Showing 75001 words to 78000 words out of 88300 words

Chapter 26 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1598

nan fa Ramlah ta samu bakinta sai tsiya take zuba musu don kowacce na d'auke da cikinta sai kwad'ayi suke zubawa Amal ma an kusa amarcewa.

Inna da Mami sun dage da gyaran Ramlah gyara na musamman irin na 'yan Sokoto Ard'o ma ya Aiko da sako, Abdool ko gida bayason komawa saboda gidan ba dad'i, yasan ko yace ya dawo Mami ba zata bari ba sai wani kaffa-kaffa take da Ramlah Sam bata barinsa zama gurinta.

Ranar suna anyi shagali wai barinyi shiru dai amma kuma dai kunsan ba dama Sa biyu da rago shida aka yanka, kaya kuwa kamar wani mahaukaci kowane jariri da nashi set, itama mai jego tasha kaya hadda kyautar mota k'arama irin ta mata k'irar Mercedes ash color.

Biki yayi biki can na hango 'yan *Abdulmajid fans* a gaban kasko my parrot an tattare zani ana gyaran hanji, mom zee sai k'ok'arin gyara wuta tace Aysha na zuba mai a kasko maman khady sai yankan nama ake ana aikawa baki anga banza ta fad'i, lubna ba sauk'i anata shan fanta, dear na Raheenat sai cin rengem ake ana korawa da coke su maman Nana, Aziza, zuzu, zee mai Kano, maryam cool sai hadije yawu ake anji hanji ya fara k'amshi, nace oh Abdulmajid fans kwad'ayi sun kama hanji sai aiki suke masa ba sassauta to kudai ragewa dotana kada Ku cinye gaba d'aya. Lol.

Yara sunci *Abdullah, Abdurrahman, Amatullah, Amaturrahman* Allah ya raya akan sunnah yasa mahaddata Qur'an ne.

Dangi kowa ya taka rawar gani yayi bajinta sun suna 'yan hud'u 'yan gatane gaba da baya, anyi suna lafia an watse lafia, Allah ya raya yaba mai jego lafiar shayarwa...........







*Remgem ren gemgem shinkafa da dad'i wlh tanada dad'i* =؃?







=؄?Meryerm Abdool=؄?
[10/13, 9:20 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*







*_Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa yana cewa "ba zaku shiga aljannah ba har sai kunyi imani, ba zakuyi imani ba harsai kunso junanku, in baku labarin ta yaya zakuso junanku? To Ku yad'a sallama a tsakaninku_*=?L?
*_Assalamu Alaikum warahmatullah wa barakatuhu ya ihwatih fil Islam* =?K?








=??? *Episode* 246--250






Abdool ya shiga busy saboda shirye-shiryen bud'e hospital nasa da sukeyi bai zaunu ba, wata rana ma through out day su Ramlah ba zasu ganshi ba saidai waya kawai, Mami kam ta dage da gyara 'yar tata,tuni na hau sheki fatarta tayi smooth tayi k'iba abinta, yan 4 sunyi bulbul dasu a dan Ramlah akwai kyawun Mama ga kuma sinadarai da madara da Abdool ya kawo musu wand'anda zasu k'ara musu lafia da kuzari, junior kullum yana mak'ale da Maa d'insa, Inna da Nany ne iyayen renon su Amatullah su Husna ma muddin suna gida suma suna tare dasu.

Bukin bud'e hospital aka gudanar Inda ya samu halartar mai girma governor na Kaduna State da k'ungiyar likitoci ta kaduna state misnistan lafia, asibitin ta samu karbesu gun k'usosin Gwannati, sannan ta cika duk wasu sharudda na asibiti mai zaman kanta, duba da yadda aka zuba kayan aiki na zamani wad'anda a yanzu ba'a cika samun a kowacce hospitals ba, an nashi number yabo tare da jinjina masa akan namijin k'ok'arin da yayi akan hospital d'in tare da jawabin yabo da mai girma governor yayi tare da Jan hankali up coming Dr dayin koyi da Matashin Dr Inda yace idan ana samun iri-irensu masu kishin k'asa to tabbas za'ayi nasara sosai a fannin lafia kuma za'a yak'i cututtuka da dama tun anan gida Nigeria basai an fita zuwa k'asashen wasu ba, haka dai kowa ya tofa albarkacin bakinsa tare da mik'a kambun girma ga iyayensa a matsayin su na wad'anda suka ginashi suka tallafa masa ta hanyar taimakonsa da bashi ilimi mai kyau har yakai wannan mataki, Aka kuma ja hankali iyaye akan suyi koyi da iyayen Dr Abdool su dage akan ilimin 'ya'yansu both islam and western dan shine kad'ai gatan da zakayi ma d'an ka a rayuwa saboda ilimi shine gishirin zaman duniya.

Mami dake gefe sai murmushi take tana jin dad'in ganin wannan rana da Allah ya nuna musu Abdool ya zama wani Abu a rayuwa har ana buga misali dashi wannan kad'ai ya isheta farinciki, Alhaji Sada hadda kwallarsa ta farinciki ina ma Auwal na kusa yaga wannan abin farinciki, Ramlah ma ji take kamar ta tashi sama dan farinciki tanaji tafi kowa sa'ar miji a rayuwa, ganin yan mata sai pics sukema Abdool yasa tasha kunu ta had'a rai ganin my parrot ta dage ta zak'alk'ale ita da my Aysha, Abdool kuwa idonsa na Kanta ganin yadda tasha kunu yasan labarin yasa sai jifarta da murmushi yake sannan yak'i kula kowa duk nacin Hafsi saida ta sarara masa, dan yak'i basu fuska, wow kawai 'yan matan gurin ke fad'i sunaji inama wannan young Dr mallakinsu ne.

Gurin dinner da akaje Ramlah na mak'ale Dr ko kunyar Mami bataji idonta ya rufe da kishi, sunkuyawa Abdool yayi Dai2 kunnenta "Haba baby irin wannan rikon ai sai ki kashemin kasuwa" harara ta watsa masa tare da kwab'e fuska tana d'an dukan k'irjinsa cike da tab'ara, nan fa masu camera suka shiga basu pics dan sun burge ba kad'an ba wasu sai fad'i suke "wow perfect match" tuni jikin wasu yayi sanyi ganin madarar k'auna a fili, Mami sai murmushi take tana k'ara godewa Allah, su sadee, Nihal duk ana gurin ana aikin na kwad'ayi. Lol

Taron yayi perfect anan aka bashi lasisi na tabbacin Asibitin sa ta samu k'arbuwa 100%, taro ya watse kowa na farinciki da murna, Abdulmajid fans baki kamar ya yage dan murna sun cika burgamensu da kayan mak'ulashe(oh wad'anda mutanen burinsu baza ta fad'i kawai subi takai) lol.



***************





Watan su Ramlah d'aya Abdool ya fara k'orafin su dawo, gaba Mami ta saka shi ta mishi tass tace suda komawa sai sun k'ara 2 months kuma da ta k'are wanka zasuje can kilgori suga halin da ake ciki dan baffa ne da kansa ya buk'aci haka, Ba yadda ya iya Ya hak'ura saidai idan Mami batanan yakan zagaya gurin Ramlah tayi masa 'yan dubaru dan tasan kalar mijin nata, duk iya nacin sa bata yadda anje can.....ba, kullum da rigima suke rabuwa dan idan ya aza mata daru ji take kamar ta bashi ta huta amma idan ta tuna da gargad'in Mami saita fasa, fushi yahau da ita ya daina kulata iyakarsa parlour idan yazo ya nan yake zama da yaran sa, haka yai fushin har ya gaji, lokacin ne tafiyarsu ta tashi gashi yayi dai2 da auren Amal kwanansu 3 a Sokoto suka sha biki sannan suka wuce kilgori...



*************



Tunda suka shigo cikin garin take binsa da kallo tsawon shekarun da ta d'auka bata ba a samu wani dogon canji a ciki ba kusan ma yananan yadda yake saidai abinda ba'a rasa ba, tsayuwar su k'ofar gidan ne ya k'ara tsananta bugun k'irjinta da Ard'o sukaci k'aro a k'ofar gidan, washe baki yayi yana musu sannan da isowa sannan yayi musu jagora zuwa ciki.

Gidan ma na nan yadda yake ba canji, k'ark'ashin bishiyar tsakar gidan ta hango Gwaggo Shatu tana yima wacce ke kwance jagab an lullub'e kusan rabin jikinta basa hango fuskarta, mahucin Shatu ta aje tare da tasowa tana musu sannu da zuwa fusksrta cike da tambaya dan itakam bata ganesu ba "sannu Gwaggo mun sameku lafia?" Ramlah tace, bud'e baki Shatu tayi tare da nunata da yatsa "Laure keta? Keta(kece) kika bacemin gaba dai ban ganeki ba" tace tana rungumeta "nice Gwaggo ya bayan rabuwa yasu Salmanu sun girma ko?" Tace suna k'arasawa gindin bishiyar da sauri Shatu ta d'auko sabuwar tabarma ta shimfid'a musu tare da kawo musu ruwan Randa masu sanyi "su Salmanu sun zama samari, wad'annan ne jikokin nawa?" Tace tana zama tare da k'ara gaisawa dasu Mami da inna da Nihal sai kuma nany, dake inna bata koma ba sai yanzu ta biyosu su daga nan su isa can.

Murmushi kawai Ramlah tayi, sai Mami ce ta amsa mata sannan tace "ya mai jikin ko tana ciki ne" dan Sam bata kula da ita ba.

"To alhmdllh ta samu sauk'i, ai gatanan ta samu yin bacci" tace tare da nuna musu ita, idon Ramlah ne ya sauka kan Iya Hari dake kwance kamar tsumma duk da dama can bamai jiki bace amma kam ta k'ara lalacewa ta yankwane ta tsofe sosai, nan take zuciyarta ta tsinke cikin sasarfa ta isa gareta tare da sakin kuka Mara sauti ta d'ora hannunta kan nata, rike hannun tayi gam tana fad'in "Laure ce dan Allah ku kawo min Laure mu gana"cikin muryan tsananin ciwo, cikin tausayawa tace "Iya nice...nice Laure iya" da sauri Iya Hari ta bud'e idonta tana son tashi amma ina ba dama.

Rik'e ta sosai tayi tare da gyara filo ta d'agota, still tana rik'e da hannunta gam "Laure kega yadda Allah ya hitar miki hakkinki gareni ko? Kega yadda nik koma ko?" Tace tana yaye zanin da ke rufe a jikinta, wani irin wari ne ya doki hancinta Ramlah ga k'afafun ba kyan gani duk sun kumbura ga tab'o a wasu guraren sai kuda ke bi.

Lokacin su Abdool suka shigo shida Ard'o da Hakeem " Laure banyi miki adalci ba keda uwayenki ban ba Modibbo hakkinsa ba na cutadda Asma'u sannan nabi ki da cuta kema gashi Allah ya nunamin iko nai...".

"Duniya kenan ka bita sannu ma ya kak k'are balle kayi garaje, kuma shi zakaran da Allah ya nuhwa da cara ko ana muzuru ko ana shaho sai yayi, wanga ya isheki darasi kisan duniya tafi bagaruwa iya jima" Ard'o ya fad'a hankali kwance.

"Wlh hakanan na Malam na yadda nabi Allah na kurena " Iya Hari tace tana kuka nan ta shiga basu labarin yadda ta cutar da Ramlah da iyayenta har zuwa zuwanta Inda boka da yadda ta had'u da Jauro ta k'ara sa "wlh sharrin shed'an na da son zucciya gashi sun kaini sun baro, Lanti da ni d'auka a matsayin d'iya gashi ta watsar dani bayan ada da ita mukayin komi ina ganin ita kanaso na bata tarbiya ta Ashe na dab'a ma cikina wuk'a na ban Sani ba gashi taje taba d'iyanta irin tarbiyar da nibbata, nidai kaico dani nayi hasara, dan Allah Laure ki taimaka ki yafemin ko zan samu sassauci daga ubangiji na" ta fad'a cikin matsanancin kuka mai ban tausayi.

Ko kai waye kaga Hari a wannan halin dole ka tausaya mata, duk ta k'ashe musu jiki, cikin sheshekar kuka Ramlah tace "ban tab'a rikeki a raina ba Iya, na yafemiki tuni, kullum babbar burina Allah yasa ki gane gaskiya, nagode wa Allah daya sa kika dawo hanya Allah ya yafe mana baki d'aya".

Cikin kuka ta shiga Neman gafarsu Inna duk sukace sun yafe sannan ta juya ga Ard'o " Hari kinyi abubuwa da dama saidai nikam ban tab'a rikeki a raina ba, kullum fatana ki gane gaskiya ko a haka aka tsaya nasan kega yadda duniya tace koda wannan azabar dake tare dake aka barki ga hasarar dukiya da kikayi Allah yasa wannan turbar shiriyarki"..

Sun jima suna jimamin abun, Abdool yana girmama abin wato ita duniya muddin kana cikinta zaka abubuwan mamaki, Al'ajabi, zalinci, cutarwa, cin amana da abun tausayi dana dariya, amma muddin bakabi hanyar koyar war Manzo S.A.W sai kayi dana sani a rayuwa, (Allah ka bamu ikon bin dai2 da aikata dai2).

Duba Hari yayi anan ya gane kafafun sun rub'e dole saidai a yankesu, nan suka k'ara shiga tashin Hankali, ana haka saiga Lanti ta shigo gidan tana ihu da kururuwa ta zube anan tana fad'a musu ga gawar Jauro nan da hinde an kawo wai ashe suna can tare birni suna bushasha da kud'in iya Hari da wad'anda Hinde ke karuwanci tana samowa shine sun samu matsala sun fito suna bala'i har bakin titi babbar mota ta kwashesu ba Wanda ya shura a cikin su.

Shine mijinta ya dankara mata kashi ya sakota saki uku yana fad'in ta cuceshi duk ita ta lalata masa d'iya, bud'ar bakin Ard'o sai cewa yayi "kega shuke- shuken ki ko Hari sai girba kikai da hannunki" fashe tayi da wani kuka mai cike da nadama, itama Lanti kukan take tana nadamar biyewa mahaifiyar tata musamman da taga yadda Allah yayi da Ramlah sai rok'on gafararta suke, tace ita bata rik'e kowa a rai ba.

Delu k'awar Ramlah tanajin labarin zuwan Ramlah tayi ma gidan Ard'o tsinke sai tayi da gaske sannan ta gane aminiyar tata "Laure keta kid dawo baturiya haka, ai in bisa hanya munka had'u aradu ban ganeki" delu ta fad'a tana zare ido.

"Kai Delu har yanzu kina nan baki canza ba ya bayan rabuwa" Nan suka shiga gaisawa da firar yaushe rabo, tana ta zuba mata godiya dan duk zuwan da Ard'o zaiyi sai bada tsaraba an kawo mata.

Anan suka kwana washe gari suka wuce Argungu Abdool yace su zama cikin shiri dan tare zasu koma ayima iya Hari Aiki dan kada k'afar ta janyo wata Marsala.......













=؄?Meryerm Abdool=؄?
[10/20, 4:55 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Real Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*




```An karb'o daga Baban Abdullah, Nu'umanu d'an Bashir (R.D) yace "naji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa " hak'ik'a halal a bayyane take haka ma haram a bayyane take, saidai a tsakaninsu akwai wani al'amari mai rikitarwa Wanda kad'an daga cikin mutane suka sanshi, duk wanda ya kiyaye shubuha(rikitaccen al'amarin da ke tsakanin halal da Haram) hak'ik'a ya kiyaye addininsa da mutuncinsa, duk Wanda ya fad'a a shubuha hak'ik'a ya fad'a a haram, kamar makiyayi da yake ciwo a iyaka ya kusa ya ketare iyakarsa, Ku saurara! Kowane mai mulki yana da iyakarsa, Ku saurara! Iyakar Allah shine ababen da ya haramta, Ku saurara! A cikin jiki akwai wata tsoka idan ta gyaru dukkanin jiki ya gyaru, idan ta b'aci dukkanin jiki ya b'aci, Ku saurara! Itace ``` *zuciya*

_Bukhari da Muslim suka ruwaito shi(arba'una hadith)_


*ya Allah ka azurtamu da zuciyar musulunci* =?O?








=??? *Episode* 251-255





Ziyara sukayi sosai a Argungu, gidan k'awayen Mami dana Asma'u, b'angaren Inna duk sunje, da sukaje gidan Firdausi suka had'u da Ameena sai hirar tuna baya suke, gashi yau sune iyaye hadda jikoki rayuwa kenan, yau da gobe ta wuce wasa, kullum ganin Firdausi na tunawa Ameena da Auwal, gashi shiru har yanzu ba labari ko a raye ko a mace allahu a'alam, sunje har Besse daga nan suke wuce mungadi inda Sakina, tayi farincikin ganin su sosai itama ta tara nata iyali hadda jikoki, nan suka shiga tuna baya rayuwar C'O'E barkwancin Yusuf da irin yadda yake assisting nasu, ita tasan tayi rashi Mara adadi ta rasa Auwal a karon farko tazo ta rasa Asma'u da mijinta, sai uwa uba jigon rayuwar ta Yusuf yanzu kam mutuwar iyayenta da 'ya'yanta kad'ai ne zatace batasan d'acinsa ba amma ai taga mutuwa mai shiga rai (Allah yayima dukkanin musulmi rahama ya kyautata tamu bayan tasu)


Sunje birnin lafia gurin dangin Baba, cike da kayan tsaraba kamar yadda suka saba, sai kunya da nadamar abinda sukayiwa Abubakar sukeyi dan sun san kaf dangin yanzu da bazar Abubakar suke taka wa, shi d'in da suka wulakanta gashi ya zame musu haske a family, ya zamo zakaran gwajin dafi, shiyasa ba'a yiwa d'a da dukiya k'eta dan bakasan Wanda zai amfana dashi ba, d'ana kowane.

Tuni su Inna sun tare sabon gidansu dake Shagari Quarters, ganin zamani ne irin mai kyau d'in nan Sosai fa, Wanda Ameena, Asma'u, Mansur suka had'u suka Gina, abinda yasa nasaka Asma'u saboda gadonta hadda shi aka hada akayi ginin da sunan ta, Mansur ma yanzu harka ta bud'e dan ya samu aiki a Navy, so yanzu familyn Abubakar sunfi k'arfin a kirasu talakawa, hakan baisa musu girman kai ko k'yamatar talaka ba face wata hanya ta taimako data bud'e musu dan sun dage gurin taimaka yan uwa da gajiyayyu(abinda ya yakama ta ko wane mai hali yayi kenan ba gina manyan gidaje a koma Abuja a lafe ba, dan sadaka haske ce gobe k'iyama, Allah ka wada tamu da halal ka bamu ikon ciyar dashi ga bayinka dominka ya Allah).




************





Su iya Hari an isa Kaduna cikin yardar Allah, akayi mata aiki, dan Dr Abdool yana da k'wararrun likitoci da suka shafi kowanne b'angare ga ingantattun kayan aiki, cikin nasara aka yanke k'afafun tare da yi mata na roba, aikin da ya d'aukesu sati d'aya, anyi aiki successfully, Iya Hari sai kuka take tana nadama abinda ta shuka a rayuwar ta ga Ramlah data wulakanta ta d'oketa a banza ta zamo silar samun lafiyar ta duk da tasamu ciwon ne a gurin cutar da ita amma ta yafe mata har da kuma taimaka mata, lallai d'an hakin da ka rena shike tsole naka ido, kuma hak'uri jigon rayuwa ne, gashi Ramlah tayi hak'uri da cutarwar Iya Hari a gareta gashi Allah ya d'aukaka ya bata komai da ake nema a rayuwa saidai godiya da hamdala ga ubangiji kawai da Neman gafararsa.

Duk da yanayin da suka shigo garin na tsananin ciwon iya Hari hakan bai hana su bawa idanun su hakkinsa ba lallai garin dad'i na nesa haka kawai su Shatu ke fad'i a ransu basu k'ara tsurewa da lamarin ba saida suka isa gidan Mami k'amshin nan daddad'a da furannin ke fitarwa da iskar ni'ima dake gidan as usual, nan fa a shiga bawa ido abinci, suna girmama Allah, ashe Laure tana cikin aljannar duniya, da aka kawo musu better sukaci nan santi ya tashi Anji girki.

Da sukaje asibiti nan ma k'auyenci tsabage suka baje abinsu wai asibiti kaman gidan wani sarki ba doyi ba komai sai k'amshi da sanyin A.C dake kad'asu a haka sukata baje gidadan cinsu har akayi aikin aka kammala, bayan ta warware sosai aka shiga dasu zaga gari kusan tashi zaucewa sukayi hadda su Iya Hari sai wasar baki ake kamar gonar auduga, banki, hanci,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login