Showing 36001 words to 39000 words out of 103127 words

Chapter 13 - DUHU Book Complete By Slimzy .txt

Slimzy   

19 Jun 2024

12521

banga takardar ba "hajiya saude ta kad'a kai tace "ya fadamun nima inaso asan inda takardar sakin take yadda zai yagata batare da kowa yasani ba"daddy ne ya shigo yace "aiko karya kukeyi naji tattaunawarku ashe gaskiya ne maganar da hajiya rabi ta fada saboda kinjini da mummunan kama kukace karya ne to tafadamun takardar sakin na hannun hafeez kuma na umarceshi da yazo da ita tare da magabatansa"gaban hajiya saude ya fadi ta ciro waya cikin sauri ta kira layin yaseer,


yana rungume da muneeba doctor ya tabbatar masa da tana dauke da ciki yana cikin farin ciki saidai dayan bangaren zuciyarsa bayaso ya rasa zukekiyar yarinyar nan gashi babban damuwansa yanda akayi idan yazo baya ganinta saidai yaga alamar tana wajen ana magana da ita, "hello momy"...yace cikin kosawa da rudewa tace"kazo kasameni a sashin momy"


"ok ok ganinan zuwa"ya gyara mata kwanciya ta ruko hannunsa cikin shagwaba zatayi magana yace "momy ce tazo take kirana"ta jinjina masa kai ya shafa gefen fuskarta ya fice yana fita muneeba ta mike ta zabura ta zauna ta leka ta window taga tafiyarsa cikin sauri jakarta ta bude ta ciro kwarya da maganin da boka ya bata akan ta fasa ta farraka tsakaninsa da husnah ta jinjina kai tace"idan kunsan wata bakusan wataba zan farraka tsakanin yaseer da husnah harabada saidai ta cigaba da rayuwa da wanan aljanin amma badai yaseer ba"cikin kishibta sa yadda boka yace ta shiga kitchen ta dauko tabarya bata ganiba tana shiga cikin store taga tabaryar ta fito mamaki ne ya kasheta ganin yadda maganin ya zube batare da antaba ba ta kalli cikin dakin bataga kowa ba waye ya kwance maganin a ledar ya zubar a kasa?tambayarr da tayiwa kanta kenan ta zauna gefen gado tana rike da tabarya kanta ya dau zafi ta dafe kanta wata dabara zatayi ta aiwatar da wanan abun?ajiyar zuciya ta sauke ummahnta zata kira suyi shawara ta jefar da tabaryar ta nufi parlor inda tasa wayarta a carji....


da baya da baya take tafiya cikin damuwa take yayi karo da ita gabansa ya fadi ya gabta tabbas itace amma meyasa dazun dayaje be ganta ba?cikin wata irin murya yace "husnah"damm gabanta ya fadi ta tsaya cakk jin muryar da aka kirata ta kasa juyowa shima ya kasa takawa ya tafi kusan seconda talatin sannan ta juyo sukai ido hudu wani Abu taji ya caki zuciyarta tayi saurin ja da baya ganin shine saidai ta kasa dauke idanuwanta daga garesa ya yafitota yace "zo nan"kasa musa masa tayi a hankaki take takowa yana kallon surar jikinta da Saida ya hadiyi wani miyau makwat ta karaso yace "ina zaki naganki a nan?me kikeyi zo muje cikin gida"ji yayi daga bayansa ance "ina ruwanka da wanda take tare dashi?nine nan take tare dani inace ka saketa?to meyafi saura?"juyawan da zaiyi yayi kicibis da hafeez wanda ba hafeez bane Abraham ne Abraham kallonsa yakeyi da mamakin yadda akayi ya iya ganin husnah a yanzun bayan abinda yasa mata a jikinta na bazai kara ganinta ba ya kalli fuskarsa take ya hango wani abu wanda ya tabbatar da narjisu ce itace ta karya masa wanan abin ya ciro takardar dayabi hafeez ya dauko ya nuna masa "gashi nan shedar saki dan haka ba sauran aure a tare da kai da ita"yaseer ya karanto ayatul kursiyyu cikin zafin nama ya tofa a fuskar hafeez wanda tuni ysseer ya gano ko waye yayi kara ya runtse idanuwansa ya saki takardar ya bace,


ajiyar zuciya yaseer yayi ya duka ya dauki takardar cike da tsananin farin ciki yasa hannu ya yayyagata husnah kuwa tsoro ne ya kamata dan tasan Abraham ne wanan ita baa hafeez take ganinsa ba tace "meye ka tofa masa a ido kagani yatafi ka kashe masa ido ko?"ya girgiza mata kai yace "ban kashe masa ido ba kinji zo muje"ya ruko hannunta suna tafiya a tare yana juyowa yana kallonta itama juyowa tayi taga ita yake kallo ta sunkuyar da kanta kasa narjisu ce ta shige jikinta suka Shiga a tare Turus daddy yayi ganinsu Tare da husnah sum shigo kallom juna momy da hajiya zainab sukayi cikin farin ciki daddy yace 'ke husnah ina kikaje daga ina kike?"ta kalli yaseer tayi murmushi tace "muna tare da yaya yaseer ne tun dazun daddy"mamaki ne ya kashe yaseer jikinsa na rawa yace "eh eh muna tare daddy naganta a wajene shine muke magana na shigo da ita"hajiya saude tace "da kyau dama abinda ya kawoni shine in sanar dakai innah daga gidanta nake akan maganar yaseer da husnah cewae ranan jumaa zaa maida aurensu"murmushi yaseer yayi cikin tsananin farin ciki ya kalli husnah ta sakar masa murmushi dik abin nan da akeyi momy na kallon kwayar idanuwan husnah tasan ba ita bace ba haka kwayar idonta take ba saidai bazatayi magana ba dan tanaso ko hajiya rabi zata mutu a maida aurensu,ta daddy cikin fushi yace "Tou yw zanyi da mutanen hafeez da nace su turo sanan nace hafeez ya tahomin da takardar sakin inga hand writing din yaseer in tabbatar da hakan saboda gaskiya bazan amince da hakan ba dan hajiya rabi ta sanarmun muneeba na dauke da ciki haka?"daddy ya tambayi yaseer ya fadada murmushi ya sunkuyar da kansa yace "haka ne daddy na kira doctor ma dazun ya dubata yanzun haka na barota tadan kwanta ne"daddy farin ciki ya cikasa hajiya saude murmushi tayi ta kauda kai tace "Allah ya inganta"husnah ta wuce su ta shige daki yaseer ya bita da kallo yana kokarin mata magana daddy yace "ka koma kaje ka kula da matarka tunda batada lafiya yanzun dai gobe ko jibi zanga hafeez zan tabbatar da hakan ingaskiya ne"yaseer ya jinjina kai daddy na fita ya zauna kujera ya dafe kai momy tace "yadai yaseer?"ya kada kai ya basu labarin yadda sukayi da husnah da aljaninta a waje momy tace "da kyau gara da kayi hakan kada ka kuskura ka rinkajin tsoronsa"yaseer yace"wata aljana dazun tazomin wai narjisu"hajiya saude ta dafe kirji tace "nashiga uku gida ya zama na aljanu kai kuma? innahlillahi wa innah ilaihi rajiun "yaseer yayi murmushin karfin hali yace "ki kwantar da hankakinki"ya kwshe komi ya fada musu cikin alajabi dik sukai shiru suna mamakin wanan masifa,


******
husnah zama tayi a kasa warwas tana mamakin yaushe ta shigo dakin ta ina?waye ya kawota tambayar da tayiwa kanta kenan Abraham ya bullo ta jikin bango tana ganin idanuwansa da fatar idonsa ta tsorata yadda idanuwansa ya sale ta mike jikinta sai rawa yakeyi ta kasa magana yace "kinga abinda dan uwanki yayimun ko?yana shirin kwaceko daga wajena ko?hmmm yana shirin haka rami ya birne kansa da kansa Kenan "cikin rashin fahimta take kallonsa tausayinsa ya kamata wata tsanar yaseer taji ya dira a zuciyarta tace"yaseer ne yayi maka haka ko?ka kwantar da hankalinka nima zan rama maka saina konasa da hannuna"cikin fushi take maganar Abraham yayi murmushin jin dadi yace "kin tabbatar da hakan?"ta gyada masa kai tana ruko hannunsa suka kwanta kan gado tana kallon fuskarsa tana shafawa a hankali a hankali ya runtse idanuwansa ta shafa cikinsa tace"kana jin yunwa ko?"ya bude ido sa da sukai jajir tsabar azaba yace"idan ina tare dake banajin yunwa bana jin kishin ruwa"yana kokarin janyota ya rungumeta tace"bari in zubo mana abinci inajin yunwa"ya zauna yace "karkije nine zani in zubo idan kika fita bazaa barki ki shigo daki ke kadai ba"ta jinjina masa kai tana murmushi ya mike ya fito ya wuce su momy a parlor yana shiga kitchen ya tarar da hajiya rabi tana barbada magani a abinci harde hannuwansa yayi yana kallonta lallai wanan bil'adamar yace a ransa amma zanyi maganinta rikida yayi ya koma lafcecen kadangare jangwalagwada kansa har sheki yakeyi......




*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 NE KACAL MAI BUKATA YA TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN....


07042277401
08036953516




DIK WADDA TA KARANTAMUN LITTAFI BATA BIYABA ALLAH YA ISA!!!!






*SLIMZY*✍🏻




25


d'ago kai hajiya rabi tayi sukai ido hudu da lafcecen kadangare jangwalagwada kansa har sheki yakeyi ta dauki muciya tace "wad'anan masu aikin anyi yan iska wato kitchen din suka bari a bude shine kadangaru suka shigo ji wani kadangare sai kace ba kadangareba kosasshe yayi girma"tayi kan kadangaren ta d'aga hannu zata kwada taji kamar an fuzge muciyar anyi jifa da ita tayi saurin zatayi wajen muciyar kawai taga muciyar na matsawa ta murza idanuwanta ta kara matsawa taga muciyar ta matsa jifa tayi da kyalen dake hannunta na magani ta kwarma ihu sam babu mai jinta yayo kanta kadangaren aguje tayi jikin bango ta hade hannuwanta biyu cikin magiya ta soma rokonsa "Dan Allah kayi hakuri nasan kaiba kadangare bane na tuba Dan Allah"hannuwanta sai rawa yakeyi gumi kuwa ta jike kashirban tana rokonsa ya bude bakinsa ya zaro harshensa taga yadda harshensa yake kawai taga ya bace ta wawwaiga bataga kowa ba ta dafe kirjinta tana sauke numfashi mararta cike da fitsari ta tsugunna zata dauki kyallen maganin daga bayanta taji ance "ban tafi ba ina nan me zakayi dashi?zakiyi cuta ko?"a hankali ta shiga juyowa bataga kowa ba yace"gani nan a bayanki juyo ki ganni mana"girgiza kai hajiya rabi tayi jikinta kamar an zuba Mata shicking tace "umm umm umm umm ba saina juyi ba"yace "saifa kin juyo idan baki juyo ba tam"da sauri ta juya tayi tozali da inuwarsa jikin bango zabgegen namiji ta gani mai masifar tsawo da jiki ta zube a kasa tana murza kafafuwa yacev"au ihu zakiyimun?"ta kada kai tasa hannu ta kama bakinta gani tayi yana tahowa tuni ta saki fitsari Nabin kafarta,


husnah fitowa tayi daga daki zata wuce momy tace "ina zakije?banaso ki shiga kitchen din nan kibari idan hajiya rabi tagama ta fito sai ki shiga"hajiya saude tace "mutum da gidan ubansa ace bazai shiga ba kikasani ko yunwa takeji?"husnah tayi fuskar tausayi ta rike cikinta tace "yunwa nakeji momy "hankakin momy be kwanta da shigar husnah kitchen babbabu yadda ta iya ta barta ta nufi kitchen din har tana tuntube garin sauri tana shiga taga hajiya rabi baje a kasa ta d'aga kai tayi tozali da Abraham yana tsaye yana murmushi ta dafe kirji tace "har naji dadi nadauka katafi ne ai daga zuwa Dibo abincu"cikin sigar shagwaba tayi maganar hajiya rabi da ta jike sharkaf da gumi ta kalli husnah dake magana take ta fahimci aljamin husnah ne,husnah ta karaso kitchen din tace "tou mai kakeyi a nan?kaida wanan matar?"ta nuna hajiya rabi da baki ya kyalkyale da dariya yace "kalli fitsari tayi a wando hussy"tayi saurin kallon hajiya rabi da take murza kafa fitsari na bin kafafunta ta kyalkyale da dariya jin shewar husnah yasa momy ta zabura hajiya saude da yan matanta suka mike dukkansu momy tace "kinga abinda nake fada miki ko?gata can zata daukar mun magana"suka nufi kitchen din husnah ke shekewa da dariya tana nuna hajiya rabi Abraham na tayata jin wata irin dariya yasa duk suka tsorata nan husnah tayi gumm ta dauki abinci ta kifta masa ido ya fice hajiya rabi tabi inuwarsa da kallo ta kwarma ihu tana kuka daddy ne ya fito daga sashensa cikin sauri sanye da jallabiya "lafiya hajiya menene haka?"ya kalli momy yace "zainab lafiya me akayi mata"Yana kokarin rukota juyawa tayi tana kokarin kai hannunta ta janye maganin bata ganiba wani miyau ta hadiye ta fashe da kuka tace "daddy bazan taba iya zaman gidan nan ba bazai yuwuba rayuwa da aljanu?yanzun na shigo kitchen in zuba abinci kawai naci karo da aljani"suka hada baki wajen fadin "Aljani?"ta jinjina kai daddy dik ya rude yace "aljanin waye to "hajiya rabi ta Kara narkewa jikinsa dikda fitsarin dake jikinta cikin kuka tace "aljanin husnah shima yazo dibar abinci nagansa sai gata tazo nan ta tasani tana zubamun shegantaka bazan iya ba bazan iya rayuwa da jinnu ba"ta rushe da kuka ta runtse idanuwanta tana fad'in "gashi nan gashi nan"daddy ya kara rungumeta hajiya saude tayi mata wani kallo tace "kodai akwai abinda kike shirin kullawa hakan ya faru?"damm gaban hajiya rabi ya fadi da sauri ta bude ido tana kallonta ido cikin ido ta dafe kirji tace "ni kuma mai zan kulla ni rabi sharri zakuyimun dama bakuson zamana cikin gidan nan nasani dukkanku bakuson auren nan"daddy ya rungumeta cikin masifa da daga murya yace "ina husnah?bazan dauki wanan rashin mutuncin da cin fuska ba koba komi rabi uwarta ce babu wasu aljanu sai rashin mutunci data tsira cikin biyu zaayi daya dolene tabar gidan nan ko hajiya rabi tabar gidan nan indai har bazata daina wanan iskancin ba"daddy ya ruko hajiya rabi "muje muje"hajiya rabi dakyar take takawa tana manna kirjinta dana daddy, hajiya saude tace "Allah ya wadaran naka ya lalace"momy kuwa wucewa tayi kawai,


husnah na manne da Abraham yana dibo abinci yana bata cikin nishadi ta ture hannunta tace"Bana ganin lokacin da kakeci gani kawai nakeyi kana kaiwa bakinka lomar karshen nan kuwa kai zakaci"dariya yayi fararen hakoransa suka bayyana ta tsura masa ido yakai cokali baki kawai taga abincin ya bace ta zaro Ido baki bude ya dire cokalin kusa da nata a plate din momy a fusace ta Shiga dakin husnah yadda ta zabura ya tabbatarwa momy gaskiyar lamari tace "kinga abinda dai kika jawomin ko?kingani ko?"ta turo baki "nifa momy banyi mata komiba kinga plate abinci kawai na dibo"Momy kuwa mamakine ya kasheta ta kalli plate din ta kalli husnah tace"kedawa kikaci abincin?"husnah taga cokali biyu ta saci kallon Abraham bece komiba sai gira daya daga mata tace"ehh momy cokali biyu nakecin abincu dashi"momy tace "tou zo ki fita zo maza kafin in sassaba miki"ta mike tana turo baki ta wuce tana waigen Abraham ta fice momy ta rufo kofar


hajiya saude tace"idan lamarin nan bazai yuwuba zainab ni zan dauki yarinyar nan ta koma gidana zuwa kwana ukun da akace zaa maida auren kuma zanyi magana da yaseer akan ya shirya ya fara gyaran wancen sashin ma husnah tunda dama nan akace zasu zauna gidan dake jikin naku momy cike da gamsuwa ta jinnina kai hajiya saude suka fara shirin tafiyasukai sallama ta rakasu har waje...


******
muneeba cikin tsananin damuwa take meyasamu ummah takw kiranta ta sanar mata matsalar dake faruwa bata dauka ta mike tsaye ga tabarya a gefe magani kuma ya zube yaseer ne ta gani jingine jikin kofar bedroom ya harde hannuwa yana kallonta rawar jiki ta kamayi kallon tuhuma yakeyi mata yana kallon tabaryar tace"yaushe ka ahigo sam banji shigowarka ba har kadawo?"tana kallonsa yace "Mai wanan tabaryar takeyi a nan"ya nuna tabaryar da fuskarsa nan da nan ta zube tace "wallahi ina kwancene nakejin motsi cikin dakuin naga gilmawar bera tacan ina tsananin tsoronsa shine na dauko tabarya zan buge nakasa"ta shagwabe murya ajiyar zucuya yayi yace "ta ina beran yake?"ta nuna ya kalli wajen ya juyo "dakin nan dik tiles ne babu yadda zaayi bera ya iya shigowa kodai immergination kikayi"ya shafa gefen fuskarta ya janyota jikinsa ya kwantar da ita ya dauki tabaryar ya nufi kitchen ajiyar zuciya ta sauke tace "Allah ya kubutar dani"ta dafe kirji yana dosar cikin kitchen din yaji bari ya tsaya jimm to waye a kitchen din dake bari?ya tambayi kansa a hankali ya shiga Abraham na ganin haka ya rufe kofar kitchen din yaseer gani yayi kofar ta rufe take ya fahimci ko waye murmushi yayi yace "ka biyoni ne ka rama abinda nayi maka?"kamar daga sama yaga mutum a gabansa saidai baya tantancewa tsakanin mutum ne ko inuwa yaseer yace"meya shigo dakai nan saahen nawa?"baiyi aune ba yaji hannu a wuyansa an shakuresa yar kara yaseer yayi numfashinsa na hawa da sauka yana kai hannunsa ya kasa rikesa cikin murya kakkausa yace"ka fita hanyar husnah ko in kasheka"idanuwan yaseer sun firfito waje sunyi ja duhu yake gani cikin ikon Allah a bakinsa yake ambatar sunan Allah cikin hukuncin ubangiji take taji harshensa na karanto masa ayatul kyrsiyyu ganin haka Abraham yayi saurin sakin yaseer ya hankadasa ya bugu da jikin bangon kichen din kasa ya bugu ya fadi kasa yana kokarin tofa masa addua ya bace Abraham yasa hannu ya shafi kansa cikin ciwo yace "ahhhshhh wayyoo Allah"yana sauke numfashi ya fito parlor a wahalce ya zauna gani yayi ana wasa da jikin windown parlorn a bude a rufe ko gezau beyiba remote ya dauka ya shiga kokarin canja Tasha zuwa ta karatun alkurani ya kalli agogo magriba ta gabato yaji an kashe tv da karfin gaske ya girgiza kai ya mike zai shiga toilet nan ma yaji yana tafiya ana ingizasa bai fasa ba ya Shiga ya dauro alwala ya fito ya rufo kofar ya fice....


******
"ummah nifa wanan abun ya bani mamaki ummah ina cikin damuwa gashi dai aikin ya tabbata tunda ga ciki ya tabbata likita ya tabbatar mun"cikin damuwa muneeba keyiwa ummah magana tagumi hajiya rabi ta zabga tanayi tana waige waige cikin tsoro tace"ni yanzun tsoron yarinyar nan kawai nakeyi domin yau naga ishara ganin idona Allah ne ya kwaceni hannun aljani,abin jin dadin ma shine yanzun Alhaji ya tabbatar mun dole husnah zatabar gidan nan kuma naji saude tana maganar dauketa daga nan kinga shikenan inta bar gidan nan sauran aikin ninasan yadda zamuyi"cikin sanyin jiki muneeba ta jibgina da jikin gado tace"ummah kina ganin yanzun fa yaseer hankalinsa ya fara komawa kanta abu daya yasa yake kula dani cikin nan dake jikina"ummah ta jinjina kai cikin jimami jin motsin zaa shigo yasa sukai shiru daddy ne ya shigo daga masallaci muneeba ta mike daddy yace "yadai ya jikin naki muneeba"


"da sauki Daddy naji sauki zan koma sashena ne"ta fice babu karfi jikinta ta fito momy da husnah ne a kan dadduma ta tasa husnah gaba tayi sallah ta mike ta cire hijab ta nufi kitchen da sauri waige waige takeyi cikin saa taga ruwan zafi a kan gas an kashe ta diba ta fito Abraham tagani tsaye "mai kakeyi a nan"ruko kwankwasonta yayi yace "naga kuna addua ne kinga in kina adduar nan babu yadda zaayi in shigo "tayi jimm kadan tace"zan rama maka abinda wancen yayi maka ne"ta kalli jajayen idonsa yaseer ta hanga yana kokarin shigowa gate din gidan cikin sauri ta karasa momy ganin husnah ta fita tabi bayanta yaseer na juyowa tana antaya masa ruwa a kafadarsa wani azaba da radadi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login