Showing 12001 words to 15000 words out of 88300 words

Chapter 5 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1604

ya kiyayi had'uwarmu, bamai kyauta ba aha" sannan ya fita yana huci kamar zaki.

Laure dake gefe tunda ya shigo gidan batace uffan ba, hasalima ko inda yake bata kalla ba saboda tsabar takaici, yanzu idan ba rashin tunani ba taya za'ace gardi kamar Jauro ya ringa shigowa mutane gida kamar gidansu, siririn tsaki taja, Wanda yayi dai-dai da maganar Iya Hari.

"To isasshiya, tsigaggga, sai kitahi ki bashi hak'uri, ke wani lahe kamar d'iyar arziki, shegiya me bak'ar aniya."

Itakam bataga dalilin bashi hak'uri ba, koda kuwa an bada ita gareshi balle ba'a bayar ba...."kin tashi kin tafi kosai nayi mid'imid'i dake anan niya" iya Hari ta katse mata tunani aiko tana shirin d'aukar muciya, aiko a guje tayi soro gidan ba shiri.

Yana tsaye yana jiran fitowarta, dama yasan zata fiton dole, had'e girar sama da k'asa tayi, murmushi yayi yace "haba gimbiyata mi'a na huskar shanu, sakin ran mana".

Harara ta balla mai " haba Jauro missa zaka yimin haka? kasan shi waye gareni?"

"To meye shidin bayan masoyinki".

Dariyar takaici tayi dama hakan ya zamo gaskiya da taji dad'i " haka ar tunanin ka dama? Mizaiyi dani 'yar k'auye? Kabar wanga tunani ma, iyaka dashi mutunci sai kara2 da yake koyamin".

Haka dai ya tafi bawai dan ya yarda ba, sai dai baison ranta ya b'aci, shiyasa ya yadda ya tafi, tare da shan zasu had'u wata rana.



**************************



Zaune Suke kamar kullum bakin rafi ga littafi da Biro gefensu dan yanzu har sun fara koyon, sai kuma k'awa'idi da ka'ida na musulunci, dan har nan Suke tab'awa, bayan ya gama koyamatasu, ta maimaita sannan yace.

"Gud gul, yanzu sai mu koma karatunmu na wancen satin ina fatar kin hadda CE".

"Eh mana, Bari ma kaji" ta fad'a tare da mik'a mishi littafin, tiryen-tiryen ta kawo su ba gyara.

Jinjina yayi mata da hannun tare da tafa mata, yana jinjina saurin ganewa irin nata, da an gayamata abu ta haddace irin su ne gifted by nature, amma anaso a kashe mata dama ga banza.

"Aboki my glass?"

Saida yayi dariya saboda sunan da take kiransa dashi "um Ramlah luv, ya akayi".

" kacce love na nuhin soyayya ko?"

Cikin mamaki yace "eh meya faru?"

"To naji kana kemin Ramlah luv, yana nufin Ramlah soyayya kenan, ma'anar sunana soyayya kenan?"

Saida yayi Jim yama rasa me zaice mata gashi ta kifeshi da ido "Aa nadai had'a sunan naki da Kalmar soyayya, kinga kenan ke soyayyar kowa ce saboda kinada ganewa sosai" ya k'arashe tare da yi mata alaman wasa, saboda ta shanshance da zancen.

Aiko dariya tahau nan sukaci gaba da karatunsu cikin nishadi(kara2 yafi jiga idan ana had'awa da wasa)lol.

"Kan ubancen yau za'ayi kazar uban nan niya" sukaji an fad'a daga sama, a tare suka juya dan ganin wane hatsabibin ne.

Kallon wannan fa Abdool ya bishi dashi, Jauro kuwa sandar da ke wuyansa ya d'aga da niyyan kai mishi bugu.

Da hannu d'aya Abdool ya rik'eta tamau yadda ko motsata Jauro bazai iya yi ba, yanzu kam da kallon kama renani yake binsa, Laure ce ta mik'e a fusace cikin fulatanci take magana.

"Haba Jauro Wanga wace irin haukata? Na hidi maka mia tsakanina dashi, wai shin imma masoyina ne, mi zakayi? Hala an baka nina?"

Ba tare daya bata ansa ba, ya dawo da kallon sa ga Abdool.

Cikin muryan 'yan tasha, yana juye baki yake magana "Hai kad'o ina gargad'inka, daga hita hanyar Laure, da duk Ahalin ard'o idan ba haka ba Hmmm".

"Kai kuma waye kai? Kuma meka isa kayimin" Abdool ya fad'a cikin gadara da binsa da kallon renin hankali.

"au bata hwadama ni'a wa ba, toni zan fad'a maka, nina mijinda zata Aura, nina uban d'iyanta, kuma kiyayi had'uwarmu ta gaba" yana gama fad'i yaja sandarsa ya kama gabansa.

Abdool dake tsaye kamar Wanda aka dasa, haka yaji zancen kamar saukar aradu, cikin jarumta da dakewa ya tattaro sauran k'arfin halinsa, ya maida kallonsa ga Laure dake tsaye tana hawaye.

Idan ka kallesa zaka tsinkayo kishi da bacin rai kwance a fuskarsa, amma da yake akwai k'arancin shekaru gareta bata fahimci komai ba.

"Abinda ya fad'a gaske ne?" Tayi ya tambayeta, girgiza kai tayi "ba haka bane hasalima dagashi sai Iya Hari suke zancen, Baffa baice komai ba...." Nan tayi mishi bayani sosai, ya d'an samu nutsuwa amma kuma jin hali irin na Jauro yasa hankalinsa yad'an tashi, dan yana tsaoron yaje yayi mata illah, amma tunda yana sonta yasan kila ba zaiyi mata komai ba.

Shikam ko batason Laure bazaiso a aura mata wannan shashashan ba, balle kuma son nata yake, ganin hankalinta bai kwanta yasa yace suje kawai an k'are kara2.

Sallama yayi Ard'o, bayan sun dan tattauna, sannan ya gaya mishi zaije gida Hutu, fatar Alkhairi yayi mishi "don Allah in kaje ka gaidasu sosai, inji ka gayama mutuniyar taka?"

"Aa Baba".

"Ato bari tazo kuyi sallama, Ramlatuna karatu zai tsaya kenan." Ya fad'a yana murmushi tare da shigewa ciki.

Da zabi da k'wayak'wayi ta fito wai inji Baffa "aboki mai glass hala ina zakana nijji Baffa yace wai ka kai Musu?".

"Gurin Mamana zanje Ramlah luv".

"La ina Maman taka take hala?"

"Can da nisa kinsan Kaduna?"

Girgiza kai tayi cikin mamaki "dama ba Yabo an garinku ba?"

"Eh".

"To nima zan biyoka inda mamar ka".

Smiling yayi " kina son zuwa inda Mamana?"

Da sauri ta girgiza mishi kai alaman eh.

"To inshaa Allah, zanje dake, idan zan koma kinji".

" Aa nidai katahi dani yanzu" ta fad'a cikin shagwaba.

"Oh friend yaushe kika iya rigima, kiyi hak'uri kinji zanje dake next time" haka ya lallab'ata har saida ta hak'uri sannan ya tafi, bye ta ringa yi mishi har saida ya bacema ganinta sannan ta share hawayen da suka zubo mata, tabbas zatayi missing d'insa.

Tafe yake yana tuk'i amma yana tuno maganganun Jauro, "Nina mijinta, nima uban d'iyanta".

Da k'arfi ya daki sitiyari " no it can't happen ever".................













=؄?Meryerm Abdool=؄?
[7/22, 6:46 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?


```Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:-```

_Hak'ik'a Allah mad'aukakin sarki baya duba zuwa ga suffofin jikinku ko dukiyoyinku, saidai yana duba zuwa ga zukatanku da ayukanku._


*kyawu da dukiya, ba zasu taba zama guarantee na shiga aljannah, gareni, gareki, garesu ba, tsarkakakkiyar zuciya da kyawun hali, shine kad'ai zai kwacemu a gun Allah ranar gobe k'iyama, nidake dasu mu guji rud'in da sharrin kyawun halitta dana dukiya, mu tsarkake zukatanmu, muyi k'ok'ari mu gyara tsakaninmu da mahaliccinmu domin goben mu, duniya labari ce, komin dad'ewa zamu barta, Allah yasa mudace da rahamarsa=?O?







=??? *Episode* 61--65



A yau ne su Zainab suka kammala attachment d'insu, k'warya-k'waryar walima mai gari yasa aka had'a musu tare da taimakon likitocin asibitin, sun yaba musu tare da jinjina musu akan k'ok'arin da sukayi, tare dayi musu fatar Alkhairi.

A tare suka wuce Sokoto da Abdool, dan shima ya d'auki Hutu gobe sai wuce Kaduna, bayan ya sauketa fitowa yayi ya fito mata da kayanta dake booth, ita kuma gida ta shiga ta kira gate man da driver domin su shigo mata da kayan ciki, ta samu har ya shiga motar yana shirin tafiya, gurin k'ofar ta sunkuya cikin marairaicewa.

"Sir pls ka tsaya Ku gaisa da Momyna har nayi mata magana".

" Oh! No Zainab ki bari next time...." Katsesa tayi.

"Pls Sir kai kayi alk'awari fa" ba yanda zaiyi, haka ya fito dole, a parlour Dadynta ta saukeshi, ga kayan motsa baki an shirya kamar hauka, ciki ta shiga ta kira Mamanta, cikin girmamawa suka gaisa, yau dai taga Dr Abdulmajeed d'inda take shan labarinsa gurin Zainab, itama ta yaba sosai da yaron, godiya tayi mai da irin kulawar da yake bawa 'yarta, tare dayi musu fatar Alkhairi, shikam kunya yaji kardai Maman tasan Zainab na sonsa.

Bayan fitar haka k'anninta sukayi ta zuwa suna suna gaishesa kudi ya basu shima dak'ar suka ansa sunayi masa godiya ya yaba da tarbiyar yaran "Sir kaci wani Abu mana" ruwa kawai yasa yace zai wuce, ba taso hakan ba amma ba yanda zatayi, dan ita idan son ranta ne, su tabbata haka har abada, har mota ta rakashi.

Wani ring ta Ciro a yatsarta ta bashi "wannan d'in na meye Zainab"?

Murmushi tayi tasan yasan tana sonsa, saidai koda sonsa zaiyi ajalinta ba zata tab'a fad'a masa ba " Sir ka rik'eshi a gunka, idan ka kalla ka tuna dani, pls Sir kada manta dani".

Sosai ta bashi tausayi, ansa yayi yasa a k'aramin yatsarsa, tare dayi mata murmushi "bazan tab'a mantaki ba Zainab ki saka wannan a ranki".

Taji dad'i har k'ashinta koda ba har ransa ya fad'i zancen ba, itakam ya faranta mata, shikam yayi hakane kawai dan ya kwantar mata da hankali.

Saida ta daina hango motarsa sannan ta juya gida cikin farinciki harda tsallenta na murna (hohoho! So manya).




??????????????????????



*Washe gari*



8:00am sukayi sallama da mutan Sokoto suka d'auki hanyar Kaduna garin gwanma, wannan k'aron Hakeem ne yaja motar sai sharara gudu yake, yayin da Abdool ya kebin k'ira'ar da ke tashi a cikin suratul Maryam, idonsa a lumshe.

12:00pm suka isa, gidansu Abdool suka sauka, sun samu Maamii ta tarbesu da tsararran girkinta ko office bata fita ba saboda d'okin dawowar Son d'inta ita Kanta tasan tayi missing d'insa sosai, su Abj ma sai murna dawowar Yaya Abdool Suke, suna nanik'e dashi suna mishi surutu, saida sukayi dam, sukayi fresh up, sannan Hakeem yayi musu sallama, da motar Abdool ya wuce gida, idan yaje ya dawo da ita.....

Hutun one month sukayi sannan sukayi shirin komawa, a wata d'ayan ba k'aramin dad'i hutun yayi ma Abdool ba duk kuwa da tunanin Ramlah na mak'ale a zuciyarsa, sukanyi waya da Zainab time to time, sai yaji inama da Ramlah ne, sai yanzu yakejin haushin rashin barma Ardo waya da baiyi ba, Aida sun rik'a gaisawa da sahibarsa.

Saura kwana uku su koma suna zaune da Maamii suna hira dan a duniya bashida abokiyar hira da shawara kamar ita, har suka gangaro kan hirar Ramlah.

"Yawwa maganar yarinyar nan da muka fara".

"To ai banji daga gareka bane Son, tunda ka dawo bakace komai ba".

Shafa Kansa yayi " Eh wlh Maamii kamar yadda na gayamiki, yarinyar na cikin k'unci, ba K'aramin wahala takesha gun Kakarta ba, gashi shi kakan nata bamai magana bane, wani abin tausayin ma very young inaga iyakarta in tayi Nihal" ya k'ara she cikin pity face.

Itama tausayi kwance a fuskarta tace "toya kake ganin zamu iya taimaka mata ne?"

"Eh ni a tunani na in nemi kakanta ya bani ita na kawo ta nan gurin ki, sai a sakata makaranta in fact dai ta dawo hannun mu sai dai takai musu ziyara amma me kika gani".

"Eh to Zamanta anan d'in ba matsala a ciki amma kana ganin iyayenta zasu baka ita haka nan daga had'uwar asibiti?"

D'an jim yayi shima dan gaskiya maganar abar dubawa ce "hakane Maamii amma zan gwada na gani idan zai yuyu".

"Ina ne garinsu naji kace ba anan Yabon bane?"

"Eh nan kusa dasu ne wani k'auye Kilgori".

"Kilgori" ta maimaita haka taji kamar ta tab'a jin sunan garin saidai ta manta ina taji, sharewa tayi nan dai sukaci gaba da tattaunawa akan lamarin..

Tsaraba sosai yayi mata na suturu dogayen riguna da d'inkuna hijabai hadda takalma da kayan rubuta da kara2 hadda Zainab saida yayi ma tsaraba dasu Ardo su Alhaji, kai har mutanen Argungu anyi ma, Maamii ma ta bada nata.

Ranar da suka dawo bayan ya huta ya bawa su alhaji tsarabarsu, a ranar ya wuce Yabo, zainab ma a tsaitsaye yaje, danko ciki bai shiga ba, mutan Yabo sunyi farincikin dawowar dan ba k'aramin k'ok'ari yake a asibitin ba, mutum zaizo bako asi ya dubasa kuma ya siyamai magani, shiyasa sukejin dad'in sa, suma Suke kawo masa kaya irin nasu na k'auye, nono, kwai, har kaji da zabi.

Da sassafe yaje kilgori, Laure tafi kowa murnar dawowarsa, sai murmushi take, ganin tayi ya kara kyau da gayu, hadda cewa "iyye d'an binni d'an gayu dai" dariya ma ta bashi cikin ranshi yace "Ramlah kuruciya ho".

Sunyi murna da godiya da tsarabar da yayi musu, yaji dad'in yadda suka yaba, bayan ya tafi Iya Hari, kwace kayan tayi ta cirema Lanti da Shatu kala d'aya 2 hadda hijab, wai ai wannan salon munafurci ne menayi mata kaya kaman ya ganta a tsumma, wannan kayan kamar na Aure, imma sonta yake yayi k'arya dan bazata bashi ba( ni kuma nace tunda ke zaki bada ita ba).

Laure kam a ranta tace mi hikai da 'yar k'auye duk matan bunni.

Cikin kala ukun da suka rage ta d'auki d'aya ta kaima aminiyarta Delu, sai murna take da sanya Albarka.

"Nidai Laure anya d'an bunnin nan ba sonki yake ba?"

Murmushi k'arfin hali tayi tace "banda ke da abinki Delu mi yakai Dani, ai wutsiyar Rak'umi, tayima k'asa nisa".

" Hmmm abokiyata ai ba daganan take".

"Kega bar wagga zance, d'auko wata" murmushi kawai tayi sannan suka canja hira.

B'angaren Jauro kuwa ya lashi takobin sai yaga baya ga Abdool muddin yaci gaba da shige hanci...............



( _tofa gamu gani, wai ansa munafiki bikon aure_=?? )









=؄? Meryerm Abdool=؄?
[7/23, 7:02 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?






=??? *Episode* 66--70





*life goes on....*



Zuwa yanzu Laure, ta fahimci abubuwa da dama game da karatun da sukeyi, both Islam and western, har rubuta ta iya, bak'ak'e da wasulla tana banbance su, har hadda izo biyu tayi a gunsa, a tak'aice ba k'aramar rawa Abdool ya taka a gun Ramlah ba, wani sa'in har Delu yake had'awa idan taje gurinsu, dan yanzu anan inuwar gidansu suke zama, da yake Laure ta gayama Ardo abinda Jauro yayi, shiyasa yace su rik'a zama nan, dan yasan kad'an a cikin aikin mahaukacin ya kwaso shegu irinsa suje suyi mashi illah.

Shikam Abdool baiso hakan ba, yaso su k'ara had'uwa da Jauro danya banbance masa aya da tsakuwa, a bangaren Jauro kuwa zuwanshi biyu bai samesu ba anan ba tare da rundunarsa kamar yadda Ardo ya tsammata, yana ganin basu nan yayi wani ihu irin na 'yan iska.

"Aradun Allah ya tsorata, saini Jauro mai sa maza su sheka da gudu, dan banza yana tsoron uwarshi ta haihi wani ba shiba" haka yayi ta cika baki 'yan korensa naci na k'ara fashe mishi kai.....

Yauma bayan sun gama kara2 zai wuce saiga Laure da leda waiya kaima Aunty Zainab, murmushi yayi tare da rik'e baki "ayya Ramlah luv baki d'oran aikin da yafi k'arfina ba yau kuwa?"

K'walalo ido waje tayi "Aboki mai glass kaima kana kyuya irin ta yara ashe?"

Dariya ta bashi yadda tayi maganar "Waya gayamiki kyuya ce, Zainab d'in ce batanan ai".

" to ina taje?"

"Tana Sokoto gidansu".

"Laa itama ba Yabo take ba kamar kaiya?"

"Um itama Bautar k'asa tazo anan kamar ni, kuma ta k'are nata tun tuni".

"Amma shina baka hwadamin ba, kuma in nicce INA gaisheta saika ke zataji" ta fad'a tana mishi kallon tuhuma.

"Oh my gosh! Mantawa nayi, amma fa ina gayamata gaisuwarki".

"A ina?"

"Ta waya mana, ko in kira maki itane?"

Washe baki tayi "eh inaso kirata".

Wayarsa ya Ciro ya danna mata Kira, ring 2 ta d'auka, bayan sun gaisa ya had'ata da Laure sannan yaje inda Ardo dake zaune yana kallon rigimarsu yana murmushi jin dad'i.

" Docta har zaka tahiya".

"Eh babba amma da magana nazo" gyara zama Ardo yayi dan yaji me yazo dashi "ince dai lahiya ko?"

"Eh lafiya lau dama akan maganar Ramlah ne nazo neman alfarma" nan dai Abdool ya kora mishi jawabinsa nason bashi ita ya tafi da ita idan ya tashi tafiya, dan duka 2week suka rage mishi.

Jim Ardo yayi yana nazari can yace "Bawai nak'i bana yaro, kuma ba ban amince maka naba, saidai hanzari ba gudu ba, kasan yanzu duniya mutum aka ciyyo ba dabba ba, kuma yana zama abin zagi gareni da ita Kanta Ramlah, kasan Abu ga k'aramin K'auye kowa da yadda zai hwassara zancen ga" tunda ya fara bayani Abdool ya k'asa kunne yana saurarensa, sai zufa ke keto mishi, yasan duk abinda ya fad'a gaskiya ne, to amma shi yanzu ya zaiyi da son Ramlah? Kar yaje yana can gida yana jiran ta girma yazo ya aureta yaji labarin an ba wani ita...Ardo ne ya katsesa "kayi shiru d'an ga da hwatar dai ba ranka ne ya b'aci ba".

Murmushin yak'e ya k'irk'iro "Aa Baba ko d'aya ai abinda ka fad'a gaskiya ne, amma kana ganin babu mafita?" danshi kanshi gabadaya ya k'ulle.

"Mahitar d'aya CE" bai San lokacin da yayi sanyayyen murmushi ba "Baba meye mafitar" cikin zakuwar son yaji.

"Aure! Idan har kana sonta ni zan baka Aurenta, saboda ka kwanta a raina" Ardo ya fad'i hakanne, saboda ya fahimci yana sonta.

Abdool kuwa k'irjinshi ne yayi mummunan fad'uwa, kamar saukar aradu yaji zancen, cikin rud'u ya kalli Ard'o duk da ba wacce yakeso kamarta, amma bai tab'a tunanin abin zai sama haka, shikam gani yake tayi k'ank'anta da Aure yanzu, bayan haka shi kanshi bai kawo yin Aurensa yanzu ba duk da yasan yana buk'atar auren.....baffa ne ya katsa masa tunani.

"Abdulmajeed kodai baka sonta na" karo na farko daya tab'a kiransa da sunansa.

"Aa Baba wlh ina sonta, Inadai ganin kamar tayi k'ank'anta da Aure ne" murmushi irin na manya Ardo yayi.

"Ina ai takai mataki, indai kana sonta kada kayi tunanin komi, katahi ka shawarci magabatanka, kace 'yan uwanka duk nan Suke ko?"

"Eh"

"To ka tahi kayi shawara dasu ba abin tashin hankali bana, sadaki kawai nika buk'ata ko nan da sati guda kazo a d'aura muku Aure".

"Inshaa Allah Baba, zanyi magana dasu zakaji yadda mukayi dasu" sannan yayi mishi Sallama.

Laure da batasan wace wainar ake toyawa ba, bayan sun gama waya da Zainab, ganin suna magana, yasa taja gefe kan dakali tana duba littafanta, wayarsa kadai ya ansa yayi mata sallama, ganin shi kamar baya cikin yanayin dad'i, yasa yaja jinin jikinta, ba surutu da salo yau, itama haka ta shige gida jiki a sabule....

Bayan gida kwantawa yayi kan kujera yana tunanin to ta inama zai fara? Daga k'arshe kawai yayi deciding d'in ya kira Maaminsa.

Bayan sun gaisa ya kora mata bayanin yadda sukayi da Ardo daga farko har k'arshe.

"Abdulmajeed" jin ta kira sunashi complete yasa k'irjinsa bugawa kaddai Maamii tace bata amince ba....katsesa tayi.

"Ka tabbatar kana sonta?"

"Eh Maamii" ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login