Showing 30001 words to 33000 words out of 103127 words

Chapter 11 - DUHU Book Complete By Slimzy .txt

Slimzy   

19 Jun 2024

12483

lokacin da yace "bani plate din abincin"galala momy tayi tana kallonsa takasa magana sa hannu yayi ya karba da cup din tea din jikinsa na rawa gashi yayi shirun zuwa aiki momy ta rakasa da ido tana kallonsa ko kiftawa batayi,


daddy ne ya shigo dakin cikin shirin fita sai kamshi yake zabgawa momy kallo daya tayi masa ta kauda kanta cike da takaici shima haushinta yakeji yace "ina takardar da yaseer ya baki jiya?"shiru momy yayi cikin zuciyarta tace takarda?tabbas taga lokacin da yaseer yaba daddy takarda amma ita be bataba tace "wace takarda kuma?"hajiya rabi tana kokarin shigowa tace "takardar sakin husnah daya rubuta mana ai biyu ya rubuta yaba daddy nasa ya baki dayake bakiso arabashi da ita yasa kika boye naki na daddyn ma kika dauke"daddy ya dubi hajiya rabi ya jinjina kai yace"da kyau yaseer ya saki husnah ko?dama ai bai dora mata idda ba tunda ko tarewa batayi ba batamasan da auren ba yanzun ta mijinta aljani takeyi dan haka nasan yanzun yaseer yaje aiki zan kirasa a waya aida ransa inji sanan ya rubutomin sabuwa saboda hafeez inbashi aurenta suje su karata dama shi ya tattagota ninafara ko kwanto ma akanta dikda ban tabbatar ba"yana gama magana yasa kai ya fice bai jira ta bakin momy ba,gaban momy kuwa dukan uku uku yakeyi wato yaseer takardar sakin husnah ya rubuto?hajiya rabi ta katse mata tunani tace "tunanin me kikeyi zainab?"ta sheke da dariya tace "husnah itada yaseer saidai ido dan tuni nasa yaserr ya rubuta takardar saki uku zaa damkawa yarki idan ma kinga takardar kin boyene to karyarki Tasha karya idan kinga yaserr be sawakewa husnah ba to niko shi wani ya mutu ne"momy ta watsa mata kallo mai cike da tsana tacev"tirre da halinki rabi dik kutungwilar da kike kullawa wallahi ta Allah bataki ba burinki bazai taba cika ba kuma yaseer da husnah babu Wanda ya isa ya rabasu dan tun husnah na cikin yaseer ke dawainiya da ita dan haka sihirin da kukayima yana gab da karyewa dan yanzun haka yaseer na cikin dakin husnah yana ciyar da ita"shekeke hajiya rabi ke kallon momy ta sheke da dariya tace "mafarkin da kikayi jiya ko tabadai ciki tare da mijinta aljani yana kwanciya da ita"tasa kai ta wuce tana dariya momy tayi kwafa maganar hajiya rabi na karshe yayi mata matukar zafi hajiya rabi kuwa ranta ya sosu cewan da tayi yaseer na tare da husnah a daki dan haka yasa ta nemi waje ta labe,


momy kuwa tsaye tayi jikin labulen dakin tana iya hango yaseer yana rike da plate din yake taku sautin takalminsa a tiles yasa tayi saurin juyowa tanayin ido hudu dashi ta mike fuskarsa ce ta shiga canja mata ta koma yaseer ta rikide ta komata Abraham tsoro ya kamata tadan ja da baya cike da fargaba take kallonsa tana ganin yadda yake rikida,ganin tanaja da baya yasa yaseer dan furgita ta zauna gefen gado bakinsa dakyar yasamu damar fusta addua ayatul kursiyyu yayi Abraham na tunkarosa ya koma da saurin jin zafi da hucin wuta a tattare da yaseer rikidewa yayi ya shige jikin husnah wani abu daga idon husnah ya fito zirrrrr kamar walkiya ko shocking Yana wuta ya shiga bakinsa ji yayi harshensa ya daure jikinsa sai tsuma yakeyi bugun zucuyarsa ya tsananta yana zama a gabanta Yana kallonta ita kuma a Abraham take kallonsa shi kuma tuni fuskarta ta rikide masa ta koma abun tsoro fuskarta ta koma baka kirin irin yadda yagani jiya take hakoranta suka zazzago masu tsayi guda biyu idanuwanta a warwaje gadhin kanta kamar kaya yaseer ya runtse ido dakyar ya kira sunan Allah kamanninsa suka koma nasa sak tace "meyasa kake canjawa kana komamun Abraham yanzun naga ka rikide ka koma mutumin nan daya rungumeni jiya"a sanyaye tayi maganar idanuwansa a rufe ruff baya kallonta daya bude ido kamanninta ke sauyawa haka ya dibo abincin a hankali yace bude bakinki "ta bude bakinta batare da tayi masa musu ba ya bata ta kara karba a haka yake bata har sau biyar daga bisani yaji wata iska mai karfin gaske ta mamaye dakin windows din cikin dakin ke kadawa fanka ta fara zazzagowa kamar zata fado ya juya yaga wardeobe dinta na buguwa yanayo kansa da karfin gaske aka fincike plate din abincin aka wurgar gefe ji kake tasssssss tasa hannu ta toshe kunnuwanta aka angije yaseer daga gefen gadon ya fadi kasa wata murya yakeji tana magana sam naya fahimtar me ake fadi ya mike cike da tsoro saidai ya kasa gudu ya kuma kasa kallon inda take ganin drwer nayo kansu yasa hannu ya fuzgota ta suka Fadi kasa ta fada kirjinsa kamar kugiya aka dauketa aguje momy ganin wanan dramer ta shigo dakin ganin yaseer warwas a kasa tace "an tureka ko yaseer tashi tashi"tana kokarin rukosa yayi murnushi yace "zan iya tashi"ya mike ya juya ya kalleta rabe a gefen gado sai gumi takeyi ta bishi da kallo ya fice yana fitowa a idon hajiya rabi ya fito ta zaro idanuwa waje tana kallon yaseer cike da tsananin mamaki tasa hannu ta murza idanuwanta tabbas shine a hankali ta taka ta koma sashenta dakyar take taka kafarta saboda yadda jikinta yayi nauyi jiri na nenan daukarta....


ko ganin gabansa yaseer bayayi ya fito kicibis sukayi da muneeba ta zuro hijab tana sauri da slippers a kafafuwanta turus tayi ta kallu agogon wayarta tana kallonsa cikin tuhuma tace "yadai har yanzun baka wuce aiki ba?me kakeyi a sashensu momy naga kamar daga nan ka fito"nannauyar ajiyar zucuya ya sauke tana kallon yadda kwayar idanuwansa suka kada cikin tuhuma take kallonsa gabanta ya tsananta faduwa ruko hannunta yayi ya shafa cikinta yace "babu komi mun dan tattauna da daddy ne yanzun ma sauri nakeyi zan fita in tafi"ta waiga bataga motar daddy ba tace "ai daddy ya dade da fita naga fitarsa ta window"gabansa ya fadi bayaso ranta ya baci sam yarasa meya shiga jikinsa yakejin yana damuwa da wanan yarinyar sam yar da ko ganinta bayasonyi bayi rasa nasaba da kamannin da yake gani da wata yarinya dayasani a baya kwalla taji ta cuko a idanuwanta ganin ya rasa me zaice masa kawai ta gifta ta gefensa ta wuce juyawa yayi yana kiranta "muneeba muneeba"ta juyo yadda idanuwanta suka kada yasa yaji ya damu saidai sauri yakeyi yayi latti dole ma ya wuce yasan idan ya dawo akwai daru ya kada kai ya wuce cikin damuwa da tsananin faduwar gaba ya bude mota ya shige yaja ya fice,






cikin kuka ra fad'a dakin ummahnta wadda ke tsaye tana kaiwa da komowa tana sakawa tana kwance yadda zatayi da wanan lamarin da yake shirin bullowa muneeba ta fada kan gado ta fashe da kuka tace "ummah nashiga uku yaseer zai dawo hankalinsa akan husnah yarinyar da tuni muka dauke masa hankali akanta idan ya dawo hayyacinsa na tabbatar tawa ta kare a gidan nan gaba daya tarewa zaiyi wajenta dikda dai nasashi ya rubuta mata takardar saki"ummsh ta karaso tace "mummunan tashin hankalin da nake ciki kenan takardar saki kuma yabawa daddy saidai daddy ya yar da takardar yanzun haka baa ganta ba"zabura muneeba tayi tace "shikenan tawa ta kare nashiga uku ummah kiyi wani abu ya zamuyi mutafi wajen boka gashi karyar ciki nayi masa sam banaso hankalinsa ya koma kan waccen matar aljan din"ta Dora hannu akai kuka takeyi hawaye na zuba ummah ta dafata tana kasa da murya tace "ki kwantar da hankalinki inada tabbas akan boka nakan tudu matsafi ne na gasken gaske na tabbatar sai yasa husnah tabar gidan nan dan haka na yanke shawarar mu shirya yau muje wajensa inaso yanxun ki kwantar da hankalinki yarinyar da rainon aljanu ce me zaayi da ita? itama durkusar da ita zamuyi yarda ko sallah kin taba ganin tunda ta dawo tayi?dan haka kara burkitar da ita zamuyi nida zanga aljanin ma zance ya sake saceta tashi maza kije ki shirya"muneeba ta share hawaye cikin kidimewa tace "karyar cikin da nayi fa?"hajiya rabi tace "zamuje wajen boka akan hakan inta kama a sama miki ciki dik zaayi kedai tashi maza kije ki shirya"ta mike cikin sauri a kidime tasa hijab din gaba a baya ta fito kicibis sukai da kanwar momy mahaifuyar husnah kallon kallo sukayi ko gaisheta batayi ba tsaki taja mata ta watsa mata harara ta wuce,


momy na zaune ta zabga tagumi batasan zuwan yar uwar tata ba ji tayi an dafata ta zabura ta juyo cike da furgici ta dafa kirjinta tace "har kin tsorata ni ya naganki haka?da sassafen nan?"zama tayi gefenta tace "dubi yadda kika sauya?kina nan kina sakacin naki ko?ina husnah"momy ta nuna mata dakin da husnah ke ciki kwance tace "tana ciki takicin abincu saboda aljaninta jiya sun samu matsala yadda yake zuwa suyi hira su wuni tare bezo ba"jinjina kai tayi tace "tabdijan lallai kinyi sakaci aljanin ke shigowa har cikin daki?kina jinta tana maganganu kamar zautacciya zainab?sakacin da kikayi ya saceta shi kike Shirin karayi?kina zaune batare da an nema mata maganin da zasu rabu ba?wai ma tsaya kin tabasa karatun kurani ko kina azkar ke kanki balle kisata tayi ki koya mata?husnah na tabbatar ko sallah batayi tunda ta dawo ko?"momy jikinta ya mutu ta tsare yar uwarta da ido taja nannauyar ajiyar zucuya ta fashe da kuka tace "wallahi wallahi damuwa tasa dik na rikice narasa yadda zanyi"tsaki tayi mata kawai ta mike ta nufi dakin da husnah take.....
*******
hafeez ya gama shiri ya makara zai fita ya tuno da takardar daya dauka ya saka a aljihunsa da sauri ya karasa basket din kayan wanki ya dauko wandonsa ya ciro takardar abinda yayi tozali dashi ne ya kare ware iso ya sake karantawa yaseer ya saki husnah?ya karasa sakin da yayi mata?ya jinjina kai amma shin daddy yasan hakan da momy?take zucuyarsa ta bashi amsa basu ganiba kenan takardar ya kawo bai samu basu ba ta fadi shi ya dauka ya gani i har daddy da momy da husnah basu ganiba bata saku ba ya kamata ya maida takardar nan yasa takardar a aljihu ya fito yana sauri sai kamshin turare yake zubaea ummahnsa tace "to dan gidan daddy albishirinka"cak ya tsaya ya juyo yana kallon ummah ta jinjina masa kai yace "yesssss..... daddy zai dawo ko?"ta jinjina masa kai meenahl ta fito itama tsalle tayi yacev"alhamdulillah ummah daddy zsi dawo a daidai dan Alhaji badanasi yace in turo maganar auren husnah"ummah jikinta a mace ta daga masa kai zuciyarta cike da tsoro ya fice cikin farin ciki aiki zashi yasan zasu hadu da yaseer zsi masa albishir da zai auri husnah zai rabata da gidan kamar yadda ya fada Allah allah yakeyi ya isa office dinsu yana parking motarsa ya kalli ta yaseer ya tabbatar yau ya shigo wajen aiki daukar takardar yayi yasa a aljihunsa ya fita yana takunsa mai cike da takama da kasaita ya tura kofar office din yaseer kansa a kasa cike da rudani yake bincike baiga hoton yarinyar ba yadaisan yanada hotonta har a office dinsa yana kallo bai ganiba hafeez ya turo kofa hade da sallama yaseer ya d'ago yana kallonsa shima ido cikin ido yake kallonsa yaseer zaiyi magana hafeez ya rigasa "nazo ne inyi maka murnar sakin husnah da kayi"dammm gaban yaseer ya fadi kansa ya shiga juyawa take ya tuno da yarinyar tabbas sunanta husnah hafeez yace "kabani lasisin auren husnah yanzun tunda baka bukatarta ni ina bukatarta zan aureta aijanin nata ya kasheni Zan aureta in rabasu ai bansan daddy baiga takardar ba ina tashi aiki zsntafi da takardar in mikawa momy tunda yarwa akai na tsinta"yana masa murmushi ya fice gumi ne ya karyowa yaseer ya dafe kansa meke faruwa dashi ne?wace takarda hafeez ke magana shin yarinyar Daya sani yana karami itace wanan husnah mai aljanu ta gidansu?mikewa yayi tsaye kansa na juyawa ya shiga cewa "no no inaaas"ya kwashi wayoyinsa cike da tashin hankali ya nufi hanyar fita ko ganin gabansa bayayi......


******
shiru husnah ke zaune bayan Antynta ta gama mata nasiha jikinta ya mutu sosai saidai can kasar zucuyarta soyayyar Abraham ke azalzalarta,....tsaye yake a kofar shiga dakin momy na zaune a parlor itada Anty sun saka karatun kurani suna tattaunawa sukaji tassss an jefo speaker radio home theater kasa ta fadi an kashe kauri sukaji alamar an kona radiom kallon juna sukayi Anty tace"an kona radion saboda karatun da nasa"tayi murmushi wucesu yayi ya shiga dakin ta jikin kofa ta gansa ya bullo kamar an wurgosa mikewa tayi tana murtsuka ido tana kallon kofa kallom kallo sukeyi wani farin ciki ne ya lullubeta ta ruga da gudu ta fada jikinsa ya runtumeta kamm kamar zai maidata cikinsa ceke da kewarta yayi kissing goshinta ya dago fuskarta hawaye tagani a idanuwansa tace "kuka kakeyi?"ya girgiza kai yana hawaye yace "ba kuka nakeyi ba"kunnuwanta ta rike alamar ban hakuri yayi saurin cirewa yace "nine ya dace in baki hakuri dana azabtar dake kuma nima na azabtar da zucuyata jnacan cikin daji cike da kewarki"murnushi tayi ta kara fadawa kirjinsa tana dariya tana kuka tace "nayi kewarka mijina ina bukatarka a kusa dani"ya shafa kanta ya zame dankwalin kanta ya tura kansa gefen wuyanta ya shiga romancing dinta yana shasshafa ta bankarewa tayi tanajin wani yarrrr idanuwanta a rufe tana sauke numfashi cakk ya dauketa yace muje?"ta gyada masa kai batare da tambayar inda zasu ba yabi ta jikin bango zasu shige tace "zaka dawo dani?"ya gyada mata kwi idonsa kirr akanta yace"zan kone in har ina nan antynki zata kona ni"ranta ya baci ta fara jin haushin Anty dikda tayi mata alkawarin sallah da ibadah tayi mata alkawarin bazata sake biyewa Abraham ba amma soyayyarsa bazata barta sukuni ba giftawa sukai suka fice....


******
muneeba da hajiya rabi zaune a gaban boka ya tasa musu kwaryar tsafi a gabansu wani ruwa mai kaman jini yanata tafasa fuskar husnah ce amma fuskar taki fitowa yayi surkulle ya mike ya daga hannunsa sama ya kira sunanta ya kalli kwaryar sam husnah bata waigo ba boka ya jinjina kai tabdijan akwai matsala muneeba tace "boka banason in koma gidan nan in tarar husnah bata haukace ba hauka nakeso tayi tabar gidan banaso ta rabi yaseer idan har yaseer ta rabeshi kishi zaisa in hadiyi zuciya in mutu"da sauri hajiya rabi ta toshe mata baki ya dauko wata kwarya da magani ciki ya bata yacev"kinga wanan kwaryar da maganin nan?"ta jinjina kai yace ki kira sunan husnah da yaseer ki fasa kwaryar kice na Farraka tsakanin husnah da yaseer harabada babushi babu ita "ta karba tana murmushi yace "sanan maganar cikin da kikai masa karya"da sauri suka gyara zama yace "akwai mafita"cikin kosawa hajiya rabi tace meye mafitar?fada mana boka ko meye zamuyi"boka yayi ihu ya mike ya hura wata hoda saiga jariri mai shegen kyau suna gani suka kalli juna yace"akwai aljanin da zai shiga jikina yanzun zaiyi amfani dake idan kin yarda yana gamawa ciki zai shiga wanan yaron zaki Haifa"hantar cikin muneeba ta kada ta jinjina kenan shine zai kwanta da ita?ta kallesa yadda yake gumi bakin kirin jikinsa sai walkiya yakeyi da datti ta kalli ummah ta ta yatsina fuska ta bata rai hajiya rabi ta rad'a mata tace "biyan bukata yafi dogon buri dan haka muneeba ki yarda kawai"muneeba gabanta ya fadi boka fa?aljani zai Mata ciki kuma cikin mutim tayaya hakan zai kasance?.....


husnah na rungume a jikin yaseer suna zaune a wata kujera a bakin ruwa mai shegen kyau ya mike tsaye yana zagaye wajen ta mike cikin farin ciki tace "ina ne nan?"yayi murnushi yace "kona fada miki baki saniba amma lambun soyayya ne"tayi tsalle sai kuma ta bata rai tace "su momy zasu shiga basu ganniba"cikin yanayi na tsoro tayi maganar yace "zasu ganki bazasu taba tunanin ba ke bace dan haka ki saki jikinki nayi kewarki taho"ba musu ta taho ya shiga tsokanarta yana zagaye wajen tana dariya kwanciya yayi ta fada jikinsa ya zame rigarta ya ajiye gefe ta rufe ido ya rada mata a kunne "kunya kikeji?"ta girgiza kai yakai bakinsa nononta ya soma tsotsa yana lumshe ido tana shafa kansa......




*WANAN LITTAFIN NA DUHU NA KUDI NE 300 ZAKI BIYA KI KARANTA IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFE BA*




3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK


SHAIDAR BIYA TA WABAN NUMBER 08036953516 KO KATIN MTN TA NUMBER....








*SLIMZY*✍🏻




23


bude labulen parlorn yayi babu kowa sai tv ke aiki yasan dama kannensa basa nan tsakiyar parlorn ya tsaya sai gumi da yake had'awa yace "momy!!"cikin daga murya yake kiran momy tana kitchen itada mai aikinta tana kokarin dama kunun gyada ta jiyo sautin muryarsa yana fad'in "momy kina ina?Dan Allah ki fito ki warwaremum wanan matsalar da nake ciki kaina zai fashe"cewar yaseer shiru momy tayi ta kalli mai aikinta tace"kamar yaseer ko?anya yaseer ne kuwa?yanzun ai yaseer na wajen aiki"tace a fili ya sake kiran sunanta mika ma mai aikinta bokitin tayi tace "tace rikemun ina zuwa ba lafiya"tana kokarin daura zani ta fito ta gansa tsaye yanayin da taga yaseer ya furgitata gabanta ne ya yanke ya fadi dakyar ta karaso cikin parlorn tace"kai yaseer lafiya naganka haka?"ta kalli kayan jikinsa fes dashi yasha bakin wando da farar riga shirt alamu daga wajen aiki yake gumi yakeyi sajensa ke d'igowa da gumi tacw"yaseer meke faruwa naganka cikin wanan yanayin?"zama yayi a kujera ya dafe kansa da ya dau zafi ya runtse idanuwansa fuskarta ya gani ya budesu momy ta zauna gefe tana kallonsa tana kuma saurarensa kasa magana yayi sai jujjuya kai yakeyi yana kokarin tuno yarinyar da yake gani ta sake magana tace "yaseer kayimun magana kodai ba kai bane kaima aljanun sun shafeka?"da sauri ya kalleta da jajayen ido harta furgita yace "momy wacece yarinyar nan ta gidan mu?wadda ke dakin momy da hafeez ya kawota?tanamun kama da wata dana taba sani a baya"murmushi momy tayi ta d'aga hannunta sama tace"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah,lallai yaseer ka dawo hayyacinka saidai ka kasa fadin wacece saboda lokacin da tazo baka hayyacinka"yace "momy kamar ya bana hayyacina gashi yanzun inayi miki magana?"ta girgiza kai kawai tace "husnah ce,itace yarinyar da kake yawo da hotonta wanda tun tana yarinya da aka haifeta mahaifinka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login