Showing 96001 words to 99000 words out of 103127 words
ina ganinki kasheki kawai zanyi"tsoro ne ya cika hajiya rabi dakyar ta yunkura ta mike jikinta da kafadarta dik ya sage muneeba tabi mahaifiyarta da kallo fuskarta jajir hajiya saude tace"yanzun mal muje cikin gida baban parlor ko?"malam ya jinjina kai ya fice hajiya rabi na hada hanya ta fito sadiya nayin tozali da ita ta fuzgi akwatunta ta baza aguje tayi gate cikin sassarfa itama tabi bayanta a waje suka hade "Anty lafiya?meyafaru kinga yadda fuskarki tayi kamar kinyi hatsari"cikin tsoro sadiya ke maganar tana waige waige "nidai mubar gidan nam kafin su fito su cinmana a nan natabbatar sunji abinda yasamu muneeba ko?"gumi ne ya karyowa hajiya rabi cike da nadama a karo na farko tace "na cuci rayuwar yata ma cuci rayuwata sadiya yanzun ina zamu gashi Alhaji badamasi yace idan har muneeba wani abu ya sameta sai ya daureni"jim haka sadiya taja akwatinta tayi gaba hajiya rabi na biye da ita hannu akai take rusa kuka tana waigen tamfatsetaem gidan tana fadin "nashiga uku na lalace na shiga uku shikenan ni rabi yanzun ina zani"....
****
shiru sukai dukkansu daga yaseer hafeez da husnah dake parlorn sautin kukan yaseer ne ya karade cikin parlorn tsananin bakin ciki yasa yake kuka husnah cikin tattausan lafazi tazo gabansa ta durkusa ya dago idanuwansa shabe shabe da hawaye Yana kallonta yadda yake kallonta taji wani abu ya karya mata zucuya ta fashe da kuka yayi saurin zamowa daga kujera ya tsugunna gabanta "husnah kukan mai kikeyi husbah?meyasa kike kuka?kina zargin na dauko cuta daga jikin muneeba nasa miki ko?wallahi"be karasa ba ta rufe masa baki ta kwantar da kanta a kafadarsa tace "haba yaya yaseer wanan kukan da kakeyi bakasan shi kadai tadamun da hankali zaiyi ba?bakasan bazanso ganinka cikin wanan yanayin ba?shin muneeba kake ganin laifi ko laifin ummah?"yayi saurin kallonta yana nazarinta ta girgiza kai ta share hawayenta da bayan hannunta tace"muneeba batada laifu hasalima yanzun itadin abar tausayi ce dan baasan menene a jikinta ba batada laifi ba ita tasa kanta ba idanuwan mahaifiyarta ne suka makance har tasata ta aikata abinda ta aikata Dan Allah ka tausaya mata yaya yaseer ko zakai wani hukunci kabari tasamu lafiya tukunna"zucuyarsa tamkar zata tarwatse yakeyi daya tuna furucin daddy na karshe dayaji akan muneeba ta aikata zina da boka,sanan furucin muneeba na daga masa hankali cewar cikin dake jikinta ba nasa bane cikin boka ne kuma ya mutu, yaseer ya cije bakinsa saida lebensa ya fashe jini na zuba a bakinsa yace "muneeba ta cuceni ta cutardani da danginmu ta bata mana suna da ace zanyi ido hudu da wanan bokan da saina rabashi da ransa"hafeez ya jinjina kai yace"ko baka rabasa da Ransa ba Allah kadai yasan Azabar dayake ciki tunda ya mutu yanzun yaseer dik wanan bashi bane a gabanmu ka duba furucin matarka"ya nuna husnah da tayi tsumu jiki a sanyaye tayi saman rakuma a jikin yaseer hafeez ya cigaba da magana "maganarta abun dubawa ce yanzun abinda zaayi shine tashi zakayi muje cikin gidan tunda kaga malam na ciki musan abinda ake ciki"kin magana yaseer yayi zucuyarsa cunkushe take da tsananin bakin ciki miyaun bakinsa har d'aci yakeyi masa ya kallesu kawai ya mike ya nufi hanyar bedroom dinsa saida yakai tsakiya yace "kuje amma bazan iya shigaba bazan taba iya kallon fuskar muneeba a halin yanzunba domin bakinkirin nake ganinta bazan taba jurar ganinta ba zan yanke hukunci a lokacin da be kamata ba dam haka kuje kawai"yana gama magana ta nufi bedroom dinsa da besan kalarsaba yaune ranar farko daya Shiga Yana shiga yasawa dakin key ya zube a jikin kofar ya dafe kansa wasu sababbin hawayen bakin ciki yakeyi yanaji husnah na bubbuga kofar dakin ta baya take fadin "haba masoyina haba mijina ka bude kofar nan ka saurareni nicefa matarka husnah kayimun alkawarin farantamun rai akan dik abinda nakeso"cikin sassanyar murya take maganar da tattausan lafazi zucuyarsa na azalzalarsa ya bude amma bazai iya budewa ba kasa magana yayi ya mike ya zare rigar jikinsa yana zuwa ya fada gadonsa ya kifa ciki husnah jin bayi da niyyar budewa ranta a bace ta shiga dakinta ta gyara fuskarta ta sako hijab ta fito ta samu hafeez tayi tagumi a parlor yana ganinta yace"yaki budewa ko?"ta jinjina kai tace "muje can gidansu momyn nasan yayi fushi ne zai bude zan lallashesa"hafeez ya saci kallon husnah tayi kyau ta koma normal mutum kamar ba husnahr Abraham ba tare suka fice.....
hajiya saude na rungume da muneeba malam yana rike da kofi ya juye ruwan zamzam husnah da hafeez suka Shiga daddy na ganinsu yace"ina yaserr din?ina kuka barosa?"husnah ta sunkuyar da kai batace komiba suna hada ido da muneeba wani tausayinta ya lullube ta ta fashe da kuka tana kallon muneeba itama muneebar ita take kallo tayi murmushin karfin hali ta mika mata hannuwanta ta taho ta rukota ta durkusa a gabanta "yaya yaserr ya tsaneni ko husnah?nasan bazai sake marmarin rayuwa dani ko zama daniba na tabbatar yanzun hakan ya sakeni"shhhhhh husnah tace "be sakekiba kuma bazan taba bari ya rabu dakeba idan har zai rabu dake to tabbas saidai ya rabu damu tare saboda kedin yar uwata ce"sosai sukaba mutanen cikib parlorn tausayi muneeba ta gyara zama sosai jikin hajiya saude tana sanye da hijab amma gumi ya gama jika wuyan hijabin gyaran murya malam yayi sukayi shiru "kun tabbatar kun amince akan ayi Mata addua ta haife abinda ke cikinta ko mutum ne koba mutum ba?"dukkansu a tare suka hada baki "mun amince"malam ya jinjina kai yace"wanan addua ce nayi a ruwan zam zam gashi Wanda mafi akasari masu nakuda akeyiwa su haifi abinda ke cikinsu dan wasu ma idan sukasha lokacin haihuwa beyiba zasu haihu a lokacin da izinin Allah dan haka gashi tasha ta shafe cikinta sai musa ido mu zubawa sarautar Allah ido"momy ta girgiza kai ta kalli muneeba rike sa kofin tana kokarin sha tausayin yarinyar ya lullubeta ta kauda kanta gefe ta fashe da kuka muneeba tashanye adduar husnah ta taimaka mata suka hude cikinta aka shafe cikin da adduar
"Tou Alhamdulillah yanzun ni zan tafi tunda bamusan lokacin da nakudar zata tashiba ko?saidai kar a barta ita kadai asamu wani yq zauna tare da ita"hajiya saude tayi ajiyar zuciya tace "mungode malam Allah ne kawai zai biyaka abinda kayi mana Allah ya saka maka da alheri"suka hada baki tare suka amsa da "Ameen"malam ya tashi hafeez yabi bayansa yacewa su momy "Bari in kaisa gida zan dawo zuwa yamma"suka fita tare da malam daddy ma ficewa yayi sakamakon kiransa da akayi a waya....
husnah ta yunkura ta mike muneeba ta rukota tayi saurin juyowa tace"ina zakije?"murmushi husnah tayi tace"zanje ne nidasu nusrah muyi aikin abinci duka gidan nasan yanzun bazaa samu sukunin dafa wani abuba yanzun zanje in dawo kinji?"ta jinjina mata kai shaawa sukabasu dukkansu tasa kai ta fice suka bita da kallo,
suna nan zaune ko minti goma sha biyar husnah batayiba da fita muneeba ta fara jin ciwo motsawa tayi dakyar ta ruko kasan mararta da yayi mata nauyin gaske tace"ciwo nakeji momy"tana kallon hajiya saude jikin hajiya saude ya mutu nan da nan gumi ya soma karyowa muneeba ta soma murkususu a kasa mararta na ciwo addua takeyi tana yarfa hannu tana kiran sunan Allah tana kiran sunan yaseer,
husnah ta gama hada abinci ta Shiga dakinta tayi wanka ta fito daure da towel a jikinta ta gansa zaune gefen gadonta tana ganinsa ta hada rai dan fushi takeyi ya saci kallonta suna hada ido tayi masa wata harara ya mike ya zuba hannuwansa cikin aljihunsa yace"fushi kikeyi dani saboda matata ta aikata zina?"damm gabanta ya fadi ta kallesa idonta jajir zatayi magana yace "Tou ki cigaba da fushin nima zan tafi inbarku kinga tafiyata"yasa kai ya fice kasa magana tayi sai zama datayi gefen gado tana tunanin me yaseer ke nufi shin besan kaddara bace?koko beyi imani da Allah bane?"nusrah ta shigo dakin cike da damuwa husnah tace "lafiya na ganki hakan meya faru?kin duba abincun yayi kuwa?"
"ehh yanzun nadawo daga dubawa Anty husnah,yaya muneeba nacan ta soma ciwo"kuuuuuu husnah taji cikinta na kugi cike da tashin hankali ta zaro Ido cikin sauri ta zura rigar data ajiye zatasa ta sa ta fice ko ganin gabanta batayi
*NAGODE KWARAI DA ADDUOI DA UZURIN DA KUKAIMUN ALHAMDULILLAH MUBEENA AN SALLAMEMU A ASIBITI SAIDAI JIKIN SAI A HANKALI A TAYATA DA ADDUA*
*GA MAI BUKATAR WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAI BIYA YA KARANTA*
07042277401
08036953516
*SLIMZY*✍🏻
51
tafe yaseer yake cikin mota tuki yakeyi hankalinsa gaba daya baya tare dashi tunanin cin amanar da muneeba tayi masa yakeyi don me husnah zatace ya yafe mata yanzun inda ciwo ta dauko fa?da yanzun tasa masa shi gaba daya hankakinsa a tashe yake dole ya dauki husnah suje a gwadasu horn yakeyiwa mutanen da sukai cincirindo a bakin titi shiru basuda niyyar matsawa a fusace ya fito daga motar "dalla kunzo kun taru a gefen titi sai kace...."cakk harshensa ya tsaya kallon hajiya rabi yayi jini na zuba a goshinta gefenta sadiya ce kwance warwas babu alamar rai a tattare da ita wani jiri ne ke neman daukarsa suka hada Ido da hajiya rabi kallonsa takeyi kamar tasanshi saidai ta kasa ganesa yaseer surutan da takeyi ne ya furgitasa "kun gani ko motace ta bugeni boka ya mutu yabar muneeba da ciki a jikinta tanacan a wani kauye yanzun gashi Alhaji yq sakeni umm kungani ko ninasan sharrin matarsa ne itace ta karya asirin da nayiwa Alhaji"damm gaban yaseer ya yanke ya fadi ya karasa inda take jikinsa na rawa wani mutumi daga bayansa yace "kai bawan Allah zaka kai kanka ne wajen wacce take tare da tsinuwar Allah bakajin kalaman da take fada ai bataga komiba yanzun tafara gani daga gani asiri tayi ya dawo mata shedaniya ka dawo Baya 'jikin yaseer a sanyaye ya hadiyi wani miyau mai kauri jikinsa babu kwari ya juya hajiya rabi ta mike ta ruko yaseer "karka tafi baka bani kudiba kabani kudi kawai ninasan me zanyi dasu"wani saurayi dake tsaye ya zabga mata mari ya fincike ta daga jikin yaserr ya hankadatw "yanzun nan mota zatazo a kaiki asibitin mahaukata a cillar dake daga ganin yadda kuke dambe a titi da abokiyar tafiyarki bakuda dangi "
"dambe?"yaseer yace a sanyaye
"ehh dambe sukeyi suna surutai mota tazo ta bugesu waccen kanta ya bugu a titi dayar kuwa har yanzun bata motsi kamar ma ta mutu"goge gumi sa yayi yace "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun umm"
"kasan su ne?"da sauri yaserr ya girgiza kai 'bansanta ba"cikin sauri yabar wajen mutane na tsaitsaye ya Shiga cikin motarsa ya had'a kansa da sitiyarin mota yanajin jiniyar mota emergency na asibiti yaja motarsa yayi kwana ya koma gida dakyar yake tukin motar ya iso kofar gida kasa fitowa yayo daga ciki motar ya kunna karatun alkurani ya kwantar da kanta a jikin seat na mota
kuka husnah keyi shabe shabe rike da muneeba dake durkushe akan gwiwoyinta gabanta ke budewa wani abu na turowa sai tayi saurin hade kafa hajiya saude ta riketa da kyau ummah hadiza addua take tofa mata ta saki wata kara cikin ikon Allah saiga abu ya fado sukuf a kasa kallon juna sukeyi a razane cike da tsoro da furgici ummah hadiza ta kalla sak mutum saidai babu ido babu komi babu baki a fuskar sai hannuwa da kafafu jikinsa tamkar kifi tarwada fatar jikinsa bakinkirin kana kallon wasu jijiyoyi cikin abun baya numfashi,hajiya saude ta janye muneeba gefe da tuni ta suma tsananin masifar da take ciki da ciwo husnah ta mike ummah hadiza tace "dauko zaninta gashi can a rufe abun"da sauri husnah tayi yadda ummah hadiza tace ta rufe tana kokarin tabawa hajiya saude ta daka mata tsawa "ke husnah bakida hankaline zaki taba wanan halittar a tare dake ga juna biyu kinadashi salon ki janyo mana fitina dama dakyar muka rabu da fitinannen aljanin nan"jiki ba kwari husnah ta fito tayi gumi kaca kaca mahaifiyarta ce ta shigo parlorn dakin "yadai husnah ina muneeba?ta haihu kuwa"gyada mata kai husnah tayi tana kokarin fita hajiya zainab ta daga hannu sama cikin farin ciki tace "Alhamdulillah "ta kutsa kai cikin dakin ummah hadiza na shafawa muneeba ruwa a fuska a hankali ta bude idonta tana kallon sama wani zugi da radadi ne takeji a kasanta ta motsa a hankali tace "washhh wayyoo Allah"ta kasa hada kafafuwanta hajiya saude wani takaici taji ya tsaya mata a wuya tsananin tsanar hajiya rabi taji da haushin ita kanta muneebar tace "gaba ki sake wanan kuskuren kindaiga ishara na tabbatar mu da wani gidan ne ko wata zuriar ne saidai kibi mahaifiyarki kusan yadda zakuyi amma dayake mahaifinki jininmu ne bazamu taba barin jininsa ya wulakanta munada rayuwa ba muneeba"jikin muneeba yayi sanyi ta sunkuyar da kanta kasa momy dake tsaye tace "sannu muneeba sannu kinji Allah ya baki lafiya"ta jinjina kai dakyar ta motsa bakinta tace "Ameen momy"wasu hawaye masu zafi ke zubowa daga idanuwanta,
momy ta kalli sashen da aka rufe da zani ta kalli ummah hadiza tace "ummah hadiza abinda ta haifa babu rai ne?meta haifa?"
ummah hadiza ta nuna mata kafin tayi magana cikin azama momy ta bude zanin da sauri ta saki tace "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"tsigar jikinta ta mike ta runtse idonta da sauri tabbas tayi gamo ummah hadiza tace "dodo ne ta haifa tayi arziki da yazo babu rai kuma yazo baa mutum ba da tasha bakar wuya kila Allah ne ya dubeta sakamakon tubar da tayi da wuri dikda saida taji wuya ta tuba"momy ta girgiza kai cikin sanyin jiki tace "ku daina fadin haka yanzun a kira yaserr a Kira malam yazo ya gani sai asan yadda zaayi da abun ko?"hajiya saude tace "hakan ya kamata amma yaserr baya daukar waya husnah ta sanar mun da yayi fushi yayi tafiyar sa ma koda tazo be gidan batasan inda yaje ba"
muneeba wani abu taji ya caki zuciyarta wani radadi takeji a kirjinta wani irin kaunar mijinta takeji da tausayinsa son da takeyiwa yaseer a halin yanzun yafi wanda takeyi masa a baya fargabar rabuwa takeyi dashi idan yaseer ya rabu da ita tabbas bazata iya rayuwa cikin gidan ba bazata iya rayuwa tana ganinsa ba wutar sonsa ke ruruwa a zucuyarta batasan sanda ta fashe da kuka ba hajiya saude da ummah hadiza suka shiga da ita toilet tare sukai mata wanka kafin su fito Momy ta gyara wajen ya fice,
husnah ta dade tsaye tana kwankwasa kofar motat tasan shine dikda fitowarta bataga motar ba tasan ya dawo tana hangensa ta glas din motar daya dan bude dago kai yayi fuskarsa jajir cikin tsananin takaici yayi tsaki yasan husnah ce yasa keyy ya Bude motar tanajin alamar budewa tasa hannu ta bude murfin motar sukai Ido hudu da yaseer ya zuba mata ido itama shi take kallo ta kasa motsawa dakyar ya bude baki yace"kinzo ki rokeni in zauna da muneeba ne?ko me kikazoyi?"ya watsa mata wani kallo tq sunkuyar da kanta kasa ta danne zucuyarta ta shiga ta rufe motar ta ruko hannunsa kasa kwacewa yayo cikin wani irin salo take murza tafin hannusa ta kwantar da kanta a kafadarsa murya kasa kasa cike da shagwaba tace"yanzun fushin yar uwata ya shafeni kenan?saboda nace ka sassauta hukunci kada ka yanke hukunci cikin fushi?bance saika zauna da muneeba ba ina tsananin tausayinta dikda tayi maka babban laifi sanan karka manta mahaifiyarta tabar gidan ta gudu baasan inda takeba"cike da karfin hali yace "ehh anyi asibitin mahaukata da ita yar uwarta kuma ta mutu an dauki gawarta"da sauri husnah ta kallesa "yaya yaserr kasame kake fada kuwa ko tsabar fushi yasa kawai kake zaro maganganu kamar wanda kwakwalwarsa ta samu matsala?'ya tallabo habarta yana girgiza kai "ko kadan husnah shine sanadin fasa fitata shine sanadin da kika sameni cikin motar nan nashiga damuwa yau nakara tabbatar da cewa mai rai baa bakin komi yakeba sanan dan adam dik iskancinsa zaiyitayi Allah na kallonsa yayi masa talala saidai da zarar ya damkesa to fa zai zama abun tausayi abun misali sanan darasi ga sauran mutane"jikin husnah yayi sanyi ta zuba masa ido cike da kwalla ya kwashe komi abinda ya faru ya fada mata jikinta ne ya kama rawa ta kasa magana ta rushe da kuka ta fada jikinsa tana shashekar kuka rungumeta yayi cikin sigar lallashi da kalamai masu dadi yake lallashinta yasamu tayi shiru ya shafa fuskarta ya hade bakinsu waje daya ya soma kissing dinta cikin wani irin salo yake tafiyar da ita yana shasshafa ta horn din mota yasa yayi furgigit ya saketa ya kalli motar dake gabansa ya girgiza kai yace "hafeez ne naga kamar shida malam ne kota haifo dan boka ne?"hararsa husnah tayi ya hade rai Shi kuma ta kauda kai tace"ta haihu tun dazun?"ya kalleta ta jinjina masa kai ta kauda kanta gefe ta bude motar ta fita jiki a sanyaye shima ya Bude motar ya fito hafeez yace "ah ah kune a cikin mota kuke zuba soyayya?"cikin kasa kasa da murya hafeez yace hakan! yaseer yayi masa wata harara suka dunguma cikin gidan.....
kamshin turaren yaseer yasa muneeba saurin dagowa daga zurfin tunanin da ta shiga ta gansa tsaye rike da hannun husnah hannunta cikin nasa Yana murzawa kafeta da ido yayi wani kallo yakeyi mata mai cike da tsana da takaici idonta ya cicciko da kwalla ya kauda kansa yana kokarin fita hafeez ya ruko dayan hannunsa "ina zakaje kuma?ai babu inda zaka inma zaka fita kabari a baka damar haka"ya dawo ya tsaya yanajin husnah tayi wata ajiyar zucuya ta kallesa ta kashe masa ido yayi murmushin gefen fuska,
malam yayi adduoi sosai sanan yasa leda a hannunsa batare daya budeba ya nade abunda muneeba ta haifa sanan ya kawo wani magani yaba hajiya saude "wanan wanka da sha da tsarki zatayi saboda yadda zataji canji a jikinta inshaaa Allah babu komi ma"hajiya saude ta karba tayiwa malam godiya yasa hannu da bismillah ya dauka ya kalli yaseer yace "muje a birne ko?"yaseer ya cije bakinsa ya sake kallon muneeba idanuwanta na kansa ko kiftawa batayi ji takeyi kamar ta hadiyesa ya zama nata suka fice tare