Showing 72001 words to 75000 words out of 103127 words
masa ya cire rai da zai kara dawowa wanan duniyar kallonta yakeyi tana bacewa a hankali a hankaki harta gama bacewa ya kalli gate din gidan wato gidan momynsa ta kawosa yayi murmushi lallai a aljanu ma akwai na kirki kallon jikinsa yakeyi yadda rigarsa tayi kaca kaca ya shiga buga kofar gidan.....
tafe suke a mota suna hanyar dawowa husnah ta kalli madubin glass na gaba ba fuskar yaseer bace ainihin fuskarsa ce ta taba yusrah dake gefenta ta nuna mata wani irin razana yusrah tayi take ta sume a jikin kujerar.....
*DUHU...WANAN LITAFIN NA KUDI NE 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFEBA*
07042277401
08036953516
*SLIMZY*✍🏻
40
tun daga kofar gate ta ke jiyo muryar daddy cikin gidan hakan yasa ummah hadiza ta shiryawa dik wani makirci da hajiya rabi zata kulla da sallamarta ta shiga yana tsaye hajiya rabi na rusa kuka tana sharar hawaye cike da kissa wani kallo Alhaji badamasi ya watsawa ummah hadiza yace "dama iskancin daya kawoki gidana Kenan?abinda kuke kullawa dik be ishekuba har sai kun hada ma hajiya rabi da duka?"kallon hajiya rabi ummah hadiza tayi tace "amma yaya ta..."tsawa daddy ya daka mata tayi shiru yace "tou Bari kiji dik abinda kukeyi kuna ganin bansaniba ko nasani tsaf kuma wanan da kuke ganin na aura babu Wanda ya isa ya rabani da ita dan haka a matsayinta na matar yayanki ki tsugunna har kas ki bata hakuri"cikin tsawa daddy yake bawa ummah hadiza umarni ta girgiza kai tace "ke rabi wallahi baki isa na tsugunna na baki hakuri ba kinyi kadan koda kike matar yayana ai na girmeki ko ban girmeki ba bokanki beyi nasara akainaba"ta watsa mata harara daddy ya daga hannu ya zabgawa ummah hadiza mari "a gaban nawa ma kin sake maimaitawa?ya tabbata sharrin da kuka kulla mata gaskiya ne Kenan hardake idan zainab tayi ai ita kishiyarta ce kedin kishiyarta ce?"ummah hadiza ta dafe kumatunta tana kallon hajiya rabi idanuwa jajir cike da takaici take kallonta "kuma ki ficemun daga gida inhar bazaki daraja matata ba karki sake zuwa inda nake kinji nafada miki"hajiya zainab hawaye ne ya wanke mata fuska kallon yadda daddy yake ciwa ummah hadiza mutunci sabida hajiya rabi yasa kai yabarsu tsaye cike da haushi,.....ummah hadiza ta girgiza kai tana kallon hajiya rabi cikin takaici da tsana tace "yau kinsa d'an uwana ya mareni ko?"hajiya rabi tayi juyi tace "kwarai dagaske kuwa ninafi karfin in mareko da hannuna saidai insaka wanki ya mareki kuma burina ya cika babban burina ma ya sake cika tunda ya haramta miki zuwa gidan"wata yar kwalla ce ta cicciko a idon ummah hadiza,momy ta rukota "kiyi hakuri hadiza ninaja miki dik abinda dan uwanki yayi miki sanadina ne kika mareta amma ki kwantar da hankalinki Allah Baya bacci"ummah hadiza ta jinjina kai tace "karki damu zainab ta tsokalowa kanta tsuliyar dodo ne sai tayi danasanin saka d'an uwana ya mareni a kumatuna yadda ya mareni a kumatuna nayi miki alkawarin sai ya mareki nan bada jimawa ba dan nida kike ganina bakisan ko waceceni ba ko?fada da aljani babu dadi anzo inda nakeso amma sai na tabbatar da na rama abinda kikaimun sai nayi sanadin da kikabar gidan nan tare da tonuwar asirinki sai alhaji badamasi ya dakeki a tsakiyar titi a gaban kowa"hajiya rabi kallon ummah hadiza takeyi shekeke kamar zautacciya rike da kumatunta tayi wata dariya,
"wanan dariyar sai ta zame miki kuka yan uwanki da kika kora kika gujesu saboda talakawa ne su zaki koma wajensu ki kwashi kashinki a hannu"hajiya rabi cikin zuciyarta wani tsoro ne ya kamata kallon yadda idanuwan ummah hadiza sukai jajir tayi ta kasa magana,muneeba ce ta fito daga sashenta taci kwalliya ta saka doguwar rigar abaya baka cikinta ya fito sosai yayi girma tana rike da kwankwaso daya hannunta rike da wayarta tana dannawa tana ganinsu ta sake canja tafiya tana yauki cike da yanga da kwarkwasa ta karaso wajen ta kalli ummah hadiza ta watsar sanan ta dubi hajiya rabi tace "meke faruwa a nan?kukai cirko curko kamar anyi mutuwa ummah?ko ana jimamin cusawa yaya yaseer matar aljan ne?"ta danyi dariya hajiya rabi ta sheke da dariya ummah hadiza tayi kwafa ta galla mata harara tace "ke kumafa?hardasu kaza acin danko an fada miki inba rashin husnah ba ke ance miki ko kallo kin ishi yaseer ne?me zaiyi dake?ina zai kaiki bayan ga wadda zuciyarsa ke mararinso da muradi?"muneeba ranta ya baci ta tabe baki zatayi magana hajiya rabi ta dakatar da ita tace "aiko soyayya ta kare akan muneeba tinda ga dansa nan a cikin muneeba yana girma idan baya sonta bazai bude kafarta ya shigeta ba"muneeba ta shafa cikinta tana sake turoshi ummah hadiza a kufule tace "wanan cikin da kuke takama dashi insha Allah sai kunyi kuka da hawayenku sai ta haifo dan aljani idan har husnah matar aljan ce ke kuma uwar aljani zaki zama"
"aniyarki ta biki"ummahn muneeba tana ruko muneeba dake shirin watso rashin kunya nan suka soma hayaniya daddy ya fito yana ganin ummah hadiza ya zaburo"wai ba nace idan masifa ce zata kawoki gidana ki ficemun ba karki sake zuwa mai kike jira"ummah hadiza tace "ki jira ramuwar gayya kijira ranan da zaa koreki da kanyanki akai"momy ta ruko ummah hadiza cikin damuwa tace "kije wajen aikin nan da akasaki karki damu zan shigo nima idan nayi sallah"ta rukota tana kokarin fita da ita daddy ya daga murya "kema kidawo ki dibi kayanki ki bita ku zama kashin awaki"ummah hadiza ta fice momy ta shigo dakyar take taka kafarta tsabar bacin Rai hajiya rabi tace "anji kunya dai ana korar mutum yana likewa"kallonta momy kawai tayi ta dauke kai hajiya rabi ta ruko hannun muneeba sukai sashenta...
******
sautin bude kofar shiga parlor hajiya saude taji ta dauko kofin data hado tea ta fito da sauri turus ta ga yaseer tsaye taba binsa da kallo ta saki cup din hannunta cike da tashin hankaki bakinta na rawa tace "yaseer?inasu husnah?lafiya hatsari kukayi da kuka fita?"yaseer cikin rashin fahimta yake kallon momynsa hawayene suka soma zubowa daga idanuwansa ta d'ora hannu akai ta fashe da kuka "yaseer kayimun magana ina kannenka daka fita dasu da husnah da kukaje siyayya dazun?ina suke kunyi hatsari ko?aljanin ya sake saka hatsari kenan nafadawa husnah dama kaine ba Abraham ba sai tacemun wai bakai bane aljani ne"durkushewa Yasser yayi yana kukan bakin ciki wato mahaifiyarsa da matarsa da kannensa da aljani suke rayuwa basu saniba?kuka yakeyi ya kalli kayan jikinsa yadda suka fita hayyacinsu dakyar ya motsa bakinsa dake karkarwa kamar ana watsa masa ruwa yace "momy nine yaseeer wanda ya fita dasu husnah banibane aljani ne"dafe kirji momy tayi cikin tsananin tsoro tad'anja da baya tana kallonsa cike da tuhuma da furgici 'Aljani fa kace ban yarda dakai ba kaiba yaseer bane kazo ne kawai ka zautar dani kaine aljani"momy ta juya zata gudu yaseer ya rukota ta runtse idanuwanta gamm jikinta sai rawa yakeyi tana karanto adduoi yaseer ya tsareta da ido yadda take gumi ya tabbatar masa a furgice take sai adduoi momy ke zubowa ta saki wanan ta kama wanan cikin sanyin murya da dasasshiyar murya yace "ki bude idonki nine d'anki yaseer dik adduoin nan da kikayi nida aljani ne aida kin konani momy danki ne yaseer wanda ya dawo daga duniyar aljanu"ya fashe da kuka ya rike kafafuwanta,a sanyaye momy ta bude idanuwa ta tsura masa ido cikin ido kallonsa takeyi tanajin wani yanayi mai wuyar misaltuwa ta tsugunna ta ruko kafadarsa ta dagosa ta tsayar dashi ta kalli kwayar idonsa take ta tabbatar da d'anta yaseer ne tabbas yaserr din da suke gani a matsayin sa ba haka kwayar idonsa take ba ta fashe da kuka tace "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun wace irin masifa muke ciki?ace dama da aljani muke cudanya bamu saniba?yanzun gashi ya fita dasu husnah da su yusrah nashiga uku karya gudu dasu duniyar aljanu"hankalin yaserr ya tashi ya zube a kasa yana kuka kamar karamin yaro cikin damuwa momy kasa magana tayi takowa tayi ta karasa parlor ta zauna turus a kujera tana rera kuka.....
rungumo yusrah tayi jikinta ganin bata numfashi jikinta ya kama rawa ya kallesu ta jikin mirror yayi murmushi husnah ta watsa masa harara tace "mugu kawai"ya juyo ya kashe mata ido yace "nine mugu husnah ni mijin naki kike cewa mugu kanki daya kuwa?"nusrah dake gefensa zaune ta juyo ta kalli husnah dake rungume da yusrah ta kara kallonsu cikin mamaki "Anty husnah meyasamu yusrah?"ta jikin madubi ya kallesu husnah ta dago ido tayi tozali da yadda idanuwansa suke ta kalli nusrah ta girgiza Mata kai tace "bacci takeyi"tayi ajiyar zuciya gudu kawai yake shararawa Allah Allah yakeyi ya shiga ya saukesu sakamakon yasan akwai matsala ganin zuhraliyya na bin su suna tsayawa a kofar gidan husnah ta rasa ya zatayi cikin ikon Allah tana motsa yusrah ta zabura ta rubtse ido ta kwalla kara jikinta na rawa"Anty husnah a ina mukene?yana tare damu?"ta radawa yusrah a kunne"shhhhh ki daure kinji babu abinda zaiyi miki aibake yakeso ba bake ya biyo ba banaso ya Gane kinga halittarsa"gumi ke karyowa yusrah ta kasa Bude idonta a haka ta fito yace "yadai lafiya yusrah?"ta girgiza masa kai "zazzabi nakeji"
"zazzabi kuma?munfita lafiya kice kinajin zazzabi karmu shiga kisa momy taji haushina"ta kada kai kawai kirjinta bugawa kawai yakeyi,
ta jikin mirror momy ta hangoso suna kwaso kaya wani kulllll taji cikinta yayi mata ta kalli yaseer dake zaune zugum zatayi magana suka shigo a tare wani shock yan biyu sukayi suna kallon yaseer suna kallon Abraham babancinsu kayan jikinsu Abraham ya hadiyi wani miyau ya waske yace"momy wanan fa?karfa ki yarda aljani yazo ya yaudareki"jikin momy ya kama rawa ta kasa magana yusrah kuwa take kamanninsa ya dawo mata ta yanke jiki ta fadi yaseer ya zabura ya karasa yana girgiza ta Abraham yayi murnushi yana kallonsu momy yace "babu yadda zaayi d'an Adam ya kalli aljani ko yaya ne ya zauna lafiya inda a halittata gaba daya ta kalleni da na tabbatar saidai mudawo da gawarta,tare nake rayuwa daku bakusan wayeni ba toni aljani ne"zabura momy tayi ta ruga aguje tayi daki nusrah ta rufa mata baya suka rufe dakin gamm sai rawar jiki sukeyi,
mikewa yaseer yayi suna kallon kallo da Abraham murmushi yaseer yayi masa yace "muguntarka tana gab da zuwa karshe nayi maka alkawarin ni zan kasheka da hannuna"
"idan baka kasheni ba ni kuma zan cika maka alkawarinka in kasheka in dauke husnah mukoma wata duniyar mu rayu yare kamar yadda na rayu da ita"husnah hawaye takeyi cikin daki ta dauko kwalbar maganin da malam ya bata dana ruwan addua ta fito a hankali take takowa ta kalli maganin ta budesa daidai Abraham ya kwalalo ido waje yana kokarin zuba masa mugunta ta watsa masa akansa zuwa fuskarsa ya juyo da sauri fuskarsa tana hayaki yake kallonta idonsa suka canja kala suna yin wani ruwa mai kamar mai jikinta ya soma rawa taji tsoro ta yadda kwalbar maganin kasa ta fadi tasssss hayakin da taga yana tashi a jikinsa da yadda fuskarsa ke salewa yasa ta furgita yaseer ya fizgota jikinsa ya rungumeta yana kissing gefen fuskarta Abraham tsaye hayaki na fita akansa cikin minti biyar yake bacewa a hankali suka nemesa suka rasa ajiyar zuciya yaseer yayi ya sake hadata da kirjinsa yana sauke wani irin numfashi lafewa tayi sosaiba jikinsa kirjinta na harbawa ta rufe idonta yadda kansa ke hayaki take gani ta bude tana kwalla yaserr ya Rabata da jikinsa ya share mata hawaye a hankali "meyasa kike kuka?"girgiza kai tayi tadan ja da baya "bashi bane ya saceka?ya tafi dakai yake zuwa nan a matsayinka"jikin yaseer ya kama rawa "inji dai be tabaki ba beyi miki komiba husnah?husnah kifadamun be kwanta dakeba"ta girgiza kai ta cije lebe "bai kwanta daniba yaya yaserr nagano shi waye su momy ne basu saniba"momy daga cikin daki takejin muryarsu sama sama tadan bude a hankali karar bude dakin yasa suka waiga a tare momy ta leko dakai ta jike da gumi yaserr ya sauke numfashi yace"momy ki fito ya fita ya tafi"a sukwane Momy ta fito tana waige waige "ka tabbatq?ohh ni saudatu yau nice da aljani ido da ido?"ta karasa wajen yusrah da take juyi a kasan tiles taki bude idonta nusrah cikin dimuwa ganin halin da yar uwarta take,ta shiga jijiigata "ki tashi yussy ki tashi baya nan'girgiza mata kai tayi tace"zan iya tashi amma sam banason kara bude idona a rayuwa"momy hankalinta ya tashi ta kalli yaseer ta karasa ta dau wayarta ta shiga Kiran malam ta shaida masa halin da suke ciki tana bukatarsa da gaggawa,
"yaserr ka shiga dakin husnah kayi wanka ka sauya kayan jikinka idan malam yazo ya tafi saimu dunguma mutafi can gidan baban naku a sanar musu da komi daya faru ko?"ya jinjina mata kai ya juya zai tafi ya saci kallon husnah dake tsaye tsumu ya kashe mata ido yayi mata alamar ta biyosa,momy na kallonsu ta gefen ido ganin ta noke masa kafada yasa ta girgiza kai "husnah kije daki ki dan huta saiki jira yaseer ya fito ko ?"ta cije baki batason yiwa momy musu cike da kunyq ta juya tabi bayansa suka shiga dakin a tare suna shiga ya rufe kofa ya cire rigarsa ya zauna gefen gado ta tsurawa jikinsa ido gashin jikinsa a kwakkwance saidai dik yadanji ciwo tausayinsa ya kamata ta karaso ta zauna ta bayansa ta kwanto ta rungumosa yasa hannu yana shafa kanta "yadai husnah?menene?"cikin siririyar murya tace "bakomi"yayi murmushi hade da gyaran murya"yau a gidanmu zamu kwana ko?"ta noke taki magana dariya yayi kawai cikin damuwa tace "inajin tsoro"da sauri ya juya ya janyota jikinsa ya rungumeta yana kallon fuskarta "umhmm tsoron me kikeji?"
"Abraham kagafa abinda ya samesa ina gudun ya dawo ramako"murmushi yayi mata ya shafa kanta yayi kissing lips dinta "babu abinda zaiyi miki kinji Allah na tare damu ko?"ya shafa kanta "muje muyi wanka tare"tana kauda kai tana dariya ya ciccibeta ya zare rigar dake jikinta yayi toilet da ita tana dukansa a kirji
*****
"muneeba girman wanan cikin naki nifa yana bani tsoro"cewar hajiya rabi tana kallon muneeba wadda ke zaune ta mimmike kafa a dakin hajiya rabi,
"ummah tsoro kuma kika sani ko yan biyu ne?"
gauron numfashi hajiya rabi ta sauke tace "tou ina fatan biyun ne inaso dai aje asibiti a tabbatar da zaman cikin nan inaso ki haifowa yaseer kyakkyawan saurayi mai kamadashi"
kasa da murya muneeba tayi "momy amma fa kinsan dai yadda aka samu cikin"
"shhhh yo ai ya tabbatar mana da d'an na yaseeer ne koda ya kasance shi ya kwanta dake ai yasa miki dan ne daga jikin yaseee"murmushin farin ciki muneeba tayi tana shafa cikinta.....
*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFEBA*
07042277401
08036953516
*SLIMZY*✍🏻
41
rungume da husnah yaseer ya fito daga wanka ya kwantar da ita akan gado yace"karki taso ki jirani nine zam shiryaki da kaina kinji?"ta turo baki cike da shagwaba tana kokarin tashi yace"wai ba nace kada kitashi ba ki jirani nine nam zan shiryaki da kaina"husnah tayi murmushi ta koma ta kwanta ta lafe yana tsaye Gaban mirror ya shafa mai a wajen da turaren daya gani juyowa yayi yace "kigafa ba wani kaya gareni a nan ba"
"ga kaya nan kamar jallabiya naga an ajiye kam gado"kallon jallabiyar yayi hade da murmushi yace "momy kenan wanan jallabiyar tana ajiye da ita kenan gashi yau zan saka"ya dauka yasa tayi kuri tana kallonsa ta lula duniyar tunani,meyasa ta kasa daina tunaninsa?bayan har yanzun akwai soyayyarsa a zuciyarta?tunowa da yadda ta watsa masa ruwan magani tayi furgigit ta furgita ta tashi ta zauna kansa hayaki yakeyi yadda taga fuskarsa tayi hankalinta ya Tashi yana tsaye yana lura da yanayinta ya girgiza kai ya dauko man shafawa ya zare towel din daya nad'eta dashi tayi saurin kare kirjinta "ka rufeni nidai ka rufeni kunya nakeji'tace cike da Yanga yadda tayi da bakinta ya dauki hankalinsa yasa hannu ya cire hannunta daga kirjinta nonuwanta ya kalle dik sun tasa sun dan kumbura ya zaro ido waje yace"husnah?meyasameki?"da sauri ta bude ido tana kalle kalle ta kallesa bata ganeba yace "kalli yadda kirjinki suka cicciko suka kumbura"turo baki tayi ta kauda kai idonta suka ciko da hawaye "nima haka na gansu"ya jinjina kai zucuyarsa cike da furgici kardai aljanin nan yazo ya tattaba masa mata,tsaki yayi ya shafa mata man sanan ya dauko mai da akabata na magani ya shiga shafa mata take taji zucuyarta na Tashi warin turaren ya bugi hancinta ta soma yunkurin amai ya rukota "sannu sannu husnah sannu kinji menene meyasameki?"ta girgiza kai a wahale tace "amai nakeji amma ya kwanta"tausayinta ya kamasa kardai malaria ce ta kama husnah yasan akwai sauro kwanakin nan wardrobe ya bude ya ciro mata kaya ya mika mata ta karba tace "brezia ta"kauda kau yayi "bazakisa ba saboda dubi yadda suka kumbura haba meyasa zasuyimun hakan bayan yau zanyi wasa dasu"ta hararesa ta zura rigar ya kurawa yadda breast dinta suke a tsaitsaye kamar tasa brezia ya shagala da kallonta yaji knocking tsaki yayi "wanene?"
"momy tace ku shirya ku fito gaba daya ga malam yazo"ya girgiza kai ya rukota sai kafkaf yakeyi da husnah tana yatsina fuska ta yane kanta da gyalen abayar datasa suka fito fuskarta tayi wani iri momy ta tsareta da ido har suka shigo parlorn,
malam na rike da kan yusrah yana tofa mata addua a idonta suka zauna sai sambatu takeyi "yanzun malam zan daina ganinsa?"yusrah tace cikin damuwa,
"inshaaa Allahu zaki daina ganinsa dama bada nufi yaso kigansa ba kuma ba halittarsa gaba daya kika ganiba yanzun bude idonki kifadamun kina ganinsa?"a hankali yusrah ta bude idanuwanta da sukai jajir malam ya tsareta da ido "kina ganinsa?"
"bana ganinsa"tace tana girgiza kai,
"tou Alhamdulillah, hajiya yanzun abu nagaba shine yadda zaku tsaya ku jajirce musamman yaseer dan nasan tabbas wanan aljanin be tafi gaba daya ba zai dawo kuma dawowar da zaiyi bazaaji dadiba saidai idan har yaseer ya rike wuta sanan kamar yadda yayi alkawarin kashesa yadda kikace ya kashesa idan ba hakanba shi zai cika