Showing 36001 words to 39000 words out of 88300 words

Chapter 13 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1596

dak'ile bata koda kalli inda yake ba, dan ita har yau haushinsu takeji shida uwarsa, Rafia kowa sai wani son munafurci take nuna masa amma shi Sam bata kwanta masa a rai ba tunda ya ganta(INA kuwa kaga shedan mai raba aure).

A tare dashi akayi jinyar Alhaji har murmure, aka sallamesu a part d'in Alhaji ya tare wadda hakan yasa ta daina shigowa, satin sa 1 yace zai koma saboda makaranta, nan Alhaji ya d'auko wasiyyar mahaifinsa ya danka masa, d'akin da ya zama NASA a part d'in Alhaji ya shiga ya, direct da diary ya fara.

_"zuwa gareka d'ana abin Alfahari sanyin idaniyata, kayi hak'uri d'ana nasan koda wasik'a ta zata sameka, zakace banyi maka adalci ba dana barka tun bakasan waye kai ba, nasan zaka zargeni da tauye maka hakk'inka, saidai ina da tabbacin Ameena zatayi dutyn ta ta kuma had'a da nawa tayi, saboda na yadda da ita"_

Hawayen da suka zubu masa ya share tare da cewa "wannan hakane Abba Mami mace tamkar dubu" sannan yaci gaba, duk wani labari tun daga had'uwarsu da Ameena auren da k'uncin da ta shiga da soyayyar da Asma'u ta nuna masa har zuwa rabuwarsu saida ya rubuta masa, zuwa yanzu kuma yake harda majina yana tausaya iyayen nasa, tare dajin k'ara son aunty Asma'u dayi mata Addu'a akan Allah ya bayyana ta, sannan yace "Abba banga laifinka akan komai ba sai akan tafiyar ka meyasa Abba? Meyasa zaka tafi ka barni, shin kayi tunanin rayuwar da zanyi? Meyasa ka guji mahaifarka kabar iyayenka da begenka, kana ina Abba!? Where r u Abba??" Ya fad'a da k'arfi cikin sheshekar kuka.

Alhaji Sada ne ya shigo jin k'aran sa, yasan za'ayi haka duk baisan mai wasik'ar ta k'unsa ba, dagoshi yayi tare da rungume shi yana dan bubbuga masa baya, alaman rarrashi "yi Hak'uri Abdulmajeed ka d'auke shi a matsayin k'addarar ka, ka yafewa mahaifinka tare da masa fatan Alkhairi kaji" rarrashinsa yayi da kalamai masu kwantar da zuciya....

A ranar yaje banking, ya girgiza da ganin tsabar kud'in da mahaifinsa ya aje, masa kud'i bana wasa ba, tun lokacin bare kuma yanzu da komai ya canja, (Allah ya zuba Alkhairi a harkar kasuwanci, don abinda annabawansa sukayi Kenan, muddin bawa zai tsarkake sana'arsa tabbas zaiga akhairai a ciki).

Transfer kud'in yayi zuwa account d'insa, nan ya nemi shawarar Alhaji akan yadda zaiyi da kud'in dan kud'in da yawa kuma shi baya da buk'atar kud'i dan Alhaji ne ke d'auke da karatunsa yanzu tun bayan rasuwar Yusuf, kuma shima yana dan business dan Abdul yarone da yasan ciwon kansa, ko lokacin da yake Argungu shik kula shagon kawu Mansur in ya shiga school kuma tsab zai dawo ya isko kayansa, haka Mami na turo mishi sosai duk da yana cewa ta barshi.

Alhaji shawarar a fara Gina mishi hospital ya bashi tun da medicine yake karantawa, hakan kuwa akayi dan itama Mami hakan tace nan suka sayi fili mai kyau aka fara tsara hospital ta gani a maganta inda kawu Mansur ke kula da ganin da yake yana gari.


*****************


B'angaren Asma'u kuwa yanzu bata da wata matsala dan ba'ayi mata sai in taje Wanda zuwa yanzu ta Saba da jarabar Iya Hari, Abdulrahim kuwa ya rik'e ta da Amana kamar yadda yayi alk'awari suna zaune lafia abinsu bakajin Kansu ko sabani suka samu suke shirya Kansu ba tare da wani yaji ba, Ramlah kuwa sai girma take abinta ga kulawar iyaye tana samu suna matuk'ar kula da ita da bata tarbiyar islama, tuni ta iya haruffa k'ananan surori tana 4 year, er lukuta da ita yanayin jikin irin na Asma'u ne, nan kad'ai suke kama.

A 'yan kwanakin nan mafarkin su Baba da Inna da Aunty Ameena, Abdool ya matsawa Asma'u har yakai ko kwanciyar rana tayi sai tayi, hakan yasa hankalinta ya koma gida baki d'aya, yanzu kam ta shirya runkarar Baba duk da tsawon lokaci bai nemata ba, amma tana fatan idan taje ya yafeta ya maida mata iyalanta, hakan yasa ta tunkari Abdulrahim da maganar son zuwa gida, hakan yayi mishi dad'i sosai dama ya dad'e yana bibiyarta suje tana cewa ba yanzu ba, suka tsara zasuje k'arshen sati.

Da sukaje Ard'o da zancen yayi murna sosai, dama shima ya dad'e ya maganan zuwan, iya Hari ce sai tace taje ita kad'ai da 'yarta amma bada d'anta garin mayu ba, nan ma Ard'o yayi mata fad'an ta daina haka aiko su waye an Riga an zama d'aya tunda ga zuria anyi dan Asma'u na d'auke da wani cikin Wanda harya fara fita.

Koda suka tashi tafiya suka nemi Ramlah suka rasa 'yar gidan Lanti ta shiga gari da ita daga zuwansu hakan yasa sukace zasu wuce, Ard'o yace suje in yaso idan sun shawo Kansa sai su je gaba d'aya hadda su, iya Hari tace bada ita ba gaisuwar uwar kishiya. Lol

Tunda suka d'auki hanya zuciyar Asma'u ta tsinke, tunanin ya zasu k'arke da Baba, tuni ta fara zubar da hawaye, hakan ne ya tada hankalin Abdulrahim ya shiga lallashinta sam hankalinsa ya koma gareta baiji odar da ake masa sai da yayi gab da motar nan ya taki birki da k'arfi Wanda yayi sanadin suka yanke daji, duk sun rud'e ya rasa makama ba abinda ke fita bakinsu sai "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" kiiiiiiii!! Kakeji sun bugi katon icce Wanda yayi dai2 da kamawar motar da wuta....

Koda ja'ama sukazo saidai gawarwaki amma abin mamaki wutar bata kai cikin motar ba so bata k'onasu ba, amma kuma ba rai a tare dasu.

_subhanallah such is life, Allah yasa muyi kyakyawan k'arshe_


Ta hanyar id card jami'an tsaro suka gane garin su, sai gawarwaki aka dawo ma su Ard'o dasu abinda bai wuce 1 hour da rabuwarsu, Allah sarki Ard'o dattijo mai nutsuwa, duk da hankalinsa ya tashi amma sam nutsuwa bata bar jikinsa ba, shida Kansa yayi musu wanka, aka sallacesu dashi aka Sada su da gudansu na gaskiya Wanda kowa sai yaje komai daren dad'ewa.

Iya Hari fa? Sai ihu take zunduma tana fad'ar maganganu na sab'o da rashin hankali, some some ko ba iya sai dai duk a banza dan wannan duk bazai dawo dasu ba, haka aka zauna zaman makoki, mutuwar Abdulrahim ta tab'a gaba d'aya k'auye Kilgori da kewaye dan kowa yasan shi yasan Alkhairinsa da taimakonsa, haka itama Asma'u ga tausayin ta na bata samu ta sadu da iyayenta ba, rayuwa kenan ga Ramlah marainiyar Allah kowa ya kalleta saiya zubar da kwalla, sai Neman Ummi da Abi take tana kuka gwanin tausayi.

Iya Hari tayi sanyi dan mutuwar Abdulrahim ta tab'a sosai d'anta mai biyayya gareta mai kyautata mata, dama sai babu kai ake gane kirkinka ko rashin sa.

Bayan sati d'aya Ard'o da kanshi yaje Sokoto ya tattara duk wani Abu nasu akazo akayi rabon gado, na Ramlah dana dangin mamarta, sokoto jaye ya bud'e account ya zuba su, sannan ya boye duk wani Abu da yake mai Amfani ne gareta, dan yasan Hari ladabin kura ne tayi, hakan kuwace ta kasance dan tunda kafafu suka d'auke ta tada mugun halin ta, har cewa tayi Asma'u takai mata d'a garin 'yan shan jini an shanye(sai kace ita bata mutu ba amma kuma Abu ga jahili ayi mata uziri) tsabar uwar sai tattaro ta dawo kan 'yar bata mata komai na dangin wanka, wanki da duk wani Abu, duk Ard'o ne keyi mata saiko Shatu in tazo kota aiko a ansa, amma iya Hari da Lanti zagi da duka ne kawai ke had'a su, haka ta kashe kayan Ramlah ta bawa yaran Lanti dan tasan Shatu kota bata bata ansa daga k'arshe ta bita da guntuwar nasiharta, tun Ramlah bata fahimtar komai ta gane Iya Hari bata sonta tun batasan meye zagi ba da duka ba harta k'ere dasu, kullum magana Ard'o keyi amma a banza bataji sai abinda ya k'aru, tuni sunanta ya koma Laure abinka da k'auye, Ard'o ne kawai ke kiranta sunanta na asali, tun tana fad'a har saba itama saidai Sam batasan sunan.

Ganin wahala na shirin kashe k'aramar yarinya yasa Ard'o zuwa Argungu kozai gane dangin mahaifiyarta ya hadata dasu amma shiru ba labari haka zaije tun safe har marece ba sa'a haka yake dawowa cike da tausaya mata, duk wani aikin gidan Ramlah ke yinsa ga zagi da duka kamar ganga, talla kuwa tafi kowa a garin safe rana dare aikin kenan, wahala kawai ta sani a rayuwarta, duk Ard'o na iya k'ok'arin amma anfi k'arfin sa ne, dan da maganar da babu duk daya ga Iya Hari.

Haka ya sakata boko, ta fara kamar abin kirki, tana aji hudu Hari ta tada k'ayar baya, ita batasan ta famdare mata kamar yadda ubanta ya famdare akan boko, haka tanaji tana gani ta fidda ta, saida Malaman makarantar suka suka gayama Ard'o dan Ramlah na cikin d'alibban da sukeji dasu saboda hazak'arta, yace suyi hak'uri, amma Iya tayi mirsisi ta hana, karshema sai dukan tsiya yaja mata dole ta gayamai bataso da Kanta, yasan ba yin Kanta bane amma ya kyaleta dan yasan tunda Hari bataso to magana ta k'are, haka Ramlah ta tashi cikin wahalar rayuwa ga Ard'o da Gwaggo Shatu kawai take jin dad'i, haka take rashin iyaye tasan da sunanan da bata tagayyara ba, suma dangin mahaiyarta kullum fatar ta Allah ya bayyana mata su, Ramlah kenan, yarinya k'arama taga rayuwa......


*ASALIN LABARIN KENAN*



MUJE ZUWA YANZU MUKE FA>?8? @&>?8? @&?& @&>?>? @&


_yan uwa wad'anda suka damu da rashin ganina suka bincikani nagode sosai da kulawarku, kuma na samu lafia sosai saidai mura ta rage>?'? #one love#_




=؄?Meryerm Abdool=؄?
[8/17, 3:52 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



*=ؘ? d best way 2 love is to love and to be loved by sake of Allah*=ؘ?





=??? *Episode* 136--140






*CIGABAN LABARI*



Kallon kallo, Abdool da kawu Mansur suka shiga yiwa juna alaman tambaya k'arara a fuskar su, Mansur yayi k'arfi halin cewa "Baba kunsan juna ne?" Kasa magana Baba yayi sai nunashi da yake da yatsa baki na rawa..

"Alhamdulillah! Mashaa Allah" shine kalmar da Ard'o ya fad'a tare da k'arasawa fitowa daga zauren ya tunkaro inda suke.


"Dak'yar Baba ya iya bud'e baki yace " Malam Umar ina Asma'u tah, ina 'yata? Ina buk'atar ganinta ina take Malam Umar" duk cikin firgici yake maganar.

Jin abinda Baba yake fad'i yasa Abdool zuwa gabanshi da sauri ya rik'e hannuwansa "Baba Aunty Asma'u kace fa? Yasan inda take ne? Yimin magana Baba" kai kawai yake juyawa ya k'asa cewa tak.

Cikin nutsuwa Ard'o ya kama hannun malam Abubakar sannan ya kalli su Abdool dake tsaye hankali a tashe "kuzo muje daga ciki wannan maganar bata tsaye bace" ba musu suka shiga ciki kamar yadda yace.

Da sauri Alhaji Sada ya taso yana bawa Alhaji Abubakar hannu don su gaisa, shima hannun ya bashi suka gaisa, saidai ganin yanayin yadda suka shigo abin ya bawa kowa mamaki Allah dai yasa lafia.

Zama sukayi bayan an gaisa a fizge abinci aka gabatar musu, amma ba Wanda yayi sha'awar yaci, Malam Abubakar ne ya sake kallon Ard'o cikin rauni "Malam Umar kayimin bayani Ina 'yata ina mijinta Abdulrahim?" Malam Garba jin an ambaci Asma'u da Abdulrahim yasa ya k'ara kallon Baba da kyau tabbas shine bazai manta fuskar ba.

Shima Alhaji Sada cikin son k'arin bayani dan yasan lokacin da abin ya faru da irin Neman da Baba yayi tayi yasa ya kalli Ard'o, su kam su Isma'il basu San komai ba shiru sukayi suna saurare.

Nisawa Ard'o yayi "tabbas bansan ya kake da Abdulmajeed ba, amma zuwanka nan yayimin dad'i ba kad'an ba, kazo lokacin muke matuk'ar son ganinka" nan ya shiga basu labarin abinda ya faru komai bai boyeba har cutar war Hari gareta zuwa Rasuwar su da halin da Ramlah ta shiga zuwa neman sa da yayi tayi sannan yace "ko cikin satin ga natahi Argungu don kawai na nemawa Ramlatuna dangin mahaifiyarta suzo ayi aurenta dasu amma ban dace ba ashe zaka iskoni har gida" ya k'arasawa maganar idonsa jajir don tunawa da mutuwar 'ya'yan NASA.

Baba kam kuka yake sai hawaye wani nabin wani duk taurin zuciya irin nashi Ashe iyakarsa da Asma'u kenan ba rabon ya kara ganinta balle ya nemi yafiyarta, haka Abdool da Mansur, Alhaji Sada sai jinjina lamarin yake yi shida malam Garba, su Isma'il ma jikinsu sanyi qlau, Abdool yayi k'arfin halin magana.

"Yanzu Baba kana nufin Ramlah 'yar Aunty Asma'u ce?" Cikin ransa kuwa girmama al'amarin ubangiji yayi "Dama asje dan wata gaskiya ta bayyana Allah ya k'addaresa da zuwa Yabo service kuma ya had'ashi da Ramlah ya kinsa mishi k'aunar ta, ashe soyayyar su ta jini da hanta ne, dole yaso jinin Aunty Asma'u dan tayi mishi komai a rayuwa.." Maganar Ard'o ce ta katsesa.

"Tabbas Abdulmajeed Ramlatu jinin jikin Asma'u CE, kuma jikar Malam Abubakar CE, saidai kai bansan ya kake da Malam Abubakar amma jikina na gayamin kaima jinin Asma'u ne?"

Kawu Mansur ne yace "tabbas Allah yayi gaskiya shine keyi a inda yaso kuma Wanda yaso, dani da Aunty Asma'u da Aunty Ameena duka abu d'ayane uwa d'aya uba d'aya".

" ikon Allah kaddai shine Abdool d'in da Asma'u ke yawan fad'a kai kuma Mansur ko? Lallai Allah mai girma ne, Ashe ma kai Yayan Ramlatu ne, kaga aikin rashin sani"(Wanda yafi dare duhu).

Sai lokacin Baba ya samu magana Wanda tsananin danasani yake k'ara rufeshi lallai idan baka godewa Allah ka godewa azabarsa, ko yaushe zai daina Dana sanin wannan kuskure dayayi? "Yanzu Shikenan nida Asma'u ta tahi ba tare data yafeni ba".

Dafashi Ard'o yayi " ka dena fad'ar haka Malam Abubakar, Asma'u bata tab'a rik'eka a rai ba kullum Kanta take d'ora wa laifi, ba safiyar da bata Neman tafiyar ka, har ranar mutuwarta maganar kenan ka yafeta" jinjina kai yayi.

"Asma'u na yafeki tun dad'ewa nifa ki yafeni, naso na had'u dake koda sau d'aya na rok'eki, Allah yayi musu rahama baki d'aya Allah ya Albarkaci abinda kuka bari" nan kowa ansa da Ameen anan aka sake kwararo musu Addu'ar Neman gafara da rahama, kowa jinjina lamarin yake, da k'ara girmama girman Ubangijin talikai (Allah mai girma buwaya).

Nan suke tambayan Ramlah, Ard'o zasu ganta bada dad'ewa ba....

Abdool kuwa zame jiki yayi ya kira Maminsa dan yanzu network a kilgori har d'akin ka, bayan ta daga ne sun gaisa yace.

"Mami yau naga wani bak'on Al'amari".

"Meya faru Abdool?"

"Hmm Mami zakiyi farinciki da abinda naji yau, nasan har tukuici zaki bani".

"Oh nikam meye wannan fad'amin mana".

"Mami maganar tafi k'arfin a fad'eta gani yafi, ki shigo mota yanzu ki ganema idonki".

"To ai bansan gurin ba matsalar".

"ki taho yabo daga kin iso kimin waya zanzo na d'auke ki"

"OK" kawai tace dan ta k'agu taga meye wannan da baya fad'uwa, shima da sauri ya koma saboda jin an fara Hudubar juma'a....


********************



Delu ce ta gifto ta masallaci ta fito da gida gurin d'akko kayanta, dai2 lokacin taji mai shela na fad'in "madallah aure ya dauru an d'aura Auren *Abdulmajeed Auwal da Ramlah Abdulrahim* kan Sadaki naira dubu 50k, lakadan ba ajalan ba fatar Allah ya d'aure ya basu hak'uri" tanajin haka cikin farinciki ta kwasa da gudu sai gidan Gwaggo Shatu tana haki tana fad'in.

"Laure Ashe dama dan binni ne mijinki, shine kika k'i hid'imana" Ramlah cikin tsananin kad'uwa ta kalleta dan son tabbatar da maganar daga bakinta take fitowa.

Gwaggo Shatu ce ta dafata tare da girgiza mata kai alaman gaske ne, da yake ita tasan komai, sauke idonta kasa tayi tama rasa gane yanayin da take ciki, jinta take kamar ba ita ba kuma kamar mafarki takeyi.

Gwaggo Shatu ce ta mik'ar da ita tsaye tare da Kama hannunta janta zuwa d'akin ta, wani hadd'ad'en materia??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????l ne milk color anyi mishi ado da fulawowi coffee color, lallausa dashi sai k'amshi ke tashi Ard'o ne ya dinka mata, Cikin sa Shatu ta shirya ta tare yi mata kwalliya mai kyau irin ta 'yan binni, mayafi coffee da shoes coffee suma wow Masha Allah zanso Ku hango Laure a kwalliyar dama gata mai kyau ce.lol ba Irina ba


A can masallaci ana maga d'aurin Aure, Abdool yaji vibration din k'aramar wayarsa dake cikin aljihu, sallat ya zare jikinsa ya fice, Maminsa ce ke kiransa ta iso yabo, hakan yasa bai tsaya ba yaja mota zuwa d'auko ta.

Jauro kuwa Wanda kamar an aiko sa yau ya halarci sallar juma'a Wanda salla sai tayi masa suger yakeyi, cikin kaftan kamar mutumin arziki, bayan an gama salla yaji ana sanar war za'a d'aura aure har zai tafi kuma sai ya tsaya, abinda kunnensa ya jiyo masa ne yasashi dask'arewa nan wai Laurensa aka aurawa wani, ihu yayi iyakar k'arfin sa Wanda ya janyo hankalin jama'a cikin d'aga murya yace.

"Kan ubanga waiisa ya Armi Laure bayan ni, kai liman maza warware armen nan dan bai d'auru, ni kad'ai ne mijin da zai Armi Laure, dan tawa ce nid'ai" sai sambatu yake, mutane kuwa sai kallonsa suke, 'yan gari kam basuyi mamaki dan sun san waye Jauro.

A hankali Ard'o ya tako zuwa inda yake, "Lamiru" Ard'o ya kirashi da asalin sunan shi, kallon shi yayi tare da ansawa dan duk iskancin Jauro yana shakkar Ard'o, duk zuwa gidansa da yakeyi sai tabbatar bayanan.

"Na tab'a alk'awarin baka Ramlatuna koda da rana guda ta?"

Girgiza kai yayi tare da cewa "Aa" murmushi Ard'o yayi.

"Madallah, to ni adda hakk'in armar da Ramlatu ga Wanda nikaso kuma Lokacin da nisso, kuma gashi nayi, dan haka kama gabanka kuma kar in sakejin ka taka gidana" babu gardama ya juya tare da ficewa daga masallacin tare da k'udure haduwarsa da Iya Hari ba kyau.

Duk Wanda ke cikin masallacin abinda Ardo yayi ya burgeshi, dama sun san shi kad'ai ne maganin Jauro da d'iyar wani daban ce da Allah kad'ai yasa yadda zasu k'arke.

Bayan komai ya lafa ne aka dunguma zuwa masauki saidai koda aka duba Abdool babu shi, haka suka koma Wanda zuwansu yayi daidai da isowar Gwaggo Shatu da Ramlah da Ard'o yace suzo bayan D'aurin Aure, tun da Baba ya ganta zuciyarsa ta bashi itace Ramlah dan ga yanayin Asma'u a tartare da ita duk kuwa da basa kama, tafiyar su tsayuwa duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login