Showing 27001 words to 30000 words out of 103127 words
haki "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun lafiya yaseer meyake faruwa?meyafaru kaida waye ko barayi ne?"nuna kofa yakeyi cikin haki yake sauke numfashi yana fadin"itace....itace wallahi dodo ce ba mutum ba"dik a furgice suke suna kallon kofar shigowa cikin rudani innah kakar husnah kamar ta ruga aguje tace"wacece?"yaseer yayi shiru ya dafe kirjinsa yana rike da takardar sakin husnah yace "hus....hus"ya kasa karasa sunan ummah hadiza da hafeez rige rigen ambatar sunanta sukai a tare "husnah?"ya jinjina musu kai momy ta rushe da kukan takaici cike da masifa idanuwanta sun rufe take fad'in Allah ya wadaran wanan aljanin da yake tare da yarinyar nan ya hanata zaman lafiya wanan wace irin masifa ce dik inda yake tsinanne ne shi bazai taba gamawa da duniya lafiya ba mugu azzalumi"hafeez bai jira cewarta ba ya fice aguje shida ummah hadiza da innah wadda keyi baya baya Abraham ne tsaye jikin bango Yana sauraren furucin momy idanuwansa suka kad'a sukai jajir cikin fushi yake mai tsanani danne zucuyarsa yayi yadda jikinsa ke girgiza dakin ya shiga juyawa yana girgiza kamar ana dukan kasa waige waige momy keyi babu kowa sai yaseer dake tsaye kamar an dasashi yanabin ko ina da kallo danne zucuyarsa Abraham yayi dan yadda yayi fushi zai iya fitowa daga jikin bango idan kuwa yayi hakan tabbas momy mutuwa zatayi ganin hafeez ya dauko husnah yasa Abraham ya mike yayi girgiza ya shige jikin husnah yayi mika mai karfi sai gashi ya watsar da ummah hadiza da innah wadda dama baya baya takeyi mikewa tayi ta tsaya tanayiwa hafeez wani mugun kallo idanuwanta sun furfito waje tayi kwafa tace cikin wata irin murya "karka sake kuskuren kai hannunka jikin husnah dan husnah matar aurece idan kuma kayi kuskuren hakan to tabbas zaka yabawa aya zakinta"momy a fusace ta mike tana nuna husnah wadda sam ba ita bace Abraham ne a jikinta tace "karya kakeyi aljanin banza mutumin banza mutumin wofi kai inhar sonta kakeyi tsakani da Allah bazaka taba zama tare da ita kana cutar da itaba mugu Azzalumi kasani akwai kiyama sai anyi mana hisabi da Kai"jikin momy na tsanani rawa takeyin maganar cike da fushi yaseer ya rukota yadda jikinta ke rawa ya zaunar da ita kiris ya rage ta yanke jiki ta Fadi Abraham jingina yayi a jikin bango a jikin husnah gashin kanta ya yamutse ya mimmike shedar ba ita bace ummah hadiza tace "wai ina Badamasi yake ne besan meke faruwa bane yazo ya kira mana malami a Diba yarinyar nan dake tsananin shan wahala"Abraham kallonsu yakeyi cike da takaici yau da adan momy uwar husnah bace yau da sai ya nakasata sai ya maidata abun kwatance batasan baa nunasa da yatsaba take nunasa take masa mugun furuci saboda tsananin son da yakeyiwa husnah yasa yau tunda yake be taba fushi da itaba sai yau darajar husnah tasa ya kyaketa innah ta karbe zancen "ina badamasi yakene shin?"momy ta girgiza kai ta nuna mata sashen hajiya rabi wanda yake a rufe,
idanuwan hafeez sunyi jajir yake takowa gaban husnah wadda ke tsaye Abraham ne yacev"kai da ace mutim na ganin aljani wallahi da sai nayi wasan Kura da kai dan na tabbatar ni dan adam nafika daraja ninkin ba ninkin saboda haka ka matsa kabani wuri kafin in tofeka da ayar Allah"hafeez yace yana kallom Abraham dake kallonsa ido cikin ido kwayar idanuwan husnah kadai yadda ya sauya zuwa kalar ruwan toka babu fari saika furgita,yaseer na tsaye gabaki daya ransa a bace yake haushin hafeez yakeyi ji wani zakewa da yakeyi akanta?wata zucuyar tacewa yaseer meye naka kaida ka rubuto mata takardar saki?mtsww tsaki yayi ya kalli takardar ya riketa da kyau gabansa ya yanke ya Fadi ji yayi yanaso ya kalli fuskarta ya kasa hakuri da daina kallonta tabbas yasan yarinya mai irin kamanninta anan gidan amma meyasa tunda tazo bai tuna da hakan ba?to wace yarinyar ce?dan tsaki yayi ya dago kai suna hada ido ya runtse ido namiji ya gani fuskarsa baka kirin idanuwansa jajir hakoransa a waje ya rufe idanuwansa jikinsa sai kyarma yakeyi tsoro da furgici suka cikasa hafeez ya bude baki cikin karfin hali da dauriya dikda yadda yakejin faduwar gaba ya soma kokarin karanto addua zai tofa Abraham ya shakesa.....
cike da kwarkwasa hajiya rabi ke zaune gaban daddy tana zuba masa shagwaba irinta manyan mata daddy washe baki yakeyi yana zaune dagashi sai singlet gefensa jug ne na juice da aka hada masa yaji magani ga farfesun Naman zabo nan ya dauki cinya ya yaga ya tauna dadi ya ratsashi ya runtse idanuwansa tayi yar dariya tace cikin kissa "yayi dadi ko? nayi makashi na musamman ne nasan zakasoshi idan ka gama akwai alkubus a waccen kular"daddy ya jijina kai yace "dik ni kadai?"ya gyada masa kai hajiya rabi najin bugun kofar da akeyi ta basar amma shi daddy beji ba ta dau remote cikin kissa tace "Bari in kara mana karar tv banaji"zata kara cikin tsawa da daga murya innah ta kwala kira tace "badamasi"da sauri daddy ya kalli hajiya rabi ya ajiye cinyar naman dake hannunsa yana kokarin hadiyewa yace "kamar muryar innah"zatayi magana ta kara kwala masa kira "badamasi ka fito mana sai kace kana zaune da kai?"ya zabura ya mike ya dauki rigarsa Ransa a bace ya bude kofar itama hajiya rabi rai a bace ta biyosa"yanzun dik bugun kofar nan da nakeyi zakuce bakujiba kazo muje husnah babu lafiya Aljanin nan ya tashi zai kasheta gatacan sai rikida takeyi"ran daddy ya Baci ya kalli hajiya rabi tai kicin kicin da rai tace "nice dai baaso aganni nasamu sukuni da mijina babu wasu aljanu wanan yarinyar karya takeyi nina gaji"a fusace daddy yayi gaba innah tana kallon hajiya rabi shekeke tace "to gamandi mai hada uba da y'a makira"hajiya rabi tai mata wani kallo tabi bayan daddy,
hafeez dakyar yajejan numfashi shakar da Abraham yayi masa cikin ikon Allah ummah hadiza da momy jikinsu sai kyarma yakeyi ya sakesa ya kwalla kara wadda daddy na kokarin shigowa sashin ya furgita ya shigo kamar an jehosa yanke jiki tayi ta Fadi idanuwanta a rufe karar faduwanta yasa yaeer saurin kallonta mamakinsa bai ganta a dodon da yake ganinta ba gashin kanta ya rufe gefen fuskarta sai wata yar kwalla dakebin gefen fuskarta.... shiru yayi daga bisani ya kauda kansa hajiya rabi ta saci kallon da yaseer keyiwa husnah ta jinjina kai tabdijan ta zame jikinta ta koma gefe ta turawa muneeba message,
"wani irin abu ne wanan gidana ya koma kamar na y'an bori zainab meye haka wani irin iskanci ne waban haka?"Yana nuna husnah wadda ke kwance a hankaki take bude idanuwanta tana binsu da kallo daya bayan daya tana kallon daddy dake tsaye a fusace a hankali ta mike ta zauna tana murtsuka udo daddy ya dakawa husnah tsawa "ke tashi ki zauna"ta kallesa tana kara kallonsa tadan tsorata yace "dake nake kitashi ki zauna"yana nunata da hannu yace "wani irin iskanci ne wanan kikeyi kega mai aljanu?babu dama in nemi inuwa in Raba in huta sai an kirani gakican kina aljanu?to bazan dauki iskanci ba kinji nafada miki idan duniyar aljanun zaki koma ki koma damacan nayi hakuri dake balle yanzun"hawaye suka zubo a idanuwanta tana binsu da kallo daya bayan daya waige waige takeyi lokaci daya ya fado mata Abraham dinta gabanta ya fadi ya bace ya rikide bata gansa ba baya mata fada tunda take sai yau gashi yayi fushi ya tafi ya barta daddy nayi mata fada ita batason fada yazo ya dauketa su tafi can inda suke rayuwa bazata iya second daya babushi ba muneeba ce ta shigo kamar an jehota idanuwanta suka sauka akan yaseer dake tsaye gefe idonsa kirr akan husnah a karo na farko ta bashi tausayi hawayen da takeyi ji yakeyi kamar yaje ya share mata hawayen,
innah ta katse masa tunani ta hanyar maganar da takewa daddy "badamasi da bakinka kake cewa husnah ta koma duniyar aljanu saboda ta hanaka rawar gaban hantsi da matarka daka aura?baka godewa Allah ba da husnah ta dawo yanzun kakeso ka butulce masa saboda lalurar datake tare da ita?"
cikin fushi dady yace "innah babu wata lalura harda iskanci nafada miki karya ne kawai so takeyi taita daukar hankakina nina gaji bazan iyaba idan tasake makamancin haka saina daureta a gidan nan"daddy ya juyo ya kalli hafeez Wanda tuni kwalla ta cicciko a idanuwabsa tsabar tausayin husnah yace "kai kuma in dagaske kakeyi tunda yaseer ya saketa saika turo iyayenka ka aureta kuje can ku karata da aljanun"...jinnina kai hafeez yayi muneeba ta matso gefen yaseer jim kamshinta yasa yayi furgigit ya juyo sukai ido hudu idanuwanta sun kad'a tsananin kishi tajashi gefe tana masa wani kallo "mai takardar sakin keyi a hannunka baka bawa daddy ba"kansa nadan sara masa ya murtsuke ido yace "au kinganiko tashin hankali da rud'ani yasa na mance"ya janye hannunsa daga rukon dayayi mata ya mikawa daddy takarda daddy karba yayi be tambayi ta ko mecece ba ya rike muneeba ta ja hannun ysser suka fice ko ganin gabanta batayi,
"badamasi kabani mamaki tayaya zakai fushi da yarinyar nan bayan kasan ba yin kanta bane dik abinda takeyi?"daddy bece komiba ya juya a fusace hajiya rabi tabi bayansa takardar hannunsa ya saki a hanyar fita batare da yasani ba,
momy ta share hawayenta ummah hadiza wadda tai mutuwar tsaye ganin masifar da daddy keyi yasa jikinta ya mutu tabbad badamasi bayin kansa bane inba hka ba tayaya zaiyiwa husnah ruwan masifa dik irin son dayake mata dik irin damudaya shiga bayan aljanu sun saceta tsawon shekara goma sha takwas,
hafeez ya karasa gabanta ya tsugunna ya dago kanta ganin hawaye na gudu ta runtse idanuwanta tace "ka daina tabani yaya hafeez ni matar aurece amma yau mijina yayi fushi dani sakamakon kulaka da nayi be tabayimun hakan ba yayi fushi ya tafi ya barni ina kewarsa gashi niba aljana bace ballantana in bace in bisa inbashi hakuri ina tsananin kaunarsa ka fadamun yadda zanyi ya dawo gareni"tsura mata Ido yayi yana hawaye tausayinta ya kamasa ta bude idanuwanta yana hango tsantsar damuwa a fuskarta da tsananin soyayyat aljani sanan dik abinda take fada gaskiyarta take fada,kasa yi Mata magana yayi dole zaije gida yasamu ummahnsa akan maganar nema masa auren husnah....ya mike ya kalli momy kallo daya ya mata ya kauda kai yadda ta fita hayyacinta yace "zantafi momy yamma tayi saida safe"a sanyaye innah tace "d'an albarka Kenan Saida safe"kicibis yayi da takardar da yaseer yaba daddy wanda ta Fadi a kasa ya dauka ya zura a aljihu ya fice....
*******
Abraham cikin dajinsu ya shiga ya tsaya tsakiyar bishiyoyi yayi ihuuuuuu da har saida dajin ya amsa ya mike yayi tsalle yana yawo a sararin samaniya yayi kuwwwa dajin gabaki daya ya sake amsawa mamah da zuhraliyya suke kalle kalle cikin tashin hankali suke waigen ta inda zai bullo zuhraliyya tace "maamah wanan yaya Abraham ne kuwwarsa ce kururuwarsa ce"zabariyya ta rugo da gudu bishiyar da suke tace "Abraham ke ihu cikin dajin nan tamkar yana cikin wani yanayi"cikin damuwa tayi maganar,
hawaye ke zubowa a idon Abraham Wanda suke rikidewa suke komawa jini hawaye yakeyi hade da majinu yaba gunji cikin kuka yakw fad'in "niba mugu bane niba azzalumi bane amma dik wanda yayi yunkurin rabani da husnah tabbas hukuncin da zan dauka akansa zai sai ya rinkamun kallon mugun aljani.....tayaya na shaku dake husnah a matsayinki na bil'adama ina tsananin kaunarki zaayi yinkurin rabani dake"hawaye ke gudu a fuskarsa suna komawa jini ya daga hannuwansa yayi ihu ya fadi kasa karar da yayi tasa dajin tasa dajin ya girgiza bishiyoyi suka shiga faduwa suna karewa iska hade da guguwa ke tashi dik aljanun dake dajin sun shiga rudani ganin Abraham zaune dirshan akan katon dutse yana kuka yana kiran sunan husnah.....narjisu ce ta fito ta gabansa tsaye tayi a gabansa rigarta har kasa ta rufe mata kafa gashin kanta ya bazu a bayanta data gaba ta dago kanta dake sunkuye wata irin dariya tayi tace "kad'an kenan daga halin bil'adama Abraham meyasa bazaka rungumi jinsinka karabu da itaba ko soyayyar dole ce?kana azabtuwa da soyayyarta?mu kuma muna azabtuwa da kaunarka?"wani irin kallo yayi mata wanda tasa habtar cikinta ta kad'a ya miko hannunsa zai damketa ta bace,
yar sandar dake hannunsa wadda yake busawa a hankali yana hawaye ya tuna runtse idanuwansa yayi take ya tuno da husnah lokacin da yake fita da ita saman dutse yanasa hannu cikin ruwa yana damko kifi yana gasawa yana bata,ya bude idanuwansa da duka sauya kala ya mike yana taku kafarsa kamar ta tsaga kasa haka ya tsaya akan dutse yana wata sarewa da sandar yana busawa yana hawaye....
kwance take kan gadonta tayi lamo ba barci takeyi ba sautin sarewar busarsa takeji a kunnenta ta zabura ta zauna tana kalle kallen cikin dakin bugun zucuyarta ne ya tsananta tasa hannu ta dafe kirjinta da yake bugawa kana iya kallon bugun zucuyarta ta zuro kafarta kasan gadon ta Diro waige waige takeyi tana jiyo saitin muryarsa yana busa yana hawaye durkushewa tayi akan gwiwarta ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi cikin rawar baki da zazzabi dake son lullubeta tace "Abraham kadaw....oooo natuba ina tsananin kaunarka nasaba dakai soyayyarka zata illatani kadawo tun numfashina bai daukeba karasani"shesshekar kukanta yana iya jiyo sautin kukanta tsayawa yayi da busar yana sauraren kukanta shima kukan yakeyi yana bukatar kasancewa da ita yanaso ya rungumeta yaji dunin jikinta yayi missing nonuwanta masu laushi da dadin tabawa ga wata matsananciyar shaawarta dake damunsa....
momy a hankali ta tako ta tsaya a kofar dakin husnah tana jiyo sautin kukanta tana Ambatar sunan Abraham cike da tashin hankali a kasa ta kwanta tana juyi minti minti takw mikewa ta shiga waige waige ko zata gansa....wani irin iska mai sanyin gaske yake kada husnah da Asuba ta muke ta runtse idanuwanta tana kallon window yadda yake kadawa gani takeyi kamar shine zaixo wajenta.....
yaseer juyi yayi akan gado idanuwansa a rufe amma fuskarsa cikin kwayar idanuwansa husnah yake gani yadda yaga rana haka yaga dare ya bude idanuwansa ana kiraye kirayen sallah asuba muneeba na kwance a kirjinsa ta baza gashinta har fuskarsa ya kauda gadhin ya tsura mata ido yadda take bacci yake kallo a zahiri kuwa hankakinsa da zuciyarsa na wajen waccen yarinyar yana shafa kan muneeba yana bubbuga bayanta cike da kulawa kansa na kallon ceiling lokaci guda ya tuno da fuskar nan tata mai ban tsoro ya runtse idanuwa dik motsinsa muneeba ba bacci takeyiba Allah Allah takeyi safiya tayi su fita cikin tashin hankali take bazata taba iya bacci ba dan tanaa gani kamar yaseer zai dawo hayyacinsa ya tuna da husnah gashi tayi masa karyar tanada ciki dole ta ziyarci wajen boka
******
hajiya rabi ce tsaye gaban daddy yana shirin fita hannunta rike da hularsa cikin kissa tace "nace kasamu karanta takardar da yaseer ya baka kuwa?"waige waige ya shigayi yace "au kinga jiya tsabar takaici bansan inda na jefa takardar nan ba wallahi"murmushin mugunta tayi tace "Tou ka tambayi zainab kila itama ya bata takardar saika karanta tata tunda taka ta bace ya jinjina mata kai ta durkusa ta mika masa hular tace "au inaso zan fita goggo batada lafiya zamuje nida muneeba mu dubota"daddy ya jinjina kai yace "yakamata dani zaaje"gaban hajiya rabi ya fadi tayaya daddy zaice dashi zaa itada zata ziyarci wajen boka yacev"amma akwai aikin da zanyi inaga yar tafiya ma zanyi gaskiya"murnushi hajiya rabi tayi tacw "har nasoma murnar zamu ka gaida goggo koda yake ba sai kajeba zan iya isar maka da sakonka"ya jinjina kai tace "allah ya tsare "ameen"ya fice dadi ya kasheta,
momy rike da plate na siyayyan kwai da doya da source na hanta da tea mai kauri tana lallabin husnah sam takicin abincin kallon bango kawai takeyi tana sauraren zuwan Abraham tayi missing dinsa sosai ta saba dashi shikadai ke debe mata kewa da soyayyarsa ga shaawarsa datakeji tarasa dalili ruwa kawai ke zuba yana jika mata pant momy kuwa tausayin husnah ne ya lullubeta batasan lokacin da ta soma hawaye ba,ta mike ta fice sukai kicibis da yaseer ya shigo,
Abraham ne ya bullo ta jikin bango jikinta ne ya bata ya shigo dakin saidai yaki bari tagansa yanaso yadan horata ne mikewa tayi tana jinjina kai "kazo Dan Allsh kana ina ka fito ina tsananin kewarka"murmushi yayi har yanzun cikin fushi yake ji tayi an rungumota ta baya ta waiga bataga kowaba bata ankara ba taji hannuwa cikin rigarta ana mulmula kan nonuwanta cike da kwarewa runtse idanuwanta tayi tana sauke numfashi.......
*LITTAFIN DUHU NA KUDI NE 300 ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI DIK WADDA TA KARANTAMUN BATA BIYABA ZATA BIYANI HAKKINA RANAN DA BATADASHI*
TURA KUDINKI 300 TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK
SHAIDAR BIYA TA WANAN NUMBER 08036953516 KO KATIN MTN TA NUMBER
*SLIMZY*✍🏻
22
runtse idanuwanta tayi wasu hawaye masu zafi ke zubowa ta dago hannunta tana kokarin d'orawa akan hannunsa taji ya cire hannun daga kirjinta ya janye jikinsa ta waiga bataga kowa ba ta mike tana magana cikin sanyin murya "kadawo gareni nayi kewarka awanni shida da suka shude kamar shekara shida da wata shida nayi na rashinka Abraham"bakinta ke rawa tana maganar jingina yayi a jikin bango yana kallonta ko kifta ido batayi waige waige kawai takeyi tanaji a jikinta yana cikin d'akin Amma fushi yakeyi da ita ta dafe kanta kamar zararriya tace cikin tsawa "wai ya kakeso inyi ne?meyasa zakayimun haka baayi maka laifi a baka hakuri Dan Allah ka fito idanuwana suyi tozali dakai ko zan samu sassaci. rad'adin da nakeji a zuciyata"ta share hawayenta tana saurarawa ko zaiyi magana,
yaseer da sukai kicibis da momy kuwa muryar husnah yaji ta daki dodon kunnuwansa ya saurara da kyau murya mai tsananin dad'i yaji tamkar tana busar sarewa wanan muryar yakanyi mafarki da ita sanan yaso yasan mai irin muryar nan a yarinta gashi yazo ne yaga yadda ta kwana yace "momy ya naganki da plate din abincin kin fito kina kuka?ita yarinyar bata karba taci bane?"momy ta girgiza kai tace "bata karba ba tayaya zata karba bayan ta kwana tunanin aljani?ta kwana kuka saboda tsananin soyayyar da takewa mutumin da ba halittarsu daya ba"shiru yaseer yayi tsuntar kansa yayi cikin tsananin faduwar gaba baisan