Showing 69001 words to 72000 words out of 88300 words

Chapter 24 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1602

jimk'e takardar tayi da duka hannayenta biyu "nima nayi kishi dake sosai Aunty Zee, na d'auka kin kwace min Yaya Abdool ashe ba haka bane, na yafeki aunty Zee bakimin komai ba, kuma inshaa Allah, bazan tab'a banbamta junior da d'an da zan Haifa ba, ina sonsa sona gaske, Allah yakai haske k'abarinki, Allah ya sadamu a Aljannarsa mad'aukakiya don rahamarsa, missing u much Aunty Zee" duk Cikin kuka take maganar cike da nadamar abubuwan da tayi ma Dr Majeed, tasan komai ya faru laifin ta dan ita taja hankalinsa kuma tasan yaso ta tun kafin ta zama abarso, to yanzu ta ina zata fara bashi hak'uri?

Turo k'ofa akayi ganin tana hawaye yazo da sauri tare da rungume ta yana bubbuga bayanta, mamakine ya kamashi ganin bata tureshi ba saima k'ara lafewa da tayi a jikinsa, bai gama mamaki ba yaji ta zagayesa da duka hannayenta ta rungume shi.

"Pls yaya Sorry 4 everything I totally misunderstand u pls forgive me....!"

"Shitttt! U don't nothing wrong!" Ya katseta tare da d'ora yatsansa akan lip nata, bud'e baki tayi zatayi magana, kafin tace wani abu har had'e bakinsu guri d'aya, cikin wani irin salo yake kissing nata, itama ware wa tayi tana tayashi, sun kai 10mt haka, sannan ya fara zare bakinsa yana kallon ta k'asa-k'asa idanunsa sun canja launi zuwa ja, ita kuma sunkuyar da kanta tayi cike da kunya, mik'ar da ita yayi tare da d'aukar ta kamar wata baby doll, bai sauketa ko ina ba sai toilet, da kansa yayi mata alwala shima yayi sannan ya sake d'aukota direta yayi tare da shimfid'a musu darduma, sif ya bud'e ya d'auko mata zane da hijab, ita dai binsa kawai take da kallo, turare ya d'auko zai fesa "aa karka saka" tace, murmushi kawai yayi tare da mik'a mata, itama murmushin tayi masa Wanda rabon da yaga irinsa akan fuskarta har ya manta "nafayi sallah na" tace cikin siririyar muryarta.

Kashe mata ido d'aya yayi yana smiling "wannan special ce irin ta ma'aura wacce bamu samu damar yi ba zamuyi k'ara'i" turo baki tayi kamar wata yarinya, cikin wasa yasa yatsarsa ya buga bakin kad'an "common baby munada abubuwa a gabanmu masu yawa ga time na tafiya" d'aura zanin tayi tare da saka hijab d'in ba tare da tace komai ba.

Shigewa gaba yayi tare da jansu, raka'a 2 sukayi kamar yadda sunnah ta tanadar sannan ya dafa kanta ya shiga kwararo musu addu'a da harshen larabci da kuma hausa duka.

Saida yayi tsawon 30mnt yana addu'a, mik'ar da ita yayi sannan ya nad'e darduma tare da cire mata hijab da zanin ya ninke, gefen bed ya zaunar da ita sannan ya zauna shima, kama hannun ta yayi yace "nagode wa Allah daya nuna min wannan ranar da muka samu fahimta juna, zanyi marking nata cikin rana mai girma bayan first night namu, sannan nayi alk'awarin zan kula dake zan tarairayeka zan zamo hango abin jinginawarki zan kare mutuncinki zan rik'e amanar ki har abada, fatar zakiyi hak'uri dani da kuskurena idan nayi miki, ina mana fatar zaman lafia mai d'orewa".

Matse hannunsa tayi cikin nata " inshaa Allah zaka sameni mai biyayya a gareka, ta kowanne fanni zanyi iya k'ok'arina, Allah ya bamu Alkhairi mai dorewa a zamanmu"

Lumshe ido yayi wani dad'i na ratsashi yana feeling special, sannan yace "ameen uwargidana, one mnt" yace tare da mik'e wa yabar d'akin, plate ya dawo dashi a hannunsa, kayan cikine masu kyau a ciki da zafinsu sunji albasa, da tumatur da yaji sai k'amshi ke tashi, aiko d'iyar baffa tuni yawu ya tsinke, table ya janyo ya girke a gabanta tare da bud'e fridge d'inta ya d'auko fresh milk, stool din mirror ya janyo ya zaune yana fuskanta "bismilla" yace tare da d'aukar yanka d'aya zuwa bakinta, itama d'auka tayi ta bashi, a haka suka ciyar da juna cike da salon k'auna.

D'auke plate d'in yayi yakai kitchen ita kuma toilet ta shiga tayi brush, tare da hayewa kan bed, d'akin sa ya wuce yayi brush shima sannan ya dawo d'akin ta, kashe wutar yayi yabar deep one, sannan ya bita kan bed d'in, kusa da ita ya kwanta tare da leka fuskarta, likimo tayi yasani, murmushi yayi mai sauti tare da janyota zuwa jikinsa, anan suka shige wata duniya mai wuyar fassarawa romancing juna suke ba sassautawa duk da ranta fal tsoro, kasa daurewa tayi "pls yaya i'm scared kamin a sannu" Cikin kasalalliyar murya yace "feel free baby, ba zakiji zafi ba wannan Karon and zan biki a sannu ki saki jikinki kawai"....






***************




Tun daga ranar zaman lafia ya wanzu tsakaninsu, soyayya suke kamar su cinye juna, ga kulawa da tarairaya da take samu wurinsa kamar wata sarauniya, lallai a yanzu ta k'ara yadda da ba kowa a zuciyar Abdool sai ita natane ita kad'ai, komai tare sukeyi tun daga, kullum suna manne da juna suna soyewa, datayi d'an motsi kad'an " mene ne, meya faru, unborn ne ko" duk ya rikice yana tambayan ta, haka idan hospital yake yana mak'ale da waya suna hira har dawo gida, baya jin shakkar nuna mata soyayya a gaban kowa, ko gidan Mami sukaje bayajin kunyar nuna mata k'auna da tarairayar ta, sai ita yake bari da kunya.

Tuni suka dawo da junior gurin su Inda suke nan nan dashi, Ramlah kuwa ta had'a kiba abinta ta k'ara haske, Abdool sai tsokanarta yake wai ta zama Auntynsa yanzu tunda ta fishi kiba, had'e fuska take kamar yarinya inya tsokaneta, junior kuwa saidai yayi ta dariya yace Maa ta dawo yayinya.


*****************

Sanda Iya Hari ta farfad'o ba abinda take fad'i sai "kai mini rai Jauro karka kasheni" sai tambayan ta ake meya had'a ta da Jauro, meya kaita jeji amma ba amsa sai kuka take tana rokon Jauro yayi mata rai.

Tsawon watansu uku a asibiti sannan Ard'o yace a dawo gida tun da raunukan sunyi sauki ayi maganin kariyar na gargajia, abun tausayi iya Hari duk ta jeme ta lalace dama can ya muke muna 'yan sarki, kullum cikin kuka take tana fad'in a kira mata Ramlah, idan aka tambayeta me zata mata saidai tai ta kuka tana ita dai a kawo mata Laure, Hinde kuwa likkafa taci gaba dan yanzu tabar k'auyen gaba d'aya tabi wani saurayinta birni, wai iya Hari ta dameta da doyi a gida, da yake ba'ayi mata wanka saidai a goge mata jiki kawai Wanda shima Shatu CE keyi kullum tana gidan tun safe sai dare take komawa gidanta, da yake mijinta bai da matsala, Lanti kam sai tayi sati bata zo ba kuma ko zuwan tayi saidai ta kame gefe tana mata sannu ko Inda take bata zuwa wai d'oyi takeyi, kuma a dalilin ta tasa 'yarta ta gudu saboda azabar d'oyi.

Ard'o ma zuwa yanzu tausaya mata yake sosai ganin yadda duniya ta juye da ita (hmm duniya kenan tafi bagaruwa iya jima).

Gashi har yanzu tak'i fad'ar meya kaita jeji amma yafi kyautata zaton ba Alkhairi bane, ga shanunta ya Nema ya rasa anyi juyin duniya tak'i fad'in in da ta kaisu, kullum saidai kuka daga an tambayeta, yanaso yaje Kaduna yaga Ramlah saidai ciwon Hari ya hanashi tafiya gashi sai kashin kud'i ake amma kamar ana k'ara ma ciwon tak'i ne (to dama duniya imma shakiran ce ko imma kafura >?7? @&) Allah yasa mudace......



Manage pls








_ina cikin damuwa ina Neman Addu'arku Friends=?#?_












=؄?Meryerm Abdool=؄?
[10/3, 10:53 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*



*_zuwa garemu writers, ban cire kaina ba, tambayace dani shin meyasa muke rubutu? Saboda samun fans masu zugamu suna cewa muci gaba da fire zasu bimu da fetur ko kuwa munayi ne saboda gyara? Bansan abinda ke ranku ba, amma abin da na sani shine kowace kalma da muka rubuta wallahi zamuyi bayani akanta a gaban ubangijinmu gobe k'iyama, shin muna tunanin idan muka doge da yadda muke rubutu a yanzu all about romancing sex, zamu tsira kuwa? Zamu iya hujja da rubutun mu gaban mahaliccin mu? As an advice we ar not too late even now, muyi k'ok'ari mu gyara mu, nidake dasu ana sabawa ubangiji dare da rana shi kuma mai gafara ne dare da rana muddin bawa yayi tuba mai kyau, so mu taimaki kanmu muyi amfani da basirar mu ta hanyar ceton al'umma daga wata musiba ba tsunduma su a ciki ba, idan har nayi/kikayi rubutu mai amfani koda mutum daya ya karanta ya amfana dake yafi mu rubuta barna mutum dubu su yaba mana, Wanda yabon iya Inda mukayi ne shikenan, ita kuwa azabar Allah tana can tana jiranmu a madakata, Allah yasa mu gane>?&? @&banyi dan cin zarafi ga kowa ba, duka nace so wacce ta tsargu ita taso ba ruwana.=?E?


*_oh!>?&? @& Readers kuma ga naku....meyesa kuke son halaka kanku Ku halaka wasu gaba d'aya, without u impossible, saboda Ku ake rubutun nan, amma abin haushi yanzu idan novel ba bad'ala ba wacce zata cigiyesa amma idan ana batsa to yanzu kunyi chaa akansa kuna nema ko meye amfanin haka? Bansan meke ranku ba, amma abinda na sani shine kuna da babban kamisho a halakar writer, a duk lokacin da kuka an rubuta barna kuya kamata kuyi zanga-zanga ku kauracewa littafin Ku nuna anyi ba dai2 ba, amma ina bakwayi saidai ma Ku k'ara zuga writer d'in kuna fashemata kai kuna nuna mata masu gayamata gaskiya hasada suke mata, ko meye abin hasada a cikin rubutu na online Wanda ba riba a ciki, ribar d'aya idan ka rubuta abinda wani ya amfana ka samu lada that all fa=?E?








=??? *Episode* 231--235






Three months da tarewarsu lokacin cikinta na four months, aka fara bikin Nihal su Ramlah an dage sai hidima ake kullum gidan Mami take wuni sai dare Abdool ke d'aukar su, da sassafe kuma zai saukesu, kallo d'aya zakayi mata ka gane tana da ciki dan duk alamomin sun bayyana duk da bai fito ba ya boye a k'irji da hips, aiko tanashan tsiya gasu sadee wacce itama saura 2 months bikinta, Amal ma an saka mata rana ita da Ismail cousin d'in Abdool, "hmmm kuyi abinku ai dad'in ta dai duk kuna hanya kuma" sannan ta kalli Nihal "hehehe ke sisto kima daina biyesu dan saura k'iris ki jona ni" ta fad'a tana dariya harara Nihal ta aika mata ba tare datace komai ba, dan tunda satin bikin ya kama tasha jinin jikinta ganin rawan kan ya Hakeem ya sai k'aruwa yake.

Mutanen Besse dana Argungu duk sun iso, gida Mashaa Allah ya cika sai hidima akeyi.

Abdool ya taho d'ukarsu a parlour ya had'u dasu Inna "oh ni Habiba! Kaidai ka zama bita zai-zai to wuce yau ba inda zata" wani malalacin smiling yayi.

"Imma da abin yafi haka ki fad'a na yadda, amma ba abinda zai hanata tafiya yanzu" yace yana dialing no nata ganin bata gurin.

Turo baki tayi ganin kiran nasa, dariya Sadee tayi " 'yan matan gidan Dr majeed yadai" harara ta jefa mata tare da kai mata duka, dariya ta k'arayi harda kashe mata ido d'aya, Amal kuwa dafa tayi "manta su sisi jeki gani ko zai barki d'in" mayafinta ta Zara kawai tana fatar Allah yasa ya barta, dan tanaso sukai k'arshen shirye-shiryen Friends day da zasuyi gobe, gashi suna tsaka da tad'i ya k'atse su.

Bata bi takan Inna dake mata tsiya ba wucewa tayi abinta harabar gidan, saman motar ta hango shi shida Junior, suna firansu, tana isowa ya diro yana mata Murmushin nan nashi mai sanyi, mayar masa martani tayi tare da tambayansa office, ansawa yayi yana tambayan ta gajian hidima da unborn.

Bud'e mata murfin yayi kamar yadda ya saba saidai a maimakon ta shiga sai rik'e murfin tayi tana kallonsa da pity face "pls Yaya one favour?"

Ido ya zuba mata "oya said it all ears?"

"Um... dan Allah ka barmu mu kwana anan yau kaga bamu gama tsara event d'in gobe ba ka taho" junior jin me ta fad'a yasa yayi tsalle "Yawwa Maa nima inaso mu kwana gidan Mami"

Harara ya watsa ma Junior tuni yayi tsit sannan ya lafe a jikinta, ido kawai ya zuba mata baice komai ba,

"Pls Yaya yau d'aya, kafa junior ma naso"

"Aa baby nida unborn bamaso" ya fad'a da tana shafa cikinta, duk da ranta yaso ta tsaya amma ba yadda zatayi tunda har yace Aa to ta hak'ura dan basu saba musu ba, kuma tasan yana bata dama sosai to bai kamata ta shiga hakkinsa ba.

Fuskarta ba yabo ba fallasa tace "shikenan bari in d'auko jakata"

Shan gabanta yayi "fushi baby.. Pls sorry banyi dan in bata ranki ba, kinsan bazan iya barin ki a wani gun ba ni kuma ina wani gu har tsawon kwana inba da lalura ba" ganin yadda ya marairaice mata, yasa ta saki fuskar hadda murmushi "am OK Yaya jaka kawai zan d'auko I understand u".

Duk da haka bai barta taje ba wai kada ta wahala sai Nihal ya kira yace ta bawa Abduljabbar ya kawo musu, ita dai sai kallonsa take wannan k'auna da Yaya ke mata anya ana yiwa wata mace irinta ko(saini akewa irinta lol)

Haka akayi bikin Nihal aka gama ta tare gidan Masoyinta dake unguwar dosa, shima cikin hospital d'in Abdool yayi nasa ginin dan shima anan zai zauna, inda hakan yaiwa Ramlah dad'i sosai sisto ta dawo kusa da ita, sun bar Mami da kewa yanzu daga ita sai su Husna.

Kullum idan mazajensu sun fita zasu had'u gidan d'aya suyi ta firarsu girki ma tare sukeyi, saidai kawai wacce ba gidanta akayi ba ta zuba a flask ta kai nata gidan basu zasu rabu ba sai dare dan bacci dan ko mazajen sun dawo saidai su zauna a yi dasu, da yake har yanzu ba'ayi lunch d'in bud'e hospital d'in ta Abdool ba.

Burin abokan ya cika na zama guri d'aya da iyalansu Wanda tun suna school suke da wannan burin, junior kam ya zama d'an gata kowa nan nan ake dashi shalelen paa da Maa da Aunty da Uncle.




***********



Lokacin da Abdool yayi mata scanning ya k'asa gane abinda ke cikin ya d'unk'ule guri d'aya, amma nauyinsa da girmansa yafi k'arfin watannin sa Wanda hakan ba k'aramin d'aga masa hankali yayi ba, saidai dole ya b'oye dan gudun tayar mata da hankali, searching ya shiga nan ya gane akwai twins masu dunk'ulewa su zama d'aya inda camera ba zata iya rabe su sai a d'auka d'aya ne, nan hankali yad'an kwanta yana jin farinciki idan suka kasance twins saidai yana tausaya mata haihuwar fari ga, amma ai yana nan zai bata dukkan kulawar da ta dace.

Cikinta na 6months akayi bikin sadee da uncle Lukman d'in ta, zuwa yanzu cikin Ramlah ya fito sosai duk kibar da tayi ta rage, ga nauyi tsiya da cikin ke mata dak'ar tayi performance a bikin Sadee, Abdool ma dan yasan matsayin Sadee ne a gurinta da irin kulawarta garesu da bazai barta taje mata ba.

Mami ma ganin yadda cikin yayi ta tausaya mata saidai ganin yadda Abdool ke bata kulawa ga kuma Nihal kusa yasa hankalinta kantawa saidai duk da haka duk bayan kwana biyu tana zagayo su.

Ard'o ma dayazo ganin halin da take ciki yasa yak'i gayamata ciwon Hari, duk da ciwon nata ba sauk'i kullum sai k'aruwa yake, ga kullum kuka take tana kiran a kawo mata Ramlah.........







_kuyi hakuri dani dai na shiga busy ne anyi mana haihuwa ga lafia bata isheni ba, satinnan dai sai a slow pls ayi hakuri dani #one love# =?
?=??_








=؄?Meryerm Abdool=؄?
[10/10, 5:46 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*






```An karb'o daga d'an Umar Allah ya yadda dasu yace "manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa yana cewa :-
An umarceni in da in yak'i mutane har sai sun yarda babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma sun yadda annabi Muhammad manzon Allah ne, su tsaida sallah su bayar da zakka, idan suka aikata haka toku tayani kare jininsu da dukiyarsu, kada a tab'a mutuncinsu sai tare da wani hakkin musulunci, hisabinsu yana a gurin Allah mad'aukakin sarki.```

*Bukhari da Muslim suka ruwaito shi(arba'una hadith)*=?L?


d'my parrot Hafsat M(rayuwar Aurena na fire aci gaba da gashi=??) love dear thanks 4 d care=?L? ?

My name sake i really miss u sweetheart=?*? Maryam Y zangod'

My neighbour Zee Yabour ina cigiyarki dear kin buya=?+?

Am back a gain my half my true friends thanks for d care=??=??=??


Ina yabawa da readers masu bibiyar rubutu na musamman masu ganin kuskure suyi gyara heart dearies aci gaba da gyara mana kuskure a duk Inda aka hangoshi zamu gyara inshaa Allah=??=??=??=??#one love #








=??? *Episode* 236--240












Kwanaki biyu Ard'o yayi ya koma bayan ya cikawa Ramlah galan da rubutu yace tana sha tana shafawa a jiki kullum safe da marece, kamar ko yaushe tsaraba sosai akayi masa, Ramlah ji take kamar ta bishi saidai ba daman haka duk da ya gayamata ko lafia yake jikinta na bata ba lafia, ga yawan mafarkin iya Hari da take a cikin mawuyacin hali, tanaso taje gareta dan komai tayi mata a rayuwa ba zata k'ita ba tunda tana sonta kuma tana mata fatar gane gaskiya.

Sanda ya koma ya isko ciwon Hari yayi tsanani ga wani wari da k'afar ke fitar wa hakan ya tilasta su komawa hospital, Shatu itama duk ta jeme itama yanzu har bacci gunta takeyi, saboda tausayin halin da take ciki, Lanti kam mijinta yace duk ta k'ara zuwa gidan a bakin aurenta, dama mai neman kuka an jefesa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login