Showing 81001 words to 84000 words out of 88300 words

Chapter 28 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1609

idanunsa suka firfito waje sunyi jajir sai kakari yake "saina kasheka azzalumi macuci mai raba sunnar manzo" shine Kalmar da ke fitowa daga bakinsa, shikam sai mutsu-mutsun kwantar kansa yake amma ina ko gezau bai ba.

Kuka yarinyar ta fashe dashi tana Jan hannun mahaifin nata "Aa Abi kada ka illatashi meyayi maka Abi ka barshi" tace fad'a Cikin kuka.

Sakinsa yayi da k'arfi tare da tura sa baya, Allah ya soshi badan kukan 'yarsa da yake matukar so ba da ba zai bar wannan azzalumin ba sai ya illatashi koya kasheshi, mugun kallo kawai yake binsa dashi.

Gurgun sai Sosa wuyar sa yake dayaji shaka ajali dak'yar ya daga keken ya sake hawa yace "na cancanci koma meye daga gareka amma dan Allah ka d'aure ka saurareni" yace, still da kallon yake binsa ba tare daya ce uffan ba.

"Nasan na zalince Ku kuma na dad'e ina Neman inda zan ganka na nemi gafararka kona samu sauk'in wannan bala'i da nike ciki, ba kai kad'ai na jefa a irin wannan halin ba hasalima Sana'a tace in bata aure a biyani, kaima ba haka kawai nayi maka haka sakani akayi inyi..."katsesa yayi da cewa "gayamin wane marar imani ne ya sakaka yimin wannan danyen aiki?"

Zaiyi magana sai wata mota ta tsaya a gabansu da mamaki na cikin motar ya fito baki bud'e ya nuna shi da yatsa baki na rawa yace "Auwal!"......








_gatan da zakuyimin d'aya ne masoyana ku nema min gafarar ubangiji dani daku gaba d'aya ya yafe mana kurakurai mu dan rahamarsa=?O?











=؄?Meryerm Abdool=؄?
[10/20, 5:27 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Real Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*




```An karb'o daga ka'abi d'an Iyadi (R.D) yace" Manzon Allah (S.A.W) yace "kowace Al'umma tana da fitinar ta, fitinar al'umma shine dukiya```

Sahihuh(hakkun mubeen)

*ya Allah kada ka jarabcemu da dukiyar da zata zamo fitina a garemu* =?O?




=?
? _kun nunan cewa ko bani media kunayi dani, kun nunan ni yar gata ce a gareku=ؕ? Ku sani Meryerm Abdool ma tana sonku sosai iya wuya ana irin mugun taren nan har abada>?? Hafsat mai Sharif, Raheenat Mahmoud, Maryam Y Zango #ILVYSM 4rm d higher rank of my d'#_






=??? *Episode* 261--265






"Yaya Rabi'u" shima ya fad'a yana kallon sa, k'arasowa Rabi'u yayi "Auwal dama kana raye a duniyar nan ka gujemu? Haba Auwal wannan wane irin hukunci ne kayi mana akan laifin da bamu aikata ba, haba Auwal! Haba! Yanzu dai mu shiga ciki wad'annan fa?" Ya nuna gurgun da yarinyar.

"Mu shiga ciki Yaya zakuji bayanin komai" tura gurgun Rabi'u yayi suka shiga ciki, direct part d'in Alhaji suka nufa, yana zaune kamar kullum kan kujerarsa carbi a hannun sa yana ja, sallama Rabi'u yayi tare da shiga.

Kasa k'ara sa amsa sallamar Alhaji yayi tare da mik'ewa tsaye yana nuna Auwal da yatsa cikin inna inna yace "Au..Auwalu kaine ko dai gizau kakemin kamar yadda ka saba"

Gabansa Auwal ya isa tare da sakin kuka "nine dai Auwalun ka Baba, dan Allah Baba ka gafarceni nasan nayi ba dai2 ba dan Allah kayimin afuwa Baba" yace cikin kuka tare da kama k'afafunsa.

"Alamdulillahillazih bi ni'imatih tatimmus salihat" shine Kalmar da Alhaji Sada keta maimaita wa, d'ago shi yayi tare da rungume shi tsam wani sanyi da rahama ce ta ratsa su irin ta uba da d'a, Rabi'u dake gefe sai murmushi yake, shikam gurgun sai kwalla yake yana kaico da rayuwar sa duk shine silar nisantar su, yarinyar kuwa sai kallon tsohon take ba tambaya tasan shine kakanta.

"Rabi'u kaje kayi sanarwar metting na gaggawa yanzu" Alhaji Sada ya fad'a.

Hajia Kaltume ce ta fara isowa parlon suman tsaye tayi tare da zaro ido tana nuna Auwal ta k'asa magana, duk Wanda ya shigo indai yasan Auwal turus yakeyi dan sun dad'e da cire tsammanin sake ganinsa, Maryam ma suna gari sunzo hakan yasa itama ta halarci taron da nata iyalan, wad'anda basu sanshi ba sai a labari duk dai sun ganshi wasu sun ganesa wasu kan basu gane ba, Rafi'a ce ta shigo last dan bata gida tana gurin shashancinta saida Rabi'u ya matsa sannan tazo, ganin Auwal bai wani d'aga mata hankali ba, sai bayan ta zauna idonta suka sauka akan gurgun, ki tayi kamar ta saki fitsari a gurin tsabar tsoro zaro ido tayi tuni ta fara gumi duk da sanyin Ac dake parlon, Ji take kamar ta zura a guje saidai ba damar haka.

Bayan an nutsu kowa ya hallara Alhaji yasa aka bud'e taro da Addu'a, sannan ya fara jawabi kamar haka "kamar yadda muka sani munyi rashi na d'aya daga Cikin 'ya'yan gidan nan tsawon shekaru 29 da suka wuce, wasu daga cikinmu sun sanshi wasu kuma basu sanshi ba sai a labari Wanda har mun cire rai da ganinsa, to Alhamdulillah a yau Allah Cikin ikonsa da ganin damarsa ya dawo mana da Auwalu cikin mu, Alhamdulillah Allah mun gode maka da wannan ni'imar da kayi mana ba tare da k'arfi ko dabarar mu ba" nan hayaniya ta tashi kowa yana fad'in Kalmar nuna farincikinsa game da dawowar Auwal, saida aka gama aka sake nutsuwa Alhaji yaci gaba.

"Kuma kowa nada labarin abinda ya faru dalilin da yasa Auwal ya tafi ya barmu duk da agaremu bai isa dalili akan tafiyarsa ba to shima dai ya gane bai kyauta ba ya kuma nemi afuwa akan hakan munsan wannan bazai wuce sharrin zuciya da shed'an ba, to kuma duk a lokaci d'aya Allah ya kawo mana warwara a cikin wannan lamarin ga Wanda ya zamo silar sabani tsakanin Auwal da Ameena yana ikirari da bakinsa sharri yayi ma Ameena sannan yace saka shi akayi dan haka waka a bakin mai ita tafi dad'i sai a bashi dama yayi mana bayani"

Nan fa kallo ya koma ga wannan gurgun kowa na jiran jin mai zai fad'a.

"Nidai sunana Saminu amma anfi sanina da Shago kashe aure, na samo wannan suna ne a dalilin sana'ata ta kashe aure duk yanda Aure yake muddin akazo gurina akace ana buk'atar mutuwarsa to zan kashesa muddin zan samu kud'i wannan itace Sana'a ta, na kashe aure Wanda ni kaina bansan adadin auren da na kashe ba, a haka ne waccen ta sameni tace zanyi mata aiki" ya nuna Rafia tare da koro musu bayani yadda sukayi da ita da yadda suka tsara komai har zuwa abinda ta bashi.

"Kai munafuki yaushe na tab'a ganinka ni bamma tab'a saninka a rayuwa ba, ni zakayiwa sharri" tashi tayi tana bobbotai da borin kunya, ba Wanda yace uffan sai ido da aka zuba mata, murmushi yayi "dama nasan za'ayi haka shiyasa na tanaji irin wannan ga duk Wanda nayiwa aiki" nan take ya danna wata mp sai muryanta Radau da yadda suka shirya komai.

Tass...kakeji hajia Kaltume ta wanke mata fuska da mari masu kyau "amma dai ke anyi tsinanniya, munafuka yanzu duk yanda na d'auke ki Ashe ke kurace da fuskar akuya kika nasa aka saki 'yar mutane, kikayi silar tafiyar d'ana da nake matuk'ar so, er banza Allah ya isa tsakanina dake" hajia Kaltume tace cikin kuka.

"Aa Kaltume mi a laifin Rafia bayan ke kika bata k'ofa da baki nuna k'iyayyar ki ga Ameena ba ya za'ayi Rafia ta samu hanyar yi musu wannan ta'adi ba, duk da bamu San hujjarta nayin hakan ba" Alhaji Sada yace, sanyi jikin Hajia Kaltume yayi tabbas tayi kuskure a baya na nuna tsanarta a fili ga talaka, amma tuni ta gane gaskiya dan miyagun halayen da Rafia ta b'ullo dasu na rashin tarbiya da musgunawa kowa na gidan, saidai ta riga ta makaro dan Alhaji ya fita batunta akan maganar Abdool da mahaifiyar sa baya fad'a mata komai game dasu gashi ya hana Abdool zuwa gaba d'aya.

Rafia sai raba ido take tana kyarma nan Rabi'u ya daka mata tsawa "meye dalilinki na wannan badak'alar?"

Cikin inna-inna da tsananin tsoro ta shiga gaya musu akan tana son ya auri k'anwarta ne sannan ta tsani Ameena saboda yanda Auwal ke nuna mata k'auna.... Ai bata k'ara sa bayani ba sai saukar naushi taji a baki, tare da rufeta da duka duk jikinta, sai ihu take zundumawa "Auwallu me kakeyi haka ka dawo hankalinka fa tsaketa" Alhaji yace cikin daga murya, saketa Auwal yayi tare da kama gefe yana huci "Alhaji daka barshi ya illata annoba guba, kije na sakeki saki uku kuma Allah ya isa da cutar damu da kikayi" Rabi'u yace.

"Kayimin dai2 Rabi'u" hajia Kaltume tace, hannu Rafia ta aza a ka tare da fashewa da kuka hadda ihunta dan tasan karyar ta ta gama k'arewa "dalla Malama fice mana a gida ko yanzu in karyaki anan" Sani yace yana binta da mugun kallo, dakar taja kafarta dan ba k'aramin duka tasha a hannun Auwal ba ga bakin ta daya fasa mata sai jini yake, nan fa kowa ya hau murna sun rabu da wahala dan a gidan ta addabi kowa, kowa sai fad'ar albarkacin bakinsa yakeyi, shidai Alhaji sai kallon su yakeyi, shiru ya biyo baya "Rabi'u me yasa ka yanke irin wannan hukuncin da Allah bayaso kai tsaye?"

"Kayi hak'uri Alhaji dole ce tasa dan Rafia tana cutar damu matuka" nan ya shiga zayyana musu yadda take shan kwayoyin rashin haihuwa har zuwa da tayi aka cire mata mahaifa da yanda take bin wasu mazaje, ba Wanda yayi mamaki a ciki dan sun san zata aikata abinda yafi wannan ma, nan dai aka shiga jajantawa kowa da San barka na rabuwa da Annoba, musamman Amaryar Rabi'u tafi kowa farinciki na rabuwa da sukayi da Rafia dan tana cin azaba a hannun ta.

"Kai kuma kaje Allah ya shiryeka" Alhaji Sada yace da gurgun".

"Alhaji na gane kuskure tuni, Allah bai bani bashi ba ya halakar duk k'azamar dukiyar da na Tara, kuma ya jarabceni da rashin k'afafu shi kad'ai ya isheni ishara" sannan ya gungura kekensa ya fice yana godiya, shiru ne ya ratsa kafin Alhaji yace.

"Tau inaso mu duka mu d'auki wannan al'amari a matsayin jarabawa daga Allah, Auwal kai kuma ina ka shige wannan tsawon lokaci ba tare daka waiwayemu ba, wannan yarinyar kuma wacce ce ita?" Alhaji sada ya fad'a, hankalin kowa anan ya dawo suna sauraron suji daga gareshi.

"Ameena sunan ta amma muna kiranta da meenal 'yata wacce taci sunan Ameena, bayan nabar nan direct Abuja na nufa bayan na share sati ina tunanin wace k'asa zan dosa dan na nisanta kaina da Ameena, daka k'arshe na yanke shawarar zuwa saudiya, zamana Saudiya bani aikin yi daya wuce zama a masallaci kullum ina can bacci kawai ke maidani gida, ganin guzurin hannuna ya d'auki hanyar k'arewa yasa na tuntub'i mak'ocina inaso zan fara Sana'a hakan kuwa akayi ya je dani kasuwa ya d'orani akan Sana'a, tun zuwana garin da malam Ikbal kad'ai nayi sabo wato wannan mak'ocin nawa, suna da matuk'ar kirki kullum zasu kawomin abincin safe rana dare basu gajia, sun jani a jiki sosai duk da ban tab'a gaya musu komai game dani ba, suna da 'ya d'aya wato Ahlam sannu a hankali sha kuwa ta shiga tsakanin mu, har takanzo ta gyaramin gida idan munje kasuwa, tana zuwa ta tayani hira a idan naje gidansu kullum taga tana ganina da foton Ameena da Abdool Dana Alhaji da Momy har dai ranar ta nuna tanason taji tarihina irin shakuwar mu tasa na k'asa b'oye mata labari na, Ahlam ta girgiza dajin labarina har da kukanta ta tausayamin, kullum bata da magana saita Abdool da Ameena irin k'aunar da take nunawa ga iyalina ne yasa na k'ara ganin kimar ta a zuciyata" nisawa yayi sannan yaci gaba.

" a haka shekaru suka ja har Ahlam ta kammala karatunta iyayenta suka bijiro mata da maganar Aure, haka Ahlam ta had'a Kai da fata tace idan bani ba ba zata auri kowa ba, tsananin k'aunar da iyayenta ke mata yasa suka amince da ta aureni d'in, bawai dan sunaso ba dan kowa yasan larabawa da nuna banbancin launin fata da tak'ama da nasaba, nidai bansan abinda ake ciki, sai kirana malam Ikbal yayi ya gayamin yadda sukayi da Ahlam, nan na gaya masa komai game dani kamar yadda na gayama Ahlam Ashe itama ta gaya musu jin banyi musu k'arya ba, yasa shima ya bada goyon baya, wannan shine silar aure na da Ahlam mutuncinta da kirkinta da kuma nuna damuwarta akan dukkanin al'amari na ne ya janyo mata k'auna ta, a haka muka zauna tsawon shekara 4 sannan Ahlam ta samu juna biyu, na bata dukkanin kulawa har lokacin haihuwar ta, ta haifo Ameena itace ta zabawa Meenal sunan Ameena, Meenal Nada shekara biyu ciwo ya kama Ahlam Wanda yayi sanadin rasuwarta, tun Ahlam na raye tayi tayi dani mu zo Nigeria, har Cikin raina inason zuwa saidai ina fargabar zuwa in samu labarin Ameena ta auri wani kuma inga inda muka rayu da Ameena amma yanzu babu ita, kullum kuna a raina musamman Abdool da bansan wace rayuwa yake ba, saidai na kasa zuwa, a haka naci gaba da renon Meenal shakuwa ce mai girma a tsakanina da ita, nina reneta da hannuna dan duk yada kamannin ta sukazo ta dawo inda suke k'i tayi ko kasuwa da ita nake zuwa muddin taje gidan kakanninta to tare dani ne"

"Har zuwa yanzu da Meenal keda shekaru sha shida bata yadda da kowa ba saini, ina yawan bata labaru game da gida hakan yasa tasan labaru game daku, kuma na koyar da ita Hausa tana jin Hausa saidai hausar tata kamar ta k'abila take don bataji ga kowa sai guna, a wannan lokacin ne gida ya dawo min a rayuwa kullum cikin mafarkin Abdool Nike yana kirana hakan ya tayar min da hankali naji dole sai na dawo gida hakan yasa naje ma su malam Ikbal da maganar tafiya ta sukace ba damuwa amma zanbar Meenal anan dan tana cire musu kewar tilon 'yarsu, ba musu nace na amince amma Meenal tayi fir tace kafarta kafata, haka suka hak'ura ba yadda suka iya amma sunce zasuzo daga baya" kallon iyayensa yayi "ina Neman gafararku iyayena akan barinku da nayi don Allah Ku yafemin"

"Mun yafeka Auwal kaima ka yafemin da abinda nayi maka kai da Ameena akan wani dalili nawa Mara asali da tushe, na gane kuskure na Alhaji dan Allah ka yafemin na tuba nabi Allah"

"Alhamdulillah nagode Allah daya ganar dake gaskiya, Allah zaki roka afuwa akan karan tsaye da kikayi akan dokarsa kin manta cewa shi yayi talaka da mai azziki ba tare daya nemi shawarar su akan kasancewarsu haka, sannan ki nemi yafiyar Ameena da Abdool akan hakkinsu da kika tauye Allah ya yafe mana baki d'aya" Ameen kowa ya amsa, kiran Meenal Alhaji yayi ya sanya mata albarka haka Hajia, nan yan uwa da iyayenta kowa ya shiga nuna mata so da gabatar da kansa a gareta.

"Alhaji ina labarin Ameena da Abdool?" Auwal ya tambaya.

Nan akayi zaman sabon labari, "Allah sarki Ameena ta, Abdool dina ya zama babban mutum harda iyali har haka, Baba ya kamata muje Kaduna a yau inaso inga Ameena da Abdulmajid" itama Hajia yanzu ba wad'anda takeson gani kamar su, haka Meenal tana cike da burin ganin takwarar ta da kuma tilon yayan nata, Alhaji cewa yayi su bari zuwa gobe sai suyi sammako suma sun d'an huta.

Da muradin ganin Ameenarsa da Abdool d'in sa, yayi farincikin jin Ameena bata da Aure yanzu kila rabon su sake zama ne.


***********


02:00pm

A garin Kaduna tayi musu, kasancewar Weekend ne, duk suna gidan Mami, k'ofar gidan suka tsaya, Hajia sai mamaki take yanzu Gidan Ameena ne nan lallai duk abinda ya baka tausayi wata rana sai ya baka tsoro, mota had'u suka ciko, waya Alhaji ya zaro tare da kiran Abdool, ring 2 ya d'aga yana fad'in "tsoho mai ran k'arfe yau soyayyar ta motsa ne" cike da zolaya.

Dariya Alhaji yayi "kamar kana kusa ko Likkita bokan turai, shiyasa ma gani k'ofar gida kazo kamin iso" dariya Abdool yayi shima.

"Banda zolaya fa Alhaji" ba zolaya fito ka gani".

"Saidai fa gani gidan Mami" ai tazo da sauk'i dan nima nan nake nufi ba dajin Ku ba"

"Naji dai ganin nan zuwa " kowa k'ofa ya zubawa ido don ganin fitowar Abdool da yake a hands free Alhaji saka wayar.

Auwal yafi kowa zakuwa son ganin gudan jinin nasa.

Fitowa yayi cikin tafiyar nan tasa ta mai nutsuwa, turus ya tsaya yana bin motocin dake gurin da kallon mamaki dan a zatonsa Alhaji kawai ne............















=؄?Meryerm Abdool=؄?
[10/23, 9:23 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Real Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*





```An karb'o daga Abu huraira(R.A) yace daga Manzon Allah (S.A.W) yace "duk Wanda ya yayewa wani mumini bak'in ciki?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? daga cikin bakk'an cikin duniya, Allah zai yaye masa bak'in ciki daga bak'in cikin ranar tashin Alk'iyama, Wanda ya sawwak'awa wani anan duniya, Allah zai sawwak'a masa duniya da lahira Wanda ya rufe asirin wani Allah zai rufe asirinsa duniya da lahira, Allah yana cikin taimakon bawansa muddin bawa yana taimaka wa d'an uwansa, Wanda ya kama hanyar neman ilimi, Allah sai sawwak'a masa hanyarsa zuwa aljannah, wasu mutane ba zasu taru a wani d'aki daga cikin d'akunan Allah ba, suna karanta littafin Allah suna mai bitarsa a tsakaninsu har sai ya saukar musu da nutsuwa, rahamarsa ta lullub'esu, mala'iku sun zagaye su, Allah ya kirasu cikin mutanen da ke gurin sa.```

Allah yasa mudace.

( _Arba'una hadith, rawahul Muslim_ )





d'd'd' *kuna raina at any cost, Fatyy Azland, Maman ussey, Abdool AAG, Sumee Homa, thanks for ur love and support*=??=?L?





=??? *Episode* 256--270






Bai gama mamaki ba sai ganin mutum na dosa inda yake yayi, ko da bai tab'a ganinsa a foto ba kamar da sukeyi kad'ai ta isa ta shaida masa Dadyn sa ne, bai San lokacin da murmushi ya sub'uce masa tare da fad'in "Alhamdulillah" shima Auwal murmushi yake farincikinsa bazai misaltu ba wai Abdool ne daya bari a shekara d'aya, shine ya zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login