Showing 60001 words to 63000 words out of 103127 words
ta razana husnah ta kwalla kara ta fadi sumammiya....
*****
muneeba kwance tana sauke numfashi zazzabi ya rufeta tsananin kishi da damuwa yasa ciwon gaske ya kamata yaseer cikin sassarfa ya shigo dakin da sallamarsa ummah ya gani zaune tana rike da hannun muneeba sai Anty sadiya data jefesa da wani mugun kallo ya karasa yana fadin "muneeba sannu meyasameki ummah meke faruwa?"hawaye ne kebin fuskar muneeba tana kallonsa cikin tuhuma gashin kansa ta kalla taji gabanta ya fadi ta mike zumbur ta zauna ummah ta rukota ganin yadda tayi "sannu muneeba sannu kinji?"Yaser jiki a sanyaye yake kallonta ta fita hayyacinta yace "shirya mutafi asibiti"ta fashe da kuka hajiya rabi da sadiya suka fice a dakin yana kokarin riketa cikin tausayawa tace "kada katabani nidai karka tabani"ta kwalla kara yaji tsoro kardai itama ta kamu da aljanun.....
a wahalce Abraham ya warware daga daurin da babansa yayi masa tare da taimakon zabariyya wadda ta kasa jure ganinsa a daure tsananin kaunar da take masa.....
*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFEBA*
08036953516
07042277401
*SLIMZY*✍🏻
35
Tallabo husnah momy tayi tace "mikomun ruwan gorarcan yusrah"da sauri yusrah ta dauka ta mikawa momy addua ta tofa ciki sanan ta guntsi ruwan a bakinta ta fesa mata a fuska wata wawuyar ajiyar zucuya husnah tayi ta bude idanuwanta tana binsu da kallo take ta tuno da abinda ta ganni ta kalli kujerar bataga kowa ba ta yunkura jikinta ciwo yakeyi mata momy ta d'agota zafi taji ya ziyarceta a kasanta momy ta tsura mata ido tana karantarta tace "husnah meyake damunki?kafarkice takeyi miki ciwo?"husnah ta girgiza kai take ta tuno da yaseer yadda ya cakud'ata daren jiya ruwa ne ya kawo a idanuwanta Momy ta taimaka mata ta zaunar da ita a kujera tace "fadamun meyake damunki?wanan aljanin yazo ne?"sunkuyar da kai husnah tayi hawaye na zubo mata hankalin hajiya saude yayi mugun tashi tace "kifadamun yaseer yayi miki wani abu ne?"gyada mata kai tayi momy ta soma tafa hannu ta kalli yan matanta biyu tace "kubani waje"suka bar wajen tace "yaseer ya taba jikinki ko?"ta jinjinawa momy kai ta fashe da kuka tace "nafada masa banaso kada yayimun shine yayi fushi ni kuma banason yayi fushi kinga yayi hatsari saboda ni"mommy ta jinjina kai tace "tabdijan lallai yaseer zanci ubansa a gidan nan wato ko kunyata baiji ba ya kusanceki? innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"husnah ta share hawayenta ta sunkuyar da kai momy ta matsa mata da plate din soyayyen dankali da kwai ta had'a mata tea mai zafi cike da tausayawa "ci abincinki kinji?kirabu dashi zaizo gidan nan ya sameni"husnah cakula abincin takeyi gaba daya hankalinta baya wajen ta juyo ta kalli plate din abincin wasu tsutsotsi ta gani cikin plate din manya manya suna yawo ta kalli cup din wani irin ruwa bakinkirin ne ciki ta kalli momy,"ci abincin mana husnah"girgiza kai husnah tayi tace "momy tsutsotsi ne gasu nan cikin kwanon bazan iyaci ba"momy ta kalli dankalin ta kalli kofin ruwan tea din"girgiza kai tayi ta mike tabar wajen inuwar mutum kawai ta gani a gabanta tana d'ago kai sukai ido hudu da Abraham zabura tayi ta mike wani irin kallo yakeyi mata wasu jijiyoyi ne koraye suka fito cikin idonsa wajen bakin idanuwansa ya koma mai ruwan toka farin kuma ya koma ja ta matukar tsorata momy ce ta dawo da karatun kurani yayiwa momy wani kallo ya bace,
a furgice Momy taga husnah tace "yadai husnah?"ta girgiza kai tace "momy banajin yunwa Bari inje wajensu yusrah kitchen na tayasu aiki"momy ta jinjina kai a hankali take taka kafarta ta girgiza kai kawai ta shiga laluben layin yaseer bata samesa ba dole zataje gidan su yau din nan....
*****
rungume muneeba yayi cikin sigar lallashi yace"kiyi shiru kiyi Hakuri nima bansan cewar hakan zai faru zam kwana can ba banje da niyyar kwana ba ankira malam ne mai bada magani shine na tsaya in shafawa husnah magani tunda ni mijinta ne"tana kokarin kurban ruwan tea batasam lokacin data furzar ba ta shiga tari sakamakon sarketa da yayi idanuwanta suka firfito ya rukota"lafiya?menene muneeba?"yake tambayarta cikin kulawa tace "yaseer ni yanzun kake fadawa cewa ka shafawa husnah magani?"wani kishi ne ya rufe mata idanuwa tace"kaje kaci amanata kenan?me kukayi daga shafa maganin?"cikin daga murya take masa magana abinda yaseer ya tsana kenan a rayuwarsa ya harzuka cikin bacin rai yace "kwanciya nayi da ita ko itadin ba matata bace?ko karuwa ce ita?"bude baki tayi tana kallonsa ta dafe kirjinta hawaye ya soma zuba a idanuwanta tace "yaseer ni kake fadawa ka kwanta da husnah?"
"na kwanta da ita me zakiyi?"yace yana kokarin mikewa ta rushe da kuka har ya kai kofa ya tsaya tausayinta yad'an kamasa dikda haushinta da yakeji ta yaya zata rinka challenging dinsa?yasan tana bashi tausayi saboda cikinsa da take dauke dashi ganin ya tsaya kawai ta soma wani irin tari tasa hannunta a wuyanta da sauri ya dawo cikin dakin "kingani ko?kinga abinda nake fada miki muneeba meyasa kikeso ki kashe kanki ne akan abinda Allah ya halarta?husnah fa matatacw kuma kece kika matsamun da bimcike yasa nafada miki abinda nafada miki har ya bata miki rai"ta sunkuyo kawai ta soma kwara amai a wajen ya dafe kansa daya dau zafi,ya furgar da iska mai zafi daga bakinsa ya dafe kansa ya runtse idonsa husnah ya tuno yadda ta mike tana d'ingisa kafa ko wani hali take ciki oho,tambayar da yayiwa kansa kenan sam bayason nisa da ita matsowa yayi ya zubawa muneeba ido yadda take kwara amai tana gamawa ta durkushe ta soma myrkususun ciwon ciki hankalin yaseer yayi mugun tashi nan ya tube rigarsa kasantuwar weekend ne ba aiki ya soma gyara wajen sanan ya dawo ya ciccibeta ya nufi toilet da ita da kansa ya tube mata kayan jikinta ta faki idonsa tayi murmushi dikda tsananin kishin dake cin ta tayi hakan ne dan ta d'aga masa hankali tsuru yayi da ido yana kallonta fuskarta ce take masa gizo tana komawa husnah yasan ba husnah bace tsabar tunanin husnah da yakeyi ne ya janyo hakan ko taci abinci ma bai saniba yayi mata wanka ya fito da ita ya nad'eta a towel sanan yana kokarin fita cikin murya mai tsananin Jin jiki tace "sweetheart karka tafi kabarni nasan nibaka sona dama husnah kakeso"cak ya tsaya badan ransa yaso ba ya dawo cikin dakin ya zauna gefen gado ya cije lebe yana kallon kiran momy ya kasa dauka tsoron me zata fada masa yakeyi haka kawai yake jin kansa cikin fad'uwar gaba....
******
daga kitchen ta fito tana jin fitsari nusrah tace "Anty husnah ina zakijene naga har yanzun kina dingisa kafa"murmushi tayi "fitsari nakeji nusrah yanzun zan dawo ai naji sauki"ta fito daga kitchen din yusrah na ganin ta fita ta matso kusa da yar uwarta tace "nifa a tsorace nake da Antu husnah gani nakeyi kamar ba ita bace kinsan aljanun nan"nusrah tayi ajiyar zuciya tace "haka ne amma fa yau kam tabbas itace saidai alamunta sum nuna tana cikin damuwa"suka girgiza kai dukkansu suka cigaba da aikinsu,
tana shiga dakin kofa ta rufe cikin sauri take kokarin shiga toilet din taga mutum kwance kan gadonta ta murza idonta "wanene waye wanan kwance akan gado na"a sanyaye tayi maganar d'agowa yayi daga kwanciyar da yayi kafin kiftawar ido har ta gansa a gabansa cikin fargaba da faduwar gaba take kallonsa ta tsaresa da Ido shima ita yake kallo saidai baizo mata a kamar ban tsoroba a kammanninsa ta gansa fad'awa jikinsa tayi ya tureta gefe tsananin tausayinsa yasa batasan lokacin data fada jikinsa ba kallomsa takeyi cikin tsananin mamaki ya girgiza kai ya cije baki fuskarsa tayi bakin kirin yace"Babu sauran soyayyarki a cikin zuciyata husnah"dam gabanta ya fadi tayi masa wani kallo ta kauda kanta gefe bugun zucuyarta ya tsananta yace"kinci amanata husnah dama ku bil'adama haka kuke amma zan koya miki hankali zakisan kin cutar dani husnah inaji ina gani jiya kika mikawa d'an uwanki bil'adama jikinki ya kwanta dake lokacin da kike tsananin kaunata kin mance yadda naso in kusanceki kika hanani?"hawaye ke zubowa a idanuwansa yana kallonta jikinta a sanyaye momy ta turo kofar ta shigo ganinta tsaye cak yasa tace"lafiya?"girgiza kai tayi bata gansa ba yana cikin dakin kuma cikin jin haushinta yake kawai ya shige jikinta, momy tace "husnah zan fita zani gidansu innah daga nan zan wuce gidanku can akwai maganar da zamuyi"jinjinawa momy kai kawai akayi ta fice dikda jikinta bai bataba tasan wanan ba husnah bace saidai ta kasa gasgata hakan tana fita ya fita daga jikin husnah dakin ne ya shiga jujjuya mata cikin minti biyar kawai taga ko ina ya zama kogi ruwa nayo kanta ta fito aguje nusrah tana kokarin riketa ta bankadeta ta fadi kasa waje tayi tana gudu kamar zararriya nusrat ta window ta leka tana kwalawa mai gadi kira "karka bar Anty husnah ta fito"
Abraham harde hannuwansa yayi a kirjinsa daga gefe yana kallon yadda ta fita a hayyacinta tsananin tsoro da furgici ta kalli gidan sauyawa gidan ya shigayi wasu dogayen bishiyoyi take ganinta wajen,yacev"husnah saina koya miki hankali sai kinsan baacin amanar aljani sanan wanan abun dake cikin mararki saina rabaki dashi"yana kallonta cike da tsana,
maigadi yace"ina zakije husnah?"fuskar mai gadin ce ta koma mata Abraham fadi takeyi "nidai karabu dani kabarni in fita karka sake maidani duniyar Aljanu kaji ina tsananin sonka bazan iya rayuwa dakai ba jinsin mu daya ba kalli yadda muke cikin daji nida kai ka maidani wajensu momy"sakin baki mai gadi yayi yana kallonta yusrah kuka takeyi ta kasa matsawa wajen husnah wadda ta runtse idi ihu kawai takeyi tana fuzge fuzgen zata gudu....
*****
muneeba kwance a kirjin yaseer yana wasa da gashin kanta tunanin husnah yakeyi inama itace haka ta saki jiki dashi suyi soyayya? yana tsananin son matarsa tunowa da daren jiya yasa yayi wata ajiyar zucuya hade da murmushi dago kai muneeba tayi ta zura masa ido baima san tana kallonsa ba wayarsa ce ta shiga ruri tunanin ko momyce yakeyi yana kokarin tashi muneeba ta rungumesa sosai batasi yabarta yadan matsa yace"wayata kw ringing bari in duba"tadan matsa ranta a bace tana kallomsa ganin number yusrah yasa yayi saurin dauka yace"hello?"kafin yusrah tayi magana yaji ihun husnah da sambatun da takeyi taba fad'in ni bazan zauna a dajin nan ba ku kyaleni"cikin rudewa yusrah tace "yaya yaseer kazo kuzo Anty husnah ce momy kuma ta fita bata nan gashinan zata fita tabar gidan"innahlillahi wa innahilaihi rajiun ya furta a zucuyarsa yace "gani nan zuwa kada kubari ta fita kiyi magana da malam shuaibu mai gadi"ya dire wayar ya ture muneeba ko ganin gabansa beyi ya zura rigarsa ya fice muneeba wata Ashar tayi tace "wato dole ma ta mike tsaye akan yarinyar nan yanzun suna soyayyarsu itada mijinta tana cikin nishadi shine zaa kirashi yaje batada lafiya?aljanu karyar banza ta duro Daga gadon yau bazaa kwana ba gidan boka zataje kota halin yaya...
*****
cikin farin ciki ummah hadiza ke magana da hajiya saude tana fuskantar innah "tabbas wanan shawara ce kika kawo hajiya saude kawai ayi tarewar yaseer da husnah su tare a gidansu inyaso maganar magani wanan ba matsala bane ni zan koma gidan da zama kawai tare da nusrah ko yusrah harta rabu da aljanin"momy ta jinnina kai cike da gamsuwa tace "bazan lamumcu iskancin banza ba kar qzo ayi ciki a gida na daga nan can gidan nasu zani insamu zainab akan maganar nan nasan batada matsala zata amince"innah washe baki kawai takeyi tanacin doya da miya suka cigaba da tattaunawa
*****
dik yadda yaseer yaso ya gane hanyar gidansu ya kasa cikin mota yake dik kwanar da yayi sai yaga wajen sai fili ko bushiyoyi ya dimauce cikin tashin hankali yake"fitowa yayi daga motar kawai yana kallon gabas da yamma kudu da arewa kansa juyewa yayi besan inda zaibi ba ganin bishiyoyi na zagayesa yayi kawai..... Abraham ne ya fito masa yana dariya "kaji dadin kwanciya da matar aljan ko?har kayi nasarar yi mata ciki amma ka kwanta da ita na karshe nine zan zama gurbinka a wajen danginka da matarka da ita husnah bazasu sake ganinka ba"yana gama magana ya daga hannunsa wata igiya ya gani hannunsa yana jujjuyawa zai bude baki yayi addua ya kasa sakamakon harshensa daya cika bakinsa sai dariya da Abraham yake masa cike dav tsana.....
*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFE BA*
08036953516
07042277401
*SLIMZY*✍🏻
36
Rungumar yaseer Abraham yayi suka bace cikin minti biyu ya gansa cikin wasu bishiyoyi masu tsawo da tsananin DUHU kalle kalle yaseeer yakeyi cike da tsoro kukan tsuntsaye ne kawai yakeji a wajen Abraham cikin kakkausar murya yace "a nan zakayi rayuwa yaseee kayi kuskuren shiga gonata kayi kuskuren son matata kayi kuskuren kusantarta"yaseeer ya runtse ido gumi kawai ke karyo masa yayi yunkurin taka kafarsa ya kasa dariya Abraham yayi yace "kasan inane nan?"yaseer ya kallesa yace"nan ba duniyar mutane bace duniyar Aljanu ce babu wanda zaisan inda kake yaseer har sai na kare rayuwata da husnah dikda babu d'igon sonta a zucuyata sakamakon butulcemun da tayi"yana gama magana ya warware igiyar dake lilo a hannunsa ya cillata sama tayi kololuwa sanan ta dawo ta zarge yaseer tayi sama dashi cikin bishiyoyi can sama haka igiyar ke nad'esa tun daga farko har karshe zuhraliyya ce tazo Abraham yace"ki kula dashi na damka miki shi a hannunki karki bari ya kwance karki bari kowa ya cutar dashi"ta gyadawa Abraham kai tana kallon yaseer can sama sanan ta kalli Abraham tayi ajiyar zuciya tace"yaya Abraham ina gudun narjisu tasan cewar wanan bil'adamar yana nan kasan ta fini karfi zata iyayin komi dan ta lalata maka abunda ka shirya"ya girgiza kai yace"itama zanyi farautarta zan kawar da ita koni ko ita"..motsu mutsu yaseee ya shigayi daga inda yake cikin tsananin tashin hankaki Abraham ya mike sosai ya kara tsayi yakai inda yaseer yake a kulle ya bude hannuwansa husnah ya gani ta had'a kai da gwiwa su nusrah zagaye da ita da malam shuaibu mai gadi sunayi mata magiya tankar zararra haka take zabura zata fita,wasu hawaye masu zafi suka fito daga idon yaseer tausayi da tsananin soyayyar husnah yakeji yana kara shiga jijiyoyin jikinsa runtse idanuwansa yayi take ya tuno da yadda jiya take hawaye lokacin da ya hau kanta waigowa yayi bega yaseer da zuhraliyya ba ya kalli bishiyoyin dake zagaye dadhi yau shine a wata duniyar ba duniyar mutane ba?yau shine a duniyar aljanu?dama cikin wanan kurgumin dajin husnah tayi rayuwa?wasu hawayen ke kara gudu a fuskarsa wani hali husnah take ciki?shine abinda ke damunsa....
*****
yusrah na rike da husnah sukaji mota a kofar gida da sauri nusrah ta zabura "yauwa malam shuaibu gama yaya yaseer din nan ya iso inata kiran momy bata dauka"juyawa yayi ya bude gate Abraham ne cikin motar yaseer sak yaseer babu banbanci yayi parking motar ko karasa rufe kofa Abraham beyiba ya fito cikin dimuwa yana fad'in "menene yasameta?meyafaru ina momy"be jira mai zasuce ba ya dauki husnah tana shusshura kafafuwa yana fad'in "mu shiga cike har yaushe zaku barta a nan ranan na kod'arta "cewar Abraham yana kokarin Shiga kofar parlorn,sautin karatun kurani ne ya gauraye kunnensa kallon speaker yayi sai kittrt ta kashe kanta daidai nan suka shigo a tare dukkansu a tsorace suke ga tsananin tausayin husnah da sukeji yana kokarin kwantar da ita a kujera yaji yusrah na dakatar dashi "yaya yaseer aida ka shiga da ita ciki kawai inyaso sai asa mata karatun kuranin kafin momy ta dawo nasan idan tadawo zaa kira malam"ya jinjina kai cike da gamsuwa ya runtumeta a kirjinsa wani irin bugun zuciya yakeji kirjinsa nayi dikda yadda yakejin haushinta da yadda ya d'aura dammarar koya mata hankali ya kalli fuskarta harta dan rame yayi shiru ya d'ago kai yaga suna kallonsa yace"husnah tabani tausayi sosai nusrah"suma jinjina kai sukayi cike da alhini yusrah tace "don ma bakaga yadda ta fito kamar mahaukaciya ba tun dazun idanuwanta suke a rufe taki budewa wai adaji take"Abraham ya cije lebe ya nufi dakinta da ita ajiyar zuciya dukkansu suka sauke tare da hamdala yadda yaya yaseer ya iso gidan da wuri da basusan yadda zasuyi da husnah ba....yana shiga ya turo kofar dakin ya rufe ruf ya kwantar da ita a kan gado juyi tayi tana bude idanuwanta a hankali ta saukesu akan Abraham take fuskarsa ta sauya ta koma Abraham daga ysseer murmushi yayi mata,ta ja baya ta manne da jikin allon gado "kina mamaki ko?ba mijinki wanda kikaci amanata bane nine dai mijinki aljani wanda kika tsana kike kirana da dodo wanda kikaci Amana kuma a haka zanyi rayuwa dake a matsayin yaseer batare da kowa ya gane hakan ba husnah saboda har yanzun akwai sauran guggubin soyayyata a zuciyarki kina wayancewa ne kawai amma nine masoyinki na asali wato aljaninAbraham"dam gabanta ya fad'i jikinta ya hau tsuma ta had'iyi wani miyau mai kauri tana bin dakin da kallo,shima kallon dakin yayi wani abu ya fito daga idanuwansa take kayan dakin suka sauya zuwa dakinta na duniyar aljanu,ta dafe kunnuwanta zatayi kara da sauri ya toshe bakinta "koda yake bari na kyaleki ko kinyi kara babu wanda zaijiki cikin gidan nan husnah kina tunanin zaki rabu dani ta dadi?kinsan wahalar Danasha da yadda nabi kafin na saceki?ko kinsan tunda aka haifeki kikazo duniya nake zuwa shimfidarki inyi wasa dake a jarinta?lokacin da momynki take ajiyeki tabarki ta tafi aikinta,lokacin da take kwantar dake goshin magriba batare da tayi miki addua ba batadamu dakeba sam sam,ina zuwa cikin gidanku inyi shawagi a hakan nakamu da tsananin kaunarki nike kula dake dik lokacin da miyagun aljanu zasuzo su saki kuka nike lallashinki"kallonsa takeyi ido cikin ido hawaye na bin fuskarta,kwankwasa kofar akayi da sauri ya juya lokaci daya ya koma yaseer yace"waye?"
"nice nusrah yaya dama nace munyi kokarin mu saka karatun kurani kamar yadda momy tace mun gagara shine nace ko zaka taimaka mana yayi'kallonsa husnah kawai takeyi yace"tasamu bacci kubari kawai kuyi kokarin yin abinci kafin momy tadawo"nusrah tace "toh yaya"ta juya ta jikin kofar yake kallon nusrah ya jinnina kai,
wani fitsari husnah taji ganin yadda yayi