta karamci yayi musu, kamar yasan da zuwansu bayan sun gaisa sukayi mishi bayanin meke tafe dasu, mamaki ya kashe shi wato shi yarinyar zata renawa hankali, tambayan Abdulrahim yayi akan bata kirasa ta gayamai komai ba yace eh bata kirasa ba(kusrensa bai fad'a masa sunada matsalar network ba).

Gyaran murya yayi Sam bai nuna musu b'acin ransa ba "ah naji mi a tahe daku, idan a shirye kuke bani da buk'atar komai daga gareku sadaki kawai zaku bani a d'aure Auren yanzu" cikin mamaki suka shiga kallon juna kamar 'yarda aka gaji da ita.

Kamar yasan me sukewa mamaki yace "ko d'aya ban gajia da ita ba saidai ta zabi abinda takeso dan haka shi za'ayi Mata, kuma in Baku taho da niyyan aure ba to Ku tashi Ku tafi abinku, amma kai kar in sake ji ko ganin kafarka a gidana ko ka kira yata, ka fita hanyar ta gaba d'aya" ya fad'a tare da nuna Abdulrahim.

Duk ya k'ara d'aure musu kai, haka malam Garba ya Zare dubu 20 ya bashi ansa yayi tare da mik'ewa 10 ya d'auka na Sadaki 2 na goro, ya maida musu da saura, cikin k'ank'anin lokaci sai gashi da goro da wasu mutane nan take akayi Addu'a aka d'aura Aure, duk wannan bidirin da ake cikin gida basusan meke faruwa ba sun dai San yayi bak'i amma basusan su waye ba.

Nan yace su jira ya fito musu da Amaryarsu su wuce da ita, sudai kallonsa kawai suke mamakin duniya ya ishesu Abu kamar tatsuniya, ciki ya shiga tare da d'aure fuska tamau ya fara kwalawa Asma'u kira kamar hauka.

A tare suka fito ita Mama Ameena suma cikin mamakin kiran.

"Asma'u ungu wannan" ya mik'a mata kud'in, ansa tayi jiki a sab'ule.

"Sadakinki na inaso ki shiga ciki ki d'auko mayafinki Angonki na waje yana jiranki, saidai inaso ki sani tunda kin zabi Abdulrahim akanmu to daga yau bamu bake, baki sammu ba haka muma bamu sanki, kada ki kuskura kiyi tunanin mu ko tunanin tahowa inda muke, mun yafe masa ke har lahira" ba Asma'u kad'ai ba har Mama da Ameena saida kalamansa suka girgiza su, sai yanzu ta gane kuskuren ta na rashin fad'a mishi, ita kuma taki fad'i gudun matsala, Ashe hakan babbar matsala zai haifar mata.

Cikin sheshshekar kuka ta isa gabansa ta duka da duka gwuiwarta, bakin ta na rawa "Baba don....." Katseta yayi

"Kul kada ki yadda kice komai kiyi kawai yadda nicce miki" rik'e mishi kafafu tayi tana gunshekar kuka, Ameena kukan take haka Mama, Don tafi kowa sanin halin mijinta idan ransa ya b'aci Sam bayaji baya gani, zuciyarsa rufewa take.


Ameena ma ta bud'e baki zatayi magana ya hanata, haka Asma'u ta rarrafa inda Mama ta rungume ta itama Ameena zuwa tayi ta rungume su, suna haka saiga Mansur ya d'auko Abdool daga school, a cikin wanga yanayi suka isko su ga Baba tsaye sai huci yake.

Da gudu Abdool ya yaje ya rungume su shima yana kuka

"Mama kukan mi kukayi, Aunty kema kuka na kikayi, Mami kema" yana tambayan su yana yi shima gwanin tausayi.

Baba ganin zuciyarsa naso ta karaya yasa ya shiga sa kanshi ya d'akko mata hijab d'inta, ya saka mata ya jata, su mama na riketa suna magiya suna komai a banza, Mansur shima tuni hawaye suka wanke mishi fuska, Abdool shima rike ta yayi GAM.

"Baba ina zaka kai Aunty?"

"Abdulmajeed, Aunty bata buk'atar Ku, zan kaita inda wad'anda take buk'ata" ya fad'a tare da banbareshi ya mik'a ma Ameena, sannan yayi waje da Asma'u, Abdool sai kuka yake yana kiran "Aunty" amma Sam bata bai saura ra ba, haka magiyar su Mama suna kika duk bai saurara ba.

Yana fita bai zame ko'ina ba, sai cikin motar ya turata tare da basu Umarnin su wuce, anan su Ard'o suka fahimci da matsala, suka shiga bashi hak'uri akan ya tsaya a sananta, amma Sam yak'i sauran su, saima kashedi da yaka k'ara yi na karta sake ta tako kafarta gurin su, tare sa gayamusu ya yafe musu ita har lahira, ganin ransa ya gama b'aci yasa suka rubuta no- da garinda Suke idan ya wuce dan Allah ya kirasu, sannan sukaje mota suka tafi...

Asma'u na ganin an tada mota ta k'ara rushewa da wani irin matsanancin kuka................



>?&? @&=?F?


_Masoyan Abdulmajeed INA alfahari daku aduk inda kuke, pls kuci gaba da karfafa mini #ILVMNMd'guys# keep fallowing_






=؄?Meryerm Abdool=؄?
[8/9, 6:17 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)





*Yakai d'an Adam meye tak'amarka/ki, meye alfaharin da kake/kike, meye fad'in ran naki/ka, meye d'agawar taki/ki, keda/kaida farkonka/ki ya kasance k'azantaccin ruwa, tsakiyarki/ki fitsari da kashi, k'arshenki/ka abincin tsutsa, mushe to meye abun jinkai da nuna isa.*

Nasiha ce=?L?



_bazan gaji da gode muku ba, a zahirin gaskiya kune ni haka nice Ku, sai daku zanyi rubutu wato masoyana masu bani k'arfin gwiwa akan rubutuna, ina alfahari daku, ina rokon Allah yaci gaba da bani damar da zan rubuta abinda zai sakaku nishadi ya kuma amfanar da Ku, #heart u d' guys# ina k'aunarku a duk inda kuke #double love=?
?#_





=??? *Episode* 116-120





Tunda suka d'auki hanya, take kuka bil hakk'i da gaskiya, kuka take mai tab'a zuciyar mai sauraro, suma mutane cikin motar duk zuciyoyinsu a tsince suke, tausayin yarinyar ya lullub'e musu zuciya, shiru kake ji ba abinda ke tashi sai sautin kukanta, ba Wanda yayi yunk'urin dakatar da ita dan wani lokaci kuka rahama kana jin sauk'i a ranka, sanda tayi mai isarta, sannan ta tsagaita, hakan yasa Ard'o fara bata baki.

"Kiyi hakur'i 'yata duk da bansan ainihin abin da kikayima mahaifinki ba, yayi miki wanga hukunci, a gaskiya hukuncin yayi tsauri, saidai ki Sani su iyaye komai suka yima d'ansu to ya zama dole yayi hak'uri dasu kuma yayi musu biyayya mudin baici karo da Umarnin ubangiji ba, saboda sun riga sun gama dashi tunda suka haifesa, inaso ki rik'eni a matsayin mahaifi a gareki ni kuma nayi miki alkawarin zan zamo uba a gareki, kuma bawai ina nufin kibar iyayenki ba aa sunanan a iyayenki ba Wanda ya isa ya maye gurbinsu a gareki, kuma inaso ki d'age da Addu'a Allah ya sassauto zuciyar mahaifinki ya yafe miki kuma ya nemeki, muma zamu tayaki da Addu'a inshaa Allah".

Sosai taji dad'in maganar Ard'o, hakan yasa hankalinta yad'an kwanta, ganin tayi sa'ar suruki na gari, cikin nutsuwa ta gayamusu abinda ya faru, sun jinjina abun a ransu tare da gayamusu kuskurensu daga ita har Abdulrahim d'in, sannan kowa ya bata baki da kalamai masu dad'i, tare da gaya mata ta d'aukeshi a matsayin k'addararta domin rabon ayi auren ne yasa hakan ta faru, tare da sanya ma Auren Albarka, Abdulrahim dake jan motar shima jiki a sanyaye duk sonsa da Asma'u baiso Auren su ya kasance haka ba, amma ba yadda zasuyi dama tun ran gini tun ran zane sai fatar Allah yasan hakan shine mafi Alkhairi a garesu, Ard'o ko tuni yaji yarinyar ta kwanta masa a rai da alama zatayi hak'uri, haka dai suka doshi kilgori kowa da abinda yake sak'awa a ransa, kowa zuciyarsa ba dad'i......




***********************

Baba kuwa yana ganin sunja mota ya buga babbar rigarsa yayi cikin gida, anan ya jefar da takardar da suka bashi nan iska yayi gaba da ita, yanda ya barsu haka ya samesu suna kuka, kallonsu yayi cikin b'acin rai yace.

"Yanzu kunaga banyi muku dai2 ba ko? Baku dubi irin abin yarinyar tayi ba, ta nuna bata buk'atar mu a rayuwarta ta zabi wad'anda takeso amma Ku duk Baku gani ba, to bari kuji duk Wanda ya yadda ya kusanceta koda hanyar bani bashi, kuma ban yafema koda kuwa keda kike uwarta ne" ya fad'a cikin b'acin rai tare da nuna Inna, sannan ya buga rigarsa yayi waje.

Bai zame ko'ina ba sai gidan aminin nasa Malam Musa, dan gayama abin ya faru da Kansa kada yaji a wani gu, yayi sa'a kuwa ya samesa bayan sun gaisa ne yake bashi labarin abinda ya faru tare da bashi hak'uri.

"Kai amma Abu baiyi kyau ba, dama ko bakazo ba inada niyyan zuwa akan maganan, dama na samu Mustapha da maganan to shine yace shi gaskiya yana wacce yakeso abar zancen kawai, to shine naso inzo in fad'a maka sai kuma ban samu zuwa ba har ka taho.

Tsananin mamaki da imani ne yayi mishi yawa, yama k'asa magana lallai kowa ya daka ta mutane toya rasa turmin daka nashi, saida sukayi da mutumin nan komai lafia amma yanzu yace ba haka ba, shiya salawantar tashi 'yar akan farinciki wasu, yayin shi kuma ya bawa d'an shi abinda yakeso, nan take nadama ta rufesa lokaci na farko d'aya yi tir da (zuciya irin tasa na Ayusher).

"Alh, Abubakar bakace komi" boye damuwarsa yayi tare dayin murmushi yake Wanda yafi kuka ciwo "ba komai Alhaji Allah ya kyauta, sai anjima" ya tashi ya wuce ba tare dayace komai ba...

Gida kuma bayan fitar baba zaune saukai jugum suna jajanta wannan Abu d'aya samesu, wannan shine ga duka ka kuma tsunka jaka, Abdool Ameena takai d'aki Wanda yayi bacci sai ajiyan heart yake, sannan ta dawo inda Mama suna tattauna wad'annan ibtila'i dake bibiyarsu a d'an tsakanin, lallai Allah shike jarabtar bawansa suna fatar su zamo cikin masu cinye ta, Ameena gani take tafi kowa ganin rayuwa, Asma'un da ta rage mata mai bata shawara sa d'auke mata kewa gashi k'addara tazo ta rabasu, yanzu ma ta ina zasu samu labarin Asma'un bayan ko waya batada ita yanzu, dan daga ita sai kayan jikinta tabar gidan komai bata d'auka, gashi ta manta sunan garin dan tabbas ta fad'a Mata amma bazata iya tunawa ba, ko wacce irin rayuwa zatayi a gidan Aurenta a wannan yanayi sa taje musu zasu karb'eta kosu wulak'anta ta? Nan tayi saurin nema mata sauk'i gurin Allah, haka suka wuni gidan ba dad'i kowa sai jimami yake.

_such is life_


Baba kuwa k'asa komawa gida yayi bayan yazo gaf k'ofar gidan ya dudduba kozai ga wannan takardar amma ina bata ba labarin ta, jin yayi komai baya mishi dad'i, sai gashi hadda k'wallarsa sam baiyima Asma'u adalci ba, yafi kowa sanin biyayya irin ta 'ya'yansa amma ya rufe idonsa, lallai zuciya mugun nama CE, kowa ya biye mata zata kaishi ta baro ne, lallai kowa yahau dokin fushi k'arshen sa nadama ne (yana daga cikin karantarwar manzo S.A.W idan kana cikin fushi kada kayi magana sannan kada ka yanke hukunci cikin fushi dan k'arshen sa dana sani ne) Allah yasa mudace.

Sai dare ya samu sukunin komawa gida, shima jiki ba k'wari ya shiga, kamar yadda Inna ta saba tarbonsa haka ta tarbesa ba tare data nuna mai komai ba, kamar ba abinda ya faru, k'ara jinjina hak'uri irin na Inna yayi sau da yawa yakan tauye mata hakki shikansa ya sani amma bata taba nuna mishi damuwar, lallai mace tagari ni'imace(haka yake duniya d'an jin dad'i ce amma mafi jin dad'in ta Wanda ya dace da mace ta gari).

Haka suma su Ameena sukazo suka gaishe shi kamar yadda suka saba, zasu tashi yace su tsaya yanada magana, ayan da yayi maganan cikin taushin murya, abun har mamaki ya basu, nan dai ya labarta musu yadda sukayi da Abokin nasa, tare da nuna musu nadamarsa.

"Alhaji ka dad'e kana tauyeni sau da yawa kana maida damuwar kowa ba damuwa, damuwarka kad'ai kake dauka damuwa, kama rayuwa da fushi kana yankewa mutane cikin fushi, to yanzu gashi wagari ya waya, ka salwantar mana da yarinyar akan son ran wasu, me kayi kenan" Inna ta gayamai magana cikin nutsuwa.

"Baba shiyasa ake son bawa mutum uziri a rayuwa, lokacin da ka shigo nida Asma'u munaso muyi maka bayani amma haka rufe ido kak'i bamu dama" nan ta basu labarin abinda ya faru a lokacin da Asma'u ta kira Abdulrahim" Amma kayi hak'uri In na fad'i ba dai-dai ba".

"To kaji ma abinda ya faru ko amma saboda rashin bata uzirunka a rayuwa kak'i sauraren kowa".

Shiru baba yayi nadama na k'ara lullub'esa, duk abinda suka fada gaskiya ba karya, sai hango lokacin da Asma'u take rik'e mishi kafa takeyi amma yayi biris yak'i saurarenta, tuni tausayinta ya kamashi lallai baiyi Mata adalci ba.

Hak'uri ya basu tare da tabbacin inshaa Allah zai nemota duk inda take.

Kwana ki sun shura watanni sun wuce kullum Baba yawon Sokoto da garuruwanta saidai kuma ba'a dace ba, ganin abin yayi yawa duk ya dami Kansa yasa Mama cewa.

"Ka hak'ura da yawon nan haka idan da rabon mu gaba zaka ganta ta kawo Kanta har gida, idan kuma babu rabo zafin nema bazai kawo samu ba, hakan ya hak'ura dole tare da bibiyarta da Addu'ar fatan Alkhairi aduk inda take.

Ameena kuwa zuwa yanzu zaman gida ya gama isanta gaba d'aya saukinta ma tana teaching da Baba ya samo mata yanzu tsawon shekara biyar kenan da rabuwarsu gashi duk masu zuwa sun d'auke kafarsa, a halin yanzu ba abinda takeso irin tayi aure shine akwai kwanciyar hankalinta (dan Mace komai kamewarta, idan batada aure to mutuncinta ragaggene a idon mutane, balle kuma wad'anda suka d'auki zawarci a lasisin iskanci suka samu tunda yanzu su zawarane ba namijin da zai Aure yace yana Neman budurci, to ai ba anan gizon yake saka ba, walla d more kikayi zina kina bazawara bakida wani hukunci daya wuce a jefeki, ba riba kenan, a tunani zawarci wata damace da mace zata K'ara sanin rayuwa, ta kuma gyara halayenta, kowanne aure yanada sila a rabuwarsa saiki duba meya kashe miki aure dan gyarawa gaba, bawai ki lalace ba, Allah yasa mudace) ayuwar zawarci rayuwace mai cike sa kalubale da tashin hankali, zaman gida ya gama isarta yau idan mace takai munzali tofa da batayi Aure ba, zaman sai kasance gashi nan dai na ganin laifi ne keda iyayenki, shiyasa Ameena ta damu sosai da rashin Auren, sai ba yadda zatayi dan tasan komai lokaci ne.

Yau kamar kullum Mansur ne yaje ya d'auko Abdool daga school, da gudu ya shigo yana murna "Mami kinga Nina yi na d'aya" ya fad'a yana nuna mata result d'in da gift d'inta aka bashi.

"Iyye yaron Inna kaifa akwai rashin ji amma akwai k'ok'ari" Jan tayi zuwa jikinta tana duba idonsa "waini kam idon nan naka Abdool anya lafia ko?"
Inna dake fitowa tace "me idon yayi?"

"Kiga farin yana surkawa da pink," duba idon Inna "tabbas ya kamata kuje asibiti" shikam sai k'ok'arin nunama inna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login