Showing 144001 words to 147000 words out of 155384 words
Chapter 49 - YAR AIKIN KARUWAI 2 cmplt By Asma Baffa -www.sufinovels.com-.txt
tayi arba'in sannan ayi bikin,abinka da me kudi maganarsa ake ji har matsayi ne da ni Rabi sai sanda nace ayi auren za ayi, har gadara nayi nace a bari sai nayi arba'in akace ba damuwa .
Ahsan ne yace da Cele kiyi sauri ki gama abinda kike mu tafi tace to,a Kaduna GRA ya siya mata katafaren gida tace ta barwa Abba gidan su tare da Umma kawai,Abba sai murna yayi gidansa me kyau na gani na fada,haka Umma ta hakura suka koma ciki har Uwa gidan Umma Kuma ta zuba Yan haya wani Ango ne manager bank ya shiga ciki da Amaryarsa,gidan Abba ma dai wani ne Shima sabon Aure ya karbe shi haya gida me kyau an kashe masa kudi,Cele tace da su Bilkisu zata Bawa mazajensu jari Bikiisu tace a'a karki sake ki bawa mazan mu wlh suje suyi mana kishiya maza ba Yan goyo bane duk suna da aikin yi da rufin asirinsu Kuma dukkan mu muna muhalli me kyau kawai mu ki bamu jarin mu kama business ki bude mana katon shago mu uku ni Nazifa da Nazira mu dinga juyawa shike nan ma ya ishe mu,Cele tace to kin San Miji ba daga aure zai ta baka kudi ba Amma ki bari abinda ke hannuna da ni da Rabi sai mu hada a bude muku a hankali,Bilkisu tace dama duk kudin Namiji zai ta daukan kudi yana baka ne sai dai da dabara har ka samu rabonka,Cele tace shi yasa fa na nace masa sai ya siya min gida shine na barwa Abba shi kawai dama sabo da Hakan nayi,yanzu yace nashi gidan zai siya a nan garin su Miracle nace ya siya wannan nashi ne ba nawa ba,Bilkisu tace Dan ubanki ya siya Miki ba wani zama zakuyi a nan ba gida ai kamar naki ne da yaranki,Cele tace tun yaushe ma zan karbe takardun Jira nake ai ya siya din wata sabuwar gra ce ake ta gina gidaje a nan zai gina gidan Nawwar ne zai wuce gaba ayi komai,Bilkisu tace Masha Allah yar nan kunyi dace sai dai a dage ayi biyayya.
Suna gama wayar Ahsan ya shugo da zanen gidan da yake so ya nunawa Cele yace yayi mata? Cele tace ae yayi,yace Idan munje Saudi fa dole na bar aiki a asibiti sabo su tsarin saudiyya indai ka auri ba Yar kasarsu ba to zasu koreka daga aiki Kuma ko me ka tara baza a bawa yaranka gado da ka Haifa da ba Yar kasar ba,shi yasa in kasan haka to ka bar aikin gomnati kawai sannan duk abinda Yayanka zasu gada ka kaisu garin uwar yaran haka suke yi wannan ba karya haifaffen dan Saudiyya baya auren yar wata kasa taci gadonsa yanzu ne ma suka dan sassauta abin nasu amma aiki dai baza ka musu a karkashin gomnati ba indai sun San ka auri wata ba Yar kasa ba,shi yasa suke aura a boye ba tare da an sani ba ko Kuma suyi ta Zina kawai suna son su aura amma da matsala,Cele tace to ai kana Business wannan Kuma ba a karkashin gomnati kake ba,yace ae ai shi yasa ma tun kafin na aureki na ajiye musu aikinsu dama na gaji da aikin,Cele tace to duk wata kadara ka siya mana a nan yanzu gaskiya yace Inshallah,tace a Arewa Kuma yace ba damuwa ai komai ma na dukiyata Basu da hadi da gomnati duk Yan uwana sun sani komai da yardar su nayi.
Washe gari Omar Baso shi ya fara tashi a bacci yayi Alwala ya wuce masallaci Omaira taji sanda ya tashi Yana fita ta tashi itama tayi brush tare da Alwala ta fito ta gabatar da Sallah tana zaune tana Azkhar ya dawo ya zauna a gefen bed yana jiranta ta gama ta juyo tace Ina kwana ka tashi lafiya,Baso yace ragas ke fa? tace Yar lafiya dai,murmushi yayi tare da shafa sumarsa Omaira ta Kalli gashinsa tace askin ya maka kyau,yace ke kin auri fine boy kamata ai mu komai sai me kyau muke yi,Murmushi tayi ta koma ta kwanta bargon ya ja musu suka koma bacci,8am suka ji ana bubbuga gidan tsaki ya ja ya fita ya Bude yaga abokansa su Only Yan kwaya akan yace su dawo gobe shine suka yi uban sammako suka zo,ba yanda ya iya yace ku shigo Yan iska sai kace dole ko da ku aka daura mana aurenta ai sai haka,suna dariya suka shigo Palo sai ihu suke sun San gidan amma cewa suke yau she aka gina wannan gida,gaskiya gidan yayi shege mutumina irin wannan gida haka Kuma har furniture din da su aka shirya su amma kwaya ta sa sun manta,Baso yace ai baza ku gane ba tunda bakwa ganewa,Only yace Allah waccen gidan ne? Wanda dai muka sani? Karya ne magina ka kawo suka canja komai,wai Ina Amaryar tazo tayi mana girki,Rabona da abinci tun jiya da dare cewar wani Jaga,Omaira wanka tayi a gurguje ta shirya cikin leshinta na lefe tayi kyau Riga da skert taci dauri ta fito Palon taga su Only suna ta hauka,Only harda mikewa ya Sara mata kamar Soja,suka ce Aunty ya aka yi ne wai,Suka daki kafadar Baso matsiyaci wannan ta gaban mota ce Ina ka samo ta,Omaira tace Ina kwananku suka ce ba yawaa ba yawaa karki damu ba sai kin gaishe mu ba yawa ne kije ki shirya mana jullof din tafiya,Jaga yace ki hadata da wake,wani da ake Kira da Hayaki yace ki Kara da Alayyahu,wani Shima yace da shayin wiwi Aunty a kawo ki dafa mana,Baso ya dura musu ashar yace zaku bar gidan nan wlh mahaukata,Only yace ya naga Kwan Palon guda Daya ne ya kawo haske? Baso yace ka hau ka gyara shi ga tv nan ka hada ta sune dama jiya baku karasa ba,Only akwai shi da basirar gyara Abu indai zai taba maka Kaya sai ya iya gyarawa,kujera ya taka yace miko min star din nan,ya bashi karamar star ta kwance abu Nan take ya gyara kwayayen Palon duk suka dauka,ya dawo ya hada musu tv din da komai har settelite shine ya hada musu yace Umarun Farooq ga channel din shegun a bar muku su,yace wlh zaka bar gidan nan channel din Bf din zaka bari,ai irin taku ce masu aure,Baso ya dada masa duka a kafada yace Dalla cire su,suna dariya yayi hiding nasu,Omaira dai tana ganin ikon Allah ta wuce kitchen ta dafa shayi tayi soye soyenta tayi warming naman jiya ta kawo musu komai ta jera a gabansu,suka ce Ina taliyar? Baso mikewa yayi ya jata kitchen yace kwaya ta cinye musu ciki Queen wannan soye soyen ba abinda zai musu ki dafa musu taliyar, Omaira tace wai kaima da haka kake? Yace ai na fisu hauka ma nine ogansu fa tunda Oga ya tuba inshallah yaran ma zasu tuba ne komai sai a hankali,Omaira tace to bari ayi musu yace yanda suka ce haka Zaki dafa fa,Omaira tace kana shagwaba su,yace baza ki gane ba mu fa sanda Ina talaka dukkansu sun fini samun kudi ba Wanda bai taimakeni ba a cikinsu tare da su muka rike Salma bata yi kukan yunwa ba ko baki gane bane? Omaira tace to ba Alayyahu ba kifi tunda ba a kawo ba,yace dafa musu haka zasu ci watarana ayi musu yanda suke so,Omaira ta dora musu girki kafin ta gama har Omar din sun cinye soye soyenta sun sha tea dinsu,Only yace Aunty muna jiran taliyar mu,sai da ta gama ta kawo musu a flask suna ta murna ko a plate Basu zuba ba a katon flask din kowa yasa cokali suka cinye tas Banda Omar Baso ya koshi shi, suna cinyewa suka tashi suka ce sai watarana Kuma Aunty a kula da Oga sosai,Omaira tace to ku gaida gida suka Kara gaba,suna tafiya Omar ya jawo Omaira ta fado jikinsa a kunne ya rada mata kin ci abinci? tace ae a kitchen naci,yace to duk Wanda Yazo a cikinsu indai yace zai ci abinci ko babu sai iya nawa ne kawai ki bashi ya cinye,kawai dai Idan Zaki fito ki Saka hijab kar a kalle min Matata,Omaira tace to shike nan lallai kana son su,yace gudun kar su min hauka a wajen daurin Aure yasa ban fada musu ba sai da aka daura,Baso ne ya mike yace bari na tayaki aikin tare suka gyara gidan ko Ina da ko Ina, fita yayi ya yo mata cefane 11:30am ta shiga kitchen zata yi girki,Yajin Albasa ya shiga idonta Baso yana kitchen din yana dariya ya mike tare da rungume ta ta baya ta cikinta ya zuro hannayensa yana yanka mata Albasar a haka yana tsokanarta da Yar gatan Mubaraq tana dariya Kasa kasa,yace yau zamu fita yawo ko? Omaira tace daga kawo Amarya jiya,to mene a ciki ni bana son wannan abin na mutanen mu fita zamuyi a machine ko a mota? Kana da machine? Baso yace sabo ma siyensa nayi Ina son machine yace irin kirar lifan ce da shi,Omaira tace to Allah ya kaimu.
Su Baso an Saba da tashanci wajen magriba Omaira ta shirya cikin kana nan kaya ta dora Abaya tare yin da rolling,Baso kuwa shadda ya Saka fara Kal ita Kuma cikin bakar a baya,a gaba ya sa Omaira maimakon a bayansa tana gabansa suka fita Ya bawa machine wuta,ga Baso popular duk inda suka wuce sai an samu Wanda ya Sanshi ana ta daga masa hannu ko yayiwa mutane horn,Baso yace dole ki koyi machine Omaira tace bazan iya ba sai kace Cele,Ko ayi Miki tukin tsaye Omaira tace ni dai a'a Dan Allah kar muyi hatsari,yace to da kafa daya fa?,ni dai a'a cewar Omaira.
Wajen shakatawa ya kaita wuri ne me kyau Omaira tana kallo tana nishadi harda riketa yace taka a hankali kar a fama ciwon jiya,dariya tayi tace yi mana pics ya dakko wayarsa ya dinga daukanta pics ya shiga suka dinga Selfie,sai bayan sati daya sannan Nazifa ta Kira Omaira ta fada mata an Maida auren Umma da Abba ta bata labari,Omaira tayi murna itama,lokacin Kuma ana gobe daurin auren Sabreen Baffa yace a daura Dana Hamra tunda shi Mijin Bai gama gidansa ba daga baya ta tare ai yace sai saura sati biyu ya gama,ba Shiri ba komai duk har lefe sai daga baya za a kawowa Hamra,Angon Hamra sai murna yake da danginsa duk sun yarda a hada daga baya a Kai Amarya,washe gari Friday ana idar da Sallar juma'a aka daura auren Sabreen da Hamra da angwayensu,
Ranar su Santana sune akan gaba kawar matarsa tayi aure,har gida Yazo ya yiwa Sabreen murna yace oh Allah yayi aure da marar kwabo to kinga dai da yanda kika lallaba kika samu shiga sai ayi hubbasa a tallafi Antena a bata muhimmanci,kina da kishiya ki zage ayi biyayyar aure ato karki bamu kunya,Sabreen tayi dariya a ranta tace wannan wahalar da Nasha kafin na samu Miji ai dole nayi biyayya,ba wani biki aka yi ba su Wise Iyayen Amarya anci gayu ana ta Kai kawo,Mama tazo zuwa yamma aka Kai Sabreen gidanta Masha Allah
Bayan kwana uku Cele ta dauki Kaka suka tafi zance wajen Maman Sabreen.
Kaka yace tunda tayi Miki kina sonta Cele Nima Ina sonta Cele tace ta hadu Kaka itace dai dai kai kana aurenta za a ga kana wani ja kana kiba,Mama tasan zasu zo harda yin girki taci kwalliya cikin Atamfa Riga da skert tayi kyau,suna zuwa gidane karami ba wani me kyau ba can,wani daki ta sa aka kaisu Wanda ba komai a ciki sai carpet,suka zauna a kasa aka cika musu gabansu da girki,Kaka yace juma'ar da zata yi kyau tun daga laraba ake ganeta Cele tace ai wannan ma tun daga talata aka ganeta,Mama ce ta shugo tana kamshi,Kaka ya sake gyara zama ya radawa Cele yace ba kujera a palon ai da nayi zaman Sarauta kin San da sanda muna Yara Kanin Babana me unguwa ne,Cele tace na gane Kuma,Mama ce ta Kalli kaka an sha shadda me tsada sky harda coka hula irin ta matasa ga babbar Riga an sha yana kamshi dariya ta kusa kamata yanda kaka yake dai daita nutsuwarsa,Cele tace Ina Wuni Kakata,Mama tace to har na zama kakar Nima,Cele tace ae mana yau dai gaki ga Ambassador Muhammadu Kaks,bari na shiga ciki mu gaisa da marikan naki,Mama tace wanne Marika da girmana Cele ta wuce ta bar Mama da Kaka,Kaka ya dago ya Kalli Mama yace haka nake son mace ko Ina a tsuke a manne amma wasu ki gansu ragajeje sunyi wani ragadada da su sunan wani nama,ya sake kallon Mama yace karki tsufa kinji kici gaba da tsukewa,ni duk wacce bata tsuke min bazan zauna da ita ba,yanda Cele take bani labarinki har kin wuce haka Kuma kin min harga Allah Ina son ki,Mama tace Allah? Yace kina shigowa naji zuciyata daga daidai hakarkarina ta buga Ina jin haka nace shike nan na kusa zama ango,Kaka yace Allah yasa ni ba wani tsoho bane ko zan girmeki baifi da shekara daya ba,Mama ta zaro Ido tace a'a wlh Sabreen ce fa Yata ai Idan aka ce ka bani shekara goma bazan mamaki ba,Kaka yace haba Yanzu ki kalleni matashin dattijo a'a ki canja zance,Mama tace wai Kai Ambassador din a Ina ka samo shi? Kaka yace na tsere ne a kasar saudiyya Idan kika ga Ina tseren gudu to sai kince dan Allah na shiga wasan gasar tsere.
Mama tace ga abinci nan,Kaka yace ai ya kamata tun yanzu nasan Zaki iya kula Dani ko kuwa a'a,Mama ta mike ta zuba masa abincin ya karba ya fara ci yace Excellent inji bature na baki maki,yanzu ya kika ce kin amince ko kuwa? Mama a ranta tace ba dole ba ma,a fili tace Idan ban amince ba ai bazan ce kazo ba ai kayi min,Yace a gaskiya Hajiya Zuwaira naji Dadi Kuma gaskiya a so na baza ki Kara sati daya ba sai a gidana,Mama tace Allah ya kaimu,yace har lefe zan Miki komai sai na cika ka'idarsa, Mama tayi murmushi a ranta tace wannan tsoho da kinibibi yake, sun Dade suna hira Kaka yana ta yabon Kansa,yace cefane sai kin ganji Allah ya hore min iya cefane,tsoro ma nake ji kar nan gaba jin Dadi da koshi ya Miki yawa ki tara kitse a jikinki ki dawo kamar bijimar saniya naganki ba ko kashin wuya tun yanzu,Mama tayi dariya tace Allah ya kaimu zan gani ai,Cele ce ta shugo tace Kaka Kun gama tashi mu tafi,Mama tace da wuri haka? Ko baki gaji da ganinsa ba ai Kun kusa zama gida daya daki daya tashi mu tafi Kaka,Mama ta raka su tace Allah ya tsare Kaka harda karkacewa ya bawa Mama dubu goma,ta karba tayi godiya su mama an saduda,da Abaya ne ai tafi karfin haka,abinda tafi karfi yau yafi karfinta.
Bayan sati daya aka Kai kudin auren Mama da lefen akwati uku manya aka,aka Saka bikin saura sati daya,Kaka sai zumudi yake kullum sai ya Kira Mama safe da dare yaji ya take,har aka daura Auren Kaka da Mama,kafin ta tare sai da taje gidan Baffa tabi kowa ta bashi hakuri tace su yafe mata tayi kuskure a baya,Iyamami harda hawaye tace ba komai Allah ya bada zaman lafiya sanadinki ni kaina yau nayi nadamar halayena da abubuwan da na aikata inshallah zan dawo Nima na gyara kuskurena,Mama dai tayi Sallama taje gidan Sabreen suka gaisa sannan Cele ta sata a mota ta koma gida,washe gari aka tura mota daya aka dakko Amarya da Yan dangi su biyar zuwa Kaduna gidan Kaka Wanda Cele ta gyara gidan ya koma hadadden gida me kyau,Mama Amarya aka bari ita kadai tana jiran angonta Kaka,Cele tana garin gidan Umma ta yiwa Kaka wayo kawai ta bashi magani ya sha a cikin lemo wai kar yayi Sanya a Raina shi, tace kaka kaga maganin nan kyau ne da shi na Karin karfi ne tunda kaga ka kwana biyu shi yasa na tsumaka,Kaka yace kina so na ni kaina bana so a rainani,Cele kayan makulashen ta bawa kaka tace sai da Safe Kaka ka kula da Amaryarka,Kaka yace kula bata wasa ba kuwa, Allah yasa kar tafi karfina ni dai kizo da safe da wuri Idan ta min illa ko gashi ayi min ko ki kaini asibiti,Cele ta dinga dariya ,Kaka Ya tafi gidansa yana Addua Allah yasa kar mama tafi karfinsa a kwanciyar auren shi Kam yace Ina lallaba tsufansa haka kawai da haka ya shiga ciki yana Addua yace Allah yasa Yar laba laba ce .
Masu sharhi Ina matukar godiya
AsmaBaffa
[8/30, 10:20 PM] AsmaBaffa: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼
MATAFIYA
BOOK 2
111-115
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN
*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka