Showing 6001 words to 9000 words out of 103127 words

Chapter 3 - DUHU Book Complete By Slimzy .txt

Slimzy   

19 Jun 2024

11807

ta girgiza kai tace "husnarka ce yaseer,husnah yar uwarka kuma matarka da akai muku aure tun haihuwarta wadda ta bace tanada shekara biyu yau da batabta kimanin shekara sha takwas kenan"yaseer yayi shocked yana kallon momy da takeso itama kanta ya juye a fusace cikin zafin rai da zafin zuciya yace "momy wai meyasa kukemun zancen wata husnah da bansanta ba idan ma da ita na saketa!!!"gaban momy ya fadi ta zabura ta shararawa yaseer mari "ka tafka kuskure babba yaseer meyake damunka?koda yake babu laifinka amma wanan yarinyar husnah ce "husnah kallonsu takeyi kamar tababbu itama ta juya tana kallon hafeez da idanuwansa suja kad'a sukai jajir kamar gauta,


yaseer ya dafe gefen fuskarsa cike da takaicin momy ya koma gefe ya Shiga dialing number muneeba....tana kishingide tana kallon tashar star life taji vibration da sauri ta dauka cike da shagwaba tace "sweettttt ka dawo ne nazo na bude maka kofa?"tana kokarin mikewa tsaki taji yaja tace "lafiya dai ko?"idanuwansa jajir yake kallon momy rungume da husnah yace "inafa lafiya ni dik nakosa in dawo inji duminki ga momy nan ta biyeea hafeez daga zuwa zamu wuce akwai wata budurwarsa shine muna zuwa fa momy na ganinta ta kirata da husnah ta amsa wai husnarta ce data bata"zabura muneeba tayi ta kalli wayar taga tabbas waya takeyi ba kunnenta bane tace "husnah?wace husna ce tata kuma babu wata husnah sweet karka kuskura ka yarda ni babu wata husnah"ta kashe wayar ta zube Turus cikin tashin hankali ta tuna da maganar da boka nakan tudu ya fada mata akan husnah na nan da rai tana wata duniyar ta zabura kamar zararriya ta nufi bedroom dinta cikin sauri ta zaro after dress abayarta ta zura ta nufi sashen mahaifiyarta,


yaseer kara burkicewa yayi yace "gaskiya bazai yuwuba ga muneeba can ta burkice fatansa karta rikice masa bari yasamu momy mutane dankam wajen.... Abraham ne ya bullo ganin jamaa babu mai ganinsa sai husnah tana ganinsa cikin farin ciki tayi tsalle ta share hawayenta gani tayi ya tsaya cakkk yana kallonta yana hawaye ga mahaifiyarta a gefe tace"nasan bazaka taba barina ba nasan zakazo gareni kazo ko?kazo katafi dani kaji nayi kewarka"ta shiga mika masa hannu tana bude hannuwa alamun ya rungumeta ya girgiza mata kai hawaye tagani a idanuwansa mutanen wajen harda masu daukar husnah video cakk ta tsaya ganin yana hawaye yana kallonta yace mata "ki kwabtar da hankalinki husnah dik inda kike ina tare dake gani nazo gareki"murmushi sukaga tayi a kufule yaseer yace "momy Dan Allah kuzo mubar nan wajen mubar wanan mahaunaciyar"wani kallo Abraham yayiwa yaseer wanda baisan Yana ganinsaba cikin zuciyarsa yace da sannu zan shayarvdakai mamaki momy tace "ai kamata zamuyi mutafi da ita saboda ka duba halin da take ciki wanan ya tabbatar mun da cewar husnah aljanu ne suka sacemun yarinya"ta fashe da kuka tana laluben wayarta hafeez ya nisa zuwa yanzun mugun haushin yaseer yakeyi dakyar ya hadiyi miyau yace "momy mutafi da ita"galala yaseer yayi husnah ta turje a kasa tana tsananin tsoronsu tace "ina zaku tafi dani?kunsanni ne ko kuma kunaso ku rabani da mijina ne?"momy ta girgiza kai takai hannu zata shafata husnah ta ture hannunta taja da baya ta matsa jikin Abraham gabaki daya ta rikice ta makarkalkale Abraham yadda tayi da hannunta ya Basu mamaki rungumeta yayi sosai yana sauke numfashi yana shafa kanta cikin takaici babu yadda ya iya haka yace "tare zamu tafi tafi dik inda kike a fadin duniya tare zamuyi rayuwa,ruwa da iska rani da damuna babu abinda zai rabani dake husnah"ya shafa kanta ya mike....








Alhaji badamasi ne ya shiga dakin momy bai ganta ba ya fito ya dudduba bai ganta ba kitchen ya laika mai aikice keta faman had'a abincin rana tana ganinsa ta tsugunna "Barka da war haka Alhaji"


"barka,ina zainab take?kota shiga sashensu yaseer ne na duba dakinta bansameta ba gashi nan ma babu ita"jimm kadan tayi tace "tare suka fita da yaseer bata dan jin dadi ne kamar sunje asibiti"


muneeba ce ta shigo cikin sauri ko ganin gabanta batayi tana ganin daddy ta kirkiro murmushi ya washe baki yace "munee kece da rana tsaka"


"ehh daddy na shigo ne can din shiru"jin motsi ya fito da hajiya rabi taba ganin Alhaji badamasi ta natsu ta kirkiro kunya ta tsugunna ta gaisheshi yacev"yanzun nake tambayar inda zainab take ashe ta fita"ummahn tace "hmmm ai bata fadamunba da zata fita"yayi jimmm bata fada ba?yace "mai aikinta tacemun taje asibiti batada lafiya"a ran hajiya rabi tace bakin ciki zai kasheta saima an daura aurenmu gobe nida kai alhaji badamasi katse mata tunani ringin wayarsa tayi ta kalli muneeba wadda keta gumi ta kosa daddy ya kauce ta labartawa momy tashin hankalin daya duso ta daddy yace"gashi tana kirana "


"hello zainab yanzun nadawo gida da rana ina tambayar inda kike kina ina ne?"momy ta share hawayenta tace "Alhamdulillah gamunan dawowa"daddy gabansa ya fadi jin muryarta a dishe alamar tana kuka yace"lafiya kike kuka ko har yanzun baki hakura akan maganar Aurena ba?"ta girgiza kai kamar Yana ganinta tace"yau shekara goma sha takwas rabonmu da husnah yau Allah ya had'a fuskokinmu nida yata can na tsinceta "ta fada masa wajen wani shock yayi yacev"what?husnah fa kikace kin tabbatar husnah kika gani zainab?"zaro ido hajiya rabi tayi ta dafe kirji ta Kasa boye mamakinta da tsoronta a fili tacev"husnah kuma wace husnah data mutu kodai taga yar mutane tanaso ta daukota ta laqaba maka alhaji"dagawa hajiya rabi hannu yayi yacev"gani nan zan sameku a wajen bari inzo"ya kashe wayar jikinsa na rawa anga husnah idan yaje wajen ya tabbatar zaigani in husnah ce iidan ba ita bace ficewa yayi cikin sauri yabar hularsa a parlor,


muneeba ta rushe da kuka "ummah nashiga uku husnah fa husnah ta dawo husnar da akwai auren yaseer akanta shikenan munzama mu biyu kedashi"ummahnta ta rungumeta cikin tsananin bakin ciki da hassada tace "husnah bazata taba zama mallakin yaseer ba indai ina raye husnah da mahaifiyarta bazasu taba farin ciki a cikin wanan gidan ba harabada ki share hawayenki"ta share mata hawaye Anry sadiya kanwar hajiya rabi ce ta shigo cikin parlorn tacev"meye na kuka keda yaseer ke hannunki ko babu boka babu malam kissa kadaib ta isheki ki kwace miji kuma kinadani"ta bugi kirji muneeba gaba daya a rikice take.....


******
ganin taron jamaa yasa daddy ya parker motarsa daga nesa ya fito yana taka kafafuwansa ya shiga turmitsitsin mutane tun daga nesa idonsa ya sauka akan husna wadda kanta babu dankwali ya kalli goshinta ya haska masa fuska tabbas wanan yarsa ce husnah yana tura mutane ya shiga hajiya zainab ta fashe da kuka ya kamo hannun husnah ba musu ta mike ta rikesa Abraham na rike da dayan hannunta ta juya tana magana daddy sakin baki yayi Yana kallonta yadda take magana kamar zararriya tacev"tare zamuyi rayuwa ko mijina?nasan bazaka barni ba kaji nifa bansan wadanan mutanen ba amma zan bisu tunda kace tare zamuyi rayuwa"


"innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"daddy yacev tabbas Aljanu ne suka sace masa yarsa ya ruko hannunta cikin bakin ciki ya waiga Yana neman yaseer ta hangensa gefe yaseer na mamakin yadda daddy ya biyewa momy zasu dauki wanan yarinyar mara hankali yace "yaseer zo nan mu riketa mukaita mota"hannunta ya sumbule a jikin na Abraham ta turje yaseer ba yadda zaiyi cikin bakin ciki ya fuzgeta yayi mota da ita hafeez yayi ajiyar zuciya burinsa ya cika muradinsa ya ganta yanzun yasan Inda zai ganta ashema ta gida ce yau zai labartawa ummahnsa labari mai dadi kasan zucuyarsa mugun haushin yaseer yakeyi ya jefata a mota ya rufe daddy ya zauna a gaban mota yaseer ya karbi key ya tada motar hafeez da momy mota daya suka shiga,


Abraham mikewa yayi yana yawo a sararin samaniya a sama yana kallon yadda motarsu husnah ke tafiya dole zai koma duniyarsu zaije yayi bankwana da jinsunsu zaije ya azabtar da narjisu kafin daga bisani yazo su shimfida rayuwa sabuwa shida matarsa husnah.....




narjisu ce cikin jinsinsu tana numfarfashi jin kugiya na ihu tasan Abraham na hanya ta dubi hajiya babba tacev"Abraham ya zama nawa tunda aka dauramun aure dashi saidai nasan bazai yafemun ba zai azabtar dani amma rabbas tsugunu bata kareba dan baxansa idon ganinsa Yana rayuwa da jinsun bil'adama ba"zuhraliyya hawayen rashin husnah takeyi ta saba da ita sosai yanxun ya zaayi ta ziyarci husnah?ya zaayi taje ta sanar da ita shirin narjisu?dibbbb Abraham ya sauka a cikinsu yayi kan narjisu......


******
fitowa da husnah sukayi momy da hafeez yaseer kuwa sashensu ya nufa muneeba na ganin haka ta nufi sashenta ko kallon inda husnah take batayiba tsananin kishi daya rufe mata ido burinta kawai ta shiga ta shiryawa yaseer maganganu tayi masa kuka,


daddy gefe ya koma gidan iyayensa ya kira ya sanar musu da ganin husnah da yan uwansa maza da mata ya shiga kiran waya yana fada musu ganin husnah....


kalle kalle husnah keyi a cikin gidan sam hankalinta yaki kwanciya gefe da gefe take kallo ko zatagansa daddy yace "husnah"ta waigo tana kallonsa yace "menene?"ya ruko hannunta tace "mijina nake nema"murmushi yayi yace "ga mijinki can ya shiga sashensa wajen yar uwarki mijinki yaseer"tana kallonsa wani iri tace "sunan mijina Abraham ba yaseer ba dan jinsin jinn"gaban daddy ya fadi hajiya rabi kuwa ji tayi tamkar ta fashe kissa kawai zatayi amfani dashi wajen ribatar zucuyar daddy akan husnah kar ya taba yarda yarsa ce....








yaseer na Shiga muneeba ta shigo ta fada jikinsa ya cire mata rigar jikinta kamshin turarenta ya baibaiyeshi yaja numfashi ya sauke ta fashe da kuka yana bin kayan jikinta da wani irin kallo idanuwansa sun kankance tsananin damuwar da yake ciki wanda besan daliliba gabaki daya hankalinsa da tunaninsa sun gushe tunda yayi tozali da husnah muneeba ta dago fuskarta hawaye na zuba tacev"ya yaseer yanzun shikenan wanan ta zama husnah bakuyi bincike ba bakuyi komiba kun daukota kun kawota?sanan idan wanan ta kasance husnah shikenan fa mun zama mu biyu matanka"ya rungumeta sosai "cikin bacin rai nake sam ganin yarinyar nan ya gusar mun da tunani nashiga matsananciyar damuwa,muneeba bansanta ba bansan daga inda ta fitoba amma daddy da momy suna lakabamun ita a matsayin matata yarinyar da gabaki daya mahaukaciya ce alamu sun nuna matar aljan ce tayaya zasu lakabamun ita?tou wallahi akwai matsala dan zan samu daddy akan hakan kar hankalinsa ya gushe a kan wanan yarinyar renom Aljanu"wani farin ciki ne ya lullube muneeba ta share hawayenta ta Shiga shafa fuskarsa a hankaki ya runtse idanuwansa fuskar husnah yake gani dazun ji yayi ta hade bakinsa da nata tana sauke numfashi tana tsotson lebensa yana shafa kanta a zahiri yana tare da ita amma a bad'ini hankalinsa ya gushe gaba daya daga jikinsa.......






*LITTAFINA NA KUDI NE KI BIYA KI KARANTA IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTA ZAKI BIYANI HAKKINA A INDA BABU DAN BAN YAFE BA*
*NAIRA 300 KACAL ZAKI BIYA DAN MALLAKAR WANAN LITTAFI*


3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK


SHAIDAR BIYA 08038953516 KO KATIN MTN TA WANAN NUMBER


DOMIN KARIN BAYANI KI TUNTUBI MARUBUCUYAR TA WANAN LAYI 07042277401


*SLIMZY*✍🏻


















13


Daddy ne ya shigo fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "ina yarinyar take?"ya tsaya daga bakin kofa momy batare da ta kallesa ba tace "tana ciki ta d'an kwanta ne yaseer ne ya shiga wajenta Yana ciki"


"Yaseer kuma?"momy ta ansa da "ehh"kawai ta mike tana kokarin barin wajen muneeba ta tsugunna ta gefen kofar da daddy ke tsaye tace "daddy barka da yamma "


"barkadai muneeba kin shigo,kema kinzo ganin husnar da akace ta dawo ne? tana ciki mai gidanki ma Yana wajenta"rasss Gaban muneeba ya fadi ji tayi kafafuwanta sun sage ta kasa mikewa daga tsuggon da tayi hajiya rabi ta karaso tana faraa ta kashewa muneeba ido tace "ki shiga mana ba kince kinzo ganin husnah bane ki shiga"muneeba murmushin karfin hali tayi daddy ya matsa yace ki shiga"


hajiya rabi tace "daddy dama angwama maka farfesun ne nace akawo maka ga dambun shinkafa nayi nasan zakaso abincin gargajiya"daddy ya washe baki yace"mashaaaa Allah ki zubo ki kawomin nan"hajiya rabi ta mike suka hada ido da momy ta kashe mata ido hade da gwalo tana yar dariya wani bakin ciki ne ya lullube momy ta Kasa magana muneeba kasa shiga ciki tayi ta zauna a kujera lallai yaseer wato zuwa yayi wajen husnah?she cant believe yaseer yaje wajen husnah me yajeyi?tambayar da tayiwa kanta batada amsa kenan kishi ya turnuke mata makoshi idanuwanta sun kad'a sunyi jajir saboda takaici kamar ta fashe da kuka takeji,




husnah kallon yaseer tayi tace "meyasa ka shigo Inda nake?ina mijina?me kazoyi waye kai?"tambayar data jero masa Kenan tana kallonsa wani mugun kallo yayi mata yace "ke ki shiga hankalinki ki saita natsuwarki na tabbatar kinada hankali kinsan me kikeyi ba mahaukaciya bace kinzo kina mana zancen mijinki waye mijinki ke kikasanshi kuma kisani idan harke ba yar daddy bace tattarawa zakiyi ki bar mana gida ko ganinki banasonyi"ran husnah ya baci a ranta tace wayeshi wanan?a fili tacev"waye yace maka nima inason ganinka?nima banason ganinka dan bansan ko waye kaiba kazo kana farfadamun magana ance maka nima inason zama a wajenku ne?suwayeku bansankuba kun raboni da ahalina"mtsww taja tsaki ran yaseer yayi mugun baci babu abinda ya tsana sama da tsaki a rayuwarsa,ya daga hannu zai kai mata yaji an rike hannunsa mamaki ya kasheshi ya waiga baiga kowaba yana kokari fuzge hannunsa yaji ya rike Abraham ne tsaye gefen yaseer wani abu na fitowa daga idanuwansa jajir yana Shiga jikin yaseer ji yayi jikinsa kamar ana zuba masa rushi wani shocking yakeji nan da nan sanyi na neman rufeshi jikinsa na rawa yayi kokarin sauke hannunsa sai yaji an saki hannun anyi kwafa tsoro ya kamashi ya juya ya kalli husnah wadda ta tsaresa da ido tana kallonsa jikinsa na tsananin rawa yabar dakin yana fitowa yayi tozali da muneeba tana ganinsa ta mike kallon tuhuma take binsa dashi jikinsa a sanyaye ya kashe mata ido ta kauda kanta gefe tace a can kasam makoshi "muje"tayi gaba yabi bayanta momy tace "husnah ta tashi ko yaseer"ya tsaya yayi shiru kamar ya fadawa momy abinda ya faru sai ya Kasa Yana inda inda bakinsa na rawa yace "ummm ahhh ehh ta tashi momy tana ciki"mamaki ya kashe momy ta girgiza kai yaseer na son husnah tasani wanan abun da yakeyi kadai yake daure mata kai dashi kamar wanda aka canja ta ajiye daddumar da take ninkewa ta wuce ciki ta tura kofar tun daga bakin kofar take jiyo maganarta,


"ina katafi mijina?"a shagwabe husnah keyiwa Abraham magana dake gefenta zaune yace "babu inda naje ina tare dake kisa a ranki ko baki ganina ina tare dake hussy"ta jinjina kai ta shafa cikinta tace "inajin yunwa"yayi shiru yace "yauwa gashi na siyo miki abinda kikafi so"yasa hannunsa ta gefen gado ya bude take saiga bakar leda cike da hollandia da gasasshiyar kaza ya bude mata ya yago kazar yace "bude bakinki matata"Yana kallonta cike da so da kauna ta natso ta manne da jikinsa ta kwantar da kai a kafadarsa ya bata ta amsa tanaci Yana bata hollandia ta gama karba"....momy dake tsaye tana jiyo sautin maganar husnah gaba daya tsoro ya kamata kardai husnah da suka dauko ba mutum bace?cikin tsoro da furgici take ta juya bayanta babu kowa gumi ya jika momy kasa daga kafarta tayi ji tayi ta kasa bude kofar ta shiga ta juya,


Abraham ya kalli sashen kofar yaga tsayuwar momy shi yasa mata nauyin da bazata iya shigowa ta katse musu soyayyarsu ba yana gama bata ya ajiye gefe ya janyota jikinsa ya rungumeta sosai yana shafa kanta cikin rawar murya tace "yaushe zamubar nan gidan ni banason zama a nan gidan abraham ka canja mana gida banason wanan mutumin daya shigo dazun"cije baki Abraham yayi idan ya dauki husnah sun koma rayuwa cikin mutane bazata iya rayuwa dasu ba ya shafa gashin kanta ya tallabo fuskarta ta Kura masa Ido Yana kallonta yace "husnah kiyi hakuri kinji? wadanan da kike ganinsu iyayenki ne"damm gabanta ya fadi ta gyara zama daga rukon da yayi mata bugun zuciyarta ya tsananta ta kasa magana bakinta sai rawa yakeyi tace "iyayena....iyayena ai sun mutu"ya girgiza mata kai yace "iyayenki basu mutu ba tsananin kaunar da nakeyi Miki ce tasa na daukeki na maidake cikin dangina"idanuwanta suka cicciko da hawaye yace "shhhh karkiyi kuka ko kina fushi ne dan na daukeki?ki kwantar da hankalinki kinji bazamu rabu ba"ta gyada masa kai zuciyarta na rawa kenan wanan mahaifiyarta ce tace "to meyasa ka daukeni?"


"saboda ina sonki"yace zaiyi magana yaji motsin mutane yace "ina zuwa"sam ba lokacin yakeso tasan shi aljani bane ya gyara mata zama ya shige toilet yana shiga ya rikida ya koma aljaninsa ya bace tabi hanyar toilet din da kallo momy ce suka shigo da hafeez da kanwar momy sai aminiyar momy tare suka shigo suna hada ido da kanwar momy "ikon Allah Zainab Allah maji rokon bawa tabbas wanan husnah ce"hankakin momy baya jikinta kallon yanayin husnah takeyi tana kallon yadda take kallon toilet hajiya hafsat kawar momy tace "husnah"da sauri husnah ta kalleta batare da ta amsa ba kanwar momy tace "husnah menene ya muka ganki hakan ko dik baccin ne kina kallon toilet?"ta jinjina kai tace "mijina ne ya shiga ciki"da sauri suka kalli juna da momy,momy ta jinjina musu kai tace "husnah da kuke gani Aljanu ne suka saceta ta koma rayuwa cikinsu abinda nake zargi Aljani ya auri husnah kuma ta shaku dashi sosai"hafeez ya harde hannuwansa a kirjinsa ya tsura mata ido ji tayi kamar ana kallonta ta kai idonta suka hada ido da hafeez kallon da yake mata yasa ta Kasa jure kallonsa ta kauda kai yayi murmushi ta turo baki tace "ni kadaina kallona"hafeez a Ransa yace "kallonki yana karamun energy ne soyayyarki na karuwa a zucuyata"a zahiri kuwa cewa yayi "shikenan naji nadaina kallonki bari inzo kibani labarin mutanenku jinnn "tayi murmushi taanajin haka ganin husnah na dariya su momy suka fita,


hajiya hafsat tace "tabdijan hajiya zainab kina cikin jarabawa dan wanan babbar matsala ce ga kuma matsalar wanan makirar hajiya rabi"numfashi taja ta sauke tace "kedai bari gashi Alhaji yace gobe da safe kafin daurin aurensa da rabi zamuje asibiti gwajin jini akan husnah ta rigada tace masa ai gwaji husnah ba yarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login