Showing 39001 words to 42000 words out of 103127 words
yaji yana ratsasa ya daga kai yaga waye husnah ya gani tsaye tace "bansoba fuskarka naso in watsawa yadda ka konawa Abraham dina fuska"Abraham na tsaye tana juyowa taga yana mata tafi murmushi yayi ya fuzgota jikinsa yace "ai ban koneba koda na Kone ni zan warke amma shi bazai warkeba"kici kicin kwacewa daga jikinsa takeyi momy ganin haka kawai ta juya tabarsu anan cikin tashin hankaki ta nufi cikin gida husnah ta kona yaseer a jikinsa da ruwan zafi? innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ta wuce ciki
.tsamm ya riketa yana addua Yana tofa mata tana kokarin kwacewa "ni ni kadaina watsamun miyau"Abraham ya dumfari yaseer gadan gadan ganin wuta na fita a bakin yaserr ya koma baya yana huci tabbas yasan bazai taba sukuni da husnah ba tunda wanan na gidan wata dabara ta fadowa Abraham cikin fushi yabar wajen yana fita ya rikida ya koma yaseer sak ya nufi gidan momyn yaseer cike da kwarin gwiwa kawai zaije yasameta husnah ta dawo gidanta yadda zai samu damar soyewa da husnarsa batare da kowa ya Gane bashi bane,
cikin karfin hali ta funcike ta barsa nan tana hararsa "karka sake tabani"dariya tabashi ma yasan kila ba ita bace ya taba kafadarsa dake masa zugi ya nufi sashensa yau ma kamar jiya ya ganta a gaban sashen sa tayi masa murmushi wanan karon yaseer ya mayar mata batare da wani tsoro ba yace "narjisu ko?"ta jinjina masa kai tacev"katafi gidan mahaifiyarka yanzun nan kasameta dikda nasan Abraham ya rigaka zuwa"ta bace hankakinsa ya tashi mai aljanin nan yajeyi gidan mahaifiyarsa?shiru yayi tsaye ya laluba aljihun rigarsa yaji makulli kawai ya juya a hanyar fita yaci karo da hafeez da mahaifinsa da kuma kanin mahaifinsa daddy ya fito daga gida cikin faraa ya tarbesu
mari momy ta zabgawa husnah tana shiga ta fincikota husnah hankalinta ya tashi take taji wani yarrr tsoron mahaifiyarta ya shigeta taga bacin ranta karara a kwayar idonta tabbas tasan abinda tayi yasa momy ke fushi da ita dole zataje tabawa yaseer hakuri momy gani tayi husnah ta zube a kasa "momy kiyi hakuri bazan sake ba"cikin bacin rai momy tayi mata wani kallo ta barta nan ta dauko mp ta kunna karatun alkurani a
dakin ta nemi waje ta zauna husnah cikin sanyin jiki ta mike ta shige daki ta fashe da kuka......
*WANAN LITTAFIN NA DUHU NA KUDI NE GA MAI BUKATA YA BIYAV300 KACAL YA MALLAKI NASA WADDA TA KARANTA BATA BIYABA BANYAFEBA*
07042277401
08036953516
*SLIMZY*✍🏻
26
ta jikin window kanwar yaseer taji shigowar mota gate din gidan tad'an leka lokacin hajiya saude na zaune tana lalubar number a wayarta ta d'ago kai tace "yusrah banason gulma karar mota ne baki taba ji ba ko yaya?"yusrah ta koma ta zauna cikin damuwa tace "momy yayah yaseer ne yazo fa?"da sauri momy ta kalleta tace"yaseer kuma?menene yazo dashi nan gidan bayan yanzun muka baro gidan toko wata matsala ta faru tsakaninsa da husnah ne ko jikin nata ne?"cikin faduwar gaba momy ta gimtse maganarta tozali da tayi da yaseer wani yarrr taji ganin tsayuwar da yayi tana binsa da kallo yaseer baya wanan tsayuwar Abraham ganin kallon da momy keyi masa karta gane ba yaseer bane yasa ya Tako cikin dakin tabi kafarsa da kallo takalmi mai rufi ne yasa tabbas kayan dake jikinsa ne amma kamar ba yaseer ba ya zauna ya dafe kai cikin yanayi na damuwa Momy tace "yadai yaseer naganka a yamutse a hargitse Kamar ba kai ba ni jinakeyi ma kamar kaima aljanun na neman shafarka"Abraham ya shafa kansa ya saita natsuwarsa da zuciyarsa dake tafarfasa yace"momy ba dole ki ganni cikin wanan yanayin ba?kina gani fa abinda ke faruwa yanzun husnah ta konani da ruwan zafi"momy tw zaro ido tace"ruwan zafi fa kace?"ya jiniina mata kai ya nuna masa kafadarsa daidai inda husnah ta kona yaseer rigar a jike momy tace "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"Abraham yayi murmushi ya hade rai yace"ni momy gaskiya so nakeyi husnah ta dawo gidan nan da zama kawai inaga zaifi idan yaso zan rinka zuwa nan ina jan raayinta har insamu ta dawo hayyacinta tunda kinga gashi zaa maida aurenmu kuma can momy bata wani kula da ita"hajiya saude ta jinjina kai cike da gamsuwa tace "tabbas munyi wanan maganar da ita ban sanar maka bane tukunna sai gobe munyi shawara dasu innah akan maganar amma tunda haka ne ni zan daukota in dawo da ita nan inga ta inda aljanin nan zai rinka shigowa dan kwana zatayi da karatu. kurani"Abraham ya cije lebe ya kalli yusrah data tsura masa ido tun shigowarsa take kallon yanayinsa gabanta na faduwa suna hada ido ta sadda kanta kasa yaji alamun kamar ta fahimci ba yaseer bane ganin kallon da yayi mata ta shagwabe masa "yaya yaseer ni tunda ka shigo ma baka wani kulamu ba nida nusrah"Ajiyar zuciya ya sauke "bana cikin hayyacina ne shiyasa gaba daya cikin damuwa nake yanzun zan tashi in koma"momy ta jinjina kai tace"ya mai jikin?"yana kokarin mikewa yace"da sauki nabarota zataci Abinci zanbkoma Dan Allah momy ki taimakeni ki dawomin da husnah nan"ya marairaice momy tayi dariya tace"mara kunya kawai"ya dagawa nusrah hannu tana daddana waya yace"saida safe Antyn waya"murnushi tayi masa ya daga musu hannu momy ta sauke ajiyar zucuya tace"ni dama nayi tunanin hakan sam ban son zaman husnah can gara ta dawo nan,
yaseer kuwa motarsa ce ta tsaya yana kokarin gyarawa cikin rud'ani yake da tsananin tsoro yana kaiwa da komowa a bakin titi babu kowa ga gari ya soma duhu ya ciro wayarsa yayi dialling wayar momy yaji ko lafiya akace masa yaje gidan momy yana tsaye irin motarsa sak tayi parking a gabansa yabi motar da kallo yana sauraren yaga waye da irin motarsa yazo har inda yaje Abraham ne ya fito da irin kayan jikinsa sak kamanninsa sak wani furgici yaseer ya shiga yana kallonsa cikin duhu ido waje cikin tsananin tsoro yace"kai wannene?"wata dariya Abraham yayi yace "badai bakajin magana ba zakaja dani ko? to mu zuba mu cigaba da fafatawa naje na aiwatar da nufi na, wanan motar da kake gani dama ka barta a nan dan bazata gyaru ba kwata kwata"ya kyalkyale da dariya yana nuna yaseer da tuni gumi ya jikasa "Mai mai kaje ka aikata karka kashemun iyaye karka kuskura zan kasheka"Abraham yana dariya yana nuna yaseer dake karamar hauka ya bace tare da motar tasa yaseer ya bugi jikin motar gumi ya karyo masa ya rasa inda zaisa kansa kaiwa da komowa kawai yakeyi yana juyowa yaganta a gabansa suna hada ido kafin yayi magana batace komiba ta wuce inda ya bude murfin motar tana kallon motar cikin duhu wani haske blue na fitowa daga idanuwanta narjisu ta dubesa tace"zaka iya shiga katafi dikda kayi latti"ta bace yace "narji....."kafin yayi magana ta bace ya dafe kansa meyasa bata tsayawa saurarensa tana tsaye a gabansa murmushi tayi ta harde hannuwanta ganin yana kokarin fadawa kogin tunani ga tsananin tsoro a tare dashi yasa tayi gyaran murya take ya dawo hayyacinsa yana waige waige ya rufe murfin motar ya shiga cikin ikon Allah yana tada motar ta tashi ajiyar zuciya yayi yadau hanya dikda akwai nisa tsakanin su amma ko ganin gabansa bayayi....
******
cikin kissa hajiya rabi ta hada tray da drinks bayan daddy ya shigarda magabatan hafeez cikin babban parlonsa na baki Abraham ne ya shiga yana binsu da kallo ya harde hannuwansa a kirjinsa hafeez ya daga kai kenan yayi tozali da inuwar mutum a gabansa ya juya ya kalli mahaifinsa yaga alamar basu ganiba ya jinjina kai ya maida dubansa garesa wato aljanin husnah ne yazo ya bata masa show kenan?daddy ya shigo da tray hajiya rabi sanye da gyale ta dire na hannunta tace"ina yininku"cikin kulawa daddyn hafeez ya amsa ta fice daddy yace"sannunku nabarku zaman jira ko?kuyi hakuri ga ruwan sanyi kusha Na kira makocina Alhaji sidi gashi nan shigowa "yana rufe baki amininsa kuma makocinsa Alhaji sidi ya shigo da sallamarsa ya mika musu hannuwa suka gaisa yace"barkanku da zuwa"ya zauna gefen daddy,shima daddyn zama yayi yace"Bismillah kusha ruwa"hafeez gabansa ya tsananta faduwa yana kallin Abraham cikin inuwarsa ya gegi jikin daddy ya zauna wani miyau ya hadiye makwat uncle dinsa Na lura da yanayinsa yace"yadai Hafeez?"girgiza kai hafeez yayi daddy yace"tou Mashaa Allah ya kamata mufara gabatar da abinda mukazoyi hafeez ina takardar sakin da yaseer ya rubuta kace zaka kawo ka tsinta a gidan nan?"damm gaban yaseer ya yanke ya fadi yana kallon daddy ya sunkuyar da kansa yace"Daddy wallahi na duba takardar nan ban gantaba saidai inada tabbaci akan ya rubuta ina zargin ta shiga cikin takardun office dina"daddy yayi jimm ya jinjina kai yace"nima inada tabbacin hakan dan hajiya rabi ta fadamun"
"Tou Alhamdulillah Alhaji badamasi kadai san abinda ya kawo mu ko?munzo ne akan neman izinin Auren yarka husnah ma yaronmu hafeez gashi yace ka bada damar muzo dan yanzun haka da sadakin mu ma mukazo idan har ka amince ka yanke zamu biya"cewar kawun hafeez
kan daddy ya sara masa take yaga DUHU kamar kiftawar ido ya koma daidai yayi murmushi Abraham ya fito da wani abu daga idonsa ya Shiga jikinsa yace "Ayya aini yanzun na fahimcu komi nadawo hayyacina akan maganar taku dama naso hafeez ya kawomin takardar sakin husnah ne amma be kawoba kuma gaskiya akwai auren aljani atare da husnah yanzun kuma tanason mijinta"a tare hafeez da uncle dinsa da daddy suka kalli Alhaji badamasi,aminin Alhaji badamasi Alhaji sidi yace"badamasi kasan mai kake fada kuwa kodai kafara jin bacci ne?auren aljani fa kace?"ya jinjina musu kai fuskarsa a daure yace"kwarai dagaske aljani take aure Kuma bazan iya rabasu ba tunda sunason juna dan haka hafeez ya hakura da wanan aure dan bazan bashiba"
hafeez ya mike idanuwansa a rufe yana kallon inuwar Abraham yana murmushi Yana nunasa da yatsa yace"karya kakeyi wallahi ba yin kan daddy bane daddy da kansa ya bani husnah gashinan ina ganinsa a kusa da daddy aljani ne gashi nan shine ke shafar daddy"hafeez cikin zafin nama Yana kokarin kaiwa Abraham duka ya bugi bango hannunsa ya fashe take jini ya soma zuba mikewa daddyn hafeez yayi cikin rikicewa yake fad'in "kagani ko kagani meye haka kai kasamu tabin hankali ne?"uncle din hafeez ya rukosa Alhaji sidi a tsorace yake waige waige daddy kalle kalle ya somayi yaba kallon hafeez yana kallon mutanen wajen,ran daddyn hafeez ya baci kasa magana yayi ya fizgo hafeez ya wanka masa mari ya dafe gefen fuskarsa ya juyo ya sake sharara masa mari yace "wuce mutafi wuce kafin a illatamin kai dama kasan da wanan maganar kasa mukazo?"hafeez ya bude baki zaiyi magana dadddy cikin rashin fahimta yace"ya zaku tafi ina zakuje ko magana bakayiba?"wani kallo daddyn hafeez yayi masa ya fuzgi hannun hafeez suka fice..... kallon Alhaji sidi yayi zaiyi magana kawai ya daga masa hannu ya soma zazzaga masa masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,
hajiya rabi ce tsaye kan momy cikin dariyar keta tace"Alhamdulillah Allah zai kad'a mana matar aljan dan gashi can anzo neman aurenta daga gidansu hafeez taje can ta cigaba da yi musu siddabarunta"momy ranta bace yake ta kasa magana sai tsananin damuwa data tsincu kanta kenan hajiya rabi tayi nasarar raba yaseer da husnah saboda yarta?daddy ne ya shigo sai gumi yakeyi yana mazurai cikin damuwa hajiya rabi saida taji yarrr tadan dake tace "Alhaji lafiya?ina nan muna tattauna yadda biki zai kasance da zainab"momy tayi saurin kallonta zatayi magana daddy yace "Wani biki?hmmm bayan wanan aljanin na husnah ya lalata komi?wallahi ni bansan meye ya faruba nadaiga mahaifin hafeez ya fusata hannun hafeez sai jini kawai yakeyi haka suka kad'a kai suka tafi babu wabda ya saurareni sai Alhaji sidi ke sanar mun da abinda nace waini nace bazan basu aureba yata tana auren aljan"dafe kirji hajiya rabi tayi taja da baya"Aljan kuma?"kasa magana daddy yayi idanuwansa sunyi jajir gumi kawai yakeyi yace"yau na kunyata shikenan mutanen nan da sukazo manyan mutane kindaisan waye haske a garin nan yau nine nayi wanan taasar wallahi bansan nayiba"momy tausayin daddy ya kamata a karo na farko yadda ya rude yana rantsuwa momy tace"Daddy ka kwantar da hankalinka zaa fahimci juna"wani kallo yayi mata cikin bacin rai yasa kai ya shige hajiya rabi ta take masa baya tana mata wani kallo....
"yaseer karya kakeyi ban yarda cewar bakai bane kazo gidan nam yanzun katafi ba dadewa kadawomin cikin wani yanayi kamar dan shaye shaye?baka isaba kayi karya dole husnah ta dawo gidan nan kamar yadda kace"yaseer cikin tashin hankali yace"momy wallahi bani bane aljani ne yazo miki a suffata wallahi tallahi bani bane idan husnah ta dawo gidan nan tabbas akwai wani nufi dake zucuyarsa wanda zai aiwatar zai kara samun galaba akanmu"yusra ce ta shigo cikin tsoro tace "momy ba yaya yaseer bane yazo tun zuwansa naji a jikina bashi bane gudun karya fahimci nagane ba yaseer bane ya cutar damu kikaji nayi masa wanan maganar"momy dafe kai tayi kanta ya dau carji ta sunkuyar da kai sukai ido hudu da kafar yaseer tabbas wanan ba takalmin da yaseer yazo dashi bane dik ta rude tace"tabdijan muna cikin tashin hankali dole zaa gaggauta maida aurenku da yarinyar nan kafin komi ya kara tabarbarewa"yaseer ya ja numfashi ya sauke ganin momy ta dawo hayyacinsa ya soma mata magiya"momy idan husnah ta dawo gidan nan bamusan nufinsa ba"momy ta girgiza kai "ka kwantar da hankalinka husnah zata dawo nan kuma babu abinda zai faru babu abinda zai iya"yaseer sam hankalinsa bai kwanta ba kenan Abraham yayi nasara akansa?dole zai samu innah gobe ita kadai ce zata warware wanan matsalar haka yayi sallama da momy ya fice dare ya somayi,
*****
tana kwance tayi lamo akan gado tana tunani shikenan momy na fushi da ita ganinsa tayi kamar daga sama ta mike da sauri tana kallonsa wani kallo yayi mata take ta dawo hayyacinta a sanyaye tace"Abraham "ta kira sunansa ya daga mata hannu yace"babu abinda zaki fadamun tunda kika iya kyale shi yake rungumar jikinki bayan da aurena akan ki husnah bayan kinyimun alkawari akan bazaki bari wani ya rabeki ba yanzun kinsan gwagwarmayar da nayi cikin yammacin nan zuwa yanzun wajen ganin na lalata neman aurenki na kwaceki batare da anyi abinda zan kasa zama dake ba"hawayene suka wanke mata ido ta rugo ta rungumesa ta kwantar da kai Abraham yana shan wahala sosai akanta su momy sun kasa yi musu uzuri da tsananin kaunar da sukeyi wa juna ya shafa kanta yace"ya isa haka kinsan banason kukan ki ko"....daga parlor momy ke kwalawa husnah kira "fito kisha maganinki"ta kalli Abraham ya jinjina mata kai yace"jeki sha na rigada na lalata maganin hakan bazaisa mu nisanta juna ba"ajiyar zuciya ta tafi tanayi tana waigensa yace"babu inda zani"ta jinjina kai ta fito jiki ba kwari ta kalli fuskar momy fuskarta a daure babu walwala yaseer ne ya shigo kamar an jehosa "lafiya yaseer daga ina kake a wanan daren"dik a yamutse yake yana kallon momy ya dubi husnah itama shi take kallo momy ta watsa mata harara husnah a sanyaye tace"momy fushi kikeyi har yajzun dani nace bazan sakeba kinji?"a shagwabe tayi maganar take yaji wani abu ya caki zucuyarsa yana tsananin son shagwabarta Burgesa takeyi ya dade da gano shagwababbiya ce Momy tace "ashe kinada hankali kinsan fushi husnah tunda bakison fushina meyasa kike biyewa aljani yana saki kina cutar damu shima yana cutar da dan uwanki?duba kigani yadda yasa kika kona dan uwanki da ruwan zafi wanda dan bakisan wahalar daya sha dake tun kina ciki ba"tayi saurin dago kai ta kalli momy ta kallu yaseer jiki babu kwari tace "yaya yaseer kayi hakuri nadaina kayafemun kace momy ta daina fushi dani"momy na rike da jarkar maganin,yaseer ya shagala da kallon husnah ko kifta ido bayayi har saida tace "kaji?"yadan razana yace "umm umm me kikace husnah"kallonsa ta saki baki tanayi momy tace"hakuri take baka"ya jinjina mata kai yace"na hakura kinji amma kisani kiyi tunani wanan aljanin naki na kaunarki yakeyi ba cutar dake yakeyi ko bakiga yaki barinki kisake da mutane kiyi walwala ba kullum kuna manne kedashi"tayi shiru jikinta a sanyaye yace"kuma kinga mu mutane yam adam bama cutar da jamaa bama rikida mu zama wani abun halitta ko?ko kin taba ganin niko momynki wani ya rikida ya zama wani abu?"ta girgiza kai tabbas ita meyasa to jnn suke rikida yaseer yace"abinda yasa suke rikida saboda mu bamu ganinsu su suna ganinmu sanan su an haliccesu daga wuta mu an haliccemu daga kasa kinga akwai banbanci ko"gumi ya karyowa husnah take wani bangare na zucuyarta ya yarda da maganarda yaseer yayi mata jikinta ya mutu tasa hannu ta karbi maganin Tasha yaseer yace"muje kiyi alwala kafin ki uwanta"momy ta jinjina kai cike da gamsuwa tace"kuje dakina ka rakata"momy ta rufe galom din maganin ta ajiye gefen kujera ta janyo mp3 din da akasa mata memory na karatu kusa da ita,
yaseer na gaba husnah na biye dashi ya tsaya a jikin toilet ya nuna mata ba musu ta shiga tayi alwala tiryan tiryan ta fito yace"da kyau husnah"tayi murmushi gaba daya hankalinta ya kasu gida biyu tana tunanin maganganun yaseer da ya gamayi mata ta nufi dakin tana shiga Abraham ya mike ganinsu tare da yaseer sanan tayi alwala ta shigo ta saci kallon yaseer ya rufe mata kofa ya juya ta dubi Abraham gani tayi ya mike yanaja da baya sakin baki tayi tana kallon kanta yadda yakeyi kamar yana jim tsoron wani abu a tare da ita tace "lafiya?ina zakaje?"ta tambayesa cike da mamaki yadda taga ya tsorata hasken alwala ke haske masa ido wani hucin zafi daga jikinta yana tunkaroshi tsaki yaja yayi Yar kara ya bace parlor yaje sautin karatun kurani nam ma cikin dimaucewa ya bace karya samu rauni....
yaseer dakyar ya shiga saboda gajiya zuciyarsa cunkushe da tunaninta shagwabarta ke rikita masa kwakwalwa bazai taba bari momy ta dauketa daga gidan nan ba dole gobe zai ziyarci innah yana kokarin rufe kofa muneeba ta zabura ta mike yana juyowa sukai ido hudu yace "umm ahhh baki bacci ba"wani kallo tayi masa ta kalli agogo sha daya da minti ashirin tun fitarsa sallahr magriba yace "baki bacci ba ya jikin naki?"wasu hawayene