Showing 75001 words to 78000 words out of 155384 words

Chapter 26 - YAR AIKIN KARUWAI 2 cmplt By Asma Baffa -www.sufinovels.com-.txt

Advertisement

19 Jun 2024

51415

da shi ya bayyana yana sheki Mami tace Masha Allah Auta ya tabe baki tare da dauke Kai,Ita Kuma Salma dama ta Saba da kuka a gida tunda kullum sai tayi ita da Baso,Basonta ta tuna ta fashe da kuka wai an mata fada sabo da samun waje,Auta a ransa yace dama talaka bai iya samun waje ba,yarinyar da kullum sai an jibgeta na tausaya mata na aureta yau na zama kamar sa'anta ba komai kaima Allah ya Kara maka da Omaira ka aura da duk ba haka ba gadon soyayya tsaki ya ja yace a fili Wanda baiji bari ba ai yaji hoho rubbish ya tashi ya fice.


Nawwar ne ya shigo ni da shi cikina ya tsufa sosai,Mami tace daga Ina haka? Nace asibiti muka je muka biyo,Salma tana ta kuka,Nawwar yace lafiya take kuka? Mami tace gata nan tambayeta ta fada muku da bakinta,Salma tana kuka da shesheka tace sh...sh..shine...Nawwar yace shine wa? Shi....nace waye shi? tana goge hawaye tace Me can wajen, na kwashe da dariya nace Auta? ta daga Kai tace shine yake tsokanata har gori yake min,Mami tayi salati tace Salma kiji tsoron Allah Auta ba abinda ya Miki yana zaune kika ce sai ya matsa Miki ke Zaki zauna kina masa rashin kunya,kiyi ta kukanki tunda ke baza a fada Miki gaskiya ba,Nawwar yace to kiyi shuru za a masa fada kinji,ta goge hawayenta tace to,Mami tace bari na dawo ta nufi kitchen sai ga Auta yayi wanka ya dawo cikin 3qtr da Riga me gajeren hannu, hannunsa daya a aljihunsa daya Kuma wayarsa a rike yana latsata.


Salma tana ganin shine ta mike tsaye taga ya nufi kujera ya zauna komawa tayi wajensa tana kallon kitchen kar Mami ta ganta tace tasar min ni nan wajen nake so a nan zan zauna,Auta iya kulewa ya kule amma ya shareta ya tashi ya koma dayar ya zauna Salma ta zauna tayi irin zaman Auta ta harde kafafu ta fito da vivo dinta tana dannawa itama,yana cin chewgum kawai ita ba chegum a bakinta ta fara tauna itama,ni da Nawwar muka zuba Ido muna kallo kamar Film,dariya kawai suke bamu,Auta yana da abin hannu a tsintsiyar hannunsa na Samari Salma ta gyara nata na mata, juyowa tayi Shima ya juyo suka hada Ido gwalo ta masa,Hannu ya Kai zai dauki Remote ta Riga shi daukewa tana sani ta Kai tashar cartoon,Auta ya zuba tagumi da hannu Daya ya ajiye wayar a gefe ji yake kamar ya lakada mata dukan tsiya.


Nawwar ne ya Kalli Auta suka hada Ido Nawwar yace Matata tafi ta kowa ya rike hannuna,yasan da shi yake sabo da status dinsa ranar da ya shiga dakin Amarya,tashi yayi a fusace ya shiga kitchen yace Mami ki wa Yaya Nawwar magana tun dazu ya zuga matarsa sai Kallona suke suna min dariya,Mami ce ta fito tace waye yake taba min Baby,Nawwar yace ba ruwanmu daga nace Matata tafi ta kowa,Auta yace wlh da ni yake ai na sani, Mami tace ku tashi ku bar mana gida ta Kori su Nawwar.


Mami tana shiga kitchen ya zo ya zubawa Salma rankwashi tare da furta marar tarbiyya yar Namiji,dama tunda Baso ne ya rike ki Ina Zaki hankali,oho maka dai .
Bayan kwanaki kadan Salma ganin Auta yana ta zuwa school sabo da kwaikwayo sai da taje gaida Baffa bayan sun gaisa tace Baffa dama alfarma nake nema,yace Ina jinki,Salma tace tunda na gama secondary Kuma result Dina yayi kyau Dan Allah ko yar college ce ka sani,Baffa murmushi yayi yace ki kawo min takardun naki ta dinga murna,dama ta taho da abinta,Mami ta samu itama ta fada mata,tace kinyi hankali Salma Kuma kin birgeni,taje ta dakko takardunta ta kaiwa Baffa Wanda ya kamata a nema aka Nemo mata aka mata registration a Makarantar da Auta yake zuwa bai ko sani ba sai da zata fara zuwa Baffa ya sanar masa,ransa ya baci akace Kuma tare zasu dinga tafiya su dawo,amma department din Salma daban ita microbiology tace tana so shi Kuma Business time table dinsu kusan lokaci Daya ne,har waya Mami ta siya mata me tsada Samsung.


Yau Monday da wuri ta shirya cikin Arabian gown peach tayi rolling ta sa jaka arsh da takalmi me Dan tufu Arsh, 9am suna da lecture har Auta,ta fito da wuri ta tsaya a jikin motarsa tana waya da Baso yana masifa karki dameni da Kira fa haba jiya kin kirani yau ma haka wanne naci ne wannan ya kashe wayarsa,Nan take idonta ya cika da hawaye sosai ta kasa cire Baso a ranta sabo da Baso take ta yiwa Auta rashin mutunci ko zai gaji ya sake ta ko ya koreta amma yaki,Auta ne ya fito cikin wankansa na farin jean rigarsa silver yayi kyau ya sa glass me kyau a fuskarsa,ganinsa da Glass Salma hankalinta ya tashi da Mami ta bata kudin Makaranta taki karba amma ganin glass din Auta ta koma ciki da gudu,Sai da Mami taji tsoro tana haki tace Mami bani kudin school din na tuna zanga abin ci, Mami murmushi tayi ta bata dubu Daya,ta fito da gudu,Auta har yayiwa motarsa key ta Bude gaban motar ta shiga tana haki, tsaki ya ja yace da kin sani karki fito ki gani Idan zan jiraki,Salma tace ai dai motar ma siya maka aka yi baka da kudin siya,zaka iya siya ne? Ina kaga sana'a baza ka iya ba,Auta yace Mannerless kawai,ya fisgi mota suka tafi,suna zuwa school din taga Yan mata masu aji sai rububin Auta suke,suna cewa Nawaf kanwarka ce? Salma tana fitowa tace matarsa ce,sai lokacin suka tuna Auta fa yayi Aure suka dinga yabawa da kyawunta wasu Kuma suna kishi,Auta yace muje na rakaki bangarenku suka jera suka wuce suna tafiya yace ba tarbiyya kwaila dake sai jaraba duk kin gado jinin Baso mayya ya hankada keyarta ta kusa kifawa,tace kana wani girman Kai da fadi Kai ga me masoya wani Nawa....kasa karasawa tayi sabo da Baso yace sai taci ubanta Idan yaji ta Kira sunan Miji gatsal sai ta fasa cewa Nawaf tace sabo da Kai Kaine,yar kauye kina birni amma kamar a kauye kika girma foolish girl,har aji ya Rakata ya juya ya koma nasu,duk ajin yawanci kusan ba musulmi Allah yasa Makaranta me kyau tayi ta samu foundation me kyau,wasu suna ta Yaba kyanta suna tambaya amma ke Fulani ce? Itama da turanci ta basu amsa tace Kuma tana da aure,suka dinga dariya suna mamaki dama wai sun San Hausawa da auren wuri yar yarinya sai a ganta da Yara su sai sun tsofe a gida yawanci.


Suna gama lectures dinsu na yau ta fito ta sha yawo kafin taga Auta ta hango shi zagaye da mata suna ta duba littafi duk christian ne,Salma ko magana tana zuwa ta kutso ciki ta fisgo Hannun Auta tace tarbiyyar taka kenan harda rike kunnenta kunnenta wato baka jin magana ko muje to,fuska ya bata yace zan karyaki wlh nan ba a gida muke ba ya fisge hannunsa,juyawa tayi ta dinga zaga school tana kallo har ta hango masu Saida glass suna wucewa ta samu Dan fake fake ba me tsada ba Dan dari takwas ta siya ta kafta abinta itama a fuska harda yanga,ta fito waje taga masu siyar da agwalima da kwakwar manja ta siyi kwakwar manja ta wanke da ruwa ta Maida cikin Leda fara,Auta ne ya mata mahaukacin horn da mota ta juyo a fusace taga shine zagawa tayi ta shiga gaba yaja suka tafi tana cin kwakwar manjanta,ta dakko guda biyu ta mikawa Auta ungo ni badan halinka ba,ko kulata baiyi ba haka suka koma gida,ta Riga Auta shiga ciki Mami tace an dawo? tace ae Mami,ke kadai kika dawo? ta girgiza Kai tace a'a da shi muka dawo,Mami sai da tayi dariya again ita baza ta fadi ko Auta ba ma,Auta ne ya shigo ya zauna a gefen Mami Salma ta dawo daya gefen ta zauna suka sa Mami a tsakiya,Auta yana ganin kwaikwayo shi Kam yace wai ke babarki ce? baki ta turo zai kwanta a kafadar Mami Salma ta ture Kansa yace wai mene haka wanne irin iskanci ne wannan ni sa'anki ne wai,Salma tace to da nawa ka girmeni,kwafa ya ja, Mami tace haka kika je Makarantar kuna yi kenan,Salma tace Mami wallahi yayi watsi da tarbiyyarki kullum a cikin Yan mata yake zama bashi da abokai maza sai mata kowacce ta dinga yagula sunansa anyhow kowacce da tazo shi, shi,Mami tace me yasa bakya fadar sunansa ne? Salma tace fada aka min akace ba kyau, Mami tace to ga Auta,ga sunaye nan ki sa masa mana wani a ciki,Salma tace wannan zanwa suna ai sai dai na kirashi da mugun bawa kawai,Auta yace marar tarbiyya,Mami tayi dariya ta mike tace sai kuyi ai kunga tafiyata,Auta ya mike tace Mugun bawa, yace marar tarbiyya.


Cele ce ta duba riyal biyu dinta bata ganta ba Kuma a saman bed dinta ta ajiye fitowa tayi tsakar gida akan riyal biyu kacal tana cewa Allah ya tsiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiinewa Yan gidan nan shegu Yayan madugo,baza Kuga Annabi ba duk wacce tasan ta dauka ta fito da ita wallahi ko ta hadu da fushin Cele yar mutanen Kaduna,wacce tasan ta dauki riyal biyu ta fito da su ko ta hadu da Halin yar mutanen Kaduna,akan haka sai na tafi Ka'abah nayi dawafi,wallahi duk wacce bata fito da ita ba sai naje nayi dawafi cikin mace ya kulle ta mutu duk shegiyar data San ta daukar min riyal biyu ta fito da ita ba mutunci gumina ce ba haramci na aikata ba na samu,banyi madugo an lagudeni na samo ba,banyi kawalci ba,ba wajen boka naje ba sana'a nayi na samu gumina nace,Babu mutunci ba tsohuwa ba yarinya wallahi a fito min da kudi baza ku amfane ni ba, 'ya'yan wata shegiya, 'ya'yan wani Dan banza,wacce ta kawo Cele tana zaune duk suna nan kowa yayi shuru sai wacce ta kawo Cele tace Dan Allah dakko kayanki wallahi ni na yafe Miki kudin haya zan biya Miki zaman da kikayi hada kayanki ki tafi,Cele tana wani jingina da bango tana dagowa tana komawa tana fari da Ido da bala'i tace ba Dan Iskan,Babu yar madugon da ta Isa na bar gidan nan zama daram sai sanda Allah yayi tashina Ina nan,Kuma bance ki biya min kudi ba yawwa ficikarki ta haramci bazan ci ba, Yayan masu baki da kunu ma basu Isa ba,Raliya tace ke wallahi ki kiyaye mu ni tunda naga harkarki ba mutunci ba arziki a cikinta na fita shirginki bana kulaki karki sa Dani wallahi zuriarki kaf har na kabari sai na zage su tas.


Bazawarar dariya Cele tayi tace ai ni bari kiji bana cecekuce budawa nake da mutum in daka mutum in lugude shi, Allah na tuba bare ke da kike kamar karmami duwawu kamar kaskon soya manja,Idan kin Isa mu hadu a filin badar sai muyi yaki a can,sai da su Samira suka yi dariya,Samira tace fadan ma sai anje filin badar? Ai ta tabbatar ni bada wasa na fito ba,ke a yanda na fito nazo takari daidai nake da ko uban waye,ni ba a tabani ba ma ni kadai bala'i nake wa kaina bare an kulani an shiga gonata ,akan Riyal biyu ta billahillazi ji nake kamar zanyi aman wuta gwara ko wace ta kiyayeni,ji nake kamar na zama dragon na muku feshin wuta karku sake kaini bango wallahi yau baza ku runtsa ba tunda baku da mutunci abu ya hade muku biyu ga madugo ga sata wannan wacce masifa ce riyal biyu ta a dauke min a dake ni Kuma ace za a hanani kuka,mace daya ce ta min abinda bana so na kyaleta a garin nan Kuma itama na Riga na Mika karata wajen Allah,Meenal ce ta zaro riyal biyu tace indai akan wannan ne gata ni na baki kyauta,Cele ta tsani Meenal ta karba ta hada kudin da kan Meenal ta maketa sosai tace na tsaneki wallahi mayya bana so ai ni dake ba sauran mutunci mun kulla kenan tunda kika taba min dukiyar maza na wallahi bana sonki,Dattijan sukayi shewa suka ce au nono ne dukiyar maza, wannan jarabar nono sai kace an taba wata tsiya,ana kera shi ne a gidanku?Cele ta tambaya, Suka yi shuru. Cele bala'i take ba ji ba gani sai ga matar da Ahsan ya turo da botikin Awarar ta kwala Sallama


Suka amsa tace wacece Rufaida Cele? Cele ta daga hannu tace I'm ya akayi ko kece kika dauki riyal biyun yanzu ki karbi rabonki? Matar tace a'a ni wani ne ya aiko ni yace a kawo Miki wai naki ya fashe gashi,Cele ta karba sak irin na awararta,tana mamaki tace waye wannan haka ni ba mashinshini ba tunda nazo garin nan banyi masoyi ba sai Yan madugo,Matar ta bude baki tace Subhannallahi Allah ya shirya su ashe ba Neman kudi suka zo ba lalata suka zo yi kusa da dakin Allah wallahi irinsu ke bata wasu gaba daya ake mana kudin goro,duk sun bata gari ana kallon takari marasa daraja,Cele tace ai mutanen banza ne wallahi da dare haka suke lalubeni wata tsinanniya ma ta taba min albarkatun kirjina Ina bacci ai kuwa na tsine mata albarka zata gani Kuma,Matar tace Allah ya shirya wannan ba gidan zama bane in kin samu dama ki tashi,Cele tace so nake dukkansu na koya musu darasi gasu nan har tsofaffin banza.


Matar tace to ni zan tafi,Cele tace wai bakar fatar ne ya baki? tace ae baki ne yace a kawo Miki zaizo yace,Cele tace to maybe a masu siyen Awara ne na gode tsaya na baki tukwici mana ta zaro riyal biyar tace ungo tukwici,haba sai kace yarinya tace Kya ci ko Altuffa,ko Laban wa buskota wai biscuits,matar ta karba tana dariya da godiya ta tafi.


Washe gari Ahsan wanka ya sha cikin kana nan kaya yasa Driver ya kaishi inda Cele ke zama tana siyar da Awara,yayi parking yana mota yana kallon Cele tana zuba ciniki,kudi ya bawa driver yace yaje ya siye awarar duka ya rabawa masu siya kyauta,Driver ya fita yaje ya samu Cele da Hausa yace Hajiya nawa ne dukanta? Cele tace duka Kuma botiki biyu fa,yace ae sadaka zanyi naga ana siya zan rabawa alumma Cele ta fada masa ya bata kudin gaba daya ta tashi tana gyara mayafinta bata San da mutun a motar ba taje jikin mudubin motar da Ahsan ke ciki a zaune tana gyara mayafinta ta zaro lipgloss a jaka ta shafa ta gyara mayafinta da tayi rolling ta jingina da jikin motar tare da harde hannayen ta a kirjinta,Ahsan yana kallonta shi fes ta ciki bakinsa ya dora a jikin glass ta saitin bayan Cele yana ta zuba kiss bata sani ba ji yake kamar ita yake wa kiss din,sai kissing din glass yake.






Ayi hakuri chaji ne ya kare




A dinga sharhi yafi Godiyar nan










AsmaBaffa


'YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼
MATAFIYA




BOOK 2




56-57




Official


By
AsmaBaffa




SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN




*MISKI 3in1 Alfirdaus*🌹 Albishirinku💃 original miski daga *Egypt* miskin da koda yaushe Kuna yabawa dashi yana dauke 1.*Musk oil* ana shafawa agaba bayan gama al'ada inda hali za'a iya ringa sawa Koda yaushe yana maganin infection yana gyara gaban mace sosai 🙈ko yaushe gurin yakasance cikin kamshi 😇bayaga haka sunnah ne amfani da miski
2.*Musk cream* Ana shafawa ajiki gaba daya musamman wajan cinyoyi yana sa jikin mace koyaushe yakasance cikin kamshi kuma yana gyara fata, yasa tayi laushi
3.*Turaren tsarki* wannan turaren karshe ne 🔥 🔥 ba lallai se bayan gama period ba koda yaushe zaki iya rinka tsarki dashi yana gyara gurinnan🙈 sosai, kuma ana shafawa a hammata yana kawar da da wari karku bari abaku labari 🙍‍♀️👱‍♀️


Masu bukata ku ne wannan number
09065959708




Page naku ne


Jannat collection
Mhiz Auwal
Faeezah
Jalloty
Zuwairayahaya8
Ameesha couture






Bazawarar dariya Cele tayi tace ai ni bari kiji bana cecekuce budawa nake da mutum in daka mutum in lugude shi, Allah na tuba bare ke da kike kamar karmami duwawu kamar kaskon soya manja,Idan kin Isa mu hadu a filin badar sai muyi yaki a can,sai da su Samira suka yi dariya,Samira tace fadan ma sai anje filin badar? Ai ta tabbatar ni bada wasa na fito ba,ke a yanda na fito nazo takari daidai nake da ko uban waye,ni ba a tabani ba ma ni kadai bala'i nake wa kaina bare an kulani an shiga gonata ,akan Riyal biyu ta billahillazi ji nake kamar zanyi aman wuta gwara ko wace ta kiyayeni,ji nake kamar na zama dragon na muku feshin wuta karku sake kaini bango wallahi yau baza ku runtsa ba tunda baku da mutunci abu ya hade muku biyu ga madugo ga sata wannan wacce masifa ce riyal biyu ta a dauke min a dake ni Kuma ace za a hanani kuka,mace daya ce ta min abinda bana so na kyaleta a garin nan Kuma itama na Riga na Mika karata wajen Allah,Meenal ce ta zaro riyal biyu tace indai akan wannan ne gata ni na baki kyauta,Cele ta tsani Meenal ta karba ta hada kudin da kan Meenal ta maketa sosai tace na tsaneki wallahi mayya bana so ai ni dake ba sauran mutunci mun kulla kenan tunda kika taba min dukiyar maza na wallahi bana sonki,Dattijan sukayi shewa suka ce au nono ne dukiyar maza, wannan jarabar nono sai kace an taba wata tsiya,ana kera shi ne a gidanku?Cele ta tambaya, Suka yi shuru. Cele bala'i take ba ji ba gani sai ga matar da Ahsan ya turo da botikin Awarar ta kwala Sallama


Suka amsa tace wacece Rufaida Cele? Cele ta daga hannu tace I'm ya akayi ko kece kika dauki riyal biyun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login