Showing 96001 words to 99000 words out of 155384 words
Chapter 33 - YAR AIKIN KARUWAI 2 cmplt By Asma Baffa -www.sufinovels.com-.txt
ka koma ko baza ka kulata ba kawai ka koma kayi hakuri,haba Autan Mami duk mun zaci I yanzu ta samu ciki ma,me kakeyi ne wai baza kaji dadin ba,tuntuni ka dame mu aure aure kace ka balaga tuni ko ba haka ka fada mana ni da Baffa ba? Auta yace hakane ai Kuma na balagan ko ban balaga ba Kalli gemuna ya kusa fin naka ma,Nawwar yayi dariya yace to aini banga balagar ba Auta kaje ka bata Service,Auta yace Yaya wlh har tsoron yarinyar nake ji fa,ba dama nayi sukuni,Nawwar ya dinga sheka dariya yace kwailar? Yace ni naga sharrin kwaila wallahi sunfi manyan gyara Namiji, kana gani Yaya ya bigi kirjinsa ni Auta Autan Mami gyarani take tsaf,bana jin kunya da fargabar kowa amma ni yanzu Yaya bana so mace ta rabeni kar ta gani,a school ta sa min Ido ta hanani sakewa sai sawa take Ina batawa da Yan mata duk sai sharara Mari nake kawai a school fas fas, yanzu duk Mata sun kiyayeni Allah Yaya.
Nawwar ya gyara kujera ya zauna yana tuntsira dariya,Auta yace hmmm shima ya zauna yana gyara wandonsa da yake ass down da shi yana zazzagowa,ya daki kafadar Nawwar yace Yaya ka gane ko? Auta ya shafa gemunsa da sajensa yace kasan Glory ko kaga yanda muke good time da ita da tausayi ya karasa maganar a sanyaye yace wallahi Yaya rannan na gwaura mata Mari itama,Chima nan tawa yarinyar nan akwai kirki amma ya sake sanyaya maganarsa yace amma itama na fesa mata Mari wlh hagu da dama,Yaya sai da ka fada min gaskiya naki ji ka Cece ni,Nawwar yayi dariya kamar cikinsa zai ciwo ya buga kafa sosai yana sheka dariya,Baffa ne ya dawo daga ganin Jaririn ya wuce su suna hira suka masa sannu ya wuce,Nawwar yace dama maganin irinku kenan Babu rainin da baka yiwa mata ba,kanwar Rabi ma cewa kayi zasu mallakeka yanda aka min,Auta yace ai ni yanzu so nake ma wannan ta mallakenin amma yar jakar Uba sai kayan haushi zan mata baki Yaya,Nawwar yayi dariya kamar me yace Autan shagali Allah yayiwa Salma albarka Karka yi mata baki kaji sai ta sake lalacewa,Auta yace saura kadan kuwa.
yanzu Yaya kune Manyan,au yanzu ka yarda? Yace ah na yarda kuje da girmanku Allah ya kara girma,Salma ta gama kukanta ta wanke fuskarta ta zo ta share dakin ta goge ta gyara komai ta dauke kwanikan ta kwashe Rabin abincin ta kulle a Leda ta jefa a shara tace Allah na tuba nayi barna,Mami ce shigo tace wai fada kuka yi da Autan? Salma ta kirkiro fara'a tace a'a Mami akan nace sai ya ci abincin da yawa shine yayi zuciya wai shi ya koshi kinga Dan Wanda ya ci ta Bude flask,Mami ta leka tace ba sai ki kyale shi ba, ki Daina biye masa,Salma zuciyarta ta karye ta fashe da kuka,Mami tace to kiyi hakuri Salma aure sai hakuri haka kowa yake hakuri da nasa,Salma tana kuka tace Mami ya Auta zai dinga min haka sabo da Allah,Mami tace ke karki sake ki masa kuka ba a yiwa Namiji kuka zai Raina ki Idan ya gani shike nan zai samu lagonki karma ki bari ya San kinyi kuka wanke fuskarki,Salma da sauri tawanke fuskarta a sink,tace yayi? Mami tace ae je ki shafa powder bari naje wajensa,Salma tace karki masa zancen Dan Allah zai ce na fada Miki kinga bazai ji Dadi ba zai ce Ina hada shi da iyayensa,irin dai Dan nasiha Zaki masa a Dan wayence kin gane ai,Mami tayi dariya sosai wai ita Salma zata koyawa duniya,tace ashe dai Salma da hankalinki wallahi kina da hankali kin Kuma birgeni,tayi dariya tace ai sai ma nan gaba sai nafi kowa hankali a gidan nan zaku gani Mami,Mami tace oh jama'a Ina da surukai a gidan nan baga Rabi ba ga Salma,ta fice,tana fita Salma ta hau tsalle tana furta yes yes.
To yau Salma za a fara kwana a dakin Auta sabo da Baso yace,Mami bata sani ba ma,bata San ance ta dinga taya Auta kwana ba,sai da ta bari kowa ya kwanta tayi Shirin baccinta cikin kayan bacci ta lallaba Sadaf Sadaf kamar zata dauki kayan wani tana zuwa kofar Auta ta Murda ta fada ciki da gudu,Auta yana cikin bargo tana fushi wai an mata dole ta janye bargon da Auta ya lulluba ta shimfida a kasa ta ja pillow daya tayi shimfida ta kwanta abinta,Auta yana jinta bai ko kulata ba,magana ta shiga yi tace shike nan mutum sai fushi,ba dama ayi abu sai fushi ai ba haka ake rayuwar duniya ba.
Auta yana kwance kamar bacci yake yace Aljanna dai Idan naga dama kafa zansa na take ko na tsinewa mutum, Kuma sai dai kiyi ta kwana a kasa baki Isa kin hau min gado na ba,tace ai Nima Ina da gadon ganin damata ce tasa nazo,suna ta carcar baki har bacci ya kwashe su.
Cele suna sauka a airport ta Kira Ahsan ta sanar masa sun sauka lafiya yayi murna,taxi suka shiga da kayansu gaba daya duk sun zo,Kaka yace to jaraba mun dawo tsiya sai kwazazzabo titin ma baza kaji luwai ba haba,kaka ya Kalli Kasuwa za a wuce yace Cele ji wai nan sababbin kaya ne ake siyarwa,Cele tace ji wata Vest a rataye kamar gwanjo,Kaka yace ai nan Sabuwa ce Kuma? tace ae fa wai gashi nan ma rubibinta akeyi,Kaka yayi dariya yace Kalli mutane Dan Allah duk sunyi baki sai jijiyoyi kamar masu cutar yunwa,ai nan a koshe suke Kaka baka gani har yanga suke ba ,Kaka ya Kalli wata mace yace Jita yar kutun Uwa to ba Madara tana tafiya kamar bata da jini,Cele tace yo ba protein,haka suka Isa gida,Cele ba Sanya dama akwai Almajirin da suka bari a gidan gashi da tsafta duk yana gyara gidan babba ne,Cele ta sake gyara gidan tayi wanka tace Kaka Allah toilet dinmu kamar ta akuyoyi,kaka Yace da kyar na iya fitsari, muje wajen Umma na matsu na gansu cewar cele,suka fice suka tafi tsohon gidan suka je,Cele taga Abba a kofar gida a Sallaya yayi tagumi,Cele taji tausayinsa abinka da mahaifi,tace Abba abin mamaki sai yayi murmushi yace Rufaida saukar yaushe tace Abba dazu dazu tace Abba kalleni me ka gani? Yace kin hadu ga kakan naki ma yayi Jajir da shi yayi kiba,Kaka ya Mika masa hannu suka gaisa yace Zauna zauna Haladu,Kaka yana mamaki Shima mutumin da baya kulashi yake gaba da shi,Cele tace Abba Umma fa? Abba da tausayi yace ai sun bar gidan nan uwarku da Yan uwanku sun ware ni kamar bani na haife su ba,Rabi aka gani yar uwarki wacce aka haifeku tare,Cele tace Allah amma naji Dadi dama itace Rabin kasan Allah Abba wata ta Dade tana tareni tana ce min Rabi to kasan ni ba mutunci naci ubanta amma naji dadi, na sake ganinta a Makkah kuwa matar naki kulata,amma da Alama a kauye ta girma naji Rabi gatsal Ina laifin Rabiat,Abba Ina da aure fa yanzu labarin sai an zauna,Abba yace gaskiya Cele kin Kara hankali,Cele tace Abba ai aure nayi shi yasa dole a Dan nutsu albarkar aure ce,Abba sai soyayya nake ta yi,amma ya za ayi su wareka Abba gaskiya Basu kyauta ba,Amma laifinka ne Kai ka jawo,badan zuciyar Musulunci da Kuma Uba ubane fa to Abba wallahi da baza mu kulaka ba,kaifinmu ne da muka zo a mata? ita Uwa da tazo a mace wani ne yace tazo a mace ba Allah ba,Abba kuka ya saki yace shike nan ni ba inda zanje naji sanyi kowa sai ta fada min abinda taga dama,Cele tace Abba bafa zuwa nayi ka min kuka ba gaisheka nazo bani kwatancen Umma,Yace bazan fada ba kema tafiya zakiyi wajenta ki barni,Cele tace Abba kasan duk da Ina maka wasu abun na bacin rai amma kasan Kai ka jawo Kuma ina da tausayi,Cele ta karkace ta zaro kudi sun Kai dubu ashirin tace ungo Kaci albarkacin macen da baka so,Abba ya karba yace kamar kin san banci komai ba tun safe dama uwarku itace take San mana abincin Idan Kun kawo mata Kuma Rabi ta auri me kudi,Cele tace me kudi ne? Yace na gagara ma Cele saurayi matashi kamar bature idan kika Ganshi ga hankali,Rabi ma ba sauki da masifa tayi mana Sallama,Cele tayi dariya tace wooo woo jinina a lafiya dai Rabi ai dole naje gidanta,Abba yace ta haihu ma yau kwana biyu,Cele tace Masha Allah da ni za aci suna,Abba yace Dan Allah duk da ta rigaki Shan iskar duniya ki mata fada ta dinga kula da Mahaifinta,Cele tace zata ci ubanta zanje tana min rashin kunya zan gurje bakinta,ta girmeki Cele da kusan awa Daya,Cele tace yo aini ko sa'ar Umma ce bana tsoro,Bari naga Uwa,Abba yace Allah sarki yau tun safe kunu ne a ruwan cikinta sabo da yunwa,Cele ta shiga tace kina inane ke Uwa fito ko yunwa ta Miki Illa ne? Uwa ta fito tana washe baki tace Cele,Cele tace kalleki abin in masge duk kece kika ja mana bala'i baki iya tarbiyya ba da ace kinwa danki tarbiyya yasan addini ai bazai yi haka ba, ta zaro dubu biyar tace ungo sabo da Allah,Uwa tana murna tace na gode dama tun safe kunu na sha,tace kyaji da shi ni kinga tafiyata Uwa kin shiga uku da gori wlh har ki mutu ko kina kabari Ina binki da gori,akan Zaki sace ni sai Umma ce ta bawa Kaka ni da yanzu Ina wani kauyen,Uwa kiji tsoron Allah tam,ta juya ta tafi,Abba yaji dadin kudi sai yayiwa Cele kwatancen gidan suka tafi da kaka,Umma sai jin Cele tayi tana kwalawa Umma Kira Umma fito yarki ta dawo na ragargaji shedan, Umma ta fito suka rungume tace Alhmdllh kin dawo lafiya Ina ta Miki Addua Allah ya tsare min ke,Cele tace kaji Uwa ta gari,Umma ban mu tafa, Umma ta harareta tace Ina su Omaira? Suna can kudu wajen yar uwarki Rabi,Naje wajen Abba ya fada min,Umma haka Abba yayi laushi? Cele ta hau bawa Umma labari har komai da ya faru a Makkah,Umma tace Allah ya rufa mana asiri baki haihu ba, wai da munji kunya,Umma ma ta bawa Cele labarin Rabi kaf,tace Allah sarki ashe Rabi har dandi aka yi,Umma tace bafa tayi ba Allah ya amsa adduata ya tsare min Yata dama Ina ta mata Addua,Cele tace gaskiya ta sha wahala daga baya dole muje gidan Dagaci ko yar magana ce in jajjefar masa duk da ya tuba wallahi sai na fadi baka,Kefa halina dake kenan,ki dai shirya zuwa suna sannan ki fadawa Mijinki Idan ya amince tace wayyo Umma ai wani Alhaji Salmanu ne zai amince ,Umma sai murna take Cele tayi aure,kaka ya shigo Shima yayiwa Umma murna,Umma ta dinga yiwa Kaka godiyar rike Amana.
Duk Cele ta zaga Yan uwa da abokan arzuka ta raba tsaraba sosai.
Masu zuwa suna Yan uwan Rabi sunyi Shiri ciki harda Cele da su Bilkisu,za a tafi,ana gobe suna suka taho gaba dayansu banda Umma.
Salma tayi Shirin school Mami tace nawa kika kudin littafin? Salma tace Haushin kare,Mene haushin kare Kuma? dariya tayi tace Mami wan wan Ina nufin one one dubu Daya da dari Daya,Mami tayi murmushi ta girgiza Kai tace a wajen Baso kika koya wannan abin sai Yan Daba.
Ba Wanda yasan za a zo da Cele har ni Miracle sun boye min wai surprise za a mana,sun cewa ma su Raheemah da suka sani sunce Cele ta fasa zuwa,naji haushi a raina nace lallai bata da mutunci sai naci uban yarinya .
Domin Karanta cigaban wannan labari ku danna bulun dake kasa ko kuma Hoton 👇👇👇
https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/yar-aikin-karuwai-book-2-page-111-115-last-page
👆👆👆👆👆
AsmaBaffa🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼
MATAFIYA
BOOK 2
71-75
Official
By
AsmaBaffa
Cele mota suka shiga da asuba a tasha ma suka yi Sallar asuba,sai da tayiwa Kaka sallama,Cele,Bilkisu,Nazira da Nazifa Suna mota an ware wuta dukkansu sunyi Addua Cele tana gama Addua sai bacci,Nazifa ta tasheta tace ke Cele a mota fa kike har kudu zamuje Ina mu Ina bacci in Banda salatin Annabi,Cele tace ni da naje Sudan a mota ai wannan hanyar lafiya lau ce Allah ya tsare karki sake tashi na gaskiya,suka kyale Cele tana ta bacci sai yamma likis kusan dare suka sauka a tashar duk suka yi sallolinsu,Auta ne zai dakko su a tasha yaci kwalliya yana taje gashinsa Salma ta dakko turare tana fesa masa tace a dawo lafiya Allah ya tsare,yace Ameen Yan mata,tace a'a kwaila dai,ni na Isa ya furta yace zan tafi tace to ai na maka Addua,yace to yau dai Yan mutuncin suna ka kenan,murmushi tayi tace Kaine dama kake tsokanata akan Basoooo....Salma ta karasa da kukan kissa tana nesa da Auta ta taho da gudu ta rungume shi,tana kuka hannayenta ta wuyansa ta sarkafo su tace I'm sorry tana goga fuskarta a wuyan Auta,Auta ya sake kankameta yana cewa to mene na kukan Kuma harda bubbuga bayanta sannan tayi shuru Salma tasan kan tsiya,yace muje ki rakani tace Mami fa kunya nake ji,to ba aure mukayi ba Ina ruwanta dake,Salma ta biyo shi suka fito taga mutane a Palo su Star dukkansu sai Salma ta fara bin bango tana dafa bango tana rabewa tana tafiya tana kallon su wise,Kowa ya bita da kallo maimakon ta raka Autan sai tabi saman bene da gudu,Wise tace Kai wannan yarinya anyi yar kanta munafunci a cikin Yar nan ya baci wai daga Ina bata maganin mata Ina fada muku yarinya kullum bata fashin zuwa harda ce min Aunty ba sabo ne,star ta kyakyace da dariya tace wlh bata San Antena ba zata ci ubanta bawa yar banza tayi ta sha Auta in ya tashi zata gane kurenta,ai da nice ke na sha'awa zan dirka mata ta tafi wajen Auta da kanta yar banza,Wise tace bazan cuceta ba yarinya ce,Star tace Allah sarki Wise yaushe kika fara tausayi iyyeee naga Malam Abhulkhairi ma karewa,suka yi dariya, Mami tana bangaren Baffa ya isheta da korafi ta daina kula da shi yanzu ta tare wajen surukanta ta kwashi su Haidar Yayan amaryar Baffa da ya saki da Hamra ta tafi dasu gidan Rukayya tare suka dawo.
Auta yana parking sun idar da sallolin da ake binsu,yana ganin Cele ya ganeta yace wlh banbancinki da Auty Rabi kawai wannan yar tawadar Allah da Aunty miracle take da shi ke Babu shike nan ni Banga banbanci ba Sam,Cele tace Kai Anya ban taba ganinka a Makkah ba amma takari ne Kai ko a can aka haifeka Dan agulla,Auta yace kece dai takari yarinya ni me zai kaini Makkah na zauna,Cele ta kalle shi kawai tace ba komai duk abinda aka yiwa zabuwa watan bakwai ne ya ja mata zaka ci ubanka muje ta mike tana Jan Jakarta tace ke Aunty Bilkisu bazan jawa kowa jaka ba kowacce ta ja abarta da kanta,Bilkisu tace sannu uwata,Cele ce ta shiga gaba, Auta shi Sam yanzu zuciyarsa gaba daya a wajen Salma take,yace Aunty kuyi sauri Ina da iyali,Cele ta kalle shi da sauri tace Kai yaro baka tafasa ba zaka Kone har Mata ce da Kai, Bilkisu tace munzo bikin ma karewa,Cele ta furta tab yanzu duk tsula tsiyar nan yi kake Dan nan? Auta yace sosai ma kuwa ai sai dai mu koyawa wani Kuma ba ace min yaro,Cele tace Kai ka kiyayeni so nake nazo lafiya na koma lafiya Karka sa kaina ya fara hayaki,tana gaba Auta yaja mota suka tafi.
Basu dade ba suka zo gidan,Cele taga gida iya gida ta Kalli Auta tace Kai yi tsiyarka yaro ka Isa ai kana da kare magana dole a maka auren gata,Auta yayi murmushi suka fito,tana Jan jaka da takalminta me tsini anci Abaya me kyau silver,wayarta a hannu,Sallama tayi a Palon ta shiga taga su Wise tace harda larabci ta wani kankare murya Aina Rabi? Star tace ke wannan kamar Cele aka ce baza kizo ba? Cele tace dama wasa nake Ina tsinau din? wai Rabi ce Tsinau,akace tana sama tace Masha Allah,Sannunku ku har Kun fara sunan ne tun yau? Star tace ba dole ba ,wai gasar ciki ake ne na ganku ko wacce da nata a gaba Star tace ba dole ba tunda mu duk bautar Antena muke,Cele bata gane Antena ba tace to shike nan ke me kama da Auta ba Kara ba kunya ki mana iso mana tace wa Hamra,Hamra ta mike tace ko kefa ai ba mazo gidan mutane mu shiga da ka,suka bi bayan Hamra,Star tace wannan za aje da ita,Suna ta kokarin banbance kamanninta da Rabi,Auta ya shugo yace tunda ban banbance ba ko wacce ta samawa kanta lafiya tawadar Allah ce kawai babancinsu,Star tace dama sarkin kurillah ai dole mu yarda da Kai.
Knocking Cele tayi shuru ba a bude ba Rabi tana bawa danta nono sai ta kulle kofa kar a kalleta,Nawwar yana gefe a kwance suna hira,sai da ta gama sannan tace bude ya tashi ya bude kofa Ido biyu suka yi da Cele juyawa yayi ya Kalli Rabi ya sake juyowa ya Kalli Cele, ya kalle su yafi sau biyar sannan yace shugo Cele,tace wai kowa ya sanni duk inda naje Cele Cele,Kaine Mijin Rabin kauye? Nawwar yace yes yanzu ai yar birni ce,ta shekara arba'in a birni? Yace a'a tace to bata dauki hanyar wayewa ba har yanzu yar kauyece,yaushe ma tazo birnin shekara biyu kacal, Rabi nace Ina jinki to ke da kike a birnin da me kika fini, Rabi kar muyi musu dake baza kiji ta Dadi ba,Rabi tace shugo ni karki isheni,dariya tayi tace akace kema masifaffiyar ce ashe Salamatu ce sanyi kalau,nace wallahi Haihuwa nayi amma ke hmmm ba a ja da Rabi duk tsiya na girmeki,Cele tace da mintuna,na dai rigaki to naji bazan