Showing 18001 words to 21000 words out of 88300 words

Chapter 7 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1606

dashi, da yake itama innarsa marainiyace, dangin mahaifi kawai suka rage mishi.

Zaman k'auye ba dad'i koga Wanda ya saba balle wanda bai saba ba, amma ya zama dole haka Abubakar ya dawo d'an gona, kullum suna gona, amma da yake jarumine hakan bai wani damuwarsa ba, lokacin da Hutu ya k'are ya taso da maganar komawa, ina wuta in fad'a haka sukayo caa su basusan wannan zancen ba, saidai yabar karatu, shi kuma ya had'e kai da fata akan yanason karatunsa, ganin ya nace suka yadda ya koma amma da sharad'in sisin su ba zata shiga ciki ba, haka ya koma makaranta bako asi nasu.

Allah ya taimakeshi daf da faruwar wannan abun babanshi ya tura mishi kud'i masu dan dama saboda karatunsa dama kuma yana d'an bige bigensa, da haka ya samu ya biya kud'in makaranta, sannan ya sayi mashin ya fara achab'a, da haka yake biyan kud'in makarantar sa yake d'aukar kan shi haka dai da dad'i ba dad'i har ya kammala diploma, bai wangarta ba ya cika D'E form ya jona HND, yakanje gida ya gansu lokaci zuwa lokaci, su kuma sun zuba mishi ido cewarsu idan ya gaji da kanshi zai dawo.

B'angare gida kuma yana gyaran tsohon gidansu daya k'one, haka ya kammala karatunsa cikin nasara, zuwa lokacin yasan rayuwa dan ya ganta kala-kala saidai ya yadda ba maraya sai raggo, dan haka ya k'ara zage damtse da neman na Kansa, ana hakane Allah ya had'a shi da Habiba anan Argungu, k'anwar wani abokinsa ne, nutsuwarta da hankalinta ne yaja ra'ayinsa gareta, bawani sha wahala ba wajen amincewarta.

Bayan sun sasanta ne yaje gurin danginsa da maganar, bud'ar bakin su cewa sukayi yanada gurin ajeta baiyi mamakin jin haka daga garesu ba, in yayi la'akari da yanda suka danne mishi gadonsa ya lura da mutane su da Kansu kad'ai suka Sani, fatan shiriya yayi musu sannan ya gayamusu ya gyara tsohon gidansu.

Ba'a d'auki lokaci ba akayi aka gama aka dangana da Amarya Habiba gidan angonta, zama sukeyi gwanin sha'awa dan Habiba akwai hak'uri, ko sabani suka samu ko itace mai gaskiyar zata hau bashi hak'uri, shiyasa ba'ajin Kansu duk da Abubakar ya zamo mai zafin zuciya da kafewa akan abu daya.

Haihuwarsu ta farko Mahmud Wanda yaci sunan babansa yana d'an shekara biyu ya rasu daga nan kuma sai Ameena, Asma'u sai auta Mansur.

Suna cikin hakane Allah ya kaddari Abubakar da samun aiki, sunyi farinciki sosai da wannan ci gaban da suka samu, sun wadatu da komai na rayuwa dai2 k'arfi baifi jiki ba, cikin 'yan shekaru ya gina musu gida mai kyau irin dai na mai k'aramin k'arfi, haka yaransu suka tashi cikin tarbiya musulunci.

Amina da Asma'u ba wasu kyakyawa bane na gani kasheshi hasalima ba za'a sakasu cikin ajin farko irin dai bamu cikin 'yan tusa 'yan zawo sun tseremana saidai kam Allah ya azutartasu da diri mai matuk'ar d'aukar hankali Wanda ba namiji ba macce ta gani sai taji kishi. Lolx

Shiyasa kullum suna cikin hijab gudun yad'uwar fitina a al'umma, sannan Allah yayi musu baiwar sauti wato murya kenan, mai matuk'ar sanyi da d'aukar hankalin mai sauraro.

Lokacin su Ameena suna SS3 sun taho ten days d'in nan da ake bayarsa dayake boarding school Suke, Asma'u tana SS2 lokacin, da yammaci taje gidan wata k'awarta Firdausi anso wani Abu data manta a hannunta, bayan ta Amsa sun fito kenan zata wuce gida, a k'ofar gidan sukaga wata mayyar mota ta tsaya k'ofar gidan, wani had'adden guy ne ya fito ciki ba laifi yanada kyau dai2 shi, ga iya wanka, dan kam ya wanku ba k'arya.

Cikin farinciki Firdausi tace "Oyoyo Yaya Auwal kaine a garin yau" glass d'in idonsa ya gyara ma zama yana murmushi yace "Fido 'yar mama kece kika girma haka?".

Murmushi kawai tayi, ita kuma Amina gaidasu tayi tare da jan hannun Firdausi alaman su tafi.

Kallonta yayi Sam bai kula da ita ba wani shock yaji har cikin d'an yatsarsa, dakyar ya ansa da lafia, Firdausi CE tace " Yaya zan rakata na dawo, suka wuce.

Baima ji me take fad'a da kallo ya bisu har suka karya kwana, sannan yayi smiling tare da Shafa Kansa.

Anan Firdausi ta sameshi yanata Murmushi shi kad'ai "Aa Yaya meyasa baka shiga daga ciki bane".

" uhm Fido wannan k'awar taki fa"?

Murmushi tayi "Laa Yaya kaddai kasa..."

Katsaeta yayi "Nidai ina ne gidansu wlh tayimin".

" Aa Yaya daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i? Nidai mu shiga ciki ka huta zan yi maka bayanin komai " ta fad'a cikin zolaya dama taubashinta ne..................





_nayi muku typing mai yawa na taho zan tura ya goge=?"? kuyi manage_ =??


*muje zuwa >?8? @&*






=؄?Meryerm Abdool =؄?
[8/1, 8:03 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)





=??? *Episode* 86--90



"Fido ina wasa dake ne wai? sai yawo da hankali kikemin, jiya dak'ar nayi bacci tunanin yarinyar ya Addabeni, sonta nike da gaske, pls joke a part ki gayamun mana" tunda ya fara magana Firdausi ta kwalalo ido tana kallonsa dan ita ta d'auka wasa yake amma yanzu kan tana gaskiya a cikin idonsa.

Zama tayi bayan ta d'ora break d'inda ta kawo mishi kan center table "Ya Auwal Allah na d'auka da wasa kakeyi, amma kayi hak'uri, indai akan Ameena ne bakada matsala".

" Ameenah!" Ya maimata sunan cikin lumshe ido.

"Wow what nice name" dariya Firdausi tayi ganin yayan nata na shirin zarewa, "lallai ma Yaya abun naka azimun ne".

"Hmmm ba zaki gane bane, yanzu dai ya za'ayi nifa tayimin sosai ina ne gidansu".

" kwantar da hankali yaya zanje nayi magana da ita nasan batada matsala, komai zaizo yadda kakeso".

"Yawwa Auntan Mama zaki kuwa samu tukuici mai tsoka" dariya tayi "yanzu dai kayi karinka anjima kad'an zakaji yadda mukayi" sannan ta fice.

Koda taje gidansu Ameena ta sameta tana taya Mamanta aiki, bayan ta gaida Maman, Ameena ta jata zuwa d'akin su.

"K'awata da sassafe haka, fatar dai lafia"?

Nisawa tayi " lafiyarce ta kawo haka...." Nan ta koro mata jawabin abinda ya kawota.

A firgice Ameena ta kalleta tana girgiza kai " Aa Fido bazan iya ba, pls ki bashi hak'uri kawai".

B'ata rai Firdausi tayi "kome yasa ko kinada Wanda kakeso ne daban?"

"Ba haka bane....." Katseta tayi.

"Nagane jini nane bakyaso wato, nina d'auka na wuce haka a gurinki Ameena, har ina bashi tabbacin samunki, ashe nice ke haukana, well thanks" tare da mik'ewa shaye da toka.

Riketa Ameena tayi "wlh ba haka bane Firdausi kuma bawai sonsa ne banayi ina tsoron Baba ne, baya barina tsayuwa da saurayi ban tab'a yi ba, amma kiyi hak'uri".

Komawa tayi ta Zauna "indan wannan ne, Baba ya hanaki kula samari saboda gudun b'ata gari da kuma karatunki, yanzu kuma meya rage mu k'are? Kad'an ne, sannan kada kiyi kwankwanto akan Yaya Auwal mutumin kirki kuma da gaske yazo gareki, amma idan kinji baki sonsa har ranki, to wannan daban ne, dan ba'a dole a soyayya" ta fad'a tana kallonta.

Ita kam tun jiya data ganshi taji ya kwanta mata a rai saidai a gaskiya tanason karatu, kuma muddin Baba ya gane tana soyayya tasan aure ne k'arshe maganar.

Tabota Firdausi tayi "bakice komai ba?"

"Fido in nace banason sa nayi k'arya, amma gaskiya karatu nakeso nayi" dariya Firdausi tayi.

"Lallai ma Meenal to aure na hana karatu ne ko karatu na hana aure?"

Lumshe ido tayi "ya danganta da kalar mijin da ka Aura".

" Hmmm Yaya Auwal baida matsala kamar yadda na fad'a miki, kedai in har kina sonsa ki amince kawai".

Ba yadda ta iya da rigimar Firdausi haka ta amince, tsallen murna kawai Firdausi keyi sunyi nasara, itadai Ameena sai dariya take mata, nan ta wuni gidan tare sukayi aikin rana sai bayan Azzahar ta wuce cike da farinciki dan zatafi kowa murna yayanta zai auri Aminiyarta.

Lokacin da taje masa da labarin amincewarta murna kamar ya taka kan jariri, amma ta bashi shawarar yaje gurin Babanta kai tsaye.

Lokacin da ya samu Malam Abubakar da zancen, yaji dad'in hakan domin ya nuna mishi yasan Kansa bai tari 'yarsa kai tsaye ba, yace yaje zaiyi bincike akansa idan ya gama zai nemesa, ansar number sa yayi tare dayi masa godiya.......



******************


*WAYE AUWAL*

Auwal Muhammad Sada shine cikakken sunansa d'ane ga Alhaji Sada canji, tsohon d'an kasuwa Wanda yayi suna a duniyar canji, mutum ne na mutane duk da tarin dukiyarsa hakan bai saka mishi girman kai ko d'agawa ba, kowa nasane, yanada matar aure d'aya Hajiya Kaltume, mace mai nuna isa da tak'ama wacce bata d'aukar raini komai k'ank'antarsa, ta tsani talaka kamar yadda ta tsani mutuwarta, ko a hanya bataso ta had'u dashi, Hajia Kaltume kenan manya masu duniya!.

Suna da 'ya'ya shida Ayuba, Auwal, Sani, Salisu, Rabi'u, sai Iggenta kuma Auta Maryam. Ya'yan sun tashi cikin kulawa, ba abinda suka nema suka rasa, a rayuwarsu sun tashi cikin tsananin gata amma hakan bai saka sun sangarce ba, sun tashi cikin cikakkiyar tarbiya ga girmama na gaba dasu, sunyi karatu a makaranta mai kyau, Ayuba da Auwal tuni sun kammala degree d'insu inda suka fad'a harkar kasuwanci kamar mahaifinsu, Sani da Salisu suna final year inda Rabi'u yake level 3, Maryam kusan sa'an Asma'u ce k'anwar Ameena, itace ta rage secondary a yanzu, Ayuba yayi aure ba da dad'ewa ba, inda ya Auri 'yar k'awar Hajia kaltume, Rafia Hajia taso Auwal ya Auri k'anwar Rafi'a wacce tunda ta ganshi ta mato akansa, amma yace bayaso, su Rafia suma sunada arziki sosai shiyasa Hajia ta yadda aka had'a auren, saidai kam ba tarbiya kota sisi, saidai gyaran Allah kawai.


( *To yanzu ga Awwalu ya d'auko magana wai yanason 'yar talakawa ya kuke gani friend?* ) >??




Too busy>?&? @& manage pls=??




=؄?Meryerm Abdool=؄?
[8/2, 6:53 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



*# ka zama mai ra'ayin kanka, bamai bin ra'ayin wasu, bazaka iya ma mutane ba, koda kuwa goyasu kake kullum kana zagaye gari dasu, tofa sai sunga laifinsa wataran, kaidai gyara tsakaninka da Allah domin gobenka#* nasiha ce=?L?

_#one love =?
? Abdulmajeed fans=?
? ina yinku guys keep fallowing=??c'd'=ؘ?#_






=??? *Episode* 91--95



Bincike sosai Baba yayi game da Auwal, sannan ya kirashi tare sukazo da Jafar yayan Firdausi gaidashi sukayi cikin girmamawa sannan suka zauna k'asa kan carpet, ya sunkuyar da kanshi k'asa.

"Nayi binkice kamar yadda addini ya tanadar, na kuma gamsu da tarbiyarka, saidai hanzari ba gudu ba, Abu na gaba shine kaje ka nemi soyayyar ta idan ta aminta walillahil hamdu, idan bata amince ba ka hak'uri ba rabonka bace".

Tunda Baba ya fara magana, baice komai ba, saida ya gama, godiya sosai sukayi masa, sannan suka tafi cike da farinciki, Jafar sai zolayarsa yake.

Bai wani sha wahala gurin shawo Kanta ba, duk da ta tsaya jan aji irin namu na Mata, amma komai yazo da sauki tunda dama Firdausi ta share masa hanyar, anan tayi masa maganar son ci gaba da karatu ya tabbatar mata babu matsala zatayi sai Wanda ta zaba.

Saida Baba ya kirata ya tabbatar tayi na'am dashi sannan ya K'ara kiransu " to Alhamdulillah ta bani tabbacin ta aminta dakai, saidai ka sani ka fito gidan arziki duk da inada tabbacin bakwa cikin masu raina ma mai k'aramin k'arfi, amma duk da haka banason wulak'anci, ina nufin kada a walak'anrta min 'ya, ina so gami da k'aunar ta amma a hakan zan hak'ura na baka ita saboda ya zama dole tayi aure koba da kai dole zatayi dan shine kimarta, ban kaba ita dan abin hannunka ba aa na bakane saboda ka nuna kana k'aunarta kuma na yarda tarbiyarka, don haka nake rokonka da kada kai ko danginka su ya walak'antamin 'ya idan naga da walak'anci to zan janye gaskiya" dago ido yayi yace.

"Inshaa Allah Baba hakan bazai faru da yardar Allah, zan kasance cikin masu rike amana".

"To shikenan sai kaje ka turo magabatan naka, Allah yayi muku albarka" da ameen suka ansa sannan suka tafi.

Dama jiran ansar Baba ya tsayar dashi, a ranar ya koma Sokoto dama a can Suke zaune.

A ranar ya Sanar da mahaifinsa yayi murna dad'in labarin dama sun k'agu ya kawo matar, bai tsaya wata ba ya kira mijin k'anwar tasa ( Dadyn su Firdausi) ya tabbatar mishi da yarinyar ta fito gidan tarbiya kuma itama mai tarbiyarce, dama abinda yakeso yaji kenan, anan ya tabbatar masa suna nan zuwa k'arshen sati saboda ayi komai cikin lokaci.

Lokacin da yajema Hajia kaltume da zancen tambaya ta farko datayi masa shine waye mahaifinta?

"Am Momy dama Babanta ba wani bane Headmaster ne a wata primary...."

"What!" Ta katsesa ba tare data barshi ya k'arasa ba.

Mik'ewa tayi tare da nunashi da yatsa "kai Auwalu idan ma barci kake toka farka, dama shiyasa kace bakason Ummita saboda saboda kanason had'ani da dangin tsiya ko? To wlh ahir d'inka badaini Hajia kaltume zaka had'a ma jini da matsiyata ba".

" Momy.... "Katsesa tayi

"Get out, banason jin komai daga bakinka" ta fad'a tana nuna mishi k'ofar fita.



Tashi yayi ya fice jiki b k'wari, dan yasan halin mahaifiyarsa tasa tsaf.



**************************

A satin Alhaji Sada da kannensa sukaje akayi komai na Al'ada aka tsaida rana, wata d'aya bayan sunyi graduation, haka suka watse cikin farinciki da ganin girman juna, dan anyi abinne na mutunci, lokacin su Ameena sun koma tuni.

B'angaren Hajia kaltume jin bata k'ara ji daga Auwal ba ta d'auka yabar maganar taci gaba da sha'aninta, aiko ranar da Alhaji ya gayamata sunje an tsaida rana, tub'ure masa tayi hauka zallah, saida yayi Mata Jan ido tare daci mata mutunci sannan yayi mata kashedi da kada ta yadda tayi abinda auren zai baci muddin tayi to a bakin Aurenta.

"Shima so kikeyi kiyi masa mugun zabin nan da kika yima Ayuba ko? To ban aminta ba tunda ya nuna Wanda yakeso, kuma bata wata matsala to banga dalilin hanashi ba, akan wani bazan dalilin ki Mara asali da tushe" a babin dole ta hak'ura dan tanason aurenta, amma tace ba ruwanta da auren kuma ko sisinta bazai yi ciwon kai akan tsinannen aure ba.

Ba Wanda ta fad'ama maganar auren, ko 'yan uwanta ko, Rafia da taji batun Auren ba k'aramin tashin hankali shiga dan ita har ga Allah son Auwal take, dan batasan dashi ba sai bayan Aurenta da Ayuba, shiyasa take wani shige masa(wa'iyazu billah kina matar aure wani namiji na burgeki wannan wace irin rayuwa ce, Allah ya gyara).

Ga k'anwar ta Ummita datake mutuwar sonsa taso ya auri Ummita ko an ta d'anji sauk'i tunda ya auri jininta, nan take taji ta tsani wacce zai aura kuma tasha alwashin rabasu, musamman ma da taga Hajia itama batason Aure, Murmushin mugunta tayi(koma take sak'awa a ranta oho! Wai Ameena tun kan ki shiga kin fara samun mak'iya =?? ).

Alhamdulillah su Ameena sunyi graduation successful, nan aka shiga hada-hadar biki ba'a kama hannun yaro, karma Firdausi taji amara k'irjin biki, itace amarya itace ango, a gefe d'aya kuwa Auwal da Ameena ji Suke kamar sun shekara goma tare saboda tsabar k'auna dake yawo a tsananin su.

Biki akayi mai k'ayatarwa inda kowane b'angare ya taka rawar gani, ba k'aramin k'ok'ari su Baba suka yi ba gurin gyara wa Ameena d'akin ta komai yaji dai2 dai k'arfi baifi jiki, sai fatan zaman lafia, haka aka gama lafia kowa na farinciki, inka d'ebe uwar ango data nuna k'iyayyarta baro-baro, danko dangin ta sai daga baya sukeji, kin gayyatar kowa tayi, duk Wanda ya kawo Kansa kuwa tas takeyi masa, tace munafukai ne.

A sabon gidansu da basu Dad'e da tarewa ba Wanda Alhaji Sada ya Gina, shida 'ya'yansa estate mai d'auke da apartment biyar, anan suka tare, akai amanar gurin surukarta, dutse idan yana magana tota tanka sai k'anwar ta ganin shirun yayi yawa tw ansa musu,haka suka dangana da ita sashinta cike da mamakin uwar mijinta, Allah ya kyauta sukace sannan suka k'ara yi mata nasiha,tare da fatar Alkhairi haka suka barta suka dawowarsu (aure kenan! Shakan yaro)

k'auna mai tsabta ma'auratan Suke gudanarwa, cikin tsantsar so da kulawa kowannesu tattalin d'an uwansa yake.

Duk safiya zataje ta gaida surukanta Alhaji har janta da hira yake dan yarinyar ta shiga ransa jinta yake kamar Maryam d'insa, sabanin Hajia da sai ta gaida ita kusan sau uku kafin ta ansa da lafia, ko inda take bata kallo, bare tayi tunanin tasan da ita haka take karake zaman ta dawo, bai hana gobe ta k'ara zuwa, haka komai ta dafa zata aika Musu, ko kallon abinci batayi balle tasaran zataci saidai in mai aiki ta taho taci ko taba almajirai.

Sabanin waccen 'yar iskar da bata iya komai ba sai fitsara da kinibibi, ko ruwan zafi bata iya dafawa saidai tazo nan inda Hajia taci ko kuma Ayuba yayi musu take away, gaisuwa ko sai tayi Mata suger takeyi, Alhaji kam saidai in hanya ta had'a su yake samun gaisuwarta.

Auwal duk yana sane da wulak'ancin da Hajia kema matarsa, shima baida bakin hanawa saidai ya sakata d'aki ya bata hak'uri da lallashinta, "lah ba komai wlh ai iyayenmu ne dole mu bisu" kullum maganarta kenan, hakan ba k'aramin dad'i yake mishi ba, yaji sonta ya k'ara nunkuwa ransa.

Kamar yadda yayi mata alkawali har makaranta yaje da kanshi ya anso mata foam, ranar tayi tsallen murna burinta zai ciki, saidai kash!.

Labari na jema Hajia tace batasan zancen ba in Aure, aure in karatu, karatu ..........



_wayyo silly Ameena_ =?F??&? @&



=؄?Meryerm Abdool=؄?
[8/3, 2:09 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)


*wata rana manzon Allah yace da Mu'azu bin jabli "ya Mu'azu shin bana baka labari akan, kan al'amari ba da kuma gimshik'insa da tsororuwar tozonsa?".*

Sai yace *" fad'a mini ya ma'aikin Allah".*

*"kan al'amari shine musulunci, gimshik'insa shine sallah, tsororuwar tozonsa shine jihadi, sannan ya k'ara cewa shin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login