Showing 18001 words to 21000 words out of 103127 words

Chapter 7 - DUHU Book Complete By Slimzy .txt

Slimzy   

19 Jun 2024

11805

shigewa jikinsa tace "zafi kaji idan bazakayimun da zafi ba kayi na amince matukar hakan zaisa bazan rabu dakai ba Abraham koda ka kasance kaidin ba jinsina bane amma gabaki daya rayuwata na tasone da kaunarka da soyayyarka"tausayinta ya kamashi wata irin shaawarta ke taso masa saidai yana hango tsantsar azaba a kwayar idanuwanta ya dagata cakk ya fito da ita daga cikin ruwan tana kallon yadda lokaci daya kamar magic ya zuba musu wanan kayan alatun a bayi yadda ta tsaya zata fadi ya tallabota ya hura iska a kasa saiga katifa mai laushi siririya ya kwantar da ita ya bude kafafuwanta yana kallo har jini ya soma fitowa jikinta a matse yake sosai ya dago ya kalleta tausayinta ya kamasa ya hura mata iska a hq dinta ta runtse ido nan da nan ta nemi zafin ta rasa ya tallabota yace "da zafi?"ta girgixa masa kai tace "kaga zafin ya tafi"ya mika mata hannu ya d'agota yace "tou zo muyi wanka"ta tura baki tana kallonsa sam bata yarda da yanayinsa ba tana kallon bukatarta a kwayar idanuwansa tunda yake da ita bai taba nuna zai kusanceta ba sai yau dik yadda take shaawarsa gashi yau ya nemeta tausayinta ya hanashi ta rungumesa ta baya cikin shagwaba tace "shikenan ka fasa?"ya shafa gefen fuskarta yana jin tausayinta da tsantsar kaunarta bayajin zai iyayin abinda zataji ciwo ko ya takurata dikda tasan shi aljanine amma ta amince take kaunarsa take rayuwa dashi.....ruwa ya kunna shower ya janyota suka shiga suna tsaye ya rungumeta sosai ruwa na zuba a jikinsu suna rungume da juna gashin kanta ya jike sharkaf a fuskarsa yana shafata zuwa cibiyarta tana kara kwanto masa dibar ruwa yayi ya watsa mata tayi yar kara....




daidai nan momyn yaseer ta kalli momy tace "yadai naji husnah na yar kara can sukaji dariya"daddy ne ya shigo dakin da hajiya rabi fuskarsa a daure ya tsaya yanayiwa momy wani kallo cike da tuhuma hajiya saude tace "lafiya kake cika kana batsewa haka Alhaji badamasi"daddy zaiyi magana yaseer ya shigo can kasan makoshinsa yacev"Assalamu alaikum"ya tsugunna yace"daddy ina kwana"


"lafiya kalau yaseer ya kwanan muneeba ina muneebar"sai Gata ta shigo sanye da hijab ta tsugunna ta gaishesu dakin yayi shiru can ta cikin dakin husnah sukaji an kyalkyale da dariya sai daddy ya kalli momy yace "husnah ita dawa take dariya"momy bata kaiga bashi amsaba suka jiyo sautin muryarta tana fadin "nidai nidai kabari kadaina"cakulkuli Abraham yakeyi mata,daddy yace "naji kamar tana ya daina shi wa"
cikin takaici momy tace "mijinta Aljani mana"....a razane yaseer ya kalli momy daddy sandarewa yayi tsaye yace "aljani kuma"momy ta jinjina masa kai tace "ehh aljani daddy jiya hk muka kwana da ita inaji daga can wajen aljanun wata ta biyota ko narjisu?"bata rufe bakiba sukaga husnah ta fito kanta jike da dan kwali a hannu aguje tana dariya sosaj alamun an biyota Abraham ne ya bisu da kallo basu ganinsa ita ke ganinsa tana nunasa,
momyn yaseer tace "tabdiban akwai babbar matsala kuwa saidai akwai maslaha"daddy yace "menene maslaha saude"yanayi yana satar kallon husnah ta shige kitchen tana dariya,


hajiya saude ta kalli yaseer tace "sau nakeyi ka maida aurenka da husnah inaso itama ta tare a matsayin matarka tunda ta dawo tun tana kankanuwa aka baka aurenta gata yanzun ta dawo inaso ka aureta ka maida aurenku yanzun"damm gaban yaseer ya fadi yana kallon momynsa Ido cikin ido nan da nan gumi ya soma karyo masa yayi kasa da kai yace "momy nifa bansan wani aure dake tsakanina da husnah ba ga matata a gefena ku kuke maganar aure bansaniba sanan yanzun ta yaya zaace in aureta bayan kuna ganin auren aljani ne akanta",
tsawa momy ta daka masa nan da nan yayi shiru tace "karya kakeyi ba aljaniba ko ifiritu ne take tare dashi baka isaba saboda ka mance sabda kake mana kuka koda yake ba laifinka bane ga mai laifin nan sun juyar maka da kwakwalwa"ta nuna hajiya rabi,


daddy yace "dakata hajiya saude baki isa kizo gidana kici fuskar matata ba kinaji ko dama ai nasan abinda ke tafe dake tunda ta fadamun ya tabbata zainab ta zugoki kizo kiyi rashin mutunci saboda yaseer ya rabu da muneeba ko to baki isaba wallahi kinyi kadan inace husnar yata ce to bazai aureta ba bazai maida auren ba sai inga ta tsiya"idanuwan momy suka cicciko da hawaye hajiya rabi ta fashe da kuka ta rungume muneeba tace "nasani dama haka zata kasance tun farko baa sonsa da muneeba da husnah ake sonsa an aura masa muneeba ne dan aci mutuncina aci zarafina dan anganta marainiya"ta finciki hannun muneeba tana kuka muneeba ta gigice cikin tashin hankali take jin furucin momy akan yaserr ya auri husnah ya dawo da aurensu da husnah tabdijan bazai yuwu ba,


suna shiga daki muneeba ta zube a kasa tace"ummah kinaji fa wai yaseer ya maida aurensa da husnah nashiga uku ummah ki taimakeni kar haka ta kasance "ta fashe da kuka hajiya rabi tayi kasa kasa tana kallon kofa tayi kasa da murya tace "kiyi shiru ki kwantar da hankalinki aina rura wuta bazan bari mijinki ya dauki matar aljan su kasheku ba"a fili kuwa fashewa tayi da kuka,


daddy ya zabura yace "dik kece kika hado wanan masifar bawaniba tou akan wanan maganar idan baku janyeba zan dau mataki akanki ke hajiya zainab"daddy cikin gargadi yake nunata da yatsa ya wuce sashen hajiya rabi har yana tunrube,


hajiya saude tace "tabdijan lallai zainab kina cikin masifa da jarabawa kice angama da mijinki kamar yadda suka gama da wanan saunar"ta nuna yaseer da ya sunkuyar da kai gabaki daya baya cikin hayyacinsa gumi ne kawai yake diga daga fuskarsa tace "ina nan akan bakata aurenka da husnah na nan daram idan ma kasaketa aibaka furta saki uku kayi mata ba dan haka dole ka mayar da ita tashi katafi kabani wuri shashasha butulu"yaser zaiyi magana ta daga masa hannu tace"ficemun daga gani"ya fice yana waigen momy yadda ta dau zafi yasan batada wasa innahlillahi wa innah ilaihi rajiun wace irin masifa ke doso shi?...


hajiya saude ta juya ta kalli momy taga zaune take hawaye ya gama wanke mata fuska tausayinta ya kamata ta girgiza kai tacev"share hawayenki dik wanan fuffukar da yaseer keyi ke kinsan yanason husnah tun yana karaminsa tun batan husnah ke baki mamakiba lokaci daya da kansa ya juya?"momy ya jinjina kai tace "sharrin rabi ne asiri ne kuma zan karyashi dani take zancen nasa ayi mishi rubutu na dafa'i mu zuba nidasu kuma daddy kome zaiyi saidai yayi bazan taba bari auren husnah da yaseer ya wargajeba koda take auren aljani!!!"momy gaba daya ta kasa magana tsananin damuwa da tashin hankalin da take ciki


tsaye yake a jikin drawers din kitchen tana duke tana firar dankali suna hira cike da shauki yace "husnah kinajin ana kokarin hanyar da zaa rabani dake ko?"ta ajiye wukar ya tsugunna ya dauka ya shiga fere dankakin yace "na rantse da Allah zan dauki mummunan mataki akan dik wanda yayi yunkurin rabani dake husnah ko wayeshi zan iya rabashi da ransa"zaro ido husnah tayi ta shiga girgiza masa kai tace "nidai kar kayi kisa bazan ma rabu dakaiba idan sun matsa ba saimu gudu ba?"ya cije lebensa idanuwansa suka sauya zuwa fari babu alamar Baki tana kallonsa taji tsoro ta kauda idanuwanta cikin furgici tace "banason wanan idon ka dawomin da idanuwanka"nan da nan ya sauya idonsa taja ajiyar zucuya kallon dankalin yayi taga sun koma a fere a yanke cike da mamaki ta kallesa ya sakar mata murmushi ya kashe mata ido tace "saura suya inaso yau kowa yaci abincina dikda ina fushi da momy banaso ta rabamu"yace "bawanda zai rabamu bari mu soya rufe idanuwanki"ta rufe idonta ya bude hannuwansa wani abu shuuruuu kanar hayaki ya baibaye dankalin nan da nan ya zama ya soyu yace "bude kiga magic" bude ido tayi ta bude baki cike da mamaki tana kallonsa yace "ya kika gani "tayi tsalle wajen plates taje ta dauka ta zuba tasa cokali mai yatsu ta nufi dakin momy a hanya sukai Karo da muneeba,wani mugun kallo muneeba tayi mata tasa kafadarta ta bangaji kafadar husnah gammm ji tayi kamar ta bangaji dutse tayi yar kara aguje momy da hajiya saude suka fito tare da daddy da hajiya rabi suna hada bakin "lafiya!"ganin husnah Sororo da plate a hannu tana binsu da kallo muneeba kuwa ta yanke jiki ta fadi tana rike da kafada tana kuka "wayyo kafadata wayyoo daddy ta karyamun kafada"Abraham murmushi yayi kawai bazau taba bari wani ya cutar masa da husnarsa ba muneeba kasa motsi tayi hajiya rabi ta d'agata tace "bazai yuwuba a sabautamun yarinya ba Alhaji tun kafin husnah ta tare a matsayin matar yaseer kagani abinda akai mata inaga ta tare kashemun ya zaayi"ummahnta tajata suka bar wajen daddy yayi kwafa kawai ya kalli husnah dake tsaye da plate kamar an dasata hajiya saude ta rike hannunta tace "taho husnah zomuje kufadamun kinason yaseer?"tambayar data girgixa husnah kenan ta kalli hajiya saude ta kalli momy wadda ke jinjina mata kai alamar tace ehh Abraham na tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa ta kalli kofa inda yake tsaye ko kifta ido batayi kallon da yake mata yasa ta juyo tace"banasonshi bazan auresa ba nida auren wani akaina koko anayin aure biyu ne dama?"momy tace "tashi kije husnah"Abraham ne ya shige jikin husnah yace "bazaku taba rabani da husnah ba saboda son da nakeyi mata idan kuma kunce zaku rabani da ita tayi rayuwa da wani to tabbas zan kashe ko waye,in bakusan ni waye ba kusani sunana Abraham nine mijin husnah wanda a yanzun tare muke rayuwa nida ita babu kuma mai rabani da ita dik inda take ina tare da ita gara in fito in fada muku nine aljanin danasacetw tun tana shejara biyu na reneta nasha wuya sanan na aureta shine yanzun zakuzo kuce wai ta auri wani da auren wani akanta?nasan da auren nasaceta saboda ta shaku dani yadda ko tasan ni aljanine bazata taba rabuwa dani ba"wani kallo yayiwa hajiya saude wadda ke zaune saida ta razana da irin muryar da yakeyi musu magana ya tabbatar ba husnah bace wanan muryar namiji ce"daddy dake tsaye ji yayi jiri na shirin dibarsa ya fadi dikda irin haushin momy da yakeji Abraham nagana magana ya fice daga jikinta ta mike tana hawaye sukaga ta nufi daki,


hajiya saude ta kalli momy wadda gaba daya ta gama razana momyn husnah tace"kar a kuskura a hada auren yaseer da yarinyar nan yanzun kinajin irin furucin da wanan aljanin yayi kada ya kashe mana yaseer"


hajiya saude tace "babu fashi maida auren yaseer da husnah koda wanan aljanin zai kasheshi kuwa ai husnah ta yaseer ce ciwo bazaisa ya gujeta ba,hakan da kikaga yanayi akwai asiri a jikinsa wanda da yazo gida nabashi maganin da malam ya bani zai sakeshi zai tuno husnah zai dawo hayyacinsa,ajiyar zuciya momy tayi hajiya saude ta mike tace "ki kwantar da hankakinki daga nan zan nufi gidan wani mutumi mai bada maganin iskokai baxama zamuyiba dikda akwai aiki a gabanmu sanan ga wanan kafirar matar ta juya miki hankalin miji ki fita hanyarta ki rike yarki"momy ta jinjina mata kai dik jikinta babu kwari haka ta dawo daga rakiyar hajiya saude tana tafe ko ganin gabanta batayi haka takesa kafarta yaseer ne ya fito sashensa bece mata komiba taga ya Shiga mota ya tayar me gadi ya bude masa gate ya fice......




*WANAN LITTAFIN MAI SUNA DUHU(sark'ak'iya)NA KUDI NE 300 KACAL ZAKI BIYA KISHA KARATU IDAN BAKI BIYA BA KIKA KARANTAMUN ALLAH YA ISA!!!*


3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK


SHAIDAR BIYAN KUDI TA WANAN NUMBER 08036953516 KO KATIN MTN TA NUMBER






*SLIMZY*✍🏻 07042277401


18
hafeez na zaune a parlor kanwarsa meenal ta shigo cikin shirin tafiya makaranta tace "har yanzun bakaci abincin nan ba yaya hafeez bayan kace zaka saukeni a school ka wuce gidansu yaya yaseer"yaseer ne ya bankado labule ya shigo meenal cikin mamaki ta bude baki tace "laaa ga yaya yaseer din ma ya shigo ni bari intafi nasan yanzun in kuka zauna hirarku"ummah ce ta fito daga kitchen rike da kofin shayi tana juyawa da cokali tace"ai in zaki shirya ki shirya yau hafeez bazai fita a gidan nan ba saboda banaso yaje yana muamala da matar aure matar ma matar amininsa"yaseer wani kallo yakeyiwa hafeez daga bisani ya maida kallonsa ga meenal da take kallonsu cike da mamaki yace "kina lafiya meenal?"a sanyaye tace "lafiya lau ya yaseer ya na ganka haka kamar kuna fada da ya hafeez kamar ba lafiya ba"a centre table ummahn hafeez ta dire kofin shayi tace "ina lafiya bayan nasan yaserr baxai tabaso hafeez yayi muamala da matarsa ta aure ba ninasan haka zata biyo baya,meenal wuce kitafi makaranta"meenal a sanyaye ta rataya jakarta ta nufi hanyar fita tana waigensu cike da sanyin jiki yaseer yace "ummah husnah ba matata bace matar aljani ce dan gaba daya yarinyar ma bata cikin hayyacinta,wanan hafeez din shi yayi silar data shigo rayuwarmu gashi yanzun mahaifiyata tace dole saina maida aurena da ita kuma ni babu d'igon soyayyarta a zucuyata sanadinta yanzun mahaifiyarta na fushi dani dik ga wanda yaja komi nan hakan yasa nazo in gargadeshi tun muna mu biyu yaje gidan mu ya kwance kullin da yayi idan ba haka ba dik abinda nayi masa shi ya siya dan ni bazanyi zaman aure da wata husnah ba wacce sam bana sonta ban santabama"cike da masifa yake maganar yana nuna hafeez da yatsa hafeez a zucuye ya mike ya kauda yatsan da yaseer ke nunasa dashi yacev"karka sake nunani da yatsa naji nine silar zuwan husnah rayuwarka amma kasan husnah yar alhaji badamasi ce tunda gwajin jini ya nuna hakan kuma tunda kace haka yanzun nafara son husnah kuma zakasha mamakina"ummah kanta ya daure kasa magana tayi yaseer yace "idan ka cika masoyinta na gaskiya mai zai hana ka rabota da gidanmu ka kawota nan kazo kayi ratuwa da ita da aljanun dake tarw da ita?"ya wuce fuuu har ya kai kofa yace "note you ka tabbatar ka kwance kullin daka kulla dan bazanyi rayuwa da husnah ba nafada maka"ya bankade kofa ya fuce hafeez na kokarin binsa a zucuye mahaifuyarsa ta fuzgosa tace "ina zaka?me zaka bushi kayi?"idanuwan hafeez jajir yace "ummah kina ganin har gida yazo yanamun rashin mutunci akan husnah ko nafada miki yasaki husnah ummah kiyimun rai ki taimakeni kisamun hannu in aureta a haka"shiru ummah tayi tana kallon hafeez wanda yake rokonta ya hada hannuwansa biyu tace "ban hanaka auren husnah ba saidai abu daya nake jiye maka yadda yarinyar nan kace rainon aljanu ce tayaya zaka aureta bayan da auren aljani a tare da ita baa rabata dashi ba?"


"ni zan rabata dashi ummah"yace cikin kakkausar murya yana kallon mahaifuyatsa zatayi magana ya jinjina kai yace "kwarai zan rabata dashi kisamun albarka kiyimun addua zan shiga sahun masu nemawa husnah magani kuma inaso idan daddy ya dawo ki sanar dashi inaso inyi aure "kasa magana tayi gumi kawai ke barkowa ta ko ina a jikinta wanan turka turkar ta yaya hakan zata kasance idan hafeez ya auri husnah ya makomar amintarsu bayan husnah matar yaseer ce tunda aka haifeta aka aura masa ita?yanzun meke damun yaserr da yake ikirarin besanta ba bayan har gidan yake zuwa da hotonta?tagumi ummahn hafeez tayi tana zaune hafeez ya wuceta tace "hafeex ina zakaje?"bai saurareta ba ya wuce ta mike tana salati tana tafa hannu cike da tashin hankali......
*****
kwankwasa dakin husnah momy tayi a tsorace tanayi tana waigen dankalin da husnah ta soya ta ajiye Sam bata yarda da wanan dankalinba ta yaya husnah da tayi rayuwa cikin aljanu tasan wata suyar dankali daga cikin dakin taji wata murya ta amsa "waye?meyene nenene kike kwankwasa mun kofa"wani miyau momy ta hadiye bakinta na rawa tace "husnah kece?ki fito inaso inyi magana dake ne"yatsina fuska husnah tayi daga ciki lokacin momy taji muryar husnah na cewa Abraham "ka kara bata amsa tana jinka"jinjina kai momy tayi ta juya batare da tayi magana ba kallonta Abraham yayi yace "kinga yanzun yau ansan da cewa kinada miji dan haka ki shirya mu fita kawai muje mushakata a waje banason kina wuni a cikin gidan nan ma bari inje in dawo yanzun"ta jinjina masa kai cike da murna yace to intafi?ta kashe masa ido ya lakuce hancinta taga ya mike tsaye ya tsaga bango da hannunsa ya shige take bangon ya koma yanda yake ta mike ta shafa cikinta yunwa takeji tana fitowa taga momy tayi tagumi ta tasa plate din dankalin data soya husnah batace komiba tasa hannu ta dauka ta somaci gashin kanta a yamutse hafeez ne ya shigo dakin da sallamarsa saidai fuskarsa babu walwala yabi husnah da gashin kanta a yamutse da ido sanan yacev"husnah bakiga yayanki ba bazaki gaisheniba?"tayi murmushi momy ta amshe zancen "wayasani ko ba ita bace hafeez"ya zauna yana fuskantar momy yace "kamar yaya"momy ta jinjina masa kai ta kwashe yadda sukayi da ita dazun da Abraham yazo jikinta ta fada masa"shiru yayi yace "momy akan maganat nazo nima zan sa hannu husnah tasamu lafiya amma momy tunda yaseer baya sonta ni inasonta yazo har gida yaci mun mutunci akanta ummah ta ta amincemun da in aureta"Alhaji badamasi ya shigo yace "na baka ita tunda yaseer baya sonta sanan ya saketa dan Haka hajiya saude ta janye ma kafin taga bacin raina"momy tace "don me zakace ka bashi ita bayan kasan furucun da aljanin nan yayi dazun akan husnah na dik Wanda ya rabeta sai ya kashesa sanan ni nafison husnah tasamu lafiya tukunna"Alhaji badamasi yace "kanki akeji ke kikasani amma baki isa ki kara hadamun munafunci irin wanda kikaimun ba wajen hajiya saude saboda yaseer ya rabu da muneeba karyarki Tasha karya munafuka kawai zan fita aiki ba zama zanyiba zan dawo kai kuma ka fadawa iyayenka maganar auren ku da husnah ka aureta "ya fice hafeez ya dafe kai sam momy batasonsa da husnah da yaseer takeso bazata fito ta fada musu bane kawai husnah na gama cin abinci ta wucesu batace musu kala ba ta wuce daki abinta ta rufo kofa,




tsohuwa ta gani tsaye a gaban gadonta da sanda a hannunta ta rufa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login