Showing 21001 words to 24000 words out of 88300 words

Chapter 8 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1607

bazan gaya maka abinda ya mallaki dukkansu ba?*

Sai yace *"sanar dani ya ma'aikin Allah"*

Sai ya kama harshensa sannan yace *"ka kiyaye wannan.*

Sai Mu'azu yace cikin mamaki *"ya ma'aikin Allah, dama ana kamamu da abinda muka fad'a?"*

Sai yace *"kaiconka ya Mu'azu, shin meyasa ake kifarda mutane da a cikin wuta da fuskokinsu ko da tsinin hancinsu sai face akan abin da harshensu yake girbarmusu.*

_Hadisul hasanu_

_to nidake dasu mu guyi fad'ar kowace kalar magana, musan mu muka fad'a, dan wallahi nidake dasu sai munyi bayanin kowace kalma bayan kalma gobe k'iyama ( Allah yasa mudace_ =?O?



=??? *Episode* 96--100





Koda Auwal ya gayama Ameena abinda Hajia tace, abin ya Sosa ranta don Allah ya sani tanason karatu, kodon halin rayuwa, amma saboda ta kwantar masa da hankali ganin ya shiga rud'u, bata nuna komai a fuskarta tana murmushi tace "ba komai mijina, bin Umarnin Hajia dole ne, koda kuwa yaci karo da nasu ra'ayin, ina k'aunar ka dole na k'auna ci, abinda Hajia takeso, saboda haka karka damu nina hak'ura da karatun".

Tsabar farinciki rasa bakin magana yayi sai rungume ta yayi yana Sanya mata Albarka, tare dajin k'imarta da darajarta cikin ransa.

Lokacin Alhaji Sada yaji zancen da kanshi ya kira Ameena akan meyasa ta yadda da barin karatunta, kodai dole akayi mata? dan baisan Hajia ta hana ba, Auwal dai yace ta fasa ne, " Ameena idan iyayenki sukaji ai ba zasuji dad'i ba".

"Baba aina gayamusu nice na fasa yi" duk da cikin ransa ya shakkar haka kawai kuwa, nan dai yayi mata nasiha kamar yadda ya saba tare da bata kud'i masu yawa akan ta fara Sana'a tunda batason karatu, godiya sosai tayi masa sannan ta wuce, girgiza kai yayi tare da cewa "Allah ya kyauta" dan yanaji duk inda aka zagayo aka dawo akwai sa hannun Hajia.

Ameena Nada wata 6 ta samu miscarriage, Wanda basu Masan da cikin ba, tsawon sati biyu tayi a asibiti, ba Wanda baije dubata ba, harda Rafia kusan kullum sai taje dayake ita 'yar duniyace bata nuna k'iyayarta a fili.

Hajia ce kawai bataje ba, saima cewa tayi ai gara da tsinannen cikin ya zube, kuma Allah yasa mahaifar ta lalace gaba d'aya, da dai a haifemata dangin tsiya, maganganu dai ba dad'in ji taita fad'a.

Ko bayan an sallamesu, saida Alhaji ya nuna b'acin ransa sannan taje ta dubata Wanda shine zuwanta na farko sasan shima daga k'ofar parlour ta tsaya tayi sannu tana wannan cika da batsewa, tayi mamakin ganin yadda aka gyarama Ameena guri, sai tab'e baki tayi tace ai duk dukiyar d'anta ce, dansu basu da komai sai tsiya (oh talaka bawan Allah, komai saidai anyimishi kenan?, kai sharri kayan kwalba=??).




*************************

Sani da Salisu sun kammala karatunsu lafia, kuma sun fad'a kasuwanci kamar 'yan uwansu dama karatun anayi ne saboda zamani da k'arin experience akan business d'in, nan maganar Auren su ta tashi to anyi sa'a sun d'auko diyan masu dashi, nan fa Hajia akayi biki na kece raini, sai bak'ak'en maganganu ake yab'awa Ameena, bawar Allah yi takeyi kamar batasan da ita akeyi haka akayi biki aka k'are amare suka tare.

Haka dai akaci gaba da zama yayin da Ameena ke k'ara fuskartar cin fuska da walak'anci ga surukar tata saboda dai ta kasance 'yar talakawa, banbancin launin fata ake nuna mata sosai, sauk'in abin mijinta ta na k'aunar ta kuma suma matan saurin nata ba wacce ke nuna mata raini a gabanta sai dai ko bayan idonta, haka share tace ci gaba da kyautata mata, dai dai da rana d'aya bata taba gayama iyayenta ba.

Haka rayuwa taita shurawa kwanci tashi hasarai ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?rai, duk surukan gidan kowa na d'auke da ciki inka debe Rafia wacce tace haihuwa ba yanzu, sai ta gama shanawa ba zata tsofe a banza ba amma da yake 'yarso CE shiru kakeji, Hajia ko tari (ooh da Ameena ce da anga yakin basasa...hhhhhh) lol


Ameena CE ta fara haihuwa, murna gurin Auwal kamar ya taka kan jariri ya zama Baba, haka ma Alhaji anyi jikan fari, kowa ya nuna farincikinsa nan da asibiti ta cika da 'yan uwa da Abokan arziki, hadda su Rafia anje na munafurci, saida aka tabbatar lafiyar uwar da d'anta sannan aka basu sallama, gida suka wuce dama k'anwar Mamanta tazo Asma'u k'anwar Ameena da yake sunyi Candy, hadda su Firdausi amarya an iso, haka suka dunguma suka wuce gida dan kankanta mata guri dan yau zasu wuce Argungu.

Hajia dak'ar taje shima ko d'an bata ansa ba daganan ta ganshi a hannun Asma'u wacce tunda yaron yazo duniya, taji k'aunar sa ta mamaye mata ilahirin zuciyarta, tanajin jinsa har ranta...

Ranar suna yaro yaci *Abdulmajeed* anyi shagali an kashe nera dan Auwal yayi rawar gani Alhaji ma yayi tashi yace jikan farine, Baba ma yayi nashi k'ok'arin, sai fatan Allah ya raya Abdool, su Firdausi da Asma'u uwar da sune k'irjin biki, Hajia kam ko kallo basu isheta ba dan da alama k'iyayyar uwar ta shafi d'an.

Auwal kuwa duk sati yana Argungu gurin d'ansa mai kama dashi fatar CE kawai baiyi hasken Baban ba, kuma yafi uwar haske yana nan dai tsakiya, Mama kuwa sai aikin gyaran 'yarta ta ciki da waje aiko tuni ta d'auki sheki tun balle bata kusa ga Hajia.

Abdool kuwa kullum yana hannun Asma'u, shan nono kad'ai ke had'ashi da uwarsa, tsabar sonda Asma'u ke mishi ko cikin barci taji kukansa saita farka, Mama tace lallai kuwa ranar da suka koma zai barki da kewa.

Auwal da kanshi ya roki Baba su basu Asma'u, ganin yadda ta shaku da Abdool, kuma tunda tace karatu zatayi, dan tunda taji abinda ya faru da yayarta(ta gayamata abinda ya faru, dan itace abokiyar shawarar ta)tace Aure ba yanzu ba, duk Wanda yazo hak'uri kawai take bashi.

Dak'ar suka shawo kan Baba ya amince, Auwal ya samo musu admission a *Usmanu danfodiyo* ita da Maryam k'anwarsa, Hajia nan habaici ya tashi hadda fad'in saboda an samu banza shine hadda kwaso k'anwa, anga dukiya shine akazo a dangwala, cin fuska dai zalla abinda Ameena ta guda kenan.
[8/6, 8:09 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



_=ؘ?=ؘ? where r u my berries=?? Fatima Bello(momy shatima), Shamsiya Isma'il(fresh daughter) Aisha wanzams (my kanwa) I heart u guys =?? *#1love#*_









=??? *Episode* 101--105







Saida tayi mai isarta ta godewa Allah, dak'yar ta mik'e idonta sunyi jajir tare da kumbura, sai Kanta dake matsanancin sarawa tsabar kukan da tasha, Abdool ta d'auka wanda shima sai kuka yakeyi ganin mamarsa nayi, dabin bango ta shiga part d'inta, saboda jirinda ke d'ibarta, a parlour ta zube zuciyarta kamar an d'ora mata dutsi dak'yar ta jawo wayarta ta kira Asma'u akan tazo gida, rud'ewa Asma'u tayi jin murya yayarta wata iri tasan ba lafia, kafin tace komai harta tsinke wayar, aiko kota kan Maryam bata bi ba tayi bakin titi tare da taron taxi.

Auwal kuwa yana shiga part d'insa ji yayi duniyar gaba daya tayi mishi zafi, ga rad'ad'in da zuciyarsa ke masa, ga kukan Ameena da Abdool da yake jiyowa yana tab'a masa zuciya, duk da cewa ita mai laifi ce a gareshi amma zuciyarsa ta k'asa yadda da bak'on al'amarin da ya same shi na rabuwa da Ameena, key kawai ya d'auka yabi ta k'ofar baya, normally kowa nada k'ofar baya wacce zai fita ba tare da sanin wani, motar shi ya d'auka ya fita gidan a tsiyace, tafiya kawai yake shi kanshi baisan inda ya dosa ba.

Ganin yanayin da ta isko yayarta ciki ga Abdool sai ihu yake amma uwar ko kallonsa ta k'asa yi balle tayi tunanin shayar da shi, Abdool ta d'auka, abinci ta had'a mishi saida ta tabbatar ya k'oshi sannan ta goyashi ba dad'ewa bacci yayi gaba dashi sai ajiyar zuciya yace, gurin yayarta ta matsa wanda itama jikinta a sanyaye yake, dafata tayi, nan ta d'ago ta kalleta da rinannun idanunta, "Aunty komai yayi tsanani maganin shi Allah, ki d'aure ki gayamin meke faruwa?"

Kama hannayenta duka biyu tayi, bakinta na rawa, sai a lokacin wasu zafafan hawaye suka zubo mata, sharewa tayi, nan ta labartawa k'anwarta duk abinda ya faru bayan wucewar ta makaranta.

"Inalillahi wa'inna ilaihirraji'un" shine kalmar da Asma'u tace maimata tawa iya tashin hankali kenan, yanzu ta fita tabar mata da mijinta lafia, amma kuma cikin k'ank'anin lokaci komai ya canja, farinciki ya koma bak'in ciki, batasan lokacin da hawaye suga zubo mata ba, nanta rungume yayarta sukaci gaba da kuka bamai lallashin wani.

Bankad'o k'ofa akayi da k'arfi, a tare suka d'ago dan ganin wanene, da kallon k'ask'anci ta bisu, ba kowa bace face Hajia "to matsiyata 'yan gadon lalata(sadnaf), me kuke jira yanzu kuma?, ina auren ya k'are ko kuma da sauran zance ne iyye" duk cikin masifa tace maganar.

Saida ta saka full stop sannan Asma'u tace "yi hak'uri Hajia yanzu zamu tafi" tsaki tayi tare da cewa "aikin banza sannan ta fice.

B'angaren Rafia kuwa suna isa part d'in Hajia bayan tayi Jim na mintuna tace "Hajia Bari in tafi zanyi wani aiki" part d'inta ta shiga, wannan gardin ne zaune a kureja amma ya maida kayanshi, wata shu'umar dariya tayi sannan ta d'aga mai babban farcenta "weldone Wizzy aikin ka ya tafi yadda akeso" murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba, bedroom ta shiga sai gata ta fito da rafar 'yan duba, bashi tayi tare da bud'emai k'ofar baya ya ware.

Asma'u ce ta d'ibo musu kayan sawarsu trolley biyu, drop suka d'auka sai k'ofar gida.



************************

Lokacin suka isa dak'ar suka shiga ciki, Mama na tsakar gida tana aiki, Mansur kuma na gyara mata alayyahu, ganin da kaya nik'i-nik'i sannan fuskacinsu a jeme duk sun wani yamutse, yasa tasan ba lafia ba, gaisa sukayi sannan suka shiga ciki, itama wanke hannu tayi tabi bayansu, ba wani boye-boye Asma'u ta gayamata abinda ya faru.

Ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, amma saita daure tace "Allah yasan hakan shi yafi zama mafi Alkhairi" dama tunda k'anwarta ta gayamata halin Hajia da irin wulak'anci da tayi musu, yasa ko sha'awa zuwa gidan bata tab'a yi ba, amma wannan sharrin dame yayi Kama, idan so take a saketa basai ta had'a da sharri ba, dan ta yarda da tarbiyar 'yarta ba zata taba aikata hakan ba koda bada Aure ba balle da Aurenta, Allah ya saka Mata, shine kawai ta fad'a a ranta.

Baba ma daya dawo yaji ba ransa ne yayi mummunan b'aci, musamman sharrin da akayi mata, dama Baba akwai zafi, abin ya bala'in k'ona ransa, fad'a yayi tayi da cewa zaije Sokoto gobe, saida Mama ta tausheshi sannan ya hak'ura, dan tasan idan yaje da wuya ayi mai kyau, amma yace gobe su Hafsat da Usman(k'anwar Mama da d'an kanin babansa) suje su kwaso kaya sannan su anso masa
takardar 'yarsa.

Auwal kuwa bayan gari yaje bakin ruwa, a can yayi zamansa dan gari ya riga yayi mishi zafi, nan yayi ta sak'awa da warwarewa har dare bai samo mafita, ganin duhu ya shigo, yasa shi hak'ura ya koma gida.

Hajia kuma ganin har dare ba Auwal ba labarin sa gashi ta kira wayoyinsa a kashe yasa hankalinta tashi, bakin k'ofar part d'insa ta tsaya zaman jiran dawowar sa.

Dai2 part d'insa yaga Hajia, jiki sukwana ya k'arasa gurinta tare da gaida ita, bata ansa sai fad'a data haushi dashi "wai kai Auwalu wane iri yaro kake, kabi ka tada hankalinka akan yarinyar da ta gama cutar da kai, gara ka fiddata a ranka dan kun rigada kun rabu kenan ehe, to garama tun wuri ka yakiceta a ranka ka rungume Ummita dan har nayi magana da hajiyarta nan ba dad'ewa za'ayi bikinku, sannan ka rubuta takardar waccen matsiyaciyar ka kawo min, zan aika mata har gida" Auwal da zuciyarsa ta gama k'ek'ashewa "tau Momy" kawai yace, sannan ya shiga ciki, itama ficewa tayi tana fad'in "daga Allah ya tona mana 'yar iska" tana shiga part d'inta nan ma Maryam ta isko ta had'a kai da guiwa, dan tunda ta dawo Hajia ta fad'a mata abinda ya faru, ta shiga damuwa hadda kukanta dan ta saba da Aunty da Asma'u ga Abdool Son d'inta, ita sam bata yadda aunty zata aikata abinda akace tayi ba, dan tasan ta farin Sani kullum cikin yi musu nasiha take itada akan su tsare mutuncinsu sannan ace ta aikata wannan barnar.

Tsaki Hajia tayi "kwayi kwa gama" sannan ta shige ciki tana mitar halin irin na 'ya'yanta Sam basu biyota ba(ai sun huta basuyi bak'in gado ba) waya ta kira hajia Umma mamarsu Rafia danso take ayi komai cikin lokaci, saboda ta k'ara cusawa Ameena bak'in ciki.

Auwal na shiga ciki jin ba motsin wata halitta ko'ina shiru, sabanin da, koda zai shigo a parlour zai samesu suna kallon sunnah TV wata ran kuwa su kalli zee TV ko kuma su zauna suna hirarsu gwanin sha'awa, Murmushin takaici yayi tare da shigewa ciki, takardar ya rubuta kamar yadda ta buk'ata yakai mata.

Washe gari kamar yadda Abba ya buk'ata haka su Hafsat da Usman Suka taho da babbar motar kwasar kaya, amma me Hajia tace ba wani kaya da zasu kwasa ai danta ne ya saya, haka aka shiga rigima sun nace sai kwasa itama tace basu isa ba, hayaniyar ce ta kawo hankalin mutanen gidan wad'anda duk abinda ya faru basuma San anyi ba sai lokacin.

Ganin rigimar tak'i k'are wa yasa Sani kiran Auwal ya tambayesa nan ya tabbatar kayanta ne ko tsinke bai siya mata ba, da yake a hand's free ya saka kowa yanaji yasa ta basu suka kwasa, tana biyarsu da habaici da bak'ak'en maganganu, ba Wanda ya kulata har suka k'are tun kafin su tambayi takardar 'yarsu ta kawo musu, tare cin mutunci.

Auwal da tun safe ya fita zuwa yayi ya tattara duk wata k'addara tasa ya sayar, banki yaje ya bud'e kid account ya zuba kudin, iya wad'anda zai rike a hannun sa ya rage, bashi ya dawo ba sai goman dare, d'akin sa ya shiga yayi wanka ya kimtsa sannan ya d'auka diary sabo kal, rubuta sosai yayi sannan ya sake rubuta wasik'u har uku, part d'in Hajia yaje yace Maryam ta d'auko mishi key din part d'in Alhaji dan duk wannan ruguntsumin da ake Alhaji bayanan ya tafi umrah, d'auko mishi tayi bud'ewa yayi sannan ya shiga bedroom, wardrobe d'insa ya bud'e wata leda ya saka daga can sama sannan ya rufe ya fito, Maryam ya kira ya bata keys d'in da wasik'a tare da tabbatar mata da ta bawa Hajia zuwa gobe da tau ta ansa masa sannan ta shige ciki.

Washe gari bayan sun gama breakfast ta d'auko wasik'ar ta bama Hajia.

"Lahaula walah k'uwwati illah billah" shine Kalmar da Hajia ta fad'i tare da zubewa k'asa a sume........




_friends ina barar Addu'arku akan wata buk'ata tawa, ina da tabbacin zan samu. Love u all_ =?
?









=؄?Meryerm Abdool=؄?
[8/6, 8:15 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



```Wannan page d'in nakune 'yan makarantar madarasatul nurul Islam littahafizil Qur'ani
Kareem,kabino area,Argungu```=?L?

_Irinsu Nafisa muh'd, Fareeda Nana b/mashaya, Mamu Aliyu, Saudat yahya, Meena dikko, Amina Garba, Bilkis, Hajjo, Aina'u Idris and rest kuna raina koda yaushe#d'd'd'#_







=??? *Episode* 106-110






Maryam wacce tana mik'awa Hajia sak'on Auwal ta shige bedroom room d'inta, sai jin k'aran fad'uwar abu tayi aiko da gudu ta fito ganin mahaifiyarta kwance ba numfashi yasa tayi Kanta cikin kid'ima tana jijjigata, amma ko alaman tashi batayi ba, aiko da gudu tayi part d'in Rafia tayi sa'a Ayuba nanan, jin abin ya faru yasa suka biyota cikin tashin hankali, Rafia ce tayi Kanta ta rungume ta yayin Auwal yace a kawo ruwa, da sauri Maryam ta kawo ruwa Shafa mata akayi, nan take ta sauke ajiyar zuciya, bud'e ido tayi a hankali ta sauke a kansu sannan ta maida kallonta ga takardar da ke jinke a hannunta, wani kuka ta rushe dashi "why Auwal, meyasa zakayimin haka".

Ayuba ne yayi k'arfin halin cewa " Momy me kuma Auwal yayi miki?" Takardar ta mik'a masa, ansa yayi tare da karantawa a fili.

_"kiyi hak'uri momynah nasan koda wasik'ata zata sameki ba zakiyi farinciki da ita ba, sai ba yadda zanyi dole ce tasa zan barku, bazan iya ci gaba da zama kusa da inda zanji labarin Ameena ba, alhalin bama tare, dole zan nisanta kaina daku da kowa nawa, kada ku wahalda kanku nemana danni kaina bansan inda na dosa ba, pls kiyafemin Momy kiyimin fatan Alkhairi, kada ki tsinemin, idan kikayi haka rayuwa zata ga garari, ma'assalam_

D'anki *Auwal Sada*

Koda ya gama karantawa zuface ke keto masa duk da fanka da na'oural sanyi dake aiki, yama kasa magana, Maryam tuni hawaye ya wanke mata fuskarta, Rafia ma tashin hankali taf fuskarta dan batasan haka abin zai zama ba.

Momy kuwa sai sambatu takeyi tana kiran Auwal dan Momy akwai son d'iya, hakan yasa wutar k'iyayyar Ameena da d'anta ta k'ara ruruwa a ranta dan duka ita d'orama laifi, wai ba a banza tabar Auwal ba, wannan son ya wuce hankali, tunda harya kasa ganin girman laifinta ya barsu saboda ita.

Nan dai suka wuni cikin jimami ga tsoro fal ranta na idan Alhaji ya dawo me zatace masa, gashi gobe Suke tsumayen dawowar sa, dak'yar ta kira Maman su Rafia ta gayamata abinda ya faru, Ummita kuwa da raji rud'ewa tayi, dan ita harta fara shirye,-shiryen Amarcewa(tab to ai sai aje a rungumi big sowie Ummita) lol.




****************************



*Washe gari*


*12:00pm.........*

Jirginsu Alhaji Sada ya sauk'a a Sakkwato birnin shehu, Sani, Hajia, Maryam ne sukaje tarbonsa, yayi farincikin ganinsu amma yafi k'osawa yaje yaga 'yan jikokinsa musamman Abdool dan yaron ya shege masa ransa, sonsa yake sosai bada wasa ba, saidai baya nunawa gudun tashin hankali, sanda suka isa kowa saida yazo gaidashi amma ba Auwal da familyn sa, k'asa daurewa yayi ya tambaya ko sunyi tafiya ne.

Ganin yayi kowa yayi shiru, hakan yasa jikinsa yin sanyi dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login