Showing 69001 words to 72000 words out of 103127 words
gadon tana laluben fuskar momy,runtse ido momy tayi cike da faduwar gaba taji bakin momy tana kokarin tura mata abu a baki momy ta dartse bakinta gamm cikin karfi suka soma kokawa momy taji nauyin hajiya rabi ga cikin,cikin saa da dabara ta cafki dan yatsan hajiya rabi da gurza mata cizo wata yar kara tayi momy ta hankadata ta mike tana fadin "waye wanene?kece wa?"tana kokarin karasawa ta kunna wutar dakin hajiya rabi tayi wuf ta fice daga dakin ta yarda layar a kasa cikin azabar cizon momy,
wuta momy ta kunna haske ya mamaye dakin ta hangi abu a kasa ta karasa ta tsurawa layar ido ta girgiza kai gumi ne kawai ke karyo mata tayi addua ta dauki layar ta ajiye gefen gado ta fada toilet ta dauro alwala tazo ta shimfida dadduma gabanta bai daina faduwa ba ta tada sallah
****
juyi muneeba tayi akan gado tayi furgigit ta tashi tana kalle kalle mamakin ganin globe na dakin kunne takeyi tayi saurin kallon gefenta bataga yaseer ba,ta daga kai ta kalli agogo karfe daya na dare ina yaje?take tambayar kanra cike da tsoro,ta zuro kafa zata sauko taji sautin karar ruwa a toilet tayi ajiyar zucuya har taji wani kishi ya caketa a kirjinta kardai fita yayi ya tafi wajen husnah jin karar ruwa yasa ta koma taja bargo taji wani sabon bacci na lullubeta hakan ya tabbatar mata da yana toilet....
*****
iskar tahowar Abraham yaserr yaji hankalinsa ya tashi sosai idanuwansa sai hawaye sukeyi yanajin narjisu na shawagi kusa dashi yasani idan har narjisu tazo to tabbas zata ceceshi,
"narjisu!!!!!"yaji wata murya na kiranta hakan ya tabbatarwa da yaseer zuhraliyya ce ta fado masa dan be sake hangen inuwarta wajen ba,narjisu wani yunkuri tayi wuta ta fara tartsatsi daga bakinta zuwa bishiyoyi wajen Dik inda ta bullo Abraham take gani ya mamaye ko ina cikin karfi da iska ta ware hannuwanta ta watsa su saiga wani abu kamar mashi kamar walkiya ya haska mata fuskar yaseer,tayi murmushi ta kalli Abraham bata nuna masa taga yaserr ba sai kawai yaga ta canja waje Abraham dadi ne ya lullubesa bata gansa ba yace ya diro kasa ya tsaya yana kallon yaseer yadda yake lilo cikin wahala,
"yadda na kasa rabar husbah ka hanani rayuwa da ita kaima bazakayi rayuwa da itaba nafada maka a nan zaka dawwama har karshen rayuwarka....
****
hajiya saude zaune a tsakiyar gadonta tayi tagumi yanayin yadda yaseer yayi dazun yake dawo mata da kalaman malam wanda ya fada mata "kisa ido sosai inhar dagaske ba yaseer bane bazai iya zaman gidan ba zakiga canji'taja numfashi ta sauke take ta tunada yadda yaserr ya fita yana tangad'i dazun a gaggauce yanayi mata saida safe,dafe kirji momy tayi kardai abinda husnah tafada gaskiya ne kardai ba yaseer bane da aljani suke rayuwa innahlillahi wa innah ilaihi rajiun tace a tsorace wata dabara ce ta fado mata dakyar ta koma ta kwanta cike da kosawar safiya tayi.....
*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFE BA*
08036953516
07042277401
*SLIMZY*✍🏻
39
Daddy na zaune parlor da safe yayi shirin fita cikin farar shaddarsa yake tasha aiki hajiya rabi ta shigo da flask na tea da cup ta ajiye,sallama sukaji a tare suka amsa Alhaji kabiru ne yayan daddy da innah suka shigo da ummah hadiza daddy na ganinsu ya kirkiro faraar karfin hali yace "ah ah da safen nan kune haka sannunku da zuwa bismillah"ya tashi daga inda yake zaune ya koma gefe "sannunku da zuwa"hajiya rabi tace tana binsu da kallo,wani kallo innah tayi mata ganin ta tsaya kikam taki fita "ba wajenki mukazo ba ga wajen wanda mukazo kuma munyi saar ganinsa shiyasa muka dako sammako"daddy ya sunkuyar da kansa,da sanyin jiki hajiya rabi ta fice ranta a bace,
"ina kwananku"daddy yace cikin ladabi yana gyara zamansa,
"badamasi ka bani mamaki dik naji irin abubuwan dakake shiryawa kuma kakeyi a gidan nan naji komi yaseer ya sanar damu hatta kayan daya siyo kasa ya maida naji komi hakan yasa nazo nida kaina tunda kasa ya maida ni idan na siya kasa ya mayar"cikin fushi baba kabiru ke maganar,daddy bece komiba sai gumi yakeyi wato yaseer ne yaje ya sanar musu kenan lallai yaseer ya girma,
"yanzun nazo da masu gyara kuma nabasu umarni su shiga sashen gidan nan dake gefe a kulle su gyarawa husnah yau da yamma zaazo daga kamfani asa mata kayayyakinta ciki inaso ta tare a yau din nan ko gobe inyaso ka koreta tinda gidanka ne kanka ya juye yarka daya tilo kake wulakantawa yanzun ga uwarta da wani cikin ai innah ta fadamun idan ta haihu shima dan ka wulakantashi da uwar zan tattaresu in kwashe ka zauna da rabi,nazo da kaina ne ba sako ba saboda kasan dagaske nake dik wani iskanci da kakeyi kai ga mai ya nasan komi"daddy yayi kasa da kai cikin ladabi yace"kayi hakuri bazaa sakeba insha Allah"
innah ta d'orada "zanbar hadiza a gidan nan gata sai angama komi dan munyi magana da saude akan zata zauna da husnah saboda lalurarta da magungunanta tunda kai baka damu da jinnun da suke damun yarka ba badamasi mu mundamu kuma jininmu ce zamu kula da ita"innah ta yunkura tace "mutafi kabiru"
"innah ku tsaya mana ku karya bari na kira rabi ta kawo muku"
"bashi mukazo ci ba,muba yunwa ta kawomuba mara mutunci"ta fice baba kabiru baice komiba ya mike Yana kokarin fita aka kirasa daddy bece komiba har suka fice ummah hadiza tace "Bari in leka wajen hajiya zainab"kafin yayi magana ta fice daga dakin,
hajiya rabice ta fito daga daki ta fashe da kukan bakin ciki yanajin haka ya mike jikinsa na rawa"kukan mai kikeyi?meyasa kike kuka?kidaina kuka kiyi shiru yaseer baxai rabu da muneeba ba dan an maida aurensa da husnah kinji muneeba da yaseer mutuwa ce zata rabasu"ta Kara rurin kuka ta shige jikinsa "yanzun Alhaji kenan muneeba suna nufin na yarsu bace ko sun manta kaninka ne ya haifeta? itama ai yarsu ce amma sun fifita husnah akan muneeba ana kokarin fitar da muneeba daga gidan mijinta bayan mijinta yana sonta?"ya share mata hawaye yanajin wani shauki akan hajiya rabi dikda yadda yake cikin bacin rai cikin sigar lallashi yace "ki kwantar da hankalinki ni nasan yadda zan bullowa lamarin baridai husnah ta tare"hajiya rabi najin haka ta goge hawayen kissar da takeyi ya jinnina mata kai tace "Mai zakayi alhaji?"yayi murnushi "ki kwantarmun da hankalinki kidaina koke koken nan banaso kinji banason kukanki"ta langabe masa a jiki tasa hannu ta dauko hularsa ta dora masa ta wani lankwashe ta langabe kai "kayi kyau alhajina kullum kara kyau kakeyi sam kamar ba tsoho ba"yayi dariya yaja hancinta suka fito a tare,
hajiya zainab ta soyo dankali da kwai ta dauko daga kitchen tayi kwalliyarta tasa wani lace blue mai golden ya a jiki tayi matukar kyau cikinta ya fito sosai tana hango tahowarsu ta hada rai tayi kicin kicin da rai tsabar kyaun da tayi daddy saida ya kalleta ya sake kallonta ta dauke kanta ganin haka yasa hajiya rabi shagwabewa daddy kamar zata shige cikinsa,..
ummah hadiza na zaune momy na Shiga ta tareta "ke zainab abinda kike gani kenan a cikin gidan nan?yanzun wanan wulakancin Shi kike fuskanta ina kallon badamasi ko kallo baki ishesa ba,momy ta dire plate din a gaban ummah hadiza tace "ai bakiga komiba ummah hadiza ai wanan kadan ne sanan maganar da kikeyi ta wai be kulaniba nida jiya ya mareni yace bayason ganina a cikin gidan nan?"zaro ido ummah hadiza tayi "mari?"momy ta jinjina mata kai tace "mari dai da kikasani harda kora ya koreni naki tafiya ne nace saida shaida idan kuma ya bani shaida zaiyi dayasani"ummah hadiza ta jinjina kai mamaki ya gama kasheta taja gauron numfashi"dik son da badamasi keyi miki"
"da ne wanan"hajiya rabi ce ta tsaya kikam akansu tayi wata dariya hade da shewa tace "andaiji kunya ankori mutum yaki tafiya saboda tsananin bakim naci miji baya raayinki kin like koda yake yar kwararoce ke"ummah hadiza kuwa cikin zafin nama ta mike ta zabgawa hajiya rabi mari ta dago ta kara zabga mata tana nunata da yatsa cike da masifa da bacun rai "ke rabi ki shiga hankalinki akwai yat kwararo irinki keda kikaje wajen boka kika shiga kika fita kika rabasu aikece yar kwararo ba zainab ba kisani zainab nada daraja da kima a idanuwanmu koda ta kasance batada kowa tafi karfin wulakanci shashasha maciya amana"momy cike da bacin rai tace "dole ki kirani yar kwararo tunda badamasi ya kirani jahila a gabanki jahilci ya kare miki da kikazo jiya kina kokarin turamun laya a baki"... dafe kirji hajiya rabi tayi"ni zakiyiwa sharri zaindb nice na tura miki laya a baki?ni bayan cin mutuncin da kuke shirin yimun saboda kunyi kunyi ku shiga tsakanina da mijina kunki shiyasa kuka bullowa yaseer da maida husnah"ta fashe da kuka "wallahi bazan dauki wanan rashin mutuncin da wulakanci da tozarci ba daddy zan kira na sanar masa koni ko ita cikin gidan nan abu. har ya kaiga mari?"sadiya ce ya fito ta ruko hajiya rabi tana harare harare "kiyi shiru ki kwantar da hankalinki zama daram cikin gidan nan tunda mai gida na kaunarki kuma sharrin da akai miki sai ya bi miki hakkinki"ta watsa musu wani kallo ummah hadiza jikinta na rawa ta cafko sadiya momy ta yunkura dakyar ta rukota "rabu dasu ba irinsu baceke karki biye musu ummah hadiza"zama ummah hadiza tayi cike da takaici,
sallama hafeez yayi a parlorn da sauri momy ta kallesa tace "hafeez?hafeez dama kana nan?"murmushi hafeez yayi yana kokarin shigowa yace "sannunku momy"
"ga waje ka zauna hafeez zauna yau nice zan baka abun karyawa"murmushi yayi "ina kwana momy?"
momy kallonsa takeyi yana kalle kalle jikinta ne yayi sanyi tausayinsa ya kamata yace "momy ina husnah ne? ya jikin nata wallahi nad'anyi tafiya ne hankalina gabaki daya yana wajenta a can inda naje ma har wani mai magani nasamu gashi nazo da maganin"Abraham ha tsaye jingine jikin kofa yana kallon hafeez wani irin kallo yasa hannu cikin izza idanuwansa na fito da wani hayaki amma abun mamaki dik yadda yayi kokari hayakin ya shiga jikin maganin dake jarkar yaki dawowa yakeyi yasa hannunsa yaji kamar anjasa,hafeez ne ya juyo ya dauko ya mikawa momy wadda Baki sake take kallonsa batasan me zatace masa ba,
"ga wanan momy inada tabbas akan wanan maganin da zarar tashashi aljanin nan zai rabu da ita zaiji bayason koda ganinta momy saidai dayake waraka ba lokaci Daya take zuwa ba"momy tai shiru dakyar ta sauke numfashi tace "sannu hafeez hakika kai namiji ne wanda dik macen data sameka a matsayin mijin aure ta dace dan zata samu kulawa,saidai husnah bata nan gidan"damm gaban hafeez ya yanke ya fadi yana kallon momy ya kasa magana ya hadiyi wani miyau ta tsaresa da ido "kayi hakuri hafeez kasan ai akwai auren abokinka a tare da ita ko?"nan da nan idon hafeez suka kawo ruwa ya sunkuyar da kansa kasa sam bayason momy ta hango karayarsa yace "nasani momy amma...."
"hafeez yaseer baya cikin hayyacinsa ne shiyasa amma yanzun haka ma kaga ana gyaran gidansu dake gefen namu ko?yau ko gobe akeso husnah ta tare sakamakon aljanin nan dake damunta"Abraham yayi murmushi hmm basusan dashi Zata tare ba yaseer dansu yana daji a daure,
momy ta kwashe komi ta fadawa hafeez jikinsa yayi sanyi yanajin jiri kasa mikewa yayi kansa a kasa ya kasa magana momy tace"yadai hafeez?"girgiza kai yayi ummah hadiza tayi ajiyar zuciya hafeez ya bata tausayi sosai tasan yadda yake dawainiya da son husnah sanadinsa aka samu husnah saidai already akwai aure akanta...."kayi hakuri hafeez kaji ai yaseer dan uwanka ne ko?"ya jinjina kai ya dago kai idanuwansa jajir yace "bakomi momy ga maganin nata yanzun zan koma ummah najirana zan fita da ita"momy ta girgiza kai cike da tausayawa "ka gaida ummahn naka kaji kuma idan kasamu lokaci kazo inason ganinka"ta jinjina kai ya fice,
"gaskiya ya bani tausayi harda dawainiyarsa gashi yanason husnah"momy ta kada kai kawai ta dauki maganin ta ajiye a gefenta,ummah hadiza tana cin dankalin kadan kadan tace "Bari intashi naje in duba masu aikin nan na gyaran gidan husnah kinsan alhaji kabiru"sukai dariya tasa takalmi ta fice momy tayi shiru tana tunani da nazari...
******
tare da husnah suke aikace aikace a kitchen saidai gabaki daya cikin tunani take da fad'uwar gaba wanda ta rasa dalilin hakan ko ina cikin gidan karatun alkurani ne momy ce ta tsaya bakin kofar kitchen din "laa momy kin tashi kenan"ta jinjina kai "Natashi jiya banyi bacci da wuri ba sakamakon motsi da nakeji a cikin gidan nan"
"nima momy naji motsi dakin anty husnah kuwa buga kofar aka rinkayi natashi yakai sau biyar bana ganin kowa kuma ikon Allah ita tanata baccinta"nusrah tace tana kallon gefen husnah,murmushi kawai husnah tayi tad'an yatsina fuska tace "momy yau tinda natashi nakejin kasala inajin amai"momy ta zaro ido waje "amai fa kikace?"ta jinjinawa momy kai,"tou bari yaserr yazo idan kunfita kundawo sai ku biya asibiti ko?"ta gyada mata kai cikin zucuyarta tace idan Abraham dai yazo momy taki yarda da cewar da aljani suke rayuwa....ta fito daga kitchen din cikin sauri ta shiga dakinta tana Shiga mamaki ya kasheta tabar dakin babu gyara amma tabi dakin da kallo hatta gadon an canja zanin gadon to waye?amai ne ya taso mata ta nufi toilet taga kofar ta bude ta dawo da sauri tana leken toilet din bataga kowa ba jikinta ya soma rawa tana kokarin shiga tanajin tsoro kawai kwara amai ta shigayi a wajen sai ynkuri takeyi kwafa taji a gefenta ta kalli bakin gado Abraham ta gani zaune ta dago kai tana hada ido dashi taga yadda jikinsa yayi,ta kauda kai "ke bakiga mijinki ba ko?"kauda kai tayi "kaiba mijina bane mijina yanacan cikin daji wanda yake cikin kaddara sanadinka"murmushin karfin Hali yayi "husnah kenan yanzun dik kin manta da soyayyar da mukasha da yadda muke kulawa da juna ko?kin tsanani kin manta da wahalar Danasha akanki ko?kalli jikina yadda yake konewa sanadin yadda nake sonki nakasa daina kusantar inda kike tsananin kaunar da nakeyi miki,"cikin lallami da tattausan lafazi yakeyi mata magana cike da tausayawa wani kallo ta watsa masa "ni baxan fita dakaiba dan bansaniba ko can daji cikin bishiyoyi zaka maidani"tana maganar tana neman abinda Zata nad'e aman datayi kallon aman yayi kawai ya bace cikin tsiwa ta karaso ta damko wuyansa "waye yace ka gogemun amai danayi?kenan hat gyaran gadon ma da gyaran dakin kai kayi ko?"momy ce ta turo kofar "yadai husnah najiki shiru ko jikin ne?"Momy taga husnah cukume da yaseer mamaki ya kashe momy yaushe ya shigo bataga wucewarsa ba?"ah ah husnah ya kika cukume yaseer meyafaru?kai yaushe ka shigo banji shigowarka ba"sosa keya Abraham yayi yana kallon yadda momy tq tsaresa da ido yace "bana d'anjin dadi ne shine kawai banaso yaran nan suzo su cikani da surutu kuma Baba kabiru na can yasa ana gyaran gidan husnah to nadan tsaya anyi hatsaniya da ummah hadiza "momy ta kalli gefen wuyansa kamar rushi ya farfadi a jikinsa gabanta ya fadi zatayi magana ya mike cikin sauri yana kallon agogo "ina mota suyi sauri su fito mutafi"ya fice kamar walkiya husnah hawaye ke zubo mata "momy wallahi ba yaseer bane ki yarda dani wanan aljani ne yaseer yana can ya batar dashi 'ta durkushe tana kuka cikin tattausan lafazi momy tace"kiyi hakuri kinji yana sauya miki kamannin mijinki ne amma shine ki tashi yanzun kuje kuyi siyayyar kayayyaki kinga idan angama gyaran gidanki yau can zaku kwana"girgiza kai husnah tayi tace "mony kiyi hakuri nibazan jeba shi aljani ne"dakyar momy ta taushi husnah ta yarda ta dau gyalenta idanuwa jajir ta fita a parlor suka hadu dasu nusrah har sunkai kofar fita Momy tace"tsaya bakisha maganinki ba"husnah ta tsaya momy ta dauko galon din maganin ta bata tasha ta shafe mata jikinta da wani turare mai karfin gaske ta fito yana mota su nusrah suka Shiga baya tana bude motar kamshin turarenta ya shaka ya soma tari idanuwansa suka firfito ya kalleta a fusace"husnah koma bayan mota nusrah ta dawo nan bazan iya zama dake kina wanan warin turaren yan borin ba,ni wanan abubuwan da momy take shafa Miki idan kika tarw kin daina shafasu"murmushin mugunta husbah tayi ta bude motar ta fita ta hararesa nusrah ta fita sumi Sumi a tsorace ta Shiga gaban motar ya tada motar layi yakeyi yanajin motar sakamakon azabar da yake ciki sukabar kofar gidan....
******
ummah hadiza cikin dakin husnah parlornta mai girma anfara saka kujeru golden da brown wani wallpaper ne mai daukar ido a parlorn "mashaaaa Allah"anata Shiga da kaya tana gefe tasa waya ta kira innah take labarta mata yadda sukayi da hajiya rabi suna cikin magana mai gadi ya shigo "Assalamu alaikum hajiya kizo inji daddy"tayi murmushi tasan hajiya rabi ta hadota da badamasi kenan tace "gani nan zuwa"tanata zuzuta kyawu irin na dakin husnah da cottons dinta sai aiki akeyi ana Shiga da kaya tun daga kofar gate take jiyo haushin daddy...
*****
cikin iska mai karfi narjisu ke rike da yaseeer idanuwansa rufe yanajin yadda suke karo da bishiyoyi cikin tsananin faduwar gaba yaje addua ce a zucuyarsa kada Abraham yazo yasamesu baya ganinta amma yanajin yadda take rike dashi kamar kugiya kimanin awa daya suna abu daya sautin kukan tsuntsaye da mugayen halittu kawai yakeji gumi ke karyo masa gashi narjisu ta gargadesa karya kuskura ya bude idanuwansa idan har ya bude idonsa zai iya haukacewa,
gashin kanta tayi masa rumfa dashi tasa hannuwanta da zara zaran yatsinta sa kumbarta ta nade jikinsa dashi haka suka shigo cikin duniyar mutane wata irin iska yakeji tana ratsashi yana jiyo maganar mutane daga can nesa ya kara runtse idanuwansa sai hawaye narjisu ta kallesa ta kad'a kai, a kofar gate din gidan hajiya saude suka tsaya,
jinsa yayi tsaye akan kafafuwansa idonsa a rufe tayi murmushi tace bude idonka"a hankali yake bude idonsa wani haske yake gani yana kashe masa ido sakamakon DUHU da yayi kwana da kwanaki ciki kallonta yakeyi ya kasa magana "karka godemun yaseer saidai akwai kura a gabanka nayi maka mai wuyar ko?"ya gyada mata kai hawaye ke zubo