Showing 42001 words to 45000 words out of 155384 words

Chapter 15 - YAR AIKIN KARUWAI 2 cmplt By Asma Baffa -www.sufinovels.com-.txt

19 Jun 2024

51336

Abba Yana ta jera musu sannunku da zuwa sannunku,Uwa tana lale marhabin marhabin lale lale ta kwalawa Rahma Kira tace kawo musu ruwa mana,Ni Kuwa mamaki ya kamani ni sunki kulani Amma Nawwar da
Auta shi Kamar sune Yan uwansu,Abba yace Allah ya muku Albarka babarku tayi farar haihuwa gaku maza Kuma gaku Kuna Kama da alama dai wa da kani ne,Auta yace ae nine kanin shi wannan yayana amma da kadan ya girmeni Wai Nawwar ne ya girme shi da kadan shi da matan ma su Sultana sun girme shi aure kawai za a musu sun girma,domin su sun shiga University tuni ma,Auta ya kalli Rahma a ransa yace wannan kwaila ce kirjinta ba komai sai tsayin kafa,Raheema ce ta fito itama ta gaida su Suka amsa Auta itam ya Kare Mata kallo sai kace munafuki a ransa yace wannan Daya tayi Mata kwari ta tsunbure baza ta girma da wuri ba kafin ta murmure za a dade itama dai kirjin ba komai kamar faifai ita kanta nonon take bukata a shayar da ita Ina zata Iya shayar da kamata Ina,Nawwar Yana kallon abinda Auta yake Yi na kallon matan hararar Auta yayi,da sauri yayi kasa da Kai da sauri.


Ni Kuwa Ina Shiga Bilkisu Babba tace Masha Allah wannan twin din Cele ce gaskiya sun zuba min Ido suna kallon suturata da irin kyan da na tsula kudi basa buya idan akwai su,baki na zumburo nace sannunku,Suka amsa da yawwa,Umma na kalla cikin doguwar rigar atamfarta me kyau kamar Yar balarabiya,na durkusa a gabanta nace Ina kwana tana Murmushi ta amsa ta rike hannuna tace ga Yan uwanki ki gaida su, yayyenki ne na juya na gaishe su su Rahma Suka gaishe ni,Omaira ma ta gaishe ni,nace Ina wacce naga hotonta a kasko tana suya? dariya Suka Yi Suka ce Yar jarfa kenan Cele a kasko kenan sunanta Rufaida ana ce Mata Cele Amma fa Cele a kasko ita Yan biyunki ce tare aka haife ku itama ba anan gidan ta taso ba,nace mijina Yana tsakar gida,Aunty Bilki tace ai ya Zama dan gida ya shugo Kawai ayi labarin a gabansa,Nawwar na Kira nace ku shigo,Abba da Uwa Suka tabe baki yace maza da Shiga cikin Mata jeka kuje Kar ace Ina bakin ciki,Nawwar ya mike da Auta tuni kamshinsa ya cika ko Ina yayi sallama ya shigo palon Kato ne,Su Aunty ne Suka tashi suka bashi doguwar kujera shi da Auta Suka zauna.


A kasa ya zube ya gaida Umma da su Aunty ma sauran ma suka gaida shi,bayan ya zauna aka kawo Mana ruwa da lemon da su Aunty Bilki Suka siyo Bilkisu ta fita ta shiga kitchen sune suka Yi girki aka kawo mana tuwon shinkafa danya miyar egusi sai meet pie me kyau, nace mun fa koshi,Aunty Bilkisu sai bala'i ai ba sai kin nuna mana mu talakawa bane dama ai mun San bamu Kai kici abincinmu ba kunfi karfinsa amma dai ke in baza kici ba ai su zasu ci,aikin banza duk Dan gidan nan inda yake sai ya nuna hali haba,Baki na bude nace ni daga nace na koshi sai ki kamani da fada haifata Kika yi,ciki ne dani ko baki gani ba abinci sai mai da yaji nake ci gashi Nan me cikin ki tambaye shi kiji,Nawwar yace kuyi hakuri bata cin abinci sai mai da yaji,Umma tace ko kunya babu Rabi kike ko,cikin shine abin kunya ni da ba shege nayi ba da ubansa kowa yasan dai me akeyi a samu ai aure nayi,Nawwar shi Kuma yace ae da auren mu Umma,su basu Saba Jin rashin kunya haka ba da tarbiyyarsu Kuma a Arewa suke da saukin fitsara sannan a gaban Mahaifiyarsu Suka taso,Bilkisu ta share zancen tace amma ai kwana zakuyi ko? Nace a'a Ina Zan iya kwana gashi nan ku tambaye shi idan zai yarda to bai Saba barina unguwar kwana ba na tafi na barshi da wa da dare fa a'a bazan kwana ba nikam, Umma tace ke a hannun wa Kika taso ne haka Rabi baki da kunya haka,Baki na turo nace ni nace ku jefar dani da Kun San da haka kuka jefar dani sai yanzu an ganni na girma na zama abar moriya za ace bani da kunya tuntuni ba sai a rikeni a bani kunyar ba,shi waccen mutumin me Jin haushina waye ne haka,Umma tace babanku ne mahaifi,nace Ni ku bani labari na sani nice yarku ko ba ni bace,Umma Ido ta tsura min ta fara bamu labarin asalinmu.


Tace Mahaifinku dan Asalin Nasarawa Lafiya ne a wani kauyen Fulani rugar Jam,Mahaifinsu da Mahaifiyarsu Abu wacce ake Kira da Uwa su Tara Suka Haifa bakwai Mata biyu maza yanda ita kanta Abu Uwa kenan dukkan Iyayenta Mata Suka Haifa mutum Daya ne Namiji a ciki su hudu Mata namijj daya Kuma duk suna nan da rai ita Uwa itace Babba a cikin Yan uwanta sai Sa'ade,Baballe da Binta Uwa Kuma data yi aure danta daya tal ta Haifa a Duniya Muazu shine Mahaifinku Abba kenan tun yana matashi mahaifinsa ya rasu Bayan sun dawo Kaduna da Zama sakamakon fada da ya barke tsakanin Fulani da manoma gaba Daya kusan Dangin Mahaifinku suna nan Kaduna Wanda basuyi aure ba ma duk a nan suka Yi aure,Uwa ta Sha wahala da Danta sabo da bata da miji sai Yan Uwa ne suke taimakonta lokacin ma a gidan haya take,sabo da danta ta kasa yin aure Wai Kar ta auri wani mijin ya tsanar Mata da tunda mazan yanzu ba kowa ke son yayan wani ba,tana sana'oi kala kala da haka ta dauki nauyin Danta har ya gama Secondary sannan aka turashi makarantar Allo can Kano har ya Zama katon Saurayi Yana Almajirci ya samu wata Hajiya ta dauke shi Yana Mata aiken gida a can har ya Isa aure a wancan Zamanin kenan.

Ni Kuwa Yar Asalin Taraba stare ce can Gembu kusa da Cameron Fulani ne usul ,iyayena ni kadai Suka Haifa tunda aka yayeni babana ya rasu sai Mamana Muna rayuwar mu nayi makaranta zuwa matakin secondary sai karatun Islamiyya Ina tallan fura da nono har kawar Mama tace tunda bamu da kudi Muna Shan wahalar Rayuwa me zai Hana a kaini gidan masu kudi wanke wanke da shara,Mama ta amince nima ita murna Zan zauna gidan masu kudi,Allah yayini da masifa kaf kauyenmu ba a taba ni a kwana lafiya bana yarda,aka samo min aikin wanke wanke da shara a Kano aka kaini gidan da Abbanku ke musu aike da wanki da guga,Hajiyar gidan da mijinta suna da mutunci matuka suna da dansu guda daya shine bashi da mutunci gashi suna ji da shi,lokacin ya so ya lalata min rayuwa Saura kadan ma yayi min fyade Allah ya kiyaye Abbanku ya kamashi ranar ya daku a wajen Muazu Almajirinsu duk da cewa kullum cikin fada muke da Abbanku Muna kishin juna shi Yana Dan aike ni Kuma nice me girki da gyaran gida.


Dama gashi masifaffe nima masifaffiya har kokawa mukeyi dashi sabo da rayuwar yanzu da ta baya ba daya bace yanzu anfi lalacewa,Watarana idan Zan bashi abinci sai na zabo nama me tauri ko Kashi shi zan sa Masa yayi ta faman wahala da hakoransa ba zagin da baya min akan haka,idan Naga dama ma Sai naci Nawa na rage jagwalgwalona sai na dan gyara shi na Kai Masa a wulakance,Dariya Muka dinga Yi Ni da su Nawwar irin muguntar Umma data dinga hadawa Abba,taci gaba tace shima duk Sanda aka aikeni na fita to bazai bude min gate ba sai rana ta gasa ni na Sha wahalar gaske sannan zai bude min kofa Watarana ma Sai dai Hajiya taji ihu na tazo ta bude min,Watarana Ina wanki yazo ya kwaso min kayansa ya tsaya da bulala a kaina yace sai na wanke Masa shima ai ya girmeni,Ina wanki Yana tsula min bulala a gadon bayana ta Dole na wanke masa tunda shi Namiji ne ya fini karfi,Muna wannan zaman kullum fada tsakaninmu har na fada sonsa ban sani ba,shi kuwa dama bai damu dani ba duk masifa ta da rashin kunya na daina yi Masa ita sai dai kyautatawa tsakaninmu na Masa wanki abinci me Rai da lafiya,dake nice a kitchen din nama ma yafi me gidan ci da yawa duk shi nake kwashewa na bashi,ko Jollof nayi to Abbanku shi inda yafi Mai da dadi nan nake Fara kwashe masa,albashina ma idan na kaiwa Innata abinda ta dauka ta bani sai nazo na bawa Muazu kudin,ganin haka sai yace Yana so na sabo da yanda nake kyautata masa,Me gidan da nake yiwa aiki shine ya dauki nauyin bikinmu kaf danginsa da Uwa ma sai kaunata saukeyi sosai aka sa bikinmu da Muazu Wanda me gidan shine ya dauki nauyin komai,Kafin biki Kuma aka samu matsala dansa shine yayi yunkurin lalata min tarbiyyar sanadin dukan da Muazu ya Masa shine masu gidan Suka kore mu daga aiki gaba daya,Bikin ma yace ya fasa daukan nauyi,haka Dangin Abbanku da Nawa Suka dage aka samu aka yi Mana aure Muka zauna a gidan Haya Wanda mahaifiyarsa Uwa ta Kama Masa,bikina da shekara daya dai dai na haifo yata Bilkisu anan Kuwa kowa Yana so ana murna, ban Dade da haifar Bilkisu ba Mahaifiyata ta rasu itace kadai gatana Kuma ta Kare sai Yan Uwa haka a can Taraba, wata kazamar kwanika nayi kafin na Yaye Bilkisu sai na samu wani cikin a lokacin ma Uwa da Abba Basu damu ba sai da Suka ga na haifo yan biyu Nazifa da Nazira,daga nan suka fara guna guni Ina ta haifo musu mata tun Abba baya Jin zuga har ya Fara dauka yana yiwa yaran wulakanci,ana haka na samu ciki sai Suka Fara Allah dai yasa Namiji ne matan nan sun ishe mu,Uwa ba zagin da bata min ta Fara min habaici tace matan ma meye amfaninsu wasu ma Karshe su Zama Yan Iska, Ina girmamata sabo da uwar mijina ce Kamar uwata ce amma bata gani,tun Ina da ciki suke hada kai da Yan uwanta su fa wallahi yanzu baza su yarda a haifo musu Mata ba ehe,Ranar da na fara nakuda Ina Shan wahala Nakuda nake me tsawo Uwa tana kallona Ina wahala taki ko kulani,ciwo ya isheni na fito da rarrafe Ina hawaye nace dan Allah kisa a kaini asibiti,Uwa tace uban wa zaiyi asarar kudinsa ya kaiki asibiti ki haifo Masa mace babu me kaiki sai dai ki mutu,Kafafunta na rike Ina rokonta Ina kuka ta kwace kafafunta ta shige daki haka na koma dakina,Bilkisu lokacin suna Yara ba abinda zasu iya Yi min sai kuka suke na tura Bilkisu ta Kira min makwafciyar mu da muke mutunci wata dattijuwa itama bata nan ranar,Abbanku ne ya shige Uwa tace Wai matarka nakuda take wasu matan suna Kan Hanya,Fuska ya bata yace ai sai tayi ta haifar matan wlh ko ta Haifa bana so ni ba nawa bane ko barka Kar Wanda ya min ya juya ya fice, ana haka sai ga Dattijuwar Attine ta dawo daga unguwa Bilkisu taje ta kirata itace ta taimaka min har Allah yasa na haifo mace katuwa,tana yanke Mata cibi Uwa ta fado dakin lokacin wata Sabuwar nakudar ta taso min bana cikin hayyacina karfina ya kare ban San ma me nake Yi ba,Uwa ta kwace jaririyar ta zazzagi Attine ta fisge Yarinyar ta sakata cikin wani tsohon zani tace bama so wallahi Indai macece shike nan kullum mace mace Ina son jikokina maza a dinga haifo Mana mace sai kace gyada, Dana bazai kare a bauta ba ta fice da Yarinyar Attine tana rokonta tayi hakuri amma ko a jikinta mota ta Shige a yanda tace ita Kano taje ta jefar da yarinyar a wani kauye bata San ma kauyen ba,kafin ta dawo na haifo wata Yar tawa katuwa,bayan na dawo Hayyacina nace Attine yan biyu na Haifa Ina dayar? Attine tace Uwa ta kwace ta fice da ita, me yasa Kika bata Attine na fashe da kuka,kuka nake gashi bani da karfi a jikina da kyar Attine ta taimaka min nayi wanka da ruwan zafi aka gyara ko Ina Kal kal,Bilkisu na aika ta siyo min abinci naci Suma Suka ci,Attine ta wanke jaririya aka sa Mata sutura kuka nake an dauke min yata,Attine tana ta bani hakuri,Abba ya shigo yana zuwa ya shigo ya kafe Cele da Ido ya ja tsaki yace aikin banza aikin wofi,mene a mace in Banda ta dinga jawo maka magana gasu Nan Muna gani duk sun lalace sai fitsara,nace wasu ba amma ba nawa ba,yace nakin fin na wasu Suka yi wa yasan me nakin zasu Yi kika sani ma ko Yan bariki Kika haifa,Salati na saki nace wallahi ka cika jahili Kuma ka sani wannan Baki ka musu wallahi idan naji yarka ta Zama Yar bariki cewa zanyi Allah ya bada sa'a tunda tun a duniya ka musu baki,Tsaki ya ja yace to suyi mana dama tunda Kika haifi mace kin sani wata ma Sai tayi ciki a gabanki ya juya ya fice,nace ta Allah ba taka ba.


Sai cikin dare Uwa ta dawo Babu yarinya,a lokacin na fito nace sai ta fito min da yata,ta zazzageni ni kuwa naci kwalarta na hadata da bango na shaketa a bango Muna haka Abba ya shugo ya kwaci uwarsa ya kifa min mari,Allah yasa dai bai sakeni ba,washe gari Uwa taci gaba da kawowa yata hari zata sace ta,har aka rada suna ko hakika bata Bari an yankawa Cele ba tace ai baza ayi asarar kudi ba,Mijin Attine Malam Jibrin shine ya bada ragonsa da yake kiwatawa aka yankawa Cele,dama su basu taba haihuwa ba,su Yara man ko macen nema suke Allah bai basu ba amma ga wani an bashi baya so shi,Cele taci suna Rufaida sabo da rashin kauna sunan ma Sai dai suce na sa duk sunan da Naga dama su basu damu ba,Yan uwan Uwa ma haka suke zuwa su fada min Maganar da Suka ga dama ban Isa Kuma nayi magana ba,Muazu kuma ga son mace bai da hakurin Jima'i amma Kuma baya so ace Ina da ciki,Rufaida tana da Sati biyu na shiga wanka itace na wanka ma Sai dai na siya da kudina idan Ina so na gasa jikina shi dai bada kudinsa ba,sabulu na manta na dawo daki Kawai nayi arba da Sa'ade kanwar Uwa zata sace min Rufaida ta goyata,riketa nayi Muka dinga kokawa Allah yasa Ina da karfi na dinga jibgarta da kanta ta kwance min yata Saura kadan ta jefar da ita a kasa na kwace abata na ajiyeta a Kan gado na Kama Sa'ade sai da na kusa kasheta a dakina da duka motsi sai data kasa,a ranar Kuma Uwa tasa danta ya sakeni nace ba inda zani Zama daram,Rufaida na dauke gaba Daya naje har gidan Malam Jibrin nace na basu Rufaida halak malak su rike min ita,suka dinga murna har danginsu ba irin godiyar da basuyi min ba, shi Kuma Abba yasa jaraba baza a bayar Masa da ya ba a dawo Masa da abarsa Kuma Uwa ce ta zuga shi sabo da so suke su sace ta,Malam Jibrin ganin ma Haka sai ya siyar da gidansa ya siyi wani a wata unguwar dama sana'arsa siyar da kayan miya,bayan na Basu Cele sai da na dade sanadin sakin kafin Muazu ya dawo dani dakinsa sannan yazo kuma Yana min naci nayi hakuri a sasanta naki yarda sai da ya Sha wahala sannan sabo da yarana na hakura aka maida auren domin na rigada na saudakar da farin cikina ga yarana sabo da dama wasu matan yawanci yanzu zaman yayansu suke yi.


Domin Karanta cigaban wannan labari ku danna bulun dake kasa ko kuma Hoton 👇👇👇


https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/yar-aikin-karuwai-book-2-page-51-55-by-asma-baffah


👆👆👆👆👆




🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2🌼
MATAFIYA


BOOK2



33-35




Official


By
AsmaBaffa




SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN




MASU AUDIO WANNAN BOOK NA SIYAR DA SHI BAN YARDA A JUYA MIN LITTAFI AUDIO BA






Ina masu bukatar unique kitchen utensils . fabrics adult and children's wears shoe's and bag's.
Da masu bukatar ahada musu lefe ko masu bukatar iya luggage's din kawai duk inkazo
R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE.
Zaku samu duk abinda kuke bukata ko a awanne state kake zaa kawo


Masu bukata ga number. 0703 455 9202




PAGE NAKU NE
Mum Basma
Hafsa Abdullahi
Faeeza
Sumayya Auwal sa'id
Ummu Lateefah
Maryam T Baliya
Murjamashi
Fatima Bintu
Mmn Mubeen
Khadijah/mashi
Aneesat
Mrs A
Hussaina S Alsn




Bayan an maida aure sai da nayi shekara hudu sannan na samu ciki,Su Uwa Takaici ya ishe su suka ce sun San ma macece,haka na haifo macen Kuwa taci Suna Omaira,bayan shekaru uku na sake Haifo Yan biyu Kuma Rahama da Raheema Wanda dukkansu babu Wanda aka yankawa ragon suna.
Cele Kuwa tunda ta shiga gidan Malam Jibrin suke gatata sai abinda take so ta taso cikin gata da Jin Dadi sabo da Attine ce take da zafin Nema komai ita kewa Cele,in banda Jan magana da masifa ba abinda Cele ta iya,sai da ta Isa Shiga makaranta Suka sata a primary tana karatunta tana gama primary Allah yayiwa Attine rasuwa tayi mutuwar farar daya,sabo da na basu Cele halak malak sai nace Kaka yasan yanda zaiyi da yarsa ya riketa Amana tasa ce,yayi murna Kuwa dalilin Cele ya sake auren wata bazawara ita kuma sai tazo tana gallazawa Cele azaba iri iri a wannan dalilin ya saketa ya sake auren wata itama dai ba irin wahalar da Cele bata Sha a hannunta ba dan ma Cele jajirtacciya ce,Watarana su Bilkisu idan zasu je su shigar Mata hanasu nakeyi nace ba ruwansu na rigada na bayar da ita,sabo da Haka ake son kyautar yaro idan ka bada to ka bada shi tsakani da Allah ba ruwanka da shishigi wajen marikinsa,sabo da yanzu abinda wasu keyi sai su baka dansu amma Kuma a sa ma Ido ana bin diddigi Yaya kake rike shi,duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login