Showing 78001 words to 81000 words out of 88300 words

Chapter 27 - ABDULMAJEED BOOK by Meryam Abdul.doc

09 Oct 2025

1601

ido sai kallo suke, wuni sukayi zungur sunje malls, da parks sosai sun cire kwarkwatar ido, anci ansha.

Adan watan da sukayi sun murmure sosai musamman Shatu tayi ja sosai tayi jiki Ashe duk wahala ce ta lalata ta, sosai suke kama da Ramlah d'an kammaninta d'aya da marigayi Abdulrahim, Iya Hari ma da Lanti sun murmure abinsu sunyi kumari da haske, saidai har yanzu sun k'asa sakewa dasu Mami suna ganin kamar suna kallonsu da cutarwar da sukayi wa Laure, duk da Mami na iya k'ok'arin ta gurin jansu a jiki, itama dai Ramlah kullum tana tare dasu, s???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?u kuma sun dage da renon su Amatullah.

Watansu Ramlah 2 amma har yanzu shiru Mami tak'i bashi matarsa tun yana ma Ramlah naci har ya gaji ya saka mata ido ga gidan a cike ba damar ya samu ya keb'e da ita, ko gidan yaje yace tazo ta kawo mai Abu a d'akin sa, cewa tace ai haihuwa d'aya horon abin..ba abinda zai kai k'afarta ya sakeyi mata wani cikin, shi dariya ma ta basa wato har yanzu akwai sauran k'uruciya tattare da Ramlah, wato ma a d'akin sa ne, takeyin cikin tun da anyi na farko.

Mami ya samu da maganar komawarsu Ramlah, b'ata rai tayi ta shiga balbale sa da fad'a tace ba zata koma ba sai yaran ta sunyi k'wari tukun, ganin ta ko'ina ba nasara yasa ya shirya nashi plan, Mami kuwa bayan tafiyarsa tace ma Ramlah ta fara shirye-shiryen komawa dam tasan halin d'an nata zai iya k'ara wata tabargazar dan idanunsa sun riga da sun soye tuni, yanzu Sam baya kunyarta Indai akan Ramlah ne.

Washe gari da wuri ya shigo a parlour ya samu su iya Hari suna ta faman kallo, gasu Abdool a hannunsu, gaisawa sukayi cikin sakin fuska, sannan yayi wa su Amatu wasa da sai b'angalar baki suke suna dariya Sam basu da matsala indai tumbinsu ya d'auka, junior rik'e a hannunsa yana masa surutun nasa daya iya, tambayan Mami yayi suka gayamasa tana ciki.

Mami na zaune gefen gado tana yiwa Ramlah bayanin kayan dake hannunta ita kuwa tana tsaye gun sif tana gyarawa Mami kayanta duk a kunyace take da bayanin da Mami ke mata, da eh kawai take binta shima can ciki ta maida hankalinta ga aikin da take.

Turo k'ofar yayi tare da sallama a bakinsa a tare suka amsa masa, zama yayi kan sofa yana gaida Mami, amsawa tayi tana tambayan sa aiki, gaidashi Ramlah tayi tana satar kallon sa dan ba k'aramin kyau yayi mata ba a Cikin k'ananan kayan da ya saka jean blue da shirt yellow mai dogon hannu an rubuta i'm d prince a gaban rigar da bakin penti sai zuba k'amshi yake.

Ko inda take bai kalla ba ya amsa gaisuwar tata ba yabo ba fallasa, shiru ne ya ratsa na d'an lokaci dan Mami ta aje kayan da takewa Ramlah bayani ta d'auko wata jarida tana dubawa, ita kuma Ramlah sai aikin gabanta take.

"Um Mami dama magana ce dani".

"ina jinka" tace a tak'aice ba tare data d'ago ba.

"Am dama Aure nakeso na k'ara am.." Sai yayi shiru.

Smiling tayi tare da kallon na d'an lokaci "to ai ba matsala sai kayi magana da Alhaji ko 'Yar inace yarinyar?" Ta fad'a cikin kwanciyar hankali, shiru yayi kansa k'asa "oh God I totally fail" ya fad'a a ransa, a fili kuwa yace "anan take Kaduna" a nashi tunanin idan yace haka Mami fad'a zatayi sannan ta bashi Ramlah cikin lokaci.

Ramlah Kuwa jinin jikinta ne ya daina aiki na d'an dak'ik'u, yadda maganar ta daki zuciyarta, k'arfin halin tattaro nutsuwarta tayi zuciyarta sai suya take tuni k'walla ya cika mata idanu, ji take kamar taje ta rungume shi tace ya fasa Neman auren su wuce gida Indai akan tak'i komawa ne.

"Ok ka samu Alhaji kuyi magana sai ayi bincike ko?" Mami ta katse musu tunani "tom" yace tare da mik'ewa yana kallon inda Ramlah take dan ya ga yanayin ta, ganin sai aikinta take kamar bataji me yace ba yasa jikinsa k'ara yin sanyi a sukwane ya fice.

"Ki kwantar da hankalinki kinji dota, ruba ce kawai yake ba wani Aure da zaiyi" sunne kai kawai Ramlah tayi tana murmushi, itama Mami murmushin tayi sannan ta fice zuwa parlour gurinsu iya Hari.

Bayanin komawar Ramlah tayi musu tace su shirya zasu rakata gidanta da anjima da dare, sannan ta basu labarin bazanar Abdool, cewa iya Hari tayi "kema dai Hajia ke rik'e mai mata da yawa ai dole yayi muku barazana kinsan yaran yanzu babu hank'uri" dariya sukayi gaba d'aya.



*************


8:00pm su Iya Hari suka kai Ramlah gidanta bayan Mami tasa an tsantsara mata Jan lalle da kitsonta mai kyau, ga gyaran jiki tasha sai shek'i take, susucewa su Shatu sukayi da ganin gidan Ramlah ashe na Mami nafila ne ga farilla anan, Dak'yar Mami ta tattarasu suka wuce sunata santin gidan.

Yara biyu Mami ta samo mata dan tayata renon yaran, nan suka shiga k'yalk'yale gidan da kimtsa sa, duk da dama a tsare yake dan Abdool akwai tsafta da k'amk'ami kullum cikin gyaran gidan yake, Nihal ma an kawo jiki dama tasan da dawowar dan tun rana Ramlah tayi mata waya dan kullum cikin damunta take yaushe zata dawo, zaman kad'aici ya isheta gashi Hakeem ya daina kaita gidan kullum yace bai son ana wahalar masa da baby da yawon hanya, abincin da ta shirya musu ta kawo musu nan ta bige da hira sai 9 ta koma kada Hakeem ya shigo bai sameta ba dan Ramlah tace kar ta gaya masa dawowarsu dan tasan tsaf zai iya tuntub'ar Abdool da maganar gashi surprise takeson bashi.

Sai 10:00pm ya shigo gidan dan a gajiye yake lilis yasha aiki, ko gidan Mami bai samu ya koma ba duba yaran sa, dan yanzu yayi giving up ya barsu in an gama ja masa rai ai ta dawo.

Tun a harabar gidan ya fara cin karo da daddad'an k'amshi, saida ya lumshe ido daya shiga parlour saboda yadda sanyin A'C ya had'e da wani tattausan k'amshi bai gama mamaki ba saida ya hango dinning d'auke da kulolin abinci aiko shawara bai tsaya ba ya haye ya kwashi gara, shi a tunanin sa Nihal ce da yake tana da spare ke na gidan kuma takan shigo tayi masa gyara girki kam kullum zata kawo mishi duk da kullum yake ci ba, wani sa'in da yaci a gidan Mami shikenan dan Sam bayacin abincin kasuwa k'yamarsa yake.

Saida yaji dai2 sannan ya wuce d'akin sa yayi wanka tare da shirya wa Cikin kayan baccinsa, parlour ya dawo dan rufe k'ofa, motsi ya ringa shi a part d'in Ramlah, rufo k'ofar yayi sannan ya nufi part d'in.

A parlour ya samu mai renon su Abdool tana bawa Amaturrahman madara, kallon mamaki ya bita dashi, ita kuma saurin sunkuyar da kanta tayi tana kwasar gaisuwa amsawa yayi tare da tambayan Mamansu bayan ya Amshi Amatu data koma bacci, "tana ciki" ta bashi amsa, wucewa yayi ita kuma ta wuce d'akin da aka keb'e musu.

Zaune take gefen gado tana feeding din Abdullah tasha kwalliya cikin wata fitinanniyar half sleepy gown Brown my santsi shara-shara sai k'amshi take zubawa, tsaye yayi ya jingina da k'ofar ya kafeta da kallon fitina.

D'ago wa tayi tare da sakar mai k'ayataccen smiling hadda kashe masa ido d'aya, da sassarfa ya isa gareta tare da kwantar Amatu gefe, matseta yayi yana hararanta matsa Maman yayi yana kallon ta " zaka sa ya kware ka tayar mana da rigima" tace Cikin slow voice nata.

Bai amsa mata ba sai d'aukesa da yayi daga kan cinyarta, ya aje shi gefe shima, sannan yayi mata mugun matsa har saida kashinta ya koka, d'an k'ara ta saki tana 'yarfe hannu tare da turo baki gaba.

Kama lip d'in yayi cike da zalama ya shiga totsar su da sauri-sauri da wasa da duga sassan jikinta cikin zafi-zafi, ganin abin nasa bana wasa bane yasa ta turesa tare da zame jikinta tana maida numfashi tare da nuna masa yaran dan har junior na kan gadon.

"Ina sauran?"ya fad'a cikin maye, idonsa sun canja launi, " suna gun masu renon su"

"Jeki dawo dasu nan" girgiza masa kai tayi alaman Aa sannan ta zura dogon hijab, ta d'auki yaran biyu ta fita dasu yasan me take nufi a can zasu kwana kenan, d'aukar junior yayi ya bita dashi, dama basa kwanciya da junior saidai in sun kammala .....abinsu suke dawowa dashi tasan yau mijin nata sai abinda hali yai kawai dan tasan yau zataci kwakwarta, (hattara iyaye Ku kad'aice yaranku koda jarirai ne bai kamata Ku tara kuna tare dasu ba, don ko jin numfashinku a garesu bala'i ne, Allah ya shirya mana zuria ameen.)

Saida ta shafesu da Addu'a sannan ta kashe musu wuta tare da ja musu k'ofa, a bakin k'ofar taci Karo da gogon nata, suntumar ta yayi kamar wata baby, muna zuwa k'ofa ya ballamin harara tare da tura kyaurensa ya barni anan ina cizon yatsa naso na d'auko muku Rahoto amma yau Abdool yace nahi(Aa).

Nan na rab'a a k'ofar ina jiran tsammani, can har bacci ya fara d'auka ta naji sai ihu Abdool ke tsundumawa, a firgice na tashi nima zan zunduma da gudu, muryan Ramlah na jiyo sannu-sannu tana magana, hakan yasa na nutsu na baza kunnena dan naji me take fad'a da kyau.

"Kada kajimin ciwo mana Yaya Bini a hankali" tace cike da shagwab'a.

"Um..aaa.. Sorry baby na ai ke d'in CE.."

"Wayyo Yaya kada fa ka sakeyimin wani ciki"

"Aa...bazan yi miki ba baby...

" toya maganar aurenka?"

"Wane auren kuma...ni ai duk maza nake kallon mata...ash.. Baby ke kad'ai ce fa......wayyo baby ina zaki kaini...wayyo! Wayyo!! Wayyo!!"......









>?#?>?#?>?#?>?#? dariya tasa na k'asa ci gaba da d'auko rahoto, kuma Ku dara amma kad'an fa=?D?=??











=؄?Meryerm Abdool=؄?
[10/20, 5:13 PM] =؄?Meryerm Abdool=؄?: =ؤ? ```ABDULMAJEED``` =ؤ?

(' *Servant of Majesty* ('



Na
=؄? _Meryerm Abdool_ =؄?


? *Real Pure moment of life writers*
P.M.L=ت?
(We don't just entertain and educate we touch the heartd' of the readers=???)



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*



```An karb'o daga Abdullahi d'an Abbas (R'D) yace "Manzon Allah(S.W.A) yace " idan d'ayanku ya mutu aka samu mutune arba'in muminai wad'anda basuyi shirka da Allah ba suka sallacesa to ana mishi kyakyawan zaton samun rahamar ubangiji ```

Hakkun mubeen


*Alhaji Waiman (Mukhtar) Allah yayi maka rahama yakai haske k'abarinka yasa mutuwa ta zamo Hutu a gareka kai da dukannin wand'anda suka rigamu ya Allah ka kyautata tamu bayan tasu ameen=?O?





=??? *Episode* 256-260







A week suka d'auka ana soyewa, Abdool duk ya susuce ya zama jela wa Ramlah duk inda tayi yana manne da ita, sambatun yau daban na gobe daban, tun Hakeem na mishi mita har gaji ya kyalesa, ganin za'a damesa da kira a waya yasa ya kashe wayoyin gaba d'aya har na Ramlah, sauk'in su yaransu basu da fitina sam kullum suna gurin maid nasu feeding kawai ke had'asu da Maman su, shima junior yana gurin k'anninsa kullum yana musu wasa, hakan yasa suka tare part d'in Abdool suna cin karen su ba babbaka, madarar k'auna ta ganta a gurin Abdool wacce ba algus ko kad'an a ciki, riritawa da tattali shine suka shiga bawa juna.

Dak'yar ta samu ta korasa ya koma bakin aiki ganin har gida ake iskoshi amma sai yace shi Amarci yakeyi a barshi ya huta, hadda dan tumbin Hutu ya ije ga wani fresh da sukayi fresh milk tayi aiki. Lol.

Ranar da ta samu ya fita ta d'auka wayarta ta kunna nan fa messages sukayi ta shigo mata na wad'anda sukayi ta Neman basu samu ba, dariya tayi ta tace "duk rigimar Yaya ce ta b'oye ni" sannan ta danna number Sadee rings 2 ta daga tana fad'in.

"Kaga Uwargida a gidan Dr wato shikenan sai mukaji shiru an shige anyi luf sai karb'ar upper ake" ta fad'a cike da shakiyanci.

"Ke Yar duniya baki yimin shi shiyasa naga kinzo min keda baki k'arbar Upper"

"Hehehe! Rufemi ki saya so kike nazo Dr ya harareni yasa na haihu ban shirya ba, banni na lallab'a da Uncle luku na har ki sarara da karb'ar upper d'in"

"Wlh kedai Besty anyi shu'umar mace kin zugani kin koma gefe kina dariya wlh duk kin lalatamu nida sisto".

" wai 'Yar air kina chan kina shan dad'in ki, zakizo kimin burga, wai ya maganar amaryarki?"

Dariyar ta sheke da ita sanda tayi mai isarta tace "ai tun ranar da muka koma aka rufe wannan babin".

" kai besty kema fa silent killer ce a wannan fannin, anya ba so kike kifi malamar taki ba" tace tana dariya

"Cap aike besty k'arshe ce adaiyi shiru kawai, wai yaushe zaki b'ullo ne?"

"Hhhhhh! Kinsan ko akwai sababbin darasi kuyi ready keda Nihal ina nan b'ullowa Akwai chapter".
" sadee fire sai kinzo muna tsumayenki, kink'i sarara wa Uncle duk da tutsetsen cikin ki"

"Kai ai ba daga k'afa......'" Hakan sukayi ta rahar su tsawon lokaci....

Watan su Iya Hari 2 a Kd sukayi shirin tafiya dan ta samu sauk'i sosai, kuma Ard'o ya matsa su koma hakanan yace dawainiyar tayi yawa, dan shi sati d'aya kawai yayi ya koma saboda jagoranci dake kansa, dan tsawon tafiyarsa 2-3 days ne, wannan Karon ne kawai yayi sati koshi dan ayi aikin yana nan ne kuma anayi ya juya ya koma yace yabar gari sakaka kar wani Abu ya faru kuma bashi nan(jagoranci Abu ne mai girma da nauyi Wanda ya zama dole ga shugaba ya kiyaye domin amanace a hannunsa wacce za'a tambayesa yanda ya gudanar da shi).

Tsaraba sosai suka sha daga gurin su ki da suka je ma Ramlah sallama itama ta had'a musu kaya sosai, ga ingantattun magunguna da Abdool ya d'ora iya Hari akai, kuka Iya Hari ta fashe dashi tana nadamar bakin halin ta na baya, da tana da damar gogesa a rayuwa data goge shi dan kullum ta tuni sai tayi kuka da nadama Mara adadi(ki godewa Allah ke kin gane gaskiya kin shiryu tun anan duniya, wasu kam sai Allah kawai, Allah ya shirya mu akan tafarkin gaskiya mu doge a kansa har abada).



**********



Rayuwa mai cike da k'auna ma'auratan ke gudanar wa, Abdulmajid hospital ta samu d'aukaka sosai saboda kyawun niyya dake kunshe a zuciyarsa, ga sauk'i da ake samu akan komai ba lalle sai mai kud'i ke zuwa ba, ta zamo kamar government hospital yanda yake taimaka talaka da marasa gata Addu'o'insu yasa hospital d'in ta samu karb'uwa a fad'in Kaduna da zagaye a yan watannin da tayi da bud'ewa kowa Abdulmajid hospital kakeji a bakin mutane suna yabawa da kod'awa..

Ramlah tuni tayi mai da zancen karatunsu ganin anaso a shantake, aiko cikin satin ya kawo musu form guda uku ita da Nihal da Sadee, mass com Ramlah ta cike dan har yanzu tana nan akan burinta na son zama journalist, Nihal ta cike nursing, Sadee kuma Pure Biology amma sai bayan su nihal sun haihu zasu fara zuwa, dake Nihal ta shiga month nata sadee kuma next month, hakan yasa Abdool ya dage da koyawa Ramlah motarta dan su samu ta zuwa school, aiko in 2 week hannunta ya fad'a dan Ramlah akwai sauk'in kai....


Nihal ta haihu successful ta samu d'a namiji chaii! Su Hakeem an zama Dady murna bata fad'uwa, anyi shagali still dai ba'a bar Abdulmajid fans ba sun zo sun kwashi banza kamar yadda suka saba, Ramlah da Abdool sun taka rawar gani sosai haka Sadee da Uncle lukman ma ba'a barsu a baya inda yaro yaci sunan Abban Nihal Yusuf suna kiransa da Aabid, Allah ya yara Aabid akan sunnah.

After month itama Sadee ta sunkuto tata 'yar mai sunan Maman Uncle lukman Salma(ihsan) still dai aminan junan sun taka rawar gani haka yan cin banza basu fasa zuwa as always, lol


Sunyi resuming school da motar Ramlah suke tafiya sai su biya su d'auki Sadee dake ita bakin hanya take, wani zubin kuma mazajensu ke kaisu saidai su had'u anan aka k'ara dink'ewa duk da kowacce faculty nasu daban hakan bazai hana idan basu da lec ba su had'u su sha chapter, dan har yanzu bakin bai mutu yana nan musamman Sadee, a gidan Mami suke barin yaran da Masu renonsu su Abdullah anyi girma sosai inka d'auka saika nisa har sun fara rarrafe ko'ina zuwa suke da rarrafe b'anna kuwa ko burgu ya sarara musu shiyasa Mami ke ce musu burguna...

Sam karatu bai hanasu bawa mazajensu kyakkyawar kulawar da ta dace ba, a cewar su karatu baya haka aure kamar yadda aure baya hana karatu saima k'ara samun experience a kowane b'angaren dan sosai majazen su ke assist nasu a kan karatun su......




**********




Wani sanyin ni'ima ne yaji yana ratsa shi lallai yayi missing k'asarsa ta haihuwa na tsawon lokaci, yaga canji sosai da ci gaba a garin, adaidaita ya tara tare da gayamasa inda zai kaishi, dake gurin sananne ne nan take mai adaidaita yace ya San gun, shiga sukayi shida matashiyar yarinyar da ke tare dashi wacce kallo d'aya zakayi mata ka gane tana da jinsi da larabawa.

A dai2 get d'in mai adaidaita ya aje su, biyanshi yayi sannan suka sauko, tsaye yayi a gun yana bin gidan da kallo duk da canje-canje da gidan ya samu hakan bai hanashi gane sa ba, itama yarinyar rakub'ewa tayi gefen sa tana kalle-kalle ta ganta a wata k'asa ta daban wacce take da matukar banbanci da k'asar ta tana rik'e da luggage nasu.

Daga can nesa na hango wani mutum a keken guragu yana tunkaro inda wannan mutumin yake tsaye cike da mamaki a fuskarsa,yana fad'in "Alhmdllh" sai sauri yake dan yaga mutumin na k'ok'arin shigewa gidan ...

"Malam dan Allah tsaya" Kalmar da ta doki kunnensa kenan, dan tabbatar da dashi ake ya juyo.

Tozali da mutumin da yafi tsana a rayuwa wanda yayi silar tafiyar farincikinsa ya dasa masa bak'in ciki a rayuwa ne yasa ya tunkaro gurin sa gadan gadan fuskar nan kamar ta zaki, itama yarinyar ganin meke faruwa ne yasa ta saki jakar tare da bin bayan mutumin tana fad'in "Abi" dayin wani yare Wanda na fahimci larabcine.

Ko saurarenta baiyi ba ya isa ga mutumin tare da cafkar wuyar sa yana huci baiyi duba da halin nakasa da yake ciki ba.

Wawuyar matsa yayi ma mutumin a wuya tuni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login