Showing 42001 words to 45000 words out of 88300 words

Chapter 15 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1594

ya wuce komai "hakan nan na Ameena amma baki tunanin in ankai haka an tauye shi Abdulmajeed"?

Tasan Abdool na buk'atar Aure, dan tun yana 18year yake fama da ciwon Mara, Wanda ke nuni dashi mai k'arfin sha'awa ne, to amma ai ita Ramlah za'a cutar ita, abinda ba zataso ga Nihal ba, so duk d'aya da Ramlah gunta, mema ta sani da Aure as 14 kuma tashin k'auye tana buk'atar wayewar kai da ilimi "Baba bana tunanin akwai matsala amma zamuyi magana".

" to ai dan dai kuna nan binni ne amma ai warin Ramlatu ta isa zama d'akin miji".

Murmushi tayi "haka akeyi a k'auyuka shiyasa zakiga anata samun matsala da wasu yaran akan Auren wuri, aje haihuwa aita had'uwa da yoyon fitsari da wasu ciwuka k'arshe mijin yaji bazai iya ba yayi saki, a maida yarinya bazawara ga kuma ciwo ga yara da k'ananun shekaru" jinjina kai yai alaman gamsuwa d'anshi kanshi ansha kawo mishi irin wad'annan cases a can Kilgori, nan dai sukaci gaba da tattauna wa ya bata goyon baya 100%.

Washe gari ya koma kice da tsaraba, hadda nasu Hari, Mami ta kira Abdool sun tattauna game da karatun Ramlah, dama shima tunanin sa kenan, toshi me zaiyi da ita a hakan ko k'irjin kirki babu, ai bayama tunanin tasan me Aure ke nufi, k'aunarta yakeyi amma badan wani Abu nata ba.

Sun yanke idan anyi Hutu tunda third term ake sai akaita JSS 3 tare da Nihal tunda tana saurin d'aukar Abu, kuma zai cigaba dayi mata lesson kafin shima ya fara aiki.

Zai fita yaci karo da ita ta shigo tsayawa tayi tare da cewa "ina wuni" hararar wasa yayi mata "um baxan ansa ba, bayan kin manta dani da karatun mu kin manta d'an binni mai glass".

Dariya ya bata a yanayin yadda yai maganar kaba baki tayi tare da cewa " Laa Ya Abdool baka barin sunan ga ko?" Tana turo baki.

Shima dariya yai "to ai ke kika sakamin INA"?

" um tona d'ebe maka".

"To 'yar k'anwata Ramlatun Baffa, ya maganan karatun mu?"

"Yawwa Yaya Abdool muci gaba".

" Allah kinaso in sakaki makaranta" gira ta d'aga mishi tana murmushi.

"Lalalala! Yarinyar nan........."





_kuyi hak'uri ban Zauna bana yau, kuma yau kiwar typing ya kamani_




=؄?Meryerm Abdool=؄?
[8/20, 11:17 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)




```Abdulmajid fans, naga kuna k'aunar sakwatanci da yawa fa=?? to Ku kwantar da mind d'inku Ramlatun Baffa tace zata koya maku=?? love u guys bohot bohot=?L?




=??? *Episode* 151--155




"Lalalala! Yarinyar nan ni kike d'aga wa gira?" Tare da zare ido hadda kama baki, sunne kai tayi Rana dariya k'asa-k'asa.

"Yo ai e a nuhina" dariya yayi tare da lak'ace mata hanci "basakkwata kawai".

Turo baki gaba tayi " kaima ai" murmushi yayi yana feeling special "ai zaki koyamun" corridor yabi tare da fad'in "jirani ina zuwa".

Dawowa yayi da wata k'aramar leda mai kyau bata yayi " sako ne daga Zainab tace tayaki murnar Aure" cikin zumud'i tace "LA Aunty Zainab tana ina?" Harara yai mata "sai yanzu kika tunata, tana gidansu".

Rungume ledar tayi tana dariya " Yaya ka had'ani da ita ta waya inyi godiya" tau" yace tare da cewa "jeki nuna wa Maminki" da sauri tayi ciki tana murmushi, binta yayi da kallo tare da shafa sumar Kansa, yana murmushi, sannan ya wuce d'akin sa.

Cikin farinciki ta shiga nunawa Mami gift d'in ta "iyye kai madallah kinga ko 'yar cas da ita zatayi miki kyau, kin gode, taji jeki aje a kayanki" da yake Mami tasan da labarin Zainab d'in, gaban madubi ta tsaya tana gwadawa tayi kyau a wuyanta gwanin sha'awa, sai juyi take tana dariya ita kad'ai, dama Ramlah da kwalliya (Ramlatu hankali).


Da dare bayan sunyi dinner suna zaune parlour suna kallo tasa TV a gaba, duk wani attention d'inta ya tattara ya koma can, gani take kamar mutanen fitowa zasuyi saboda girman Tv gashi kuma ta zauna daf da ita, su husna kam rabi ne kallo rabi Assignment Mami kuwa nakan computer tana aiki, Abdool ya shigo har gaida Mami su Husna suka gaidashi, Ramlah kam batasan ma ya shigo ba.

Daf da ita yaje ya saka waiwaya mata hannun sa gaban idon ta "La Ya Abdool yaushe kazo?"

"Ina kuwa zaki sani duka imaninki na a watching, kinga ki dena zama kusa da TV haka kada ya bata miki ido".

Dariya Mami tayi " Ai Ramlah tawa ne da kallo" Tab'e baki yayi "aiko daga yau zata daina dan gobe zamu fara lesson ya zube mata text book da lesson book da sauran instrument a gaban ta.

" hada tadai rage amma ba maganar dainawa, kaima dai ka fad'a ne" Mami ta fad'a.

Itakam Ramlah ganin littafin birjik gabanta haka ta manta da maganan kallo sai tab'a littafan take tana murmushi, yadda takesan karatu aiki daina kallon zata iyayi....


**********************



Kullum da safe da marece suke lesson wata rana ma hadda su Husna akeyi idan basuje gurin lesson d'insu ba, islamiyya kuma da rana sukeyi anan ta unguwarsu mai had'e da tahfiz, uniform hijab har k'asa.

Garden suke shigewa suyi lesson d'in, idan aka gama ta koya masa sakwatanci, in yanayi taita dariya bai iya amma ya daga anan wai ya iya, musamman inya karemata bayan, sai yace "ke hwahinta" waita gane yake nufi aiko dariya takeyi harda rik'e ciki, shiko kallo yake bin ta dashi komai tayi burgeshi takeyi shidai yana k'aunar Ramlah, amma ai dole ya sota kodon k'aunar da Aunty Asma'u ta nuna masa.

Zuwa yanzu kam ta fahimci abubuwa da yawa, dama gata da saurin gane Abu, har turanci tana ji saidai bata iya mayar da kowanne, math ma haka take tsargesa tsab.

A General hospital ta Kaduna Abdool ya nemi aiki, dama Neman ma'aikata suke so nan take suka bashi upper, Hakeem ma anan ya nema shima dai sun dauk'eshi so ana tare har yanzu, kullum suka had'u zai ta tsokanar sa ina 'yar renonsa, banza yake yi masa wata kuma yake "kaji dashi aini naji dad'i tunda inada 'yar reno, kaifa ba wadda ta taya" dariya yakeyi "tab na daik'i rayawa aini matata Unique ce".

Tab'e baki yake "munji zamu gani".

Tuni aka kammala ginan asibitin an zuba komai na amfanin asibitin saidai yace saiya k'ara samu experience tukun zai bud'e ta.

Ranar da akayi Hutu Nihal ta dawo, tana ganin Ramlah nanfa murna ta k'aru dama Mami tayi mata waya gurin malaninsu ta gayamata komai, nan da nan suka sarke kamar dama sun San juna parrot ta had'u da parrot dan kowacce ba baya ba, musamman Nihal ga barkwanci kamar Yusuf, nan ta shiga bata labarin makaranta,

Ramlah sai murmushi take tana imaging irin gata a school a class ana damawa da ita a hostel suna shagalinsu, oh ji take Kamar ace gobe za'a koma duk ta matsu ta ganta da uniform a school, kamar yadda take ganin yara da safe idan sunje kaisu Husna, kaga yara da uniform kala2 kowa tsaf dashi zaije makaranta shi yake burgeta ba kamar k'auyensu ba da sai can suke zuwa kuma sai rana ta fito muraratan wani ma sai yayi sati baije ba, kuma ba wani kwakwaran dalili.

Yanzu Abdool ya rage zama gida tun safe idan ya fita sai shida yake dawowa wani sa'in kuma inyai fitar marece sai 10 yake dawowa shiyasa basu cika had'uwa ba, lesson kuma ya dawo end of week.

Yanzu girkin gida sukeyi sun hutar da Inna kande da Mami, komai sun iya dama ita Nihal ta iya tun can, Ramlah ma yanzu anyi expert........

Hutu ne ya kusa k'are wa hakan yasa Mami taje school din tasu Nihal ta nema nata sukace a kawota ayi mata interview, sun yaba da kwazonta JSS 3 suka sakata kamar yadda Mami ta buk'ata aji d'aya da Nihal, uniform da house wears suka bata nan ma house d'aya aka ajesu, provision sosai Mami tayi musu, komai nasu a had'e, shima Abdool ya dad'a musu, Husna ganin tulin kayan da aka jibgo musu yasa tace itama a had'a da ita a kaisu tare, dariya sukai mata Mami kuwa tace "kwantar da hankalinki baby na 'yar k'anwata aike naki lokacin damasu zakiyi a komai ko school taki ta daban ce".

Dariya ta ringayi tare dayi musu gwalo, dariyar kawai sukayi dan sun San baho ne Mami ta maida ita, satin da aka koma Ramlah ta matsa a kaisu haka aka tattara aka kaisu bayan Mami ta sanbad'a musu kashe din kada su fad'i Ramlah matar Aure ce, musamman ma Nihal dan ta Santa da mugun surutu.

Ita Ramlah har ga Allah mantawa take da Auren sai sha'anin gabanta takeyi, tau 'yan boarding dai an isa ko wace wainar za'a toya a can oho!>??



*********************



Yauma kamar kullum Mami ta fito zataje office, sai ganin motar Abdool tayi alaman bai fita ba, mamaki ya kamata dan a tunanin ta ya fita tun dazu dan dama bai cika tsayawa ya karya ba, ciki ta koma, can kan bed na hango shi yanata murk'ususu, cikin gid'imewa ta isa garesa " menene Abdool?"

Cikin muryan wahala yace "Mami cikina marata, Mami ciwo sukemin kamar su balle" tallabe kansa tayi ta d'ora akan cinyarta tana Shafa masa kan cikin tausaya wa tace "ka kuwa sha maganinka Abdool?"

Kaiya d'aga mata alaman eh, cike da tausayinsa tace "kuma har yanzu bai daina ba?" Nan ma da kai ya ansa mata.

Daga shi take son yi "Mami bazan iya tashi ba, d'an samo ruwan zafi ki dannamin gurin" cikin hanzari ta debo a flask tare da k'aramin towel sannu a hankali ta shiga Danna mishi, tun yana 'yar k'ara yana lumshe ido har ya rufesu ruf sai saukar numfashi Mami taji alaman ya samu bacci.

Gefe ta zauna tare da tallabe kumatunta ganin yadda d'anta keshan wahala, kuma tasan maganin abin amma ta zuba mishi ido, to amma meye mafita har ga Allah idan ta bashi Ramlah yanzu ta cutar da ita, dan tayi k'ank'anta a wannan sabgar, kuma hakan na nufin barin boarding kuma a shekarunta aka had'a mata karatu da Aure an cutar da ita, idan kuma aka cireta itama cutar wa ce "meye mafita" ta fad'a a fili.

Ta dad'e tana sak'awa da warware wa kafin wani tunani yazo mata murmushi tayi ganin ta samo mafita.

Sai 2 ya farka, jikin ya saki gaba d'aya, ciwon ya rage sai kad'an ya rage, kusa dashi tazo dan tana d'akin dawowar su Abj ne ya fitar da ita ta sallamesu suka wuce lesson tayi sallah sannan ta dawo, office ma anata kiranta sai excuse ta basu.

"Abdool ka tashi? Sannu ya k'arfin jikin?"

Murmushi yayi yana k'arajin k'aunar mahaifiyarsa a ransa "da sauk'i Mami kina nan baki fita ba?"

"Bazan iya fita ba Abdool kana wannan halin" mik'ewa yayi tare da rungume ta "love u so much Mamina" itama peck tayi mishi a kumatu tare da Shafa sumarsa "bari inyi wanka Mami".

Fresh up yayi yai sallah, tea mai kauri ta kawo mishi tare da farfesun hanta, kad'an yaci sannan yasha tea tare da shan magani.

Zama yayi kusa da ita " Abdool" ta kirashi, d'ago wa yayi "na'am Mami"

"Ya labarin Zainab?"

Jim yayi danshi harga Allah ya manta da wata Zainab "tana nan Mami wani Abu ne"?

" batayi aure ba?"

"Eh gaskiya banji ba".

"In har bakada wata wacce kakeso bayan Ramlah, to kaje ka nemi Auren Zainab".

A firgice yace " Mami Neman Auren Zainab kikace fah?"

"Hakane Abdool kuwa kai kanka kasan dalili na nayin hakan, bazan iya baka Ramlah a yanzu ba, haka bazan iya ci gaba da ganin ka a wannan halin ba, kuma banyi dan rashin Adalci wa Ramlah ba, nasan ko ita taji zata fahimceni, dakai a matsayin ta ita kuma a matsayin ka, iya abinda zanyi kenan" jinjina kai yayi Cikin gamsuwa da zancenta.

Saidai ta ina zai fara tambayan da yayi ma Kansa kenan...

Sallamar Hakeem ce ta katsesa yayi ta kiran wayo yin sa shiru, ya biyo yaji lafia......



_wata sabuwa_ =?3?

*wai ina labarin Zainab*





=؄?Meryerm Abdool=؄?
[8/21, 10:58 AM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)







=??? *Episode* 156--160






Gaisawa sukayi da Mami tana tambayan iyayensa sannan ta wuce, kusa dashi ya zauna "wai ya haka ne yau ba'a ganka ba, ba'a kuma jika ba, menene inata kiran wayoyinka a kashe" yamutsa fuska yayi.

"Hmm ka Bari kawai ciwon ne ya zagayo, na yau is too pain, maganin ma kamar bansha ba, na jigata fa, sai yanzu nake tashi, ga Mami ko fita batayi ba yau".

Cikin tausayawa ya da kulawa yace " ayya sannu to ya jikin yanzu?"

"Not bad! da sauk'i" ya fad'a ya lumshe ido,

"Haka zakayi ta zama Abdool bayan kasan maganin matsalar ka? Fisabilillah?"

"Maganar da muke yi da Mami kenan, wai in nemi Auren Zainab".

Murmushin jin dad'i yayi " best way, kai gaskiya Mami tayi tunani mai kyau"

Girgiza kai yayi "ba zaku gane bane, nifa ba mata biyu a tsarina, ni Ramlah is OK for me".

Dafasa yayi " common my friend, sau nawa muke tsarama kanmu rayuwa, kuma ba shine tsarin Allah ba, kuma ita Ramlah koda baka ita akayi yanzu I believe ba abinda zaka iya mata cos kana sonta kuma tausayinta kakeji, as her age, so as an advice kayi amfani da wannan damar ka Samar ma kanka lafia, and then in ma son Zainab ne bakayi saika nemo wacce kakeso ba dole sai ita ba, mu'allin shahid d'in dai kayi aure".

Ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?bbas gaskiya ya fad'i Ramlah is too young so bazai so ta cutu ba, and shi k'aunar ta yake so yanason ci gabanta ilimi shine gishirin rayuwa sai dashi ne zatasan yadda zata Zauna dashi ma, anan yayi na'am da shawarar abokin nashi, shi baya ma tunanin matsala daga Zainab dan yasan tana matuk'ar k'aunar sa, kuma tana son Ramlarsa so shi kad'ai ya isa yasa ya koyi sonta ko kad'an ne, nan dai sukaci gaba da tattaunawa.


************

B'angaren Zainab kuwa tun ranar da Dr Majeed ya gayamata Auren sa take k'ok'arin yakiceshi a ranta, saidai abun ya faskara kullum iyo take cikin sabuwar k'aunarsa, shawarar Momyn ta tabi, duk lokacin da abin ya dameta sai ta dangana shi da Qur'anil Kareem, sosai takejin sauk'i a ranta, hakan yasa ta fara kula wani d'an uwanta dake bacin sonta, amma badan tana jin sonsa ba, danso d'aya ne tak kuma Dr Majeed takema shi, dan shidai take gani a matsayin namiji, amma kuma hakan bai hanata kula Waleed dan tana yak'inin tunda yana k'aunarta zai kula da ita, ba dole ka rayu da abinda kakeso ba kaidai kawai kaso mai sonka, shiyasa take kula Waleed.

Yauma zaune take dawowar ta kenan daga hospital ko uniform bata cire ba, taji k'arar wayarta, "Dr Majeed" ta fad'a tana zare ido, dan rabon tun ranar da sukayi wayar nan, shine last, 5 months kenan a tunanin ta yama manta da ita, ita kuma tak'i kiransa ne saboda batasan abin da tayar mata da hankali shiyasa ta nisanceshi gaba d'aya.

Duk da Murmushin farinciki da take yi, dan har ga Allah taji sanyi a ranta, amma sai ta samu Kanta da k'in d'agawa.

Shi kuma tunanin bata kusa da wayar ne yasa ya k'ara kira nan ma sai nada daf da tsinkewa ta d'aga, sallamrsa ce cikin muryan nan tasa mai sakata suman dad'i, jin tayi kafin ta ansa tana cin magani kamar a gabansa take, tambayan mutanen gida yayi da kuma ita da bayan rabuwa.

"Lfy" ta ansa a tak'aice, sam bai kawo komai ba yace.

"Zainab Inaso ki bani aron hankalin ki magana mai muhimmanci zamu tattauna".

" inaji" ta fad'a in short.

"OK magana ce ta Aure in har kin aminta inaso mu kulla dangantaka ta aure".

" Aure" ta maimaita a ranta "anya Dr Majeed ne kau" amma a fili yi tayi kamar ba zata ansa har saida yace "kinaji na kuwa".

"Eh naji me kace, saidai sorry to say bana burin hakan".

Mamaki ne ya kashe shi wai Zainab ce kuwa mai k'aunar nan tasa ya fad'a a ransa.

" meyasa kikace haka Zainab? "

"Nothing bana dai ra'ayine so sai anjima" kitt yaji ta katse wayar, sororo ya bi wayar da kallo yana Mamakin Zainab ce kuma to amma ai muryanta ne, dogon tsaki yaja.

"Aikin wofi, har ma kin isa".

Ita kuma tayi hakane saboda ta kwatar wa Kanta 'yanci in har gaske yake zai bibiyeta.

Lokacin da ya gayama Hakeem dariya yayi " tokai ka d'auka sauk'i ne dashi dole ta kwaci 'yancinta a hannunka tukun" siririn tsaki yaja, tare da tab'e baki.

"Dama dai son karya ne take min, ta samu wani ne".

Danne dariya Hakeem yayi "haba Malam ai saurin fushi ba naka bane, Aure fa kake nema, ka yarda dani nasan tana sonka kai kanka kasan da hakan son da take maka yafi gaban yaudara, just be patient itama mace ce so dole ta ja aji irin nasu musamman ma idan ka duba yadda kayi auren ka ka kyaleta".

" aiko sai tayi tayi can mata" dakyar Hakeem ya lallasheshi yace yaji, wasa wasa Zainab sai garashi take dan yanzu yana kiranta kullum yana lallashinta ko don cika Umarnin Mami da Samar wa kansa lafia, har saida Hakeem ya saka baki sannan ta sassauto, shiya bata labarin yadda Aurensa ya kasance da yadda suke da Ramlah, da kuma makarantar da aka maida ita "to kinga ko abin a tausaya masa ne, kodon lalurarsa sannan yana sonki Zainab ki kwantar da hankalin ki, ko nacin da yake miki ya isheki shaida".

Nan take tausayinsa da sabuwar k'aunar sa suka mamayeta, nan ta gaya masa ta Amince suzo su sami Dadynta, ita da Kanta ta gayama Momyn ta yadda sukayi tace" ke gani ko Zainab na gayamiki ai idan rabonki ne zaizo har inda kike, dama hak'uri ne kawai idan ba'a saba, jinjina kai tayi Cikin farinciki.

Mami suka gama yadda sukayi kuma cikin satin sukaje Sokoto, Babanta ya karb'esu cikin karamci, da yake yasan Alhaji Sada, nan take yace su turo magabatansu, tare da Hakeem sukaje inda Alhaji sukayi mishi bayani, har Kilgori suke inda Baffa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login