Showing 84001 words to 87000 words out of 88300 words

Chapter 29 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1603

complete man, abin alfahari wa kowa "mashaa Allah" shima ya fad'a, rungume juna sukayi cikin tsananin farinciki wata k'auna na ratsasu.

Da gudu Meenal ta fito itama tayi joining nasu "Abdulmajid Ahih" ta fad'a tana jin farincikin ganin tilon yayan nata da kullum take mafarkin gani, d'ago ido yayi ya kalleta tare da kallon Auwal "sister kace My Son, kada kace komai nasan ban kyauta maka ba ka gafarceni, baice komai ba sai k'ara rungume su da yayi yana jin k'aunarsu na ratsasa yau mai zai kira wannan rana mai daraja wacce ya dad'e da cire ran zuwanta.

Gyaran murya Alhaji yayi " umm likita an manta damu ko" ya fad'a yana murmushi dan shi kansa farincikin sa bazai misaltu ba, kallon yabi mutanen dasu, tun daga Haj, Kaltume, uncle Ayuba, Sani, Salisu, Rabi'u, Aunty Maryam da zuriarsu gaba d'aya hadda Ismail da amaryarsa Amal sai murmushi sukeyi suma Hajia CE kad'ai ke sunkuyar da kai cikin farinciki da kunya.

Nan aka shiga gaggaisawa sannan yace suzo su shiga ciki, Auwal yace yaje dai yayi musu iso, yace ai sanda ya gaya musu sannan ya fito.

Alhaji ne ya fara shigo bayan Abdool, Mami ta bud'e baki tana gaida Alhaji Kalaman bakinta ne suka tsaya chak, tare da mik'ewa tana nuna shi da yatsa "Auwal!!" Ta fad'a Cikin shock da daukewar wuta.

Suma su Ramlah kallon mamaki suke masa ganin tsananin kama da yake da Abdool, ga kuma sunan Baban Abdool data kirasa dashi kenan Dadynsa ne da aka basu labari.

"Ameena nine Auwal dai na dawo gareki" still shi take kallo, sai can ta nisa tare da d'auke idonta a kansa ta sauke ga bataliyar Ahalin nasa, da wad'anda ta dad'e bata saka a ido ba da wad'anda bata masan dasu ba, da wad'anda sukan had'u wasu lokuta duk dai gasunan.

Da murmushi ta bisu tana musu sannu da hanya haka su Nihal ma, duk girman falon Mami dakyar ya d'aukesu, sai nan na ake dasu su Ramlah sai hidima suke tuni suka cika su da kayan mak'ulashe da motsa baki sannan suka ja Amal da Meenal, Husna da sauran 'yan matan suka shiga kitchen dan girki.

Duk yanda Auwal yasu su had'a ido da Mami tak'i bashi dama saima basar dashi da take, Hajia kam sai kunya takeji ganin yadda Ameena keta hidima dasu ba tare da nuna komai ba, lallai Ameena ta daban ce a cikin mutane, sai yanzu take gane ba k'aramin kuskure ta tafka ba a rayuwa.

" 'yata Ameena da fatar mun sameku lafia dai" smiling tayi "Alhmdllh Alhaji muna lafia qlau inshaa Allah, sannunku da zuwa kunsha hanya" nan suka k'ara gaisawa.

"To 'yata kamar dai yadda kika gani ga Auwal Allah ya dawo mana dashi, bayan mun cire rai da sake ganin sa, kuma Allah cikin ikonsa ya wankeki a idon kowa wad'anda ke shakku akan zargin da akayi miki har ya zamo sanadin rabuwarku da Auwal" nan ya bata labarin komai.

Sannan yace " sai mu d'auki wad'annan al'amura a matsayin muk'addari ne ba makawa ba gurin gudu ba gurin tsira, sannan ga Auwal nan gabanki tare da Mahaifiyar sa sunzo Neman yafiyarki dama duk Wanda ya zargeki".


"Wallahi Baba ba komai ni ban tab'a rik'e kowa a raina ba hasalima na dad'e da yafe musu, kuma nayi farinciki da ganin wannan babbar rana mai girma".

"Don Allah Ameena kiyafe mini laifuna a gunki nasan ban tab'a yi maki ko nuhwarki da alkhairi a tsawon zamana dake saboda son zuciya irin nawa da son kai da wani dalili Mara tushe da asali dana rik'e, wanda yasa Rafia tayi amfani da wannan ta cutar damu duka, na rok'eki badan halina ba kiyafemin"

"Don Allah Hajia ki daina fad'ar haka wlh ban tab'a rik'e ki a rai ba, itama Rafia na yafe mata Allah ya yafe mana baki d'aya" ameen suka amsa gaba d'aya, sai mamakin kyawun hali irin na Ameena suke shiyasa Allah ya d'aukaka saboda kyauwun zuciyarta.

Auwal ma ya bud'e baki yayi zaiyi magana ta katse sa "Aa Auwal bakamin laifin komai ba, Iyayenka da d'anka kayiwa, ka bani mamaki na rashin yadda da K'addara da d'aukarta meyasa kayi haka Auwal"?

"Na sani Ameena ban kyauta ba kuma Allah ya jarabceni da kadd'ara na d'auka nisantar Ku zai kawo mini sasauci Ashe ba haka bane, saima azabtuwa da nayi da rashin, Son ka yafemin ban kyauta ba" yace yana kallon Abdool.

"Na yafeka Dady kuma nagode wa Allah daya karb'i Addu'armu ya dawo mana dakai lafia, Mami da Alhaji da Uncles' dasu Baba sun yaye maye mani gurbinka sun d'auke min kewarka, Aunty Asma'u tayi nata duty a kaina itama Allah yayi mata Rahama" duk aka amsa da Ameen sannan suka shiga yi mata gaisawar Asma'u da da mijinta da Yusuf, "nagode sosai Ameena da rawar da kika taka akan rayuwar Abdool, nagode sosai Baba, nagode Yaya, Sani, Salisu, Rabi'u, Maryam, Allah ya jikan Asma'u da Abdulrahim da Yusuf yakai haske k'abarinsu" ameen suka sake amsawa, sannan itama tayi masa gaisuwar Ahlam.

"Yanzu wad'annan duk jikokina ne duk yaran Abdool ne, wannan kuma Yaya ne da surukata 'yata 'yar Asma'u?"

Dariya aka saka Maryam tace "ai Yaya girma ya Riga yazo tuni" aka sake kwashewa da dariya, "Abdool sannu kuma da Rashin Zainab Allah yasa ta huta" Auwal ya fad'a, nan ma aka sake gaisawar Zainab.

"Ina Neman alfarmarki Ameena a karo na biyu ki k'ara yadda da auren ki da Auwal dan Allah" Hajia Kaltume ta fad'a cikin rauni.

Tana kuwa kallon gefensa ita yake kallo murmushi tayi "ba komai Hajia, zanyi shawara dasu Inna" tace don kada tak'i Hajia da d'auka ko bata huce bane da ita, "Ameena au wannan ba matsala bane, gobe duka zamu d'unguma muje can suma a nemi yafiyarsu" Alhaji ya fad'a.

Sai dare suka wuce tare da Meenal data Saba dasu Ramlah sosai basu Amatu da suka shige ranta lokaci d'aya...

"Yaya yau kam Ur complete am so glad 2 inama Ummi da Abi na raye" ta fad'a cikin raunin murya tana jin k'ewar iyayenta.

Bubbuga bayanta yake Cikin sigar rarrashi cike da tausayinta "Allah yayi musu Rahama Baby, kada ki damu su Mami zasu maye maye maki gurbinsu kuma ba gani ba?"

"I know Yaya kunyimin komai Wanda ko sune a raye ba zasu wuce hakan ba, i just missing them" rarrashinta ya shiga yi cike da tausayi, lafewa tayi a kirjinsa sosai.....





****************




Flight suka bi saboda basu gama huce gajiyar jiya ba, Argungu ma mamaki ne ya cika Hajia Kaltume ganin inda su Inna ke rayuwa lallai duk Wanda ya dogara da Allah to fa zai Isar masa, bayan an maida bayani an yafi juna a ranar a maida Auren Dady da Mami, Hajia ta bada sadaki da kanta, kashe gari suka wuce sokoto saida suka biya ta Kilgori suka gansu, Hajia ta K'ara girmama Allah da gode masa wato nata yazo da sauk'i sosai, sabanin na Hari, kai lallai ba inda mugun Abu zai kai mutum face nadama Mara adadi (Allah yasa mugane gaskiya).

Satin su d'aya a Sokoto suka shirya komawa Kaduna dan aikin Abdool, Dady ma ya tattaro nasa da nasa ya bisu Kaduna dan Mami ta Riga ta saba da zaman can so bazata iya dawowa Skk ba ga kuma aikin ta, kasuwancinsa yaci gaba dayi, inda suke zaune lafia Cikin aminci da soyayya (soyayya bata tsufa saidai ba'a botanta su tsufa).

Ya rik'e su Nihal da Amana ba banbanci kamar shiya haifesu, ita dai tana jin Meenal dai2 dasu Husna a ranta mashaa Allah komai Alhamdulillah.

Gyara sosai Abdool yayi wa su Ard'o dan yace ya dawo Kaduna yace shikam Kilgori ta isheshi anan ya saba, ga kuma mulki ina zai barshi, hakan yasa ya gina musu gini mai kyau na zamani, sannan ya bawa su Shatu da mazajensu jari mai tsoka, dan Lanti tayi aure ta auri wani mutum mai kirki itama ta gyara halayenta suna zaune lafia.........



************







Hadin guiwa sukayi suka d'auki jirgi sukutun sukaje umara tun daga kwansu da kwarkwata ba Wanda aka Bari har su Iya Hari (hoho wayaga Hari a saudiya, kada ki manta Iya Hari ki kaiwa aminiyarki ta gani kashe ni ziyara wato Mom Zee) lol.

Gidansa na can wasu suka sauka wasu gidan Ikbal, wasu kuma aka kama musu.

Ikbal sunyi farinciki da ziyarar ta ba zata sun tabbata lallai Auwal d'an dangi ne, yau dai ga Ameena da Abdool sun gani da suke shan labarin su, sunyi ziyara sosai, watansu d'aya suka dawo, anyi sa'a ana Cikin Hutu su Ramlah, Sadee Ansha tsaraba har da sakwannninta an kawo mata da k'ari.

Tare dasu Ikbal suka dawo Nigeria inda sukaga mazauninsu, sun zaga garuruwa da dama a Nigeria sunyi dad'in ziyarar dan Nigeria ta burgesu sosai musamman suturun su da al'adunsu, wani abun ma sai a Argungu sunga gargajiya tsantsa( Argungu garin nabame kowa sarki, kabawa ikon Allah Ku adda ruwanan! Hmm da k'asar wasu gwara k'asa ta, da garin wasu gara garina.)...........








>?'? _mura on top, ur supplication is needed my Fan's, love as always #1love# going 2 missing u_ =?%?=?*?














=؄?Meryerm Abdool=؄?
[10/25, 8:37 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Real Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*




*_Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa yace "Ku ladaftar da 'ya'yanku akan Ladubba guda uku, Son annabinku, da son iyalan gidansa da karatun AL-QUR'AN, don su makaranta AL-QUR'AN suna Cikin inuwar Allah ranar da ba wata inuwa sai tasa, tare da annabawansa da zab'abb'unsa.(majma'ul baharai)_*

=?O?

*komai yayi farko zaiyi k'arshe, amma banda ikon Allah, nagode sosai masoyana masu bibiyar rubutuna da hak'urin da kukayi dani har zuwa yau, nagode da soyayyar Ku gareni da k'arfafarku nagode sosai thanks 4 care and supportd'd'd'=?? bazan manta daku ba gidan amana da had'in kai, gidan karamci da girmamawa, Allah ya barmu tare cikin aminci da k'aunar juna P.M.L gaba dai gaba up!=?M?













=??? *Last Episode* 271--275









*_AFTER TEN YEARS........._*






" A yau gamu tare da shahararriya, hazik'a, jaruma, zak'ak'urar 'yar jaridar nan wacce ta kware gurin tono gaskiya da rubuta ta ba tare da tsoro ko shakka ba, wacce ta sadaukar da rayuwar ta gurin rubuta gaskiya komai d'acinta kuma kome zata zama wato, koda yace wak'a a bakin mai ita tafi dad'i, ko meye sunan Hajiyar? Masu kallo suna son sani"

Sanye take da dakakken les dan ubansu brown colour mai adon milk flowers, hakan yasa hihab d'inta ya kasance milk haka bag and shoes nata(mashaa Allah na fad'a tare da sake baki lallai da banyi mata farin sani ba bazan ganeta ba, ta canja d most tayi fresh tayi jiki ga wata irin wayewa da tayi wacce tayi dai2 da islama bata turawa ba).

Smiling tayi "Sunana Ramlah Abdulrahim Modibbo wacce akafi sani a harkar rubutu da Mrs A.A"

"Mashaa Allah Mrs A.A nima dai shi nafi sani amma a yau ni da masu kallo munji ainihin sunanki mai cike da tarihi Allah yayi albarka"

"Ameen nagode sosai"

"To idan ba damuwa munaso muji tarihin jarumar tamu a tak'aice, gwagwar mayar da tayi da rayuwa har zuwa yau data zama mai nasara?"

Anan ta shiga bata labarin ta a tak'aice mai cike da tausayi, koda ta kammala daga ita har mai tambayan kuka suke, handcart tasa ta share hawayen tana murmushi sannan ta mik'a wa mai tambayan tata d'aya ta goge nata itama.

Gyaran murya tayi "na dad'e banji labari mai tab'a irin wannan ba, lallai Mrs A.A kinga gwagwar mayar rayuwa, saidai kuma hak'uri da kikayi ya zame miki alkhairi, Allah ya sauya miki rayuwa ya d'aukaka ki ya maye miki gurbin duk wani rashi da kikayi, hak'ik'a labarin ki ya isa misali, ishara ga mutane, Allah ya jikin magabata yakai haske k'abarinsu ya kyautata tamu bayan tasu"

"Ameen ya Allah nagode"

"Shin ko zamu iya sanin dalilin da yasa kika zabi ki karanci aikin jarida? me yaja ra'ayinki a aikin jarida? Ko akwai Wanda ya k'arfafa maki akan haka? meye nasarar da kika samu cikin aikin? Shin kin tab'a fuskar wani k'alubale ko barazana a wannan aikin?"

"To a gaskiya tun farko ina sha'awar zama journal and inaso na wanke rad'e-rad'in da akeyi game da journalist akan suna rubutu ne kawai don 'yan siyasa wato ya basu amma basa tono gaskiya akansu suna cover na laifukansu, in fact an d'auki d'an jarida baisan me yake ba sai abinda aka saka shi, to wannan yana d'aya cikin abinda yasa na zabi harkar"

"Dukkanin 'yan uwa sun k'arfafa min kuma sunyi supporting d'ina ta ko'ina musamman mijina abin alfahari na ba abinda zance sai Allah ya saka musu da mafificin Alkhairinsa"

"A gaskiya nasarorin da na samu ba zasu k'irgu ba, mafi girma irin Addu'o'in da nake sha gun jama'a shima wani babbar nasara ce gareni, k'alubale ba'a rasa ba, don akwai time d'in da aka tare ni na d'auko yara daga school, Allah ne dai ya karemu a ranar, barazana kuma ina samu a kowacce rana, saidai na wannan bai tab'a karya min gwuiwa ko yasa naji jikina yayi sanyi ba, saima k'arfafamin da yake akan ina ba k'asa ta gudummawa kenan"

"Hakane kam, tabbas kin kawo canji Sosai a harkar jarida, kuma an samu ci gaba sosai a harkar jarida, ba abinda zamuce sai Allah ya kara dafa mana ya kuma k'ara shige mana gaba, ya kuma karemu daga sharrin mak'iya da mahassada"

"Ameen"

"Yau fa masu abune da abunsu to tambayoyi sai kin ture, ko zaki iya gama mana meye ma'anar " Mr A.A d'in nan"ta fad'a tana dariya.

"Hmmm kada ki damu zaki samu amsar kowacce tambaya taki" smiling tayi mai sauti "Mrs na belonging ga miji to A.A na nufin Abdulmajid Auwal wato Yayana mijina"

"Kai mashaa Allah, lallai Dr Abdulmajid ya taka babban matsayi a rayuwar ki, to Allah ya raya zuria ya k'ara k'auna a tsananin Ku madawwamiya"

"Sosai Yaya Abdool shine duniya, Ameen Ameen nagode"

"Ko zaki iya gaya mana matsayin Abdool a gurinki? Kamar yadda koma komai da kika mallaka yana d'auke da tambarin Abdool kamar irinsu Abdool oil&gas naki, Abdool supermarket, Abdool Islamic scholars da dai maka mantansu"

"Hhhhhh! Abdool uba ne, Abdool yayane, Abdool miji ne, Abdool k'anine, Abdool d'ane kuma inshaa Allah har jika sai nayi Abdool, so kinga kenan Abdool na nufin Ramlah, da ina damar zama Abdool kacokam to tabbas zan zama, Abdool shine rayuwar Ramlah" (nima dai nace Abdool ne rayuwar Meryerm).

"Tofa lallai Mrs A.A kin tara Abdool koma ince ke zama Abdool ko zaki bani d'aya ne?"

"Hmm idan kinada k'ari zaki iya bani, dan ko zan tara haifi yara d'ari bazan gaji da saka musu Abdool ba, inason Abdool sosai musamman *Abdulmajid* Yayana mijina, jigon rayuwa ta, abin alfahari na, farincikin rayuwa ta, Allah ya barmu tare har mutuwa" ta fad'a cikin shaukin soya year mijin nata.

"A gaskiya kin burgeni, inama kowace mace zatayi koyi dake, taso mijinta kamar yadda kikeson Dr Abdulmajid da an samu zaman lafia sosai a gidaje da ana soyayya domin Allah, Allah ya barku tare cikin Aminci"

"Ameen nagode"

"Ko zaki iya gaya mana me kikafi so a rayuwa?"

"Yayana mijina *Abdulmajid* mijin da babu kamar sa yayan da babu irinsa, mafi tausayi a cikin mutane, mai karanci da mutunci a gurin kowa mai tausayin iyayensa mai kyautata wa iyalansa, guda d'aya tak tamkar da dubu"

"Ya ilahi da fatar Dr Abdulmajid yana gaban tibinsa yana kallon wannan hirar tamu, yana kallon yadda matarsa ke Koran ta ka da yaba ka nasan ka tsuma da zantukan ta, ina fatar Allah ya raya wannan k'auna har abada"

"Ameen ya Allah"

"Munaso ki mik'a godiyarki da gaisuwar ki zuwa ga wasu mutane masu muhimmanci a gareki"


"Tofa! Hmm da farko ina mik'a godiya ta ga Allah mad'aukakin sarki, wanda ya samar dani daga babu, ya sanyoni cikin al'ummar musulmi ba tare da iyawata ba sannan zan godewa iyayena da suka zamu sune silar zuwana duniya, ina godiya ga kakana Ard'o Wanda ya reneni cikin soyayyar da k'auna, ina mik'a godiya ta ga mamata uwar goyona kuma surukata Mami tare da Dadyn mu Allah ya saka musu da alkhairi, dole na mik'a gaisuwar had'e da godiya ga gimshik'in rayuwa Yayana Mijina Dr *Abdulmajid* gaisuwa zuwa ga Aminan Arziki 'yan uwa na jinin jiki Nihal, Sadee, Amal Meenal, Aunty Zee Allah yayi mata rahama dama sauran wad'anda ban ambata ba duk ina mik'a gaisuwa, gaisuwa zuwa ga manyan gobe 'ya'yana abin alfahari Allah yayiwa rayuwa albarka"

"Kai madallah da fatar duk kunji sak'on Mrs A.A kuma kunyi farinciki"

"Daga k'arshe meye sakonki, ga masoyanki harma da mak'iyanki, meye shawarar ki zuwa garesu? A gurguje dan na fahimci idan muka barki ba gajia zakiyi ba" tace tana dariya.

Itama dariyar tayi "sak'ona zuwa ga masoyana har mak'iyana shine ina sonsu gaba d'aya, shawara ta itace ayi hak'uri da komai na rayuwa mai wucewa ne kuma duk abinda akayi hak'uri a kansa inshaa zai wuce muddin anyi hak'uri mai kyau, hak'uri bai tab'a zama cuta saidai alkhairi ayi hak'uri nothing is parmanent even our live and world so be patients, behind every success there ris many obstacles but at d end there ris way inshaa"

"Wannan haka yake dan rayuwar ki kad'ai ta isa misali gamai lura, mun gode da wannan lokaci da kika bamu muna miki fatar alkhairi a rayuwa, muna mik'a jarumin maza Wanda ya ciri tuta a mazaje angon gurin jarumar mace mai kishin k'asarta wato Dr *Abdulmajid* likita na talaka Allah ya k'ara girma"

"madallah nima ina godiya da wannan karramawar da akayi Mani, nagode sosai da Addu'a da muka sha yau sai mun k'ara had'u wa wani lokaci, nagode"

"To jama'a duka duka anan muka kawo k'arshen firarmu da fittacciyar 'yar jarida jaruma, hazik'a Mrs A.A Wanda ni Hafsat mai sharrif na gabatar fatar kunyi farinciki da wannan firar mai cike da darasin rayuwa, saduwar alkhairi......."



********""


Abdool dake zaune kan sofa cikin d'akin sa tun da aka fara firar ko motsin kirki bayayi saboda yadda bada duka Attention nasa, hakan yasa yabar yaran parlour su kalla ya keb'e kansa saboda muhimmancin da bawa firar...


"Oyoyo Maa, oyoyo Maa..." Yaran ke fad'a cikin murna ganin mahaifiyar tasu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login