Showing 72001 words to 75000 words out of 155384 words
Chapter 25 - YAR AIKIN KARUWAI 2 cmplt By Asma Baffa -www.sufinovels.com-.txt
ta Ganshi ya fito harda carbi da jallabiya,Baffa ta Kira tace zo kaga Auta me gida,window din ya karaso tare da rungume Mami ta baya suna kallon Auta suna dariya,Baffa sahu daya suka yi da Auta yau,sai da aka idar da Sallah ya tsaya harda azkhar sannan suna fitowa yace Baffa barka da asuba Ina kwana? Baffa yace sai kazo ma gaisa a hanya zaka gaishe ni,yace ni fa yau bazan zo ba bacci zan koma 12pm Kuma ina da lecture,au yau ma baza ka hakura da school ba kana Angon,yace me zan mata to shike nan sai na dinga zama,Baffa ya Kalli Auta yace Auta Anya kuwa kana son yarinyar nan duk mugun son aurenka,Ina sonta mana ya furta a ransa yana cewa karya nake bana sonta,sai da zasu rabu kowa zaiyi bangarensa yace ka gaida Mami,Baffa yayi dariya yace to zata ji ya tafi,Yana komawa bacci ya kwanta ya dinga bacci,Salma kuwa tuni ta koma bacci,sai 10am tashi tayi ta gyara gidan tace wallahi bazan gyara masa daki ba,wanka tayi taci kwalliya cikin leshinta na lefe brown and golden color tayi kyau,mayafi ta yafa ta fita taje part din Mami ta isketa a kitchen a kasa ta durkusa tace Ina kwana Mami,Mami taji Dadi taga hankalin Salma,ta amsa da fara'a,bayan nan ta fice tace zata je ta gaida Sauran tana mikewa Baffa ya fito cikin Shiri zai fita,ta sake zubewa a kasa guruf tace Ina Kwana ya amsa tace an tashi lafiya ya amsa da fara'a dama Baffa ya tsani gaisuwar zamanin nan da akeyi mussamman yaran yanzu ana ganin wayewa ce ko wacce Ina kwana wasu ma kafin ka amsa sunyi gaba Babu mutunci ba girmamawa Ina kwana kawai sai yarinya ta wuce ta barka nan,Baffa yace Honey zan fita,Salma kunya ta kamata a ranta tace bariki kan Uba tsofai tsofai a gabana cab wai honey,tana tsugune taga Mami ta rike hannayensa tana kwarara masa Addua,Salma tana satar kallon su ta mike sum sum ta fice kunya ta isheta ita Kam,part din wise ta shiga dauke da Sallama a bakinta Papa ya wani kwantar da Kansa a kirjin Wise suna Palo kuma,Baffa ganin surukarsa ce ashe ya tashi da sauri,Shima durkusawa tayi ta gaida shi ya amsa da fara'a ya tashi ya koma bedroom,tace Aunty Ina kwana? Wise tace ai ni kawarki ce yarinya tashi ta jawota saman kujera tace da Alama kalau kike wlh Auta ba abinda yayi gaskiya Ina Jira nazo gashi,Salma tana jin kunya tace sai kace wata kaza,bata Dade ba ta tafi wajen Iyamami Sabreen ta koma can da kwana ta gansu tare suka mata wani kallon banza suka watsar da kyar ma suka amsa gaisuwarta,Iyamami tace ashe da sauran hankalin da kika San kizo ki gaida manya Allah ya kyauta ko a Ina Auta ya kwaso Sabreen ta karasa da oho masa,Salma ta kalle su ta balla musu harara ta juya fiya fiya ta fice, Iyamami tace Iyye kaga yar iskar yarinya to dama tun kafin a aurota an zuga ta,lallai an sanar mata mune shegun gidan nan zata ci ubanta,Sabreen tace kyale banza can zata yanka.
Salma part dinta ta koma tana shiga ta samu Mami har ta Aiko musu da abinci,Auta ta gani ya fito daga shi sai wando 3qutr ya fito da mopper da tsintsiya ya gyara bedroom dinsa tsaf da toilet,tazo zata wuce yace dadin abin Allah ya mana hannu Kuma ya bamu lafiya mu bamu Saba kazanta ba,binsa tayi da kallo gaba daya ta shagalta da kallon surar Auta Dan dagwas har ta manta ma a Ina take ta shagalta ta tsura masa Ido,yace Hello,hankalinta ta dawo tace ai kasan ba Kai kadai bane a gidan da mutane to baka birge ba ka Maida rigarka ka Saka ya fiye maka na gaji da ganin muninka,Auta yace sannu uwata Mami ya ja tsaki yaje ya ajiye mopper ya dawo ya wuce sama abinsa wanka ya fesa ya sha kana nan kaya ya dakko yar jakarsa ya ratayota ta wuyansa ya fito Dan gaye anci swagg, Salma ta zuba abinda take so tana ci,ya fito ko kulashi bata yi ba tana Shan tea tana danna wayarta karama Vivo,cup ya dakko ya zuba tea ya hada abinda ya sha yaci chips kadan ya dauki chegum me tsada ya jefa a bakinsa,ta kalle shi ta tabe baki tace Iyayi mu ayi mana Iyayi mene bamu sani ba Mami Son kawai, komai sai an baka ai Kai a garin nan baza ka taba samun aikin yi ba,ga mate Dinka nan suna Neman na kansu kaje gari ka gani Yara kanana sun zama attajirai Kai kuwa sai dai a baka ka dogara da kudin Iyaye,a haka Zaka iya daukan nauyina,Auta yace Allah ya baki lafiya naga Alama baki da hankali,Salma ta mike tare da rike kugu tace Kai waye da zaka fada min magana,tsaki ya ja ya fice ya barta tana kwafa,cikin fushi ya fito a fusace yana cewa yarinyar nan naga Alama bata da hankali,Nawwar ne ya juya kan kan motarsa yayi parking ya iske Auta yana Shirin shiga motarsa da Baffa ya siya masa gaf da aure,yace Ango Makaranta Kuma? Auta ya kalle shi kawai ransa a bace,yace Auta kalau Ango Kai da za a ga kana nishadi,Auta harara ya zubawa Nawwar ya shige motarsa ya wuce,dariya ta kama Nawwar yace duk yanda akayi Amarya ta hana Auta kanta haka ya kwana Babu komai, haka nema ya furta tare da shiga bangaren Mami.
Mami tace Kai Kuma lafiya kake dariya Kai kadai yace ni da Auta ne kinga uwar hararar da ya min ya tafi fa school,Mami tace so soon haka har ya tafi? Yace ae Kuma yana fushi,tsokanarsa kayi maybe,Nawwar yayi dariya yace Anya kuwa Auta yana son yarinyar nan Mami,Mami tace Nima Ina ganin da wani abu kawai bazai fada bane sabo da Auta da aure amma ace gidan ma sai da na tasa keyarsa gaba yaje,Nawwar yace Allah? tace ae fa abin da mamaki wlh Kuma shi ya zabo abarsa bare ace mun takura masa,Nawwar yace lallaba shi zakiyi ya fada Miki ke Zaki iya jure iskancin Auta, kyale shi Idan haka yaci gaba da faruwa zan gane ai,Nawwar yace shi yasa na fada muku Auta ba wani hankali gare shi ba girman ne kawai kuka ki ji,da masifa Mami tace to munyi masa din kaji min yaro ka fa damu Autana,ai shi baya laifi dama,ae naji Dalla tashi ka tafi ni,Nawwar yace yau bazanje aiki ba fa Kuma Rabia na Kai Unguwa bata nan,Ina taje? Gidan Seraline wai zata yini a can,Salma tana gama karyawa ta wanke kwanikan ta yafa mayafinta ta taho part din Mami ko ta samu saukin tunanin Baso a ranta.
A hankali tayi sallama ta shugo ciki Nawwar ta gani taga suna kama da Auta tasan shine yayansa harda jin kunyar Yaya,a gaban Nawwar ta durkusa tace Yaya Ina kwana,ya amsa tace Ina Auntyn fa? Yace taje unguwa kuna lafiya? tace lafiya Alhmdllh, gaban Mami ta koma ta sake durkusawa tace Mami ga kwanikan Ina za a ajiye? Mami tana sani tace ya tashi kuwa? tace ae ya tashi,Nawwar yace wai wa? Salma tace me can wajen take nufi fa,Nawwar da hannaye ya dafe bakinsa dariya zata kamashi wai Auta ne me Can wajen sai kace tsohuwa ita baza ta fadi sunan Miji ba Babu kyau wai,dariyarsa ya boye yace ai ya tafi school tace ae,yace a gaishe ki Mami cewar Salma,Mami tace wa fa? tace shi din,Nawwar jaridarsa ya dauka tare da rufe fuskarsa yana dariya a boye,Doguwar kujera ta samu ta kwanta a kai sai bacci, Ya kwashe ta ta dinga bacci sai gani suka yi tana ta uban bacci sai da azahar tayi sannan ta tashi lokacin Nawwar har yaje masallaci ya dawo tana yin Sallah ta Kuma kwanciya a saman Sallaya sai bacci,Nawwar suna ta jira da Mami suna kallonta ta dunkule waje daya tana ta uban bacci,sai ga Auta ya shugo da Sallama ya ganta tana bacci,Mami ta kalle shi tace Yan Makaranta,yace Naam na dawo ya mikawa Nawwar hannu suka gaisa,ya nemi waje ya zauna yana satar kallon Salma yana Galla mata harara Mami tana kallonsa duk abinda yake Nawwar tayiwa signa da Ido Auta harda turo baki yana kallonta yana auna mata zagi a hankali,Nawwar da Mami suna ta masa dariya a boye har Salma ta Farka tana tashi taga Auta itama Ido ta faka ta zabga masa harara har da ce masa Yan Yan Yan kasa kasa a boye,ta murguda masa baki tayi fari ta masa wani up and Down,Mami suna ganin komai ga Auta ya nuna kamar baida hadi da Salma itama haka ba ruwan wani da wani,ganin Mami zata gane su sai Salma tace sannu da zuwa,Nawwar yace lallai yarinyar nan ta iya munafurci ta gama hararsa,Auta yayi murmushin dole sannan yace tashi mu tafi oya come come let's go,ta mike tace Yaya ka gaida Aunty yace to,Auta harda sakalo hannunsa ta wuyanta suna fitowa ya hankadeta saura kadan ta fadi,ta juyo a fusace tazo ta hankade Auta da karfi ta wuce tana tsaki.
Mami kuwa tace ka gani ko ji yanda suke harar juna,Nawwar baki ya tabe yace matsalarsu ce ki kyale su kawai.
Salma kitchen ta shiga ta dakko juice zata sha Auta yace mayunwaciya look at you kinga banza ta fadi kin wani dakkowa mutane lemo ya fisge ya Maida kitchen,tace ai Kai Kam baka gaji iyayenka ba wlh marowaci akan lemo kalleni tsaf na maka kama da yar yunwa,Kai kana da kudin siya ne? Ba su Mami bane suka zuba maka komai ba ina kaga kudin ko zaka iya siye ne? baza ka iya siyan ko tissue da kudinka ba komai sai an maka Kai tafi can Kuma lemo ne sai na sha sai dai ka mutu,ta Koma kitchen ta dakko, sai ga abincin Mami an kawo musu ,tace nikam na shiga uku komai sai anyiwa me gida bashi da ko taro,Auta ya tsaya kawai yana kallonta sabo da ta buwaye shi ta rainashi da yawa, ta jawo abincin tace mutum komai sai dai ayi masa na zama matar ladan Noma,flask din ya fisge yace ai ba daga gidanku aka kawo ba,hannu tasa itama zata fisge ya rike gam ta kama hannunsa ta gartsa masa cizo,Kara ya saki ya saki flask din ta kwace tace sai na ci to Dan bakin ciki sai dai ya mutu,Auta yana yarfe hannu yace hungry girl mayuwanciya ko kunya bakya ji,tun Ina yarinya na siyar da kunyata ni Kuma a gidana ba Wanda ya Isa ya hana ni cin abinda nake so gidana ne dole inyi abinda nake so yawwa ehe sai dai ka mutu,Auta ya rasa ma me zai ce sabo da haushi yace na tsaneki,Nima haka ta furta tana cin fried rice dinta da kaza tana wani zukar kemo harda wani Jan lemon yana Kara zuuuu zuut tashi daya ta shanye karamin kwalin guda tace Dan jeka kitchen ka dakko min wani,yace baki da kunya ya juya haura sama,sai da yayi wanka ya shirya cikin kana nan kaya marasa nauyi ya fito yana zuwa ya samu taci iya nata ta kwashe komai ta maidawa Mami sauran,tace ya naga kadan aka ci? tace yace ya koshi shi yaci a waje,Mami tace Autan? tace ae yace yaci a school,shike nan cewar Mami ta juya ta tafi ta iske Auta a zauna yana latsa waya yace Ina abincin? Na mayarwa masu shi tunda Kai komai sai dai ayi maka baka San ka nemi na kanka ba,Auta baki Bude yake kallonta yace Amma dai wiwin Baso ta taba Miki kwakwalwa kema? Karka dameni bani da lokacinka,kwafa Auta ya ja ya fita tace yaro karami kusan sa'ana sai Iyayi da nawa ya girmeni ta gyara zama tare da harde kafafu tana cewa wahala ma sai ta sa ka sakeni na koma wajen baso na.
Auta bai je wajen Mami ba tunda ta Riga ta fadawa Mami ya koshi sai ya shiga wajen Wise yace wai abinda baya so aka dafa taliya,Wise ta zuba masa abincin ya ci ya koshi yayi tafiyarsa ya bar gidan gaba daya.
Bacci taci ta koshi, kamar taci kafar Kare haka yamma nayi tayi wanka ta shirya cikin shadda ta tafi bangaren Wise suna ta Hira tana rage tunani.
Washe gari ma haka suka yini fada da Auta ba ji ba gani,har suka kwashe sati biyu a haka fada baya karewa, basa Shiri Sam ganin haka Mami tana fahimta taji tsoro tunda Yara ne kar azo ayi saki, Auta ta samu Yazo gaisheta,tace fada min uban abinda kake boyewa wallahi ko na fita harkarka,yace me kuma Mami? Karka raina min hankali nifa na haifeka nafika sanin waye Kai wallahi Idan baka fada min dalilinka na auren wacce baka so ba to ba ruwana da Kai Karka sake zuwa inda nake,Auta badan ya so ba kawai yace kiyi hakuri Mami ya bata labarin Salma kaf ya fadi gaskiya,Mami tace Auta baka da hankali ashe,Matar da bata sonka kasan kuwa kiyayyar mace Idan ba ta son mutum,me ya kaika wani biyan kudi ka aureta bayan kasan wani take so,Auta yayi mukus Mami ta dinga zazzaga fada,yace Idan kin yarda nan gaba ai zan rabu da ita ma,shut up zaka Raina mana hankali mu ai wasa muka maka ba cewa mukayi zamu yi maka auren dole ba shine ai gashi Kai ka yiwa kanka auren dole Mafi Muni ma,wacce zuciyarta wani take so,to ko da wasa ba saki kayiwa kanka wlh baka Isa ka sake ta ba sai kuyi ta zama a haka matsalarka ce,Mami taji zafin Salma bata son danta dama,amma Kuma Auta shi ya jawa kansa.
Zuwa Mami tayi tace Salma ta dawo part dinta kawai aka kwaso kayan Salma na sawa aka bata dakinta a kasan Mami,Shima Auta ya dawo part din Mami da dakinsa,Mami tace kowa yayi harkarsa muga abinda Allah zaiyi.
Salma kawai sai ta mike kafa kamar gidan ubanta a gaban Mami ma fada suke yi da Auta.
Yau Auta yana zaune Mami tana gefensa tana Yanke masa farcen hannu, Salma ta biyo ta saitin kafarsa tayi fatali da kafar Auta,Mami ta kalleta kawai harda shagwaba kamar uwarta ce Mami tace a canja min channel,Auta yace wai gidan ku ne kin fa ishe mu kina gani Mami ta min ball da kafa Autanki guda kisa ta bani hakuri,Mami tace ke Salma ki Daina haka Mijinki ne fa,Salma tana dire diren kafafu tace ni Allah Allah...shike nan sorry ta zauna ragwaf a kujera,Auta yace bata da kunya fa Mami shame on you ya furtawa Salma,tace na karbe hakuri na Dana baka nafi karfin na baka hakuri,yace ke Dalla kucaka,tace ai gwara ni kaifa kwaila da Kai zaka iya siyen tv ne ko tv Kana da kudinta ta fisge Remote din,Mami tana jinsu bata ce musu kala ba dariya ma take a ranta ana mata maganin Auta,haushi Auta yaji yace Mami kina jinta ko garin kwace hannunsa Mami ta Yanke shi kadan da razor Auta kamar Wanda aka kwadawa Adda ko wani takobi haka yake yana yarfe hannu,Mami tace Kai Kam Allah ya sawwake maka kamar ba Namiji ba,tissue ta sa tare da danne masa wajen,Salma tana masa dariya tace sai kace ba Namiji mu kayi mana shuru.
Yace Mami bani ruwa na sha ko na ji salama,Mami ta mike zata dakko masa ruwa Salma tace Mami da kanki kamar wannan ya aikeki ki zamanki ya tashi da Kansa ya sha ya dawo,ke da uwata Zaki rabani marar tarbiyya ya ja tsaki,Salma ta dauke Kai taci gaba da kallonta.
Salma Allah ya yita da gasa sabo da yarinta da kuruciya Idan taga kusan sa'anta yana abu sai ta fara yi itama,Auta ta Raina an mata kananan kaya sunfi akwati biyu sabo da su can normal ne ana sawa bare Kuma matar aure,ganin Auta kullum cikin kana nan kaya yake sai itama ta koma sawa su normal ne amma sabo da ita ba a can ta taso ba tana ganin ko mace ce ta shugo sai taje ta Sako katon Hijab,komai Auta yayi sai tace sai tayi itama,Idan Mami ta masa abu itama fa sai anyi mata,daga gani Mami ta taje masa gashi,sai bayan kwana biyu tazo gaban Mami ta durkusa har kasa tace Mami kin iya kitso ki min Nima? Mami tace na iya,tace kalaba nake so,tace to bari ayi Sallar la'asar tace to,ita Salma tana birge Mami sabo da biyayyar ta da kunya sannan ga addini Sallah bata wuce,Auta 4pm ya dawo daga school ya shigo ya dora Kansa a cinyar Mami sai ga Salma ta fito ta bata rai tace matsa min,ko kulata baiyi ba,tace Mami kice ya matsa min ai kitso za a min tsaki ya ja ya tashi ya koma daya kujerar kasa kasa tace kwailan Miji kawai tana turo baki,Mami dariya ta kamata haka yake cewa Mata ko wacce yace kwaila ce yau gashi an ramawa su Omaira cikin ruwan sanyi,ran Auta Idan yayi dubu to ya baci kamar zaiyi kuka zaiyi magana Mami tace enough haba Enough of this nonsense ku kullum fada ke Salma Mijinki ne fa kike masa, haka kikaga anayi akan banzan tunaninki,sabo da bakwa son juna ku zauna lafiya mana,bana son rashin kunya Salma Mijinki ne fa ke ana lallaba Miji ana masa biyayya ke Banda ke kowa haka kika ga yana yi,Kai ma ba ruwanka da ita kowa yayi harkarsa, Auta yace dama matsalar da nake gudu kenan da auren kwailar yarinya indai ka hada harka da kwaila to ka shiga uku yanzu babba me hankali wacce tasan me takeyi zata yi abinda wannan sharar takeyi wannan tarkacen,indai mace ta mallaki hankalinta Ina zaka ga wannan shirmen,Ya Isa haka kayi hakuri kuyi hakuri da juna shi yasa fa na dawo daku nan gabana wato ban Isa ba ko bani da amfani,Salma zama tayi a kasa a gaban Mami tace kiyi hakuri Dan Allah tana so tayi kuka,Mami ta cire mata dankwalin gashinta dogo baki yala yala