Showing 39001 words to 42000 words out of 88300 words

Chapter 14 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1610

iri d'aya haka yanayin jikinsu saidai ita tafi Asma'u tsayi tun yanzu da take yarinya kuwa.

Itama tana ganinsu saida k'irjinta ya harba, ciki suka shiga gaba d'aya.

"Malam Abubakar ga Ramlah nan" kallon yayi tare da cewa "zonan 'yata" ba musu taje ta tsugunna a gabanshi Kanta k'asa.

"Ba shakka wannan 'yar Asma'u nah ce, wannan jinina ce"cikin firgici ta d'ago ta kalleshi jin ya ambaci sunan umminta, saidai me kama taga yanayi da Umminta duk da foto kawai ta Santa amma tabbas suna kuma ga abinda taji yana fad'i.

Kallon tambaya tabi Ard'o dashi " tabbas Ramlatuna duk Wanda ya dogara ga Allah to zai Isar masa, kuma akai hak'uri akan tabbas zai wuce akai ga nasara, lokacin da muke tunanin da yanke tsammanin ganin dangin mahaifiyarki sai gasu Allah ya kawo mana har gida".

Sannan yaci gaba, "kinga ikon Allah ko, wannan shine kakanki mahifin Asma'u" ya nuna Malam Abubakar, "wannan kawun kine, k'anin Asma'u" ya nuna Mansur, "wad'annan dangin mahaifin Abdoolmajeed ne" ya nuna su Alhaji.

"Kuma wani abin jin dad'i Abdoolmajeed yayanki ne na jini Ramlatuna d'an Innarki Ameena ne" hawaye kawai ke fita daga idonta tsabar farinciki tama k'asa magana......


***************


Tunda ya d'auko ta take tambayan sa ya gayamata menene hak'uri kawai yake bata tare da cewa ta kwantar da hankalin ta Alkhairi ne, kuma yanzu zata gani, hakan tasa taja bakinta tayi shiru taga inda zai kaita, daidai k'ofar shagon yayi parking tun kafin ya kashe motar ta fito.

Cikin shagon tasa Kanta saboda yadda taji k'irjinta na bugawa, bayan kawai take kallo tana tsugunne gaban Babanta ta bata baya, Sam bata kula da wad'anda ke Cikin shagon ba, Kanta tayi gadan gadan.

"Asma'u nah!"......










=؄?Meryerm Abdool=؄?
[8/18, 5:45 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



_A sanadin *HAD'UWATA DAKE* nayi tunanin *WATAN WATA RANA* ni *ABDULMAJID* zan ciri tuta, saidai ina tsoron na shiga musiba kamar yadda *A DALILIN PRE-WEEDING PICS* wasu suka shiga matsala (my next novel inshaa Allah)_


*ina kike k'awata ta kaina, 'yar mutan Niger Raheenat mohmodou, Allah ya barmu tare ya kuma raya mana Nana khady=??*


_Momyn zee, Aysha D na fahimci kuna k'aunar sakwatanci to kuyi cooling zan koya muku=??, wallah kuna k'aunar Abdulmajeed nima ina yinku=??_






=??? *Episode* 141--145





Kallon kallo suka shiga yiwa juna cikin mamaki, "lallai Allah mai girma na, tabbas badan nasan Ummina mutuwa tayi ba, ba Wanda ya isa yace wannan matar ba itace ba wanga irin kama ta b'aci" Ramlah take fad'a a zuciyarta.

Itama Ameena fad'i take a ranta" wannan ba Asma'u bane, amma behaviors d'in Asma'u kaf irin nata amma basa kama wacece wannan" Baba ne ya bata ansa kamar yasan me take sak'awa "Ameena 'yarki ta, d'iyar Asma'u ce, jininta ce".

Jan Ramlah tayi zuwa gaban Baba " Baba ina Asma'u nah idan wannan 'yarta ce?"

K'wallar da ta taru idonsa ce ta zubo, kafin tace wani Abu Ard'o yace " 'yata Ameena saidai mu d'auki hak'uri" muryan sace ta ganar da ita da mutane a gurin "Kamar ya Baba?" Ta tambaya cikin son jin meke faruwa.

Nan fa labari ya dawo sabo, koda aka gama gayamata hawaye sun gama wanke mata fuska, "Allah sarki Asma'u ashe ba rabon mu sake had'uwa Allah ya had'a fuskokin mu a Aljannah don rahamarsa" Ameen suka ansa daga ta shiga gaida iyaye dake gurin sannan su Hakeem suka gaida ita.

"Zo nan 'yata Ramlah zo kiji domin uwa wanda kika rasa, daga yau baki ba maraicin uwa da yardar Allah" tare da ware mata hannayenta, cikin nutsuwa taje gareta tare dayin lup a jikinta wata sansanyar ni'ima na ratsata wacce bata tab'a tsinta a Cikin rayuwarta ba, lallai uwa rahama ce, dangin uwa ma rahama ne (duk Wanda yayi nasarar rayuwa da uwarsa ya godewa Allah)

Duk Wanda ke Cikin shagon sunyi matuk'ar bashi tausayi musamman yadda Ramlah ke sauke heart, Abdool dake tsaye bakin k'ofa ya rungume hannayensa a k'irji sai kallon su yakeyi, wani farinciki yakeji burin Maminsa ya cika kullum maganar ta kenan K'anwarta Ameena, yau gata ga d'iyar Ameena, gyaran murya yayi tare da Wanda yasa hankalin mutanen ya dawo kansa karaf idonsa ya had'e dana Ramlah wacce ta d'ago, dama shi ita yake kallo tayi kyau abinta kamar ba Laure ba, inji 'yan garin.

Kallonsa take bata ko kiftawa tsawon sati biyu rabon ta dashi, har ta d'auka sun rabu kenan, Ashe yayanta ne, Ashe shine mijin da Ard'o ya zaba mata, oh yau ina zata saka kanta don murna gata ga dangin mahaifiyarta, ga d'an binni mai glass a matsayin Yayanta kuma mijinta......

Ard'o yace "shigo ciki koni Abdulmajeed, kayi tsaye ga kulkin kohwa"

Murmushi ya sakar mata Wanda yasa tayi saurin sunne Kanta k'asa, shigowa yayi ya zauna kusa ga Alhaji Sada.

"Tau Alhamdulillah mashaa Allah dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah, daya nuna muna wagga rana mai cike da Albarka da farinciki, Abdulmajeed bakada buk'atar ince zan baka Amanar Ramlatuna, k'aunarka ta kuma matarka nasan zaka aza bisa inda nittsaya (zaka d'ora inda na tsaya).

Sannan yaci gaba da cewa " haka kema 'yata Ameena su duka d'iyanki na Allah ya baki ikon rik'o, Ramlatuna" ya fad'a yana dubanta jiki a sanyaye tace "na'am Baffa".

"Ke d'iyata ta gari mai hak'uri, karki canza daga halinki na kwarai da nissanki kici gaba dashi, gida zakina ba daji ba inda 'yan uwanki na, zakina don Allah Ramtuna kici gaba a yadda nissanki Allah ya arbarkace ku gaba d'aya" tuni idanunta suka kawo k'walla duk son da take na had'uwa da dangin ummin nata, gata kuma gaban su a yau amma kuma sai taji batason rabuwa da mahaifarta batasan rabuwa da Baffanta mai k'aunarta, shi kanshi Ard'o daurewa kawai yakeyi amma yasan zaiyi kewar Ramlatunsa...

Mami CE ta share mata hawayen da zuka zubo mata tare da bubbuga mata baya.

Suma Malam Garba da Alhaji nasiha sukayi musu da sanya musu Albarka, anan Ard'o yace zasu iya wucewa, Mami ce tace a kaisu inda iya Hari suyi mata godiya sannan tayi sallama da Ramlah, shikam Ard'o yama manta da wata Hari dan baiyi niyyan sakota a ciki, kai ya jinjina lallai karamcin dangin Asma'u yawane dashi duk da sunji kalar cutar war da Hari tayi ma Asma'u da Ramlah amma duk da haka godiya zasuyi mata..

"Aishatu kikai su inda innarku" Shatu da itama farinciki da ganin yau Ramlah ta had'u da dangin umminta, dama ta dad'e tama mata fatan Alkhairi a rayuwarta ga Alkhairin yazo kuwa, "to Baffa" sannan ta wuce gaba sukabi bayan ta...


*****************

Su Iya Hari da ke zaune zugum kamar masu zaman makoki, tunda sukaji karar mota suka leka, dawowa sukayi suna jiran shigowar Ard'o, saidai babu shi babu labarin shi, kamar an aiki bawa garinsu, tuni suka shaka wai ya wulak'antasu(ji hauka ita da akaba kud'i tayi abinci batayi ba) suna zaune sai zaginsa suke shida Ramlah ko salla sunk'i tashi suyi, yo dama sai anga dama akeyi, sallamar Shatu ce ta katse su.

Ganin Ramlah bayanta yasa Lanti mik'ewa da sauri da niyyan zuwa ta cafkota, ita kuma Iya Hari tana shirin bud'e baki ta fara cin mutunci, sai suka ga ta shigo, a firgice iya Hari ta mik'e tsaye tare da zaro k'ananun idonta, itama Lanti tsayawa tayi cak, kamar photo, murmushi Mami ta sakar musu tuni tsoro ya lullub'esu dan sun d'auka Asma'u ce.

Shatu ce taje ta d'auko tabarma ta shimfida mata, zama tayi sannan tace "ina wuni Iya mun sameku lafia" sai nan Iya Hari ta motsa tabbas kama sai yanzu da taji muryarta tafi ta Asma'u girma, jiki a sab'ule ta ansa itama Lanti haka ta jayo kafafu tazo ta Zauna.

"Nasan ba zaki ganeni ba, sunana Ameena ni yayar Asma'u ce kuma mahaifiyar Abdulmajeed mijin 'yata Ramlah" wani irin kwarjini tayi musu cikin rawar murya tace "Toto madallah" taja baki ta tsuke.

Shatu ce tayi musu cikakaken bayani sun girgiza ainun dajin wannan sabon Al'amari, amma maimakon suyi nadama sai b'acin ciki ne ya rufesu saidai ba damar su nuna dan suna tsoron matar danko shigarta abin dubawa ce.

"Iya dama naso ne da d'iyata tayi muku bankwana sannan kuma nayi godiya da rik'on da akayi mata, mungode Allah yayi Albarka".

Wani irin gunguru gum taji kanta yayi " kodai batasan irin rik'on tayi mata bane ita da Uwarta" ta fad'a a ranta, a fili kuma murmushi yak'e ta k'irk'iro Wanda Sam bai mata kyau ba dan bata saba yi ba.

"Aa babu komi d'iyagga, tau Laure a tahi aita Arme Allah ya Baku zama lahiya" Ameen" tace itama Lanti sanya Albarka tayi, nan Mami ta tashi ta debo kud'i cikin jakarta ta raba musu, sannan ta dunk'ule wasu masu yawa taba Shatu, nan kuwa su Lanti sai hararan Shatu ake, har waje suka rakasu koda suka fito harsu Baba sun fiffito sun tsaya a bakin mota suna jiran su, gaisawa sukayi dasu Iya Hari, sai wani d'ari d'ari sukeyi, ba Wanda ya nuna musu komai a fuska.

Hakan yasa suka d'auka basu sani ba suka d'an saki jiki, hadda yi musu gaisuwan rasuwar munafurci, shikam Abdool kallon su kawai yana jinjina kai lallai mutum ba kyau, nan k'awayen Ramlah suka iso rungume ta sukayi suna kuka itama kukan take, kud'i Mami ta raba musu suma suka wuce Delu ce kawai ta tsaya tana ta kuka, sun rungume juna ita da Ramlah dama itace k'awar ta ainihi sauran duk copy ne.

Ard'o ya rabasu tare da basu hak'uri, Cikin jikinsa ta shige tana Mara yan kuka, shi kansa ya sakata mota tare da rarrashinta "keko dai Ramlatun Baffa ai nace miki idan Mijin naki ya tashi tafiya zan biyoshi inga Mazaunin Ku, ko bakiso in taho na"?

Kai ta girgiza alaman tanaso "Yawwa share hawayen kije kinga ke kawai ake jira" da wayo ya samu tayi shiru Mami kam mamaki wannan soyayya kawai takeyi, Abdool kuwa kallon yadda take kukan take Cikin shagwaba shi dariya abin yake bashi shine zaija motar sai kawu Mansur gaba, ita da Baba da Mami ne baya, kwantar da ita Mami tayi kan cinyarta, tana rarrashinta sannan yaja suka wuce, dama su Alhaji tuni suka wuce.....

Wasai Ard'o kejin ransa yau ya sauk'e wani nauyi a kansa, saidai zaiyi kewar Ramlatunsa, godiya yayi Malam Garba sannan ya shiga gida.

"Tau Hari kega yadda Allah ka ikonai ko, Yau dai keda dangin Asma'u dakikai mata gori kullum akansu kuma ke tabbatar da suna sonta, inama tana raye taga wagga rana...."

Cikin harara ta katsesa "yo Malam mi a sabo nanga (meye sabo anan) dan Mayu sun d'auki d'iyarsu daga sun taimaka mana ma, kuma in kudd'i wane irina a bangani".

Murmushi yayi tare da cewa " baki tab'a ganewa Hari, Allah ya ganar dake" sannan ya wuce abinsu, nan kuwa suka zauna sai fad'a suke ita da Lanti kamar su ari baki (kuwwa baya ga yak'i) itakam Shatu zamewa tayi tai gida abinta tana nema musu shiriyar Allah dan ta fahimci sunyi nisa har yau basu san Annabi ya faku ba(rayuwa shirin Allah inji k'awata swerry)...


********************

A Argungu zabon zaman makoki akayi kowa yazo ganin Ramlah sai yayi hawaye, shikam Abdool ganin abin yayi yawa yasa ya zame ya dawowar sa yabo sai waya yayi ma Mami cewar ya koma, kwanansu biyu har birnin lafia sunje inda dangin Baba, sunyi farinciki da ganin Ramlah da akayi imma iya baki ne can musu, a kwanakin Mami ta Samar ma Ramlah passport sukabi flight sai Kd dan tabar su Husna inda Nanny su Saboda school, Inna kuwa ji tayi kamar a barmata Ramlah saidai ba dama hakan, saukinta ma yanzu matar kawu Mansur nanan tana debe Mata kewa, dan ya dawo yayi aure har da 'ya.

A yau ne mutanen yabo suka shiryama Abdool walimar girmama sunyi k'ok'ari Sosai to ai Abdool d'inne na mutane kowa nashi, sun bashi kyaututukka sosai haka ya baro Yabo cike da kewar garin dan adan zamansa ya saba dasu, suma dai basu so tafiyar sa saidai ta Riga ta zama dole.

Saida ya biya ta Kilgori ya d'auki Ard'o sannan suka biya Sokoto suka sallami Alhaji Sada, tare da d'aukar Hakeem suka nisa hanya.........




=ؗ?

Safe trip





=؄?Meryerm Abdool=؄?
[8/19, 10:15 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)







=??? *Episode* 146--150




Ramlah data rud'e da ganin Argungu ta d'auka k'arshen kallo kenan, ashe kallo na gaba, balle ta taga jirgi ai gigicewa tayi, saida Mami ta rik'e ta a kafad'arta aiko ta k'ank'ameta, Aa ashe da sauran rigima da jirgi ya tashi, kuwwa tasa saida Mami ta rufe mata baki, tare da boye mata fuska a cinyarta, nan tayi baccin tsoro(tsoron k'arya ne Ramlatun Baffa aida bakiyi bacci ba).

Suna sauka driver yazo ya d'auke su, nan fa kallo ya samu ga Ramlah ido, baki, hanci duk abu d'aya sukeyi taga garin Gwamna ashe na Argungu wasa ne, lokacin da suka isa gida, nan ma wani sabon kallo ganin furanni ko'ina sai kalolin k'amshi suke fitar wa, ita dai Mami sai dariya take mata, ganin Abin bana k'are bana yasa Mami taja hannunta tana fad'in "Ramlah muje ki huta ai idan kallo zakiyi har ki gaji tunda kinzo kenan" kunya taji ta kamata tayi d'an Smiling.

Su Abj da Husna ne suka fito a guje suna fad'in "oyoyo Mami" dama ta kira Naninsu ta gaya mata dawowar ta, jin tsayuwar mota yasa suka fito, turus suka tsaya suna kallon Ramlah.

"Mami wannan wacece?" Cewar Husna.

Janyota zuwa jikinta tayi tare da fad'in "sannu sarkin surutu bako sannu da hanya sai tambaya ko? To Aunty Ramlah ce, itama kamar Aunty Nihal auntynku CE" Ajb zaiyi magana tace.

"Enough kids Ku bari mu huta mana, Mrs Ask" itakam Ramlah kallon take gwanin sha'awa, sun had'e cikin k'ananan kaya sunyi kyau 'yan birni dasu, rik'e mata hannu da Husna tayi tana murmushi "Aunty Ramlah muje" itama murmushi tayi mata, ciki suka shiga Ajb na rik'e da hannun Mami..

Da murna Inna Kande ta tarbesu, nan suka naje Parlour su Husna sai surutu suke ma Ramlah, abinci Inna kande ta gabatar musu bayan sunci sukayi hamdala, d'akin Nihal Mami ta bud'e ma Ramlah sannan ta nuna mata yadda zatayi amfani da komai, wanka tayi tare da d'auro alwala, gefen wardrobe d'inda Mami ta nuna mata na kayanta ta bud'e daga sama har kasa cike da suturu, wata atamfa ta d'auko a aje gefen gado, gaban mirror taje tayi Shafa, tare da fesa turare powder kawai ta shafa sai lip gloss, kayan ta saka, juyi tayi gaban mdubin tare da sakin murmushi har da rufe fuska da tafin hannunta "nita shin? Yau Ramlah nita a birni cikin daula, ba bugu ba b'aci sai lelena akai" ita kad'ai ke sambatu murmushi ta sake yi.

"Allah na gode maka" dadduma ta shimfida tayi sallah sannan ta fita parlour, da kallon sha'awa Mami ta bita itama da alama yanzu ta fito "iyye 'yar gidan Mami har kin fito, ba zakiyi bacci ki huta ba?"

Murmushi kawai tayi dan batasan tayi magana ayi mata dariya, zama tayi k'asa, tace "Mami ina wuni".

" lafia lau 'yata, ya gajia? "

"Uhm" ta kawai tace.

"Ki saki jikin ki kinji Ramlah nan ma gidane kamar inda Baffa, ni mamanki ce ga k'annin ki".

"Yawwa Mami kikace Aunty Ramlah itama Auntyn muce to ita take ne bamu ganta ba sai yanzu?"

"Oh Abduljabbar rigima, ba gata kun ganta yanzu, Bari dai ina Aunty Asma'u da nake nuna muku fotonta?"

A tare da Husna sukace "an ganta Mami?" Kai ta jinjina "eh kuma wannan 'yarta ce kunga kenan itama Auntyn Ku CE ko?"

"Eh Mami" suka fad'a tare.

Gata sosai Ramlah ta sameta gurin Mami gasu Husna suma suna nan nan da ita, gari aka zaga da ita Tasha kallo kamar idanu su cire, tun tana d'ari d'ari harta sake dasu, haka zatayi ta biyema su Husna, suyita wasansu da hira, maganar ta dad'i take musu suyita kwaikwayonta suka cewa ta koya musu, Mami dad'i takeyi a ranta ganin yadda ta saki jiki dasu, haka take tasata gaba suyi fira kamar k'awarta, dama haka take da 'ya'yanta tana jansu a jiki(sai mun ja yaranmu a jiki mun kusantosu damu muke gane damuwarsu harma mu samar musu mafita, yin watsi dasu ko d'aure musu fuska shike kaisu ga fad'awa a halaka, Allah ya shirya mu dasu baki d'aya).




*********************



4:00pm cikin Kd tayi musu Hakeem suka fara saukewa sannan suka k'araso gida, tarba sosai suka samu gurin Mami, dan tun safe suke kitchen ita yaran dama idai tana gida ita ke shiga da kanta kuma tare da yaranta saboda su koya, Ramlah da yake akwai kaifin baseera ga tambaya tuni ta fara gane makamar aiki irin na birnin, dama ta iya na k'auye tunda ita keyima Hari.

Baffa yaji dad'in yadda yaga Ramlatun sa ta saki jiki, tana mak'ale dashi sai firan birni take mishi dama Ramlah badai surutu ba.

Abdool kam tun da sukayi lunch yayi sallah ya kwanta so ko gaisawa sosai basuyi ba.

Baffa ne zaune da Mami suke fira, k'aramar jakarsa ya d'auko ya fito da takardu da ya mik'awa Mami "Ameena wanga takardu ne da suka shahi gadon Ramlah danaku na wajen Asma'u, sauran takardun haihuwar Ramlatu na, gasunan kuyi mata abinda ya dace dasu, ayi mata komai na d'aki irin naku na nan idan zasuyi, kuma don Allah kada Ramlatuna tazo garemu nan kusa, ni zan ringa zuwa da kaina ina ganinta".

Takardun ta duba kud'i ne masu d'an dama " to Baffa ban katse maka hanzari ba, amma ni ana tunanin tariyar Ramlah ba yanzu ba, karatu nakeso tayi".

Sannan taci gaba "idan akayi la'akari da k'arancin shekarunta, duka shekara 14 tayi karanta da Aure, to ana tunanin in siya mata shares da kud'in ta kamar yadda nayi ma su Nihal, ni zan d'auki nauyin karatun ta, sa'an Nihal ce to ina tunanin kaita school d'in su Nihal amma ya kake gani."

Murmushi yayi yasan karatu shine babban burin Ramlah duk kuwa da Hari ta tauye ta yasan hakan zai sakata farinciki, amma kuma ai Aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login