Showing 54001 words to 57000 words out of 103127 words

Chapter 19 - DUHU Book Complete By Slimzy .txt

Slimzy   

19 Jun 2024

12482

ganmu a haka ni kabari"dariya yaji tana kokarin kwace masa yace"tou shikenan naji Tashi muje kiyi alwala kiyi sallah nima masallaci zani"daga tsaye ya mika mata hannu ta kama lallausan hannunsa ta rike ya d'agota kafarta ce ta rike ta kasa motsa kafarta yana kokarin janta kafar ta lakwashe tayi yar k'ara da sauri ya tallabota "lafiya lafiya?"


"kafa na yaya yaseer na kasa motsa kafana"ya dauketa cakk ta boye kanta kirjinsa kunya takeji matuka zuciyarta na harbawa ya shiga da ita ciki,


ta jikin labule Abraham ya makale yana kallonsu inuwarsa ta gani bata gansa ba ta kalli yaseer ta kara kallon labulen yaseer ya juya baiga kowa ba yace"shiga kiyi alwala'ta jinjina masa kai haka kawai ta tsincu kanta cikin matsanancin tsoro ya nemi gefen gado ya zauna tana shiga ta gansa a jikin bangon toilet din cikin mummunan kama idanuwansa sunyi jajir wasu ruwa na zubowa na jini a guje ta kwaso da gudu ta fito tana haki ta durkushe "lafiya?"ta girgiza masa kai tana nuna masa cikin toilet din wucewa yayi ciki ya leka baiga kowa ba yana waige waige daga bayansa yaji anyi masa tsaki ya jinjina kai ya fito yace "taho muje in rakaki kiyi alwalar"


"tsoro nakeji yaya yaseer"tace muryarta na rawa,ransa a bace yake yasan tsoratata kawai akeyi ya rukota bata iya taka kafarta ya shiga da ita toilet din duhu kawai take gani yasa ta runtse idanuwanta ya rik'eta da kyau tayi alwalar suka fito ya shimfida dadduma yace "zo kiyi sallahr bari inje masallaci"girgiza masa kai tayi "banaso ka tsaya a nan nidai"kada kai yayi jin ruwa ya kece a garin ya kalli window walk'iya ke haskawa ya shige toilet don yayi alwala tana zaune kan dadduma take ganin windown na kad'awa a hankali labulayen na budewa bishiyoyi masu tsawon gaske take gani d'akin ne ke rikidewa Yana koma mata irin d'akinta nada a duniyarsu Abraham kallon ko ina takeyi kamar wadda ta warke makanta ya fito yace "yadai"nuna masa dakin takeyi da yatsanta yace"yadai?"tace "d'akin yana canjamun ne"


"ba abinda ya canja a d'akin kinji muyi sallah kinga an soma ruwa gashi inaso intafi gida da wuri kar daddy yasan cewa bana gidan yayi fushi dani"ta gyada masa kai suka tada sallah....


******
"muneeba kina nufin tun fitarsu hajiya saude yaseer yabar gidan nan har yanzun bai dawoba?daga cewa ya tafi asibiti?"ta jinjina kai cikib fushi take gumi ne kawai yake karyo mata tace "Anty sadiya tunda yaseer ya dawo hankalinsa na rasa gane kansa nasan wanan shegiyar bak'ardagar mahaifiyar nan tasa ce ta karya asirin da mukayi masa gashi kiri kiri yana neman juyamun baya ko ince ya juya ma tunda hankalinsa gabaki daya ya koma kan sauran jinnu"y'ar dariya sadiya tayi tace"ki kwantar da hankalinki sai munsa auren nan ya k'are tsakaninsa da ita yanzun abinda zaayi zo kiji?"ta rad'a ma muneeba a kunne muneeba kallonta takeyi ta gyad'a mata kai tace "alamu sun nuna so yakeyi ya kwana a can wajen ta tunda har yanzun bai dawoba yanzun zan koma cikin gida ki aiwatar da abinda na fada miki Na tabbatar tunda yanason cikin nan dik inda yake a gigice zai dawo"murmushi muneeba tayi "shiyasa nake sonki Anty sadiya ina matukar jin dadin kasancewarki cikin gidan nan idan baki nan gidan kango yake komawa,suka tafa Anty sadiya ta fita,




momyn husnah na zaune cikin ruwa taji shigowar mutum sadiya ce harta gifta ta dawo ta tsare hajiya zainab da ido ta kalli cikinta da kyau yadda yad'ab tasa tayi shiru hajiya zaibab itama kallonta takeyi cikib wani yanayi na rashin fahimta tace "lafiya?"jinjina kai sadiya tayi tace "ehh lallai abu ya bunkasa tunda gashi ya leko"tayi tsaki ta wuce momy ta kalli cikinta gabanta ya fad'i ta manta da irin rigar dake jikinta saboda cikinta ya fito yasa bataso tanasa kayan da zai nuna,


daddy ne ya shigo dakin fuskarsa a daure tace "sannu da zuwa"ya amsa ciki ciki dik ranan girkinta haka yakeyi baya ma zuwa sashenta yau ma yazo ne kila saboda husnah bata gidan nan,
wayar daddy ce ke kara ya duba muneeba ce yacev"lafiya muneeba ke kirana cikin daren nan?"


ya dauka "hello muneeba ya akayi meyafaru"sautin kukan muneeba ne ya gauraye kunnuwansa kirjinsa ya buga cikin sassarfa yace"lafiya muneeba meyafaru keda waye?waye menene ina yaseer din?"a rikice yake maganar daga inda take zaune ta harde kafa ta kara rushewa da kukan karya tace "daddy cikina da marata daddy ciwo sosai yaseer ya fita tun yamma bai dawoba"ta rushe da kuka "ya fita bai dawo ba yanzun meke faruwa?"ta kwalla ihu cikin wayar tana kiran mararta daga inda momy ke zaune take jiyo sautin kuwwar muneeba tayi saurin mikewa daddy ya kashe wayar momy tacw "lafiya?"wata uwar harara ya watsa mata yace "kinsan komi kinsan koma menene tunda kun dauki husnah daga gidan nan kun kaita gidan hajiya saude ne dan a dauki hankalin yaseer daga muneeba gashi yanzun batada lafiya kukan mararta takeyi kuma kinsan juna biyu gareta"


"innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"momy tace cikin tashin hankali kenan dama yaseer baya gidan? hajiya rabi ce ta fito cikin kuka "alhaji ga muneeba can babu lafiya Alhaji ciwon mara takeyi kuma kasan cewar karamin ciki gareta damuwa ma kadai ya isa ya Sanyata tayi b'ari"sadiya ta zunguri hajiya rabi ta nuna mata cikin momy daya tasa gaban hajiya rabi ya yanke ya fad'i,
cikin bacin rai daddy ke kiran wayar Yaseer ringing takeyi amma bai dauka ba yace "Baya daukan wayata"hajiya rabi ta fashe da kuka "ni bari inje in duba y'ata insan halin da take ciki"tayi gaba daddy da sadiya suka rufa mata baya,


*****
nusrah ta kwankwasa kofar dakin husnah kasantuwar Yaseer na ciki da sauri ya mike zai duba mai kwankwasawar ta rukoshi "ina zakaje?"ya kalleta ya girgiza kai "ana kwankwasa kofa ne?"ta jinjina kai gabaki daya a rude take tunanin yadda zata kwana a wanan dakin takeyi komi na dakin ya sauya ita kadai ke ganin hakan ya bude nusrah ce "yaya yaseer momy ce tace wai ka shafawa Anty husnah maganin nan kada ka manta kafin ka tafi tace idan ka gama shafa mata ka sauko kasa" jinjina mata kai wayarsa daya ajiye gefen gado yaga tana haske ya duba miscalls dayawa yagani harda daddy yasan zaisha fad'a dan haka bazai ma dauka ba sai ya gama shafa mata maganin gashi yasan wanan kafar dake ciwo bata rasa nasaba da Abraham ne ya rike mata kafafuwa,


ya karaso "zo zan shafa miki magani,nasan kinji abinda malam ya fad'a dazun ko?"ta jinjina kai gabanta ya yanke ya fad'i tunowa da yadsa ya mammatseta da safe yasa ta kallesa zatayi magana yace "shhhhhh"ya soma kokarin zuge mata zip din rigarta jikinsa ne kawai ya kama rawa wata irin iska mai karfi yaji tana bugawa cikin d'akin hatta da fankar dakin saida ta soma bugawa kamar ana kadawa ya kalli sashen madubi yadda yakeyi kamar ana tursa Abraham ne yake kallon komi na dakin na matsowa yana bugawa cikin tsoro da furgici husnah tace "fanka zata fado mana yaya yaseer"ya zare mata rigar ta kasa wata iska ta bugo window globe din dakin daya ya fad'i kasa tassssss ta zabura ta rungumesa tsamm nonuwanta suka hadu da kirjinsa wani dumi yaji jikin husnah ga wanan kamshin dake tashi mai tayar masa da tsigar jikinta kara matseshi takeyi ganin komi na dakin na motsi ciki fanka sai bugawa takeyi tayi nan tayi nan ya riketa sosai yana kokarin janyeta daga jikinsa tana shigewa cikin tsananin tsoro ta soma hawaye hawayenta na d'iga a kafadarsa tana fadin "Dan Allah yaya yaseer kada ka tafi tsoro nakeji kaji?"


Abraham na tsaye cikin tsananin fushi yake watsa hannuwansa komi na rikicewa a d'akin waigowa yayi gefensa yayi tozali da mahaifinsa cikin kayan saki da sandarsa yana kallonsa farin gemun sa ya kalla ya koma jajir yasan mahaifinsa cikin fushi yake yasa zaiyi magana ya d'aga sandarsa sama saiga wata iska da tasa Abraham yayi matukar tsorata yasan mahaifinsa fushi yakeyi dashi yasan tunda ya saki iskar nan azabtar dashi zaiyi ya fuzgi Abraham suka bace,


kamar kiftawar ido sukaji shiru yadda iskar d'akin ke kadawa haske ya mamaye ko ina idanuwansa ya sauka akan nonuwanta da suka cicciko ya tsareta da ido ita kuwa idonta rufe yake ta sadakar cikin tsananin tsoro......


*kuyi maneji zakujini da yamma insha Allah inada mara lafiya*


*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFE BA*


07042277401
08036953516




*SLIMZY*✍🏻


33
muneeba ce kwace shab'e shab'e tana rike da mararta jin takun tahowarsu yasa ta kara volume din kukanta murkususu take tana fad'in "wayyo Allah zan mutu wayyoo marata innahlillahi wa innah ilaihi rajiun yaya yaseer kana ina kadawo?kaji meyasa ka tafi ka barni?"tun daga kofar shigowa suke jiyo sautin kukanta da abinda take fad'a kuka takeyi sosai hawaye ya wanke mata fuska bankado kofar hajiya rabi tayi tana fad'in "nashiga uku muneeba muneeba meyasameki haka?"ta rungumeta tana kallon daddy dake tsaye a kofar shigowa tace "Alhaji kana kallo fa muneeba kwance take tana murkususu dik kiran nan da akeyiwa yaseer bai dauki wayat ba tun dazun ake kiransa kaga kenan ya tafi can ne dama da niyyar ya kwana wajen husnah"ta fashe da kuka momy ce ta shigo dakin sanye da hijab tana kallon fuskar muneeba yadda takeyi tana yatsina fuska tana kuka ta tabbatar da shiri ne murkususu takeyi ganin Momy ta rushe da kuka tace"daddy momy tasan cewar yaseer ya tafi wajen husnah ne saboda dama kafin ya tafi wajenta ya soma biyawa cemun yayi bari yaje wajen momy"ta rushe da kuka ta shige jikin ummahnta ta kara rungumeta ran Alhaji badamasi ya baci ya kalli momy da ta saki baki tana sauraren yadda muneeba ke zuba kirsa yace "zainab kinbani matukar mamaki wallahi kuma dagake har hajiya saude zanyi maganinku kun shirya haka ne daman dan ku wulakanta wanan yarinyar ko shiyasa aka fake da aljanu aka kaita can gidan to gobe gobe idan Allah ya kaimu zani in dauko y'ata in dawo da ita gidan nan tunda rashin mutunci ne"momy tace "Alhaji dik wanan maganar da kakeyi bansan komi akaibafa dan ni banyi magana da yaseer bakida baki ba yadaicemun zaije asibiti a duba lafiyarsa daganan ban sake ganin yaseer ba Alhaji"tsawa daddy ya daka mata saida ta razana tayi baya kamat xata fadi yace "karya kikeyi munafuka kawai duk abinda kuke shiryawa nasani kallonku nakeyi to tun baaje ko inaba asorinku ya tonu gobe goben nan husnah zata dawo gidan nan"muneeba ta kwalla kara ummah ta rungumeta "Alhaji ko zaa kai muneeba asibiti ne?"


"nakira doctor gashinan zuwa zaizo a dubata already yanzun ruwa akeyi kuma kinsam idanuwana basuda lafiyar da zan iya tuki daddare"cikin bacin rai yake maganar cike da haushin yaseer ya fice momy hawaye ne ke zubo mata ta kallesu tana kallon sadiya na boye fuska tana murmushi bataga laifinsu ba sai laifin yaseer daya tafi ya jawo yau ake kiranta munafuka,juyawa tayi ta fice daga dakin tana fita suka saki shewa muneeba tayi zumbur ta mike ta zauna tana kallon ummahnta ta toshe bakinta kar dariya ta kwace mata hajiya rabi tayi murnushin nasara tace"na yarda da tuggunki sadiya yanzun kiri kiri kin had'a abinda ya hargitsa Alhaji na kuma tabbatar yadda yaseer keson cikin nan gobe zai rasa sukuni akan hakan bazai sake waiwayar renom aljanu ba"suka sheke da dariya momy na tsaye ta jiyo muryar sadiya tana fad'in "ni wanan mara hankalin bata gabana yanzun yadda zamuyi da wanan cikin daya leko nakeso musan nayi dashi dan Alamu sun nuna tuni yayi kwari"gaban momy ya fadi ta shafa cikinta ta sake saurarawa da kyau ummah taji tace"wanan cikin ai cikin biyu ne kodai yazo duniya a mace ko kuma ya zama shege dan bazai taba zama d'an Alhaji badamasi ba indai ina raye"hmmmm "ummah kenan ai kawai kashe cikin nan zamuyi idan yazo duniya ko ya zama shege komi zai iya faruwa gara musan nayi dashi tun kafin yazo "hajiya rabi ta jinjina kai tayi kasa da murya momy batajin mai suke fad'a ta saurara da kyau dariyarsu kawai taji cikin dimuwa da rud'u ta soma tafiya ko ganin gabanta batayi cikin rashin saa ta zame ta fadi ta zauna da duwawubta bayanta yayi kara kadan wani radadi ne ya ratsata daga tsakiyar kanta ta dafe kwankwasonta da yakeyi kamar ya balle daddy ne ya taho cikin sauri likita na biye dashi ya gifta ta gefenta yana kallonta durkushe ko kallo bata ishesa ba jin sautin takun takalmi yasa muneeba ta makale jikin Momy tana sauke numfashi daddy da sallama ya shiga likita ya tsaya daga kofa daddy yace "Bismillah doctor shigo"ya kalli hajiya rabi yace "gyarata hajiya ga likita zai dubata ko zamu Basu waje?"cikin fuskar damuwa hajiya rabi tace "bazan iya barin muneeba cikin wanan halin ba har yanzun baasamu yaseer ba ko?"daddy yayi tsaki kawai ya sake ciro wayarsa....


******
d'ago husnah yaseer yayi daga kafadarsa yayo tozali da hawayen dake zubowa a idanuwanta yarrr yaji a jikinsa zuciyarsa ta kara narkewa da tsananin kaunarta da tausayinta ya zura mata idanuwa, idonsa ya sauka akan kirjinta da suka cicciko wani miyau ya hadiye ya sake hadata da jikinsa yasa harshensa yana tsotse hawayen dake zubowa a idanuwanta tana jin harshensa a fuskarta taji tsigar jikinta ta Tashi kirjinta ke bugawa sama da kasa yana kallon yadda take numfashi ya kasa dauke idanuwansa daga kirjinta da suka dauki hankalinsa nipples dinta jajaye yake kallo yakai hannunsa yad'an shafa da sauri ya dauke hannunsa jin wani abu na yawo jikinsa yasa ya lakuto turaren da malam ya bashi ya soma shafa mata a sassan jikinta babu inda bai kai hannunsa ba gaba daya yaseer ya rikice ya kalli wandonsa yadda bananarsa ta mike tsammm ta tsaya cikin tsananin shaawarta yake gashi idanuwanta a rufe taki bude ido ya kwantar da ita yazo ta gefenta yana shafa fuskarta "husnah husnah ki bude idanuwanki kinji?"ta makale kafad'arta tace "banaso inga kalar dakin nan sak dakin da mukai rayuwa ne nida Abraham ya canja dakin ya maida kalar wancen"yaseer ya kalli cikin dakin sam bega abinda ya sauya ba yace "tou kitashi kinji dare nayi gashi inaso intafi gida"rukosa tayi a hankali ta bude idanuwanta ta Tashi ta zauna kallonsa takeyi tuni yayi nisa wajen kallon jikinta ta kalli jikinta tsirara ta kallesa tayi saurin saka hannu ta rufe kirjinta tace "ina kayana nidai?"ya shafa keyarsa ya dauko rigarta dake gefe ya mika mata tace"ba ita nakeso insaka ba"ya mike ya bude drawer wata rigar bacci yayi tozali da ita mai laushi yacev"karbi wanan kisa"tasa hannu a kunyace ta karba tasa rigar yace "Bari insamu momy babu abinda kikeso ko?"ta gyada masa kai ya fice kalle kalle takeyi ta bayanta taji kamar motsi ta zabura ta diro daga gadon tana kalle kalle,


"yaseer yanzun nakeso ince ya zaayi gashi har yanzun ruwan nan bai tsayaba Kuma dare yayi gashi banaso ka kama hanya ka fita kadaiga abinda yasameka ballantana yau da nasan dik inda aljanin nan yake cikin fushi yake"yaseer yace "momy to tsoronsa zamuji babu abinda zai faru zan iya tafiya ai yanzun bawani dare bane goma da minti sha biyar"ta girgiza kai tace "ban aminceba ka kwana a nan tare da husnah mugani mai zai faru zuwa safiya da nace sai su nusrah su kwana da ita to kagansu nan matsorata sunce tsoro yau sukeji"ya jinjina kai cikin zuciyarsa kuwa fari tass saidai yasan muneeba nacan tana jiransa gashi bai fada mata cewar? wajen husnah zai kwana ba fatansa dai kawai kar ta had'asa da daddy momy tace "yusrah ta kai muku abinci ko husnah bataci komi ba"
"muje kibani abincin na barota wai tsoro takeji dakin ya canja mata zuwa dakinsu na duniyar aljanu"momy ta girgiza kai cike da tausayin husnah yaseer yabi yusrah kitchen ta zuba musu abinci ta bashi ya nufi dakin tana tsaye jikin kofa yana turawa ta dafe kirji ta runtse ido zatayi kara yace 'nine"ta ruga ta fada jikinsa tana sauke numfashi "dakin ne yake rikidewa"a tsorace tayi maganar gadon taga kamar yana matsowa taja da baya ya rukota "ya isa gani bazan tafiba zan zauna tare dake"yayi kissing din goshinta tayi saurin kallonsa ganin shine yasa ta sadda kanta kasa Abraham yana yawan kissing din goshinta da zarar aka tsoratar da ita haka....


*****
durkushe Abraham yake gaban mahaifinsa yana rokonsa cikin tashin hankali "baba karka daureni idan ka daureni komi zai iya faruwa"cikin fushi mahaifinsa ya bude baki zaiyi magana wani mulmulallen abu kamar kankara ya fito ya fashe a fuskar Abraham ya kwalla kara da saida dajin ya amsa yace "zan cigaba da azabtar dakai da zarar ka cigaba da bibiyar wanan bil'adamar wadda ba jinsinka ba shin ka taba ganin inda akai aure tsakanin jinsin mutum da namu jinsin?"cikin daga murya yake magana idanuwansa na fito da wata irin wuta tana haske idon Abraham yana jin rad'adin zafi har kwakwalwar kansa ganin yadda yake runtse ido yasa baban Abraham yace"ka bude idanuwanka ka kalli cikin idona"cikin tsawa Abraham ya bude ido ya kalli babansa wata azaba ce tasa ya zube kasa kwance yana kare fuskarsa da take tafarfasa yasan karfin mahaifinsa tsaf zai halakasa akai sa can inda ake girke marasa karfi cikin jinsunsu "zaka sake bibiyar waccen bil'adamar?"ya girgiza kai mahaifinsa ya saki sandarsa akansa wadda ta dannesa ko motsi bayayi dik girma da karfi irin na Abraham murkususu yakeyi yana kokarin tashi ya kasa narjisu na gefe ta sunkuyar da kai Gaban baba ya kalleta yace "ki cigaba da bibiyarsa ke matarsa ce na aura miki shi tun tuni dan haka dik abinda yayi ki sanar dani dauresa zanyi nad'an wani lokaci"kallon sandar yayi take ta kankance ta koma karama ta rage nauyi ta koma hannun baba ya kai hannu ya cafko Abraham a wahale idanuwansa sun firfito hawaye yakeyi na zaa dauresa bazai taba iya minti ashirin ba batare da husnah ba sanadin soyayyar da yakeyiwa husnah yau mahaifinsa ke azabtar dashi akanta?gashi ta butulce masa tayi masa alkawarin bazata barsa ba dikda kasancewarsa aljani amma son zuciya da butulci irin na bil'adama ta mance da kaunar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login