Showing 45001 words to 48000 words out of 155384 words
Chapter 16 - YAR AIKIN KARUWAI 2 cmplt By Asma Baffa -www.sufinovels.com-.txt
abinda kake Masa ba'a gani sai ace kana zaluntarsa ba dama ka Masa fada idan yayi laifi uwarsa ko danginsa na uwa da uba duk sa Ido suna Munafunce munafunce amma idan danka ne ko kashe shi zaka yi babu me magana Dan riko Kuwa shi Kansa kana Masa amma baya gani tunaninsa Kawai zaluntarsa akeyi aike ko aiki baza ka sa yaro ba sai ace ka takura masa,ko uwar yaron suyi ta munafunci suna zuga yaron sai kaga yaro ya Raina marikansa Yana musu wulakanci iri iri.
Nidai nasan dukkan Yan uwan Cele suna makaranta amma Kaka Malam Jibrin bashi da kudi da kyar ma suke ci su Sha Watarana ma Ina aika musu da abinci dama Attine ce me Neman kudin shi nasa sana'ar bata kirki bace Kuma ya tsufa,baya so a takurawa Cele shi yasa ma ya saki matar tasa bai Kuma kara aure ba daga shi sai Cele har ta Zama budurwa,batayi secondary ba ni Kuma banyi shishigi ba nayi Kara Kar Kaka yace na nuna ya gaza, duk yarana babu me zafin Nema irin Cele babu kuma me jaraba da masifarta,tun tana karama take Sana'a iri iri Kaka Yana bata jari har ta Fara kosan siyarwa safe da yamma,da rana Kuma tayi fanke da miya,dama Kuma tun tana Karama tasan mune iyayenta tasan Yan uwanta ba a boye mata ba labarin komai ta sani,ganin Yan uwanta suna zuwa makaranta sai tazo duk da Abba baya kulata Kamar ba shi ya haife ta ba haka Uwa ma,haka Cele take zuwa tace dan Allah a sata a makarantar boko amma sai dai ma ya daddaketa ya koreta Yana zaginta,Uwa ma haka tun tana hakuri har ta daina kyale su,in tazo gaishe ni ma Sai ya koreta yace ke tafi gidanku Yana kyararta,Uwa ma Haka take hantararta,inyi ta kuka ita kuwa Cele Allah ya bata jarumta bata damuwa,Watarana tazo gaisheni da yamma ta iske Abba a waje ya tareta yace ke gidan ubanwa Zaki shiga tace gidan Ubana,yace to baza ki shiga ba tace sai na shiga ko Kai baka Isa ba,baki ya rike yace ni din ? tace Kai waye ai ba ubana bane kai Allah ya kiyaye ace Kaine ka haifeni,yace to uwarki cikin Shege tayi ta sameki,tace ae ai gwara Yar shege ta tafi zata shiga gidan ya rukota Cele tace ita kuma sai ta shiga ya Kama yarsa da kokawa Suka dinga kokawa da Cele Kamar sa'arsa sai da ta shiga gidan Uwa ta samu a Hanya ta dauketa ta kaita cikin toilet ta jefata a ciki ta fito abinta.
A haka Cele ta Raina su kullum tazo fadansu baya karewa ita Kuma baza ta kyale su ba data sake girma ma idan tazo duk inda taga Uwa to idan Uwa bata gudu ba sai ta dauketa tayi waje da ita ta ajiyeta a wajen ta kulle kofar gidan sai Sanda ta Gama abinda takeyi zata fita sannan Uwa ta shigo,wanka Cele bata Isa tayi a gidan ba sai sun ci Mata mutunci shi yasa itama bata daga musu kafa gashi bata taso tare da su ba Babu wannan shakuwar kuma ma su ba Wanda suka kyale a yaran sabo da Mata ne su, Ni Kuma tunda Suka girma sune farin cikina su suke min komai haka Cele Yar Albarka Sana'ar nan tata kusan kullum sai ta kawo min kudin kashewa,sabulun wanka sabulun wanki omo duk suna tafe zata kawo,Yan uwanta ma Slifas ma tana siya musu har Uniform ta Sha dinka musu na school da kudin sana'arta ta min dinki bazai irgu ba,da tazo taga ba abinci a gidan zata Aiko min da su taliya Yar macaroni ko ba yawa Yar shinkafa kwano daya biyu haka,har su Bilkisu kafin su gama secondary sai data biya musu Rabin kudin waec da kudin da take sawa a asusu sauran Kuma na cika tunda Ina sana'ar Alala da kunu nima.
Ko ni Cele ban Isa da ita ba Matukar akan su Abba ne,Uwa dai itace ta sa Muazu ya sake sakina,Yana sakina Cele ta shigar da Kara Kotu akan Uwa tace sai na bar gidan,Muka je kotu aka zube zance Alkali yayi Nasiha ya jawowa Uwa da danta Aya da hadisi ya fada musu Allah sannan yazo ya musu fata fata yace ba inda zanje,Cele tace to azo a nunawa uwar mu wajen zamanta,Alkali yazo da shedu ya ware min dakina biyu da Palo da bedroom Dole Su Uwa badan sun so ba nake zaune a gidan,Cele ita ko da yan uwanta basa Zama lafiya Sabo da idan tayiwa Abba rashin kunya Su kan Mata fada sai ta hada dasu karshe ma ta tsani kowa tace duk bamu da hankali bamu san me muke ba bamu San yancin mu ba,ta daina zuwa gaishe ni amma duk da Haka tana aiko min kudin da sauran abubuwa,aka zo bikin Bilkisu Cele kayan kitchen da yawa ita tayi su ashe tunda aka sa bikin take tari ta sake dagewa da Sana'a badan cele ba da munji kunya a bikin Bilkisu Kuma ko bikin bata zo ba ,Bilkisu ta auri mijinta Yaseeer,har gida naje wajenta taki kulani sai da Kaka ya sa baki sannan ta kulani,Dariya Muka Yi har su Nawwar, Bayan shekara itama Nazifa da Nazira Suka samu Miji amma duk har na Bilkisu basu da karfi talakawa ne,Nazifa mijinta Usman,Nazira kuma Ishaq, suma dai sai rufin asirin Allah amma suna zaune lafiya.
Cele da tace zata tafi Saudiyya Neman kudi babu yanda banyi da ita ba tace sai taje ai da bama sonta bayar da ita muka Yi kyauta sabo da ba a kaunarta sabo da Haka ita ta gaji da takaici tafiyarsu zasuyi ita da Kaka,Shima Kaka biye mata yake idan tana neman kudi to girki ma shi yake musu ta hanashi Neman kudi tace ita zata dinga yi shi Kawai ya dinga girki Kaka ya Zama shine macen ita Cele itace Namijin,amma ke Rabi Uwa itace ta jefar da ke koma Ina ta kaiki ta fimu sani.
Nawwar ne yace a kirata,Omaira ta fita ta Kira Uwa da Abba suna tattabe baki Suka shugo, badan Nawwar ba ma baza su shugo ba,waje aka basu Suka zauna Nawwar yace Uwa dan Allah Sanda Kika dauke Yar uwar Cele Rufaida Ina Kika kaita,Uwa tace na manta memory na kwakwalwata ya goge lokacin bana iya tunawa kasan tsufa,Ni miracle Nace karki Raina mana hankali ki fada mana bamu da lokacin saurarar zancenki,Abba ya min tsawa yace ki kula ba a taba min Uwa,Uwa ta fashe da kuka tace kowa sai ya zageni tana matse hawaye,Miracle tace wannan kukan fa sai kace kinyi Zina ance za a jefe ki kinga wallahi Wallahi tun wuri ki Fadi gaskiya kafin na ebo Miki gayya guda su tara Miki gajiya ni kadai ma na isheki kafin nazo Miki da gayyata wallahi ba abin kunya bane in Miki zigidir, Uwa tace ni din? Ke dinfa kin San gwagwarmaryar dana Yi Kuwa,to bazan fada ba ki sa kaina gabas ki yanka ni dan ubanki,badai ubana ba,sai dai Nawa? Naki cewar Rabi,Uwa ta fashe da kuka,nace tabara idan ban ruguje Miki Baki ba shegiya nake kaji mata,Abba yaga Nawwar me kudi yayi mukus,Nawwar ne yayi magana yace Kinga dan Allah ki fada mana wannan kiyayayar ta Isa haka,shegu kudi me kudi ya sa baki Uwa tace dan Ina ganin mutuncinka ne Kawai a can kauyen Ungoggo naje na ajiyeta a jikin wani masallaci na dawo gida ta fadi sunan garin su Dagaci.
Na kalleta nace Amma ban taba ganin marar Imani irinki ba Kuma wallahi sai Allah ya saka mana,ko a gidanku ana iya kera ko hanci ne bare mutum sabo da Kawai Allah yayo mu Mata,ke mecece ai sai ki canja kanki ki koma namiji,ki kerawa kanki Antenar maza kawai ki saka ki koma namiji,ke me yasa kika zo a mace? Da nasan haka kuke da wallahi da zuga guda zanzo muku su tara Miki gajiya,Ni dama ban sanku ba ke da Wanda Zan wuce a kwararo duk daya bare na daga Miki kafa,Ina ma na sanku da wuri Kuna yiwa Umma haka sai na kawo wani ya dirka Miki ciki,Uwa ta bude baki tace ku kashe ni ku huta,Nace Inshaallah bakin cikinmu sai ya kashe ki azzaluma,Kai Abba baka Yi dacen uwa ba wallahi bata kaunarka sam tunda bata son jininka,Jahila ce Kawai kaima ka biye mata,mu da Allah ya Mana baiwa masu tausayi da Jin kai,ka raine mu ka bamu tarbiyya karshe mu Zama sanadin shigarka Aljana duk abinda Allah ya lissafa akan niimar mace baka ji Ina almajirantar taka take ko ba karatun kayi bane aikin gadi kayi a gidan Hajiya,dama wasu almajiran kaga sun Dade shekara da shekaru ko izu biyar Basu haddace ba sai yawon bara da iya shege kala kala,ni na taba Jin ma irinku sai kace Wanda aka haifo ku ana dura ashar babu Bismillah,Uwa na nuna da hannu nace duk yanda akayi lokacin da za samu cikinki Oven din da za a shiga shedan ne ya Fara shiga sannan baban Suka dinga gwamutse da Shedan Yana Jin dadi shedan ma na ji ta ta Zaki Yi Imani.
Umma ce ta bige min baki tace Kinga bamu labarin naki bana son fitsara,Zama nayi na dinga Basu labarina kaf komai da komai ban boye musu komai ba,Umma tace wannan barikin da Kika je bakin babanku ne gashi nan bazan ce komai ba wlh shi yace Yan bariki na Haifa a haihuwarki da Cele,ya kalli Cele tana jaririya yace sai tayi cikin Shege a gabana Kuma Allah ya taimakeni yaga zuciyata da zuciyarku Babu Wanda ya lalace Cele tafi kowa taka tsantsan da kame kanta nasan duk inda taje ba abinda zai same ta akwai kamewa.
Uwa da Abba ne Suka tashi suna bata rai suna tsaki Suka fice suna cewa ayi mu gani ko a jikinsu Babu alamun nadama,Kallon Umma nayi da Yan Uwana nace ya Naga bakuyi min kuka bane Kun gama Jin labarina a banza ai ya kamata kuzo ku rungumeni kowa ta fashe da kuka Yan Uwa sun hadu Yar uwarku ta dawo amma kunyi kiyau miyau har Umma ma Ni baza ayi kukan ganina ba,Dariya sukayi Suka ce tab ai mu a jajirce muke ba komai ke bamu kuka ba,Kawai Dan mun ganki sai mu Fara kuka sabo da me,Nawwar ya kalli Auta shi tuwonsa yake ci ma Yana Shan lemo ba abinda ya dame shi,yace Kai sai ci ka iya ana ta labari kana nan,yace to labarin dogo yunwa nake ji,Aunty Bilki tace a'a kyale shi, Auta yace Yaya ka bar Aunty tayi ko kwana biyar ne,Nawwar yace to in tana so ta zauna,nace dama ka gaji dani daga tambaya sai kace to ai shike nan wlh zaka ga tsiya,Auta yayi dariya yace to ke ba a iya miki shike nan ki taho mu tafi tunda bakya son Umman taki, Nawwar yace zamu Zo dasu Mami sai mu koma tare ai,Auta yace Zan zauna Nima,Nawwar yace a Ina zaka kwana to yace a dakin su Omaira su bani gadon su koma kasa su sai su kwanta ni ba ruwana da mace yaro ne ni haka kuka ce,Omaira tace Allah ya kiyaye,Auta yace haba kawata harda ke,tace sai dai a kaika shagon Sagiru gashi nan makwafcinmu,yace ae a kaini Zan zauna akwai toilet hadaddiya bana son kazanta ni a unguwa sabo da toilet ba ko Ina nake kwana ba,Raheemah tace gidan su Sagiru me kyau ne ko Ina tiles dakinsa ma me kyau da toilet dinsa,ai kune kuka ce shago sai kuce dakin Sagiru,Rahma tace kuma Yana da tsafta Kamar mace,Auta yace ku fadawa Sagiru abokinsa ya zo, dariya Suka kwashe da ita,Nawwar yace Wai a Nan zaka kwana karya kake yanda Muka zo Haka zamu koma idan zamu Zo da su Mami ka dawo,Umma tace ka kyale shi Mana tunda Yana so,Nawwar yasan Auta Yan matan da ya gani ne ya makale sai ya zauna shima ba yanda ya iya da shi haka Suka Kira Afif zai maida Nawwar Airport, Nawwar ya bawa Umma dubu dari,dubu dari ya bawa su Bilkisu yace su raba ba yawa kafin nan gaba suna ta godiya,a gabansu na rike Masa hannu Muka fito tsakar gida zai bawa Uwa nace wlh kana bata munyi fada kasan da ya kamata Zan sa ka bata da ita da Abba ko kwabo sai uwata ta jika tukun muje na tura shi ta baya nace muje muje,dariya yayi yace Umma fa tana kallonki zasu ce bamu da kunya,nace muje ni dai,Uwa taga samu taga Rashi a gabanta na Hana a bata ko sisi wani Takaici ya sake kamata,Muka fito yace Abba fa nace Ina bazai ci kudina ba ai cewa Suka Yi basa son Mata,shiga mota please na bude Masa gaban mota ya shiga yace sai munyi waya,nace Bye yace I will miss you,me too My love su Bikisu suna Masa Allah kiyaye Auta yazo yace Yaya banzo da kudi ba ka bani kudi,yace bazan bayar ba,Yaya nifa na gano maka Dangin matarka shine kake min Haka,Zan maka transfer yace ni cash zaka bani, yace Auta baka ji wlh ya zaro kudi ya bashi yace Yaya Dubu ashirin kacal da me zanyi chilling a garin nan Ina fa da abokai,Nawwar yace muje Afif,Suka tafi aka bar Auta a wajen ya Kira Baffa ya tura Masa kudi ta account Kuma ya tura Masa,yasan Mami baza ta bashi ba ma.
Ciki Muka koma da Auta nace Kai da kake da abokai ma Kar dai su dauke Mana Kai,yace ai Ni yanazi nan nazo ba wajensu ba zadai su zo muje yawo ya kalli Raheemah yace kece kadai karama a gidan Nan ba tsayi ba kiba sai kace kece Cele da baki Sha nono na sati biyu bama ga Cele a hoto ma katuwa ita da Bata Sha nono bama ke kin Sha na shekara biyu amma sai kace me cutar yunwa gaskiya kiyi tsayi da Yar kiba haba,Raheema tayi dariya tace Rahma ce ta min kwari ance itace ta kwace girman,yace to ke Rahma ki dawo Mata da nata ku raba biyu,Umma tayi dariya tace Kuma ita aka fara haifa,Na jawo tuwon gaban Auta nace ku bani Mai da yaji,Umma tace ki bari a Miki wani abin mana Raheemah dafa mata wani abin,Nace ayi min danwake,Umma tace to ai Kuwa Babu kayan yi zo ki karbi kudi ki siyo nace a'a akwai kudi na zuge jaka aka bawa Omaira ta taje ta siyo,Muna ta hira Ina Basu labarin kawayena su Star da gidan su Nawwar a hankali Ina ta karasa musu labarina,sai magriba Muka Yi Sallah Auta tuni ya fice yawo da abokai sun dauke shi a mota.
Sai Bayan Sallar Isha masu auren Suka tafi gidajensu sabo da Bilkisu yaranta biyu duka maza,Nazifa mace,Nazira ma namiji,Sai wurin 9pm Muna hira Auta ya shigo yayi sallama nace Auta Dadi aka siyo min naga leda,yace Yaya ne yace fa a siyo Miki kaya baki zo da Kaya ba ya Mika min naga dogayen riguna guda Uku masu kyau nace dama gobe nake cewa Zan siyo ko kala biyu ne kayan Omaira sun min kadan na Umma sun min yawa,dama Zanin Umma na daura da t-shirt,nace shi ya fada ma size din? Yace ae ya Mika min Daya ledar ta take away na kaji da Yogourt da lemo yace na Umma ne na siya mata ba naki bane karki Fara murna,Umma tace an gode dan Albarka,Omaira ce ta raka Auta gidan su Sagiru dama sun gayawa Sagiru,Suna Hanya Auta Yana bayanta Yana Kare Mata kallo.
Cele Fitowa tayi ta a fusace tana hawaye cike da bacin rai ta nuna Maheerah da Yatsa tace Ittaqillah dan kutmar....ta tafi Kamar walkiya Maheerah ta zaci wajenta ta nufo tace bari na Fara cin uban Uwarki me warin tafarnuwwa tukun tayi wani mugun tafiya da Babar Maheera Kamar guguwa ta hada kanta da bango,ji kake kummm ta shaketa ta dinga jijigata ta jefar da ita a kasa,Maheera zata gudu tayi kanta Ahsan ya riko Cele ta juyo ta Kai Masa duka ya saketa ba shiri ta damko Maheerah ta gwarata da bango nan take ta Fadi ta sume sabo da kanta ya bugu Kuma cele bata hakura ba ta haye ruwan cikin ta tana dukanta baban Maheerah yazo zai masge Cele Ahsan ya rike hannunsa da sauri cikin larabci yace karka sake ka taba ta dashen ciki tayi mata ba izininta kuma budurwa ce bata San Namiji ba Kuma kudin Dana bata ko kwandala bata bata ba ai zalunci ne wannan, Baban Maheerah ya fisge hannunsa yace sai me akan anyi Mata dashen ciki wasu ma suke zuwa suna karuwanci su haihu bare dashen ciki,ita wacece bakar fata da ita bayi,Cele tashi tayi daga Kan Maheerah ta shatulo kafafun Baban Maheerah dake banbamin masifa ya Fadi kasa tim yaji targade a kafarsa, Ahsan ne ya rike ta ganin duk ta haukace tana ta kuka tana kwacewa tana fisgewa taga Babar Maheerah ta tashi Zata sake masgeta ya riketa sosai Yana lallashinta ya rungumeta sosai a jikinsa yana lallashinta,Kansa ya Dora a dokin wuyanta yana lallashinta Yana Bata hakuri,Babar Maheerah ruwa ta samo ta kwarawa yarta ta farfado Suka tashi jiki ba kwari da kyar Baban Maheera ya iya tashi Suka mike a gigice Suka bar gidan gaba daya.
Ahsan sai da ya lallashi Cele ta dan daina kukan sannan ya shirya ya rubuta takardar saki ya tafi gidan su Maheerah zai Kai misu,Yana tafiya kuma Cele ta tattara nata ya nata kaf ta Masa rubutu da hausa normal ta ajiye a kujera, ta shiga dakinsa ta Bude inda yake ajiye kudade ta iba zasu Kai dubu dari uku a nan Nigeria tayi tafiyarta ta bar gidan,tana Fitowa Mota ta shiga taxi tace a kaita garin Makkah tasan acan Inshaallah zata hadu da hausawa Kuma Nigeria zata dawo baza ta zauna a Saudiya ba ta Gama Zama a Saudiya har abada, so take tana