Showing 93001 words to 96000 words out of 155384 words
Chapter 32 - YAR AIKIN KARUWAI 2 cmplt By Asma Baffa -www.sufinovels.com-.txt
su fito dan Allah ni zanga Matata wannan masifa haka duk Auta ne ya jawo da ya Kira su,Sai ga Auta ya dawo da ledojinsa na kayan marmari da nama da su Madara tarkace dai,dama yana kawo Nawwar ya bar asibitin,Nawwar ya kalle shi yace Auta ikon Allah ,Murmushi yayi kadan yace sai Aunty ta haihu zanyi dariya,yace ai kayi Da Autan Mami ta haihu tun yaushe kana can gantali,Auta yace haba ana ganinta? Yace ae mana an canja mata daki ma har taci abinci,Auta yace nayi Da shike nan na zama Daddy ya shiga ciki da Sallama suka Amsa,yace Masha Allah Aunty ya jiki? tana cin abinci tace Alhmdllh Nawaf,ya karbi yaron a Hannun Mami ya masa Addua yace kamar Yaya Nawwar kamar Aunty miracle suka yi dariya,Santana ma ya shigo yaga jariri ya tafi, sai da suka gama rubibinsu Mami tace duk su tafi gida suka fito suka tafi Banda Salma yar anace kamar danta ta karbe shi harda jijjiga shi,tsokanar Rabi tayi tace bari a masa rawa,da sauri na nunata da yatsa ina karkadawa uhm..uhm..uhm wai kar ta sake tayi masa,Auta yace to anyi da Kuma ba Saban ba,Nawwar ne ya shigo suka mike suka fito duka har Mami,ni kuwa na durfafi abinci sai yi nake,ya kalleni kawai yace sannu ya jikin? Nace da sauki na ajiye plate tass na cinye abinci,na bude ledar Auta na dauki yogurt sai da na kusa shanye roba guda,na dakko fruits nan ma naci wannan naci wancan sai da naji na koshi sannan na sha ruwa Faro nace Alhmdllh,sai lokacin na Kalli Nawwar dake tsaye yana kallona,nace zauna mana,ya sake cewa ya jiki nace da sauki lafiya nake,nace Baby local government ta fafe Yasin ta afka ai wani ruftawa tayi Kai naga bala'i,dariya Nawwar yayi, na dafa kafadarsa nace kaiiiiiii haihuwa da wahala yanzu su Wise nake tausayawa zasu dandana kudarsu, Nawwar ya zuba min Ido kawai, ina uban bashi labari na nuna kugu na nace aka rike ni ta nan,aka damki nan,aka tattaro marata aka yamutsa aka yamutsa sai naji kamar kasusuwana sun watse, Subhannallahi sai yanzu nake jin kunyar Mami tsirara nayi a gabanta,dariya Nawwar yayi yace shike nan ai kayan danta ne dan ta gani ba komai ai Larura ce,duk da haka da kunya Allah,itama ai mamanki ce ko? Nace ae mana,Allah yasa an mana hutun school Nawwar yace ai naji dadi nima,ki Kara hutawa zuwa yamma a sallamemu bari na Kira Umma,na Kira Umma ta daga nace Umma na haihu,Umma tace Masha Allah me aka samu? Namiji Umma,tace to Allah ya raya bari gobe su Omaira su taho ko kafin manyan su zo,nace to zan turo musu kudin mota,Umma tace akwai kudi fa,nace ai baza a kwashe naki ba Umma zan tura musu,to Allah yayi Albarka Ina me gidan, nace gashi bari na bashi ta mikawa Nawwar waya,ya karba suka gaisa ta masa Allah ya raya yace Ameen Ameen Umma.
Bacci na kwanta na fara shakar uban bacci tun safe bayan na haihu har 5pm sannan na tashi,Mami tace dama ke muke Jira ki tashi an sallame mu,nace to na mike a hankali ina yatsina fuska,Salma tana wajen ta kalle ni tace rauni kika ji a wajen? Mami tace shegen baki kamar kinci aku,dariya Salma tayi tace Mami yanzu ai kuna so na ko? Mami tace dama muna sonki ai horaki aka yi dauki kayan mu tafi,Nawwar ya dakko flasks da sauran tarkacen Itama Salma ta dauka suka dawo gida abinsu,bangaren Mami a sama aka bawa Rabi daki,Suka shiga na zauna a gefen bed da kyar ina yatsine fuska,Mami tace ai ruwan zafi Zaki shiga gashi Zaki na sosai shine Zaki samu afwa,Wise ta hada min ruwan zafin harda zuba shegun magungunansu na tsumi a ciki,na tafi toilet naga magani a ruwan nace Wise ni yaushe zan koma wajen Nawwar a sake abin nan,Wise tace hehehe sanda Zaki koma ma ku zuba sex wa ya sani,wlh Idan baza ki shiga ba zan Kira Mami sai ya Huce abin haushi ke ba Salma ba bare nace zan Kira Baso,nace zan rama wlh ai kema Zaki haihu so soon,da kyar na shiga ruwan ina zama na Kwalla ihu tare da mikewa,Nawwar yace kinji Mami ta Kone,rabu dasu wanka take fa,na sake zama zan mike Wise ta danne min kafadu kamar zan mutu haka nake kuka sabo da zafi,sai da ya huce sannan na mike,Wise ta wanke min gashina tas da shampoo me kamshi ta barni ciki nayi na sabulu da kaina na shirya kaina na fito daure da towel da karami a kaina ina tsanewa,Nawwar yana gefen gadon a zaune shi kadai,nace Ina Mamin? ta tafi yiwa jariri wanka,ya taso a hankali yace shike nan na zama Gwauro ya rungume ni ta baya,hannu ya dora a kaina yana tsane min gashin, Mami ce ta shugo ta zuba masa harara tace a gaskiya ka dame mu ka tafi mana haka tunda kaga jaririn kaga lafiyarta,yace irin wannan shi yasa ba a son a bar mace ta tafi gidan Iyaye,ya mike ya fice yana cewa mutum da matarsa kawai sabo da ta haihu sai a Hana mutum sukuni,Miracle nace ka kwaso kayan jaririn nan daka siyo a kawo nan,yayi tafiyarsa gida ma gaba daya,wanka yayi ya shirya cikin kananan kayansa hadaddu purple ya kwaso kayan jaririn ya kasa zama a gida shi kadai ya dawo gidan,lokacin anyiwa yaro wanka an shirya shi cikin fararen kaya,nima na saka doguwar rigar material readymade me siririn hannu na shafa turaruka masu tsada ni da yaron sai kamshi muke me dadin shaka,dakin Salma tazo ta gyara ta dame bed din ta kwashe tarkacen fitarwa ta fitar dasu komai neat daki yana kamshi,Auta ne ya shigo ya sha gayu zai fita yace Hajiya Aunty me jariri inyeee ba Saban ba anyi da mun shiga uku Kuma, Yaya Nawwar ya kenan naga karyar maita yanzu gwara ya karo aure kawai,na harare shi ina dariya nace ya karo mana Idan ya Isa,ai sai ka auro masa wata mu gani dan iya Kai da ka kasa komai wlh ka bani kunya Auta Kai da muke ta Jira yarinyar nan sarkin giringidishi kayi mana maganinta ka kasa duk son aurenka,Auta yace sannu sannu dai Aunty a sannu sannu sai Kun kaita asibiti an mata dinki,Allah ya shiryeka Auta Dan Iska a baki,dariya yayi yana kallon Kansa a mudubi, Salma ce ta dawo cikin yar fitted gown dinta me dogon hannu itama an sheka kyau harda kwalliya,tazo ta ture Auta daga jikin mudubin matsa Nima na Kalli kaina,Auta ya kalleta yace to baki kyau ba,a boye Kuma yana kare mata kallo yana yiwa Rabi signa da Ido yana nuna duwawun Cele da hannu yace harka iya harka,Rabi ta sheke da dariyar iskancin Auta,Salma ana ta faman gyara kwalliya bata San me suke ba,Wise ce ta shigo taga Abinda Auta yake tayi dariya tace yau na shiga uku,Salma ce ta juyo tace me ya faru Aunty tace ba komai,Auta fita zaiyi yace nikam sai dare,Salma da sauri tace Ina zaka je Kuma,yawo ya furta,ka tafi dani,yace a'a ni Ina ni Ina ke ai ke sai Baso ki zauna ki karbi Yan barkar jariri ya bude kofa ya fice,Salma ta biyo shi da gudu tabi steps da uban gudu,da Mami suka ci Karo,tace ke Kam Salma bakya rabo da gudu Ina Zaki haka,tana haki tace Abu na manta ta fice,Auta har yayi nisa ta cin masa tana hakki tace wallahi Idan ..Idan ..ka kula wata bazan yafe ba,ta juya ta dawo kafin Auta ya juyo har tayi nisa,baki ya tabe ya wuce ya shiga mota abinsa.
Nawwar ne ya shigo ya iske Salma da Wise a dakin suna hira,Salma tace sannu da zuwa Yaya ya farincikin an Baby,dariya ta basu ta mike ta fice,itama Wise ta fito,Salma wajen Mami ta dawo tace ki kawo jaririn a Kai shi ga Babansa can Yazo,Mami tayi dariya tace sai yace a Kai masa abinsa? tace ae yace son ganinsa yake bai karewa dansa kallo ba,Mami tace sannu zubaida wai yau kinwa Auta girki ma kuwa? tace banyi ba muna ta cuku cikun haihuwa,Mami tace to tafi kitchen ki Dora girki ba iya na Auta ba kowa da kowa,Hamra gobe zata dawo daga gidan su Aunty Rukayya a Katsina ta dinga tayaki aikin,tace to Mami ta wuce,Mami ta shiga da jariri ta iske Nawwar a zaune nace ai har naji sauki da nayi gashin nan,wani karfi naji,Mami tazo ta Miko min jaririn na karba tace bashi nono ya sha yunwa yake ji,Miracle na wani jawo bargo na lulluba wai a ciki zata bashi kar a kalle mata Nono,Mami tace a haka ake bawa jaririn nono a kwance cikin bargo baza ki fito ba,na mike zaune na jawo mayafi me kauri na lubbe nononta da jaririn,Mami tace hmm ta juya ta fita,tana fita nace sa key a kofar Baby, Nawwar ya Saka key kuwa ta bude nononta da jaririn.
Nawwar ya kalleni nace zafi zafi wlh in yana ja,yace ai baki Saba ba ne shi yasa,Nawwar yana ta kallon dansa yace wannan yaron Allah me Iko yanzu da nine nake sha da yanzu kin zauce ko? nayi dariya nace ae ma Idan Dan uban ne ba ajin komai amma da uban ya sa baki wayyo sai sweet,Nawwar yace hukuncin Allah kenan to na bashi aro ya zanyi,aka juya jariri daya barin nan ma ya sha nace ya koshi kai gashi har yayi bacci.
Sai da na gama gyarawa ya bude kofar su Sultana Amare anzo,Jamcy ma a ranar Santana ya kawota,Mandula da Yar zabil duk laulayi suke sunzo suma da mazajensu sunga jariri,Star kuwa Malam ya kawota da dare again ta Kai masa jariri ya masa Addua yace saura namu,Star tace kwana nawa ne wai star da ya wohoho ta karbi jaririn tana masa Addua Karka sake kayo Halin mamanka na fada maka Ameen,nace amma baki da mutunci ni halin tsiya ne da ni? Masifar wai take nufi ayi mata afwa cewar Malam Abhulkair harda fada da kalar tausayi.
Wise da Salma sune Yan zaman barka suna makale, washe gari su Omaira suka dira a gidan,Omaira, Raheema da Rahma,Salma ba zaman lafiya ganin Yan mata sunzo suma Kuma kyawawa, gashi Auta nasu ne dama,Auta suke ta nema kawai,ni kuwa Ina satar kallon Salma yanda hankalinta ya tashi,nace Omaira kuje kuyi aiki fa ana baki wa zai dinga abinci duk da akwai masu aiki dole kuyi min,Omaira tace to suka fita,suna fita nace Salma tace Na'am nace ya kamata ki fara gyaran jiki,murmushi tayi tace wa zan wa? Nace in Zaki fara ma ki fara kinga dai ke baki da Uwa a gaban Namiji kika girma, ni Ina da su ba siya zakiyi ba zan baki ana Shan na Infection sabo da tsaro da na niima da sauransu,Salma tace Idan da Zaki zan sha ni bana son magani,tsaki nayi nace Wise ce fa zata hada Miki komai ki dinga zuwa wajenta zata baki munyi zancen,Salma tace to na gode.
Kamar muryar Auta taji a kasa da sauri ta fita,nayi dariya nace wannan yarinya ta fada son Auta bata sani ba,fitowa tayi taga shine suke ta labari da su Omaira suna dariya,kishi me tsanani ya kama Salma ta sakko kasa,Auta yana kallonta sai da gabansa ya fadi shi Kam har tsoron Salma yake ta ganshi da mata, Salma cikinsu ta shiga aka ci gaba da hirar da ita tana hararar Auta a boye, tashi tayi ta rike Hannun Auta tace muje,Omaira tace Auta ango gaskiya Amarya kina ji da Autan Mami,Salma tace ba dole ba aje ayi min awon gaba da shi,suka yi dariya su Basu San ma kishi take ba,ta ja Auta cikin bedroom dinsa tace zauna ya zauna tace me zaka ci? Auta shi mamaki ma yake matar da watarana Idan zata bashi abincin ma sai da masifa,yace yau na koshi ya furta
Kallonsa tayi da sauri tace me? na koshi yau ya sake fada,Salma tace ai kasan Ina maka girki ko shine kaje ka fita Kaci a waje wa ya sani ma ko wasu Yan matan ka Kai joint to sai Kaci ko cikinka zai fashe Allah ta juya ta fice,Auta ya zaro wayarsa yana dannawa yana murmushi,tana fitowa tace Omaira an kusa bikinki ne? Omaira tace a'a ni dai Ina da Wanda nake so amma ba lallai a barshi ya aureni ba iyayensa sun ce yayi yarinta Kuma fa wallahi ya ma fi Auta shekaru,Salma tace ke karki yarda duk yanda za ayi ki auri Wanda kike so,ke aure akwai dadi ni dake ne wannan zancen sabo da ni kin min a rayuwa jininmu yazo Daya,Omaira tace Nima Ina sonki,Salma tace ke tun wuri kiyi aure kiji dadin da ake ji kema,soyayya akwai dadi ki dafa abinda kike so kici kiyi iko da mulki a gidanku yarinya Malam sai ma dare yayi,Omaira itama yarinya ce bata gane Salma wayo take mata ba wai kar ta so Autanta tayi aurenta kawai,Omaira harda mikawa Salma hannu suka tafa tace ke Allah kice akwai harka? Salma tace ta gaske karki bari kanki ya kulle,tace kin ganni sakata nake na Wala,Omaira tace shegiyar gari ai gashi nan kuwa kin kwace Auta ke kinga irin kallon da yake Miki nace jar Uba kina fama,Salma tace ai missing dina yake shi yasa kwana daya baiji Industry ba,Omaira itama harda washe baki tace ke karki sake a kwace Miki shi ki tarairayi abinki,Salma ana kasa da muryar irin munafuncin nan low down your voice abeg surukata tana nan,Omaira tace tsiyar zama da suruka waje daya kenan,tace Dan ma mun samu ta kirki ai Mami ta waye tsakaninmu da ita sai Addua,kinga bari na Kai masa abinci,Omaira tace iceko kin hada juice? tace tuni ma ai no kidding,Salma yau a abinda ma ta zubawa Auta abincin na daban ne ya sha kyau,Omaira tace gantsare Baby chest ya yo waje baya ma out,kin san kan gari dole muyi kawance,su Rahma ne suka shigo Omaira tace Kai ku fita zancen manyane muke Yara sai shegen son zance ana zance kuna kallon bakin mutane,Raheemah tace dama munyi waya da Umma tace Cele ta dawo a fada muku zata zo ma suna,Omaira tayi murna tace tab ni wallahi tsoronta nake ji tunda ta fasa min Kai fada da ita baya mutuwa tana zuwa na shiga uku,da su Aunty Bilkisu zasu zo ai bata Isa ba,Celen lallai to Cele ba Wanda ta dagawa kafa,Rahma tace Kuma Umma tace tana nan da bala'inta inda kisan bata zaga dakin Allah ba,Omaira tace Ina ga shedan ta jefa ya rama suka yi dariya tace muje wajen Aunty Rabi,tace cab mijinta ya manne da shi ake karbar barka wannan bala'i wallahi zai mata wani cikin da wuri, Mami ma tayi fadan ta gaji,to muje muyi kallon tv.
Salma ce ta shiga dakin Auta dauke da abinci sai da ya bi flasks din da kallo ya sha mamaki,ta zuba a plate tace to zan baka a bakin? Auta harda shagwaba nace na koshi fa,itama fuska ta shagwabe ta kwaikwaye shi tace nifa wlh sai ka ci harda shure Shure,Auta bai san sanda ya fashe da dariya ba,Mami ce tayi knocking taji suna ta faman dariya ta juya ma bata shugo ba Kuma basu Bude ba sai driver ta aika ya siyowa Rabi wani nama me Dadi.
Auta yace bani dai naci kadan ta dire gwiwoyinta a kasa yana bakin bed tana bashi a baki yana ci,Baso ne ya dinga Kiran Salma ta Kalli wayar my love bata canja suna ba,Auta ya kalla ya sake lekawa cokalin da zata bashi abinci ya bige yayi fatali da shi da abincin gaba daya tayi watsa watsa a dakin ya mike ya fice,Wayar Salma tana ta ringing ta dauki wayar a fusace ta danna wajen kashewa da karfi tana jijjiga wayar kamar zata fasa ta tace Dalla Malam Daina Kirana ta ja tsaki ta jefa wayar a kan gado ta kwantar da kanta a saman bed ta fashe da kuka.
Mami suna Palo da baki Auta ya fito fuuuuuu kamar zai tashi sama ya fice,Mami ta kalle shi kawai,da Nawwar suka hadu a hanya ya wuce shi rai a bace,Nawwar hannunsa ya rike ya juyo da sauri,yace Auta lafiya ne wai? Auta kamar zaiyi kuka yace wannan yarinyar ce Yaya can you imagine tana da aurena tana sawa wani my love a wayarta mahaukaciyar Ina ce ita,Nawwar yace Baso ne fa,Bason banza Bason wofi ni wlh inda kasan mutuwata haka na tsani Baso,Nawwar yayi dariya yace Soyayya ta kama Auta fa, Auta in love,Auta yace Allah ya kiyaye na so wannan yarinyar ko zan fara sonta sai na roki Allah ya yaye min wannan wacce irin jarfa ce, Nawwar yace calm down su fa mata ba a musu haka ba da fada ake samun soyayyar mace ba Auta,wannan Kai ka dakkowa kanka tunda kasan tana son wani,wlh tayi kokari ma yarinyar nan ka duba horon da aka mata ko Yan aikin gidan nan basu aiki haka,ta tura gate ta karfi ta zama me gadi,aka bata duk wani aiki na gidan nan,aka canja mata abubuwa da yawa na wahala Idan wata fitsararriyarce zata yi wannan Kuma tasan bata sonka,Amma bata taba Raina wani naka ba ko Abu zata maka sai dai Kai da ita,Ka duba yanda bata gajiya tana girmama iyayenka da duk Wanda ya shafeka wallahi lokacin da na dakko miracle Idan itace baza tayi ba duk da tana girmama mutane amma rashin kunya ma ta Isa a kyaleta,yanzu bata yi kokari ba,sabo da iskanci abinci ma a baki ake sawa ta baka tana da kunya ba a nan ta taso ba haka ta daure take maka har kace sai ana shafa maka gashi ,Sabo da kawai kaga ta sawa Baso My love,Iyaye ma suna sawa yayansu my love,lovely Mum,wayata fa Sweetheart na sawa Mami, Auta yace ai Baso ba muharraminta bane kuma kasan sonshi take ta ya zaka ce hankalina ya kwanta,Ka fara sonta Auta itama naga Alama tama fika kamuwa,mace ce Mai rauni sai anyi hakuri shine auren ai,Yanzu