Showing 84001 words to 87000 words out of 155384 words
Chapter 29 - YAR AIKIN KARUWAI 2 cmplt By Asma Baffa -www.sufinovels.com-.txt
ya juyata yanda baza ta Kalli gaban glass ba,Ahsan yana ciki yana kallonta,suka gaisa tace Kaine ka siyo min botikin Awara? Sannan kana ta min Aiken kudi? Hammad yayi murmushi yace ae nine,a gaskiya na ganki Ina sonki,Cele ta kalle shi tsaf tace kayi hakuri ni zuciyata ta Saba da ganin me haske balarabe nake so ga Wanda yake jajir kullum idona Idan Ina kallonsa zasu Kara haske,Hammad yayi murmushi yace kiyi hakuri ki bani dama,Cele tace bafa zan soka ba ni Karka takura min wani nake so ni,Hammad yace larabawan nan basu da kirki,Cele tace Allah ya kona me karya Karka harzuka ni,ko Ina akwai na gari akwai na banza,Wanda nake so na gari ne,Hammad yace kiyi hakuri naga har kin harzuka,please Idan ba damuwa zan canja miki gidan zama,Cele ta kalle shi tace bada ni ba ka hada Kai da wasu larabawan a siyar dani yanda suka yiwa kaka,Yace haba dai Ina muamula da larabawa amma na kirki tace Kai ka kiyayeni munga Abila habee ma karewar tuggu,mu fa a tafin hannu mu kuke muna da tarihin garin nan abinda suka aikatawa masu Imani nasan akwai burbushin su Abu jahal har yanzu ba ruwana a Africa ma akwai nasu,ka kyaleni na bar garin nan lafiya ana aikin hajji zan tafi Idan na sauke farali,driver Hammad yace ni dai Ina rokonki Idan kina so ma zan hadaki da Yan sanda su ai baza su cuceki ba,Cele tace amma ba mutun daya ba a taho da bataliya guda ayi min kwambo da su sannan na je,yace to na gode ya juya ya mata Sallama,Cele tace jibe shi wani guntu da shi Dan banza suffa kamar gajeren wandon Kaka ta juya ciki,yana komawa mota ya fadawa Ahsan yanda sukayi yayi dariya yace ai Yan Makkah suna Shan gori a wajen baki sabo da Annabin Rahma yayi Hijira sun Kori Dan uwansu.
Washe gari motocin Yan Sanda sun Kai hudu ga mota Ahsan ya bada suka zo kofar gidan su Cele ba Ahsan a wannan karon,Yan gidan suna ta murna anzo kama Cele wai ta tsokani wani balaraben za ayi maganinta,sai suka ga ta hado kayanta ta fito tsakar gida tace na gaji da kwasar zunubi kullum Ina gidan fasikai,Boobs dinta tallafe tace abuna ya huta da kawo hari yanzu zai Kara bulbul,shegu inshallah sai an kamaku Daya bayan daya sai kunyi bursuna a kasar nan,suna jinta tana masifa tace Allah yasa na hadu da wata a hanya ta min magana ko ta nuna ta sannu wallahi sai na mata daga daga,in ance a fita filin badar Kun kasa sai madugo matsiyatan banza baza Kuga Annabi ba ta fice ta barsu,tana fita suka ce Alhmdllh haba jaraba ta tafi yau zamu huta.
Kaka aka biya ya fito da kayansa Shima zai shiga gefen Cele yayi Bismillah yace Ubangiji ka rabu da sharrin Yan uwan kafiran zamanin baya ya shiga mota suka tafi,Cele tace kaka muyi alkunutu tun a mota suka fara karanta alkunut ita da kaka har aka kaisu dai wani gida a unguwar takari ne amma gidane dogo a hawa na biyu Cele take ita da Kaka,gidane hadadde na glass da Glass gidan glass takari suke Kiran gidan,2bedroom and Palo sai kitchen kowanne daki da toilet komai sabo ne a ciki me kyau Palo yasha kujeru da center carpet,Hammad yace Alhmdllh kuyi zamanku a nan Kuma ku daina wata sana'a zan dauki nauyinku,Cele tace Masha Allah,Allah yasa na soka a haka,nidai ba ruwana Idan ban so ka ba Karka kace na yaudareka ko na cuceka naci kudinka,bani na Saka ba ato,Kaka yace kwarai kuwa,Hammad yace sabo da Allah nayi suka masa godiya.
Washe Gari Ahsan shopping yayi na suturu masu tsada da kyau harda agogo Rolex ya bawa Hammad yace gashi ka kaiwa Cele a matsayin Kaine,Hammad ya tafi gidan su Cele suna ta kallonn film da Kaka,Kaka ga lemo a gabansa yana korawa yace Ina goge duniya Alqur'an bana son barin garin nan,kinji Ko ciwon Kai banyi ba har yanzu,Cele tace to komai me kyau ake ci ba cuta,Kaka yace da a Nigeria ne da yanzu na shanye paracetamol yafi carton guda,maganin ma baya aiki duk kamfanunuwan mu sun gurbata maganin basa aiki Idan cuta ta kamaka ayi ta gabza maka kwaya da Allurai basa aiki,komai namu Babu me kyau,asibiti ma abinda aka ga dama akeyi,sai ayi ta shirme ga inda ya dace a gyara baza ayi ba Kai muna Shan wahala a Nigeria kawai rayuwa muke,muma da halinmu muyi ta sabon Allah ana jika kasa da jinin bayin Allah Wanda jinin mutum Daya mumuni ya Isa ya haifar da masifa a kasa yau mutane million nawa aka kashe,a kama wasu a gana musu azaba,a kama wasu masu aure mata a auri matan wasu aure kan aure su haihu da wasu,cin Amana,yaron me gida ya kashe me gidansa,a danne hakkin marayu,zinace zinace,luwadi ga lasbiyalizim wai yan Lesbian inji Kaka alkalai zalunci kowa zalunci,masu siyar da kayan masarufi zalunci awo ma baza a baka dai dai ba,Yan kasuwa su boye kaya su tashi abinsu kullum sai an Kara kudin kaya,daga an fitar da doka kafin ta fara aiki mutanen kasar sun karawa kayan Abinci tsada, awannan zunubin da zalunci Ina zamu kaishi,Cele tace kyale su Kaka Allah zaiyi hukunci ga shugabanni sabo da suna da ikon su sa baki a gyara baza su ce komai ba su suna da kudinsu ba abinda ya dame su komai tsadar Abu zasu iya siya ba ruwansu,mutane Yan kadan sun jefa milliyoyin mutane a mafisa.
Hammad ne ya shigo yayi knocking Cele ta Bude masa ta gaida shi ya amsa yace gashi ya Mika mata,tace Kuma ma dai? gaskiya kana kashe mana kudi mun gode fatan dai nan gaba Idan banji sonka ba baza aji haushina ba? yace ba damuwa tace to na gode Allah ya Kara maka so na ya links shi sai dari indai hakane ni kuwa na sha kyauta,dariya Hammad yayi yace kefa baza kice Allah ya sa Miki so na ba,tace wayyo bana mararin samunka yayi dariya ya juya yace na tafi tunda babu Kara abin,tace yo ai gaskiya na fada.
Salma tana ta aikinta kullum bata hutawa,Mami ce ta shigo kitchen ta iske ta tana girki tace sannu Mami,Mami tace yawwa kawai ta shareta,kamar tayi kuka tunda Auta ya fara ciwo basa zuwa school dukkansu,jinyar Auta take fama.
Washe gari da sassafe ta tashi ta tafi barruwan flowers tana sanye da Doguwar Riga yar fitted me siririn hannu dark blue me layin layin fari tana aikinta Auta yana zaune a garden din yana latsa waya yana kallonta tana rike tiyo tana fesawa flowers ruwa tana bi layi layi ta bata rai kamar zata yi kuka,ta Kalli Auta ya dago ya kalleta ta dauke kanta yaci gaba da kallonta ta sake kallonsa ta gasa masa harara,tana gamawa ta wuce gate ta budewa Baffa zai fita ta yafa Dan karamin mayafinta,tana rufewa na shugo da motata ta Bude min gate ta kalleni na kalleta nace Masha Allah gaskiya Allah yayi halitta itama,Ina fitowa ta karaso da gudu tace Aunty Ina kwana,nace lafiya Alhmdllh nayi wucewata,Salma ta tsaya tace kowa ya tsaneni ta fashe da kuka ta koma kujerar me gadi ta zauna,dakin Auta ta shiga yace ki kaini Palo,ta rikeshi tana dafa bayansa yana dogarawa da sandunansa suka fito Palo,ta karbi sandunan ta jingine gefe,Mami tana kallo tace Auta bai karya ba,Salma ta fada kitchen da gudu ta fara girki,tana jin Karar mota ta fito da gudu ta fice ta bude gate aka fita ta rufe ta dawo kitchen da gudu ta iske Auta yana kwance a cinyar Mami sai shagwaba yake,Ina wajen Wise sai daga baya na shigo bangaren Mami na samu Salma ta fito daga kitchen da tire ta jerawa Auta komai a dining tazo tace ka taso,Mami tace jeka ka karya, tace ke a baki Zaki bashi sometimes baya ci da Kansa,Salma kamar ta fashe tace to ta koma dining tayi serving nasa ta hada masa tea tace Bude bakin ko Shima sai an bude maka? yace ae,Hannu tasa a kumatun Auta ta matse masa baki ya saki Kara tace to ka bude ance,ya Bude kadan tana bashi a baki,yana ci yace nifa Idan Ina cin abinci ana shafa min gashi fa inji Auta,Salma tace nidai mutuwa zanyi kowa ya huta kawai ta saci kallon Mami taga tana kallonsa hannunta ta sa a cikin gashinsa tace ko kunyar Iyaye Babu a gabansu za ayi wannan aikin ni wlh Ina da kunya ba a nan na taso ba, Auta yace ko a Kira Baso ne? tayi shuru taci gaba da bashi a baki tana shafa masa gashi,Mami ce tace dani Rabi Idan cikin ya cika watan haihuwa ki dawo nan sabo da gudun matsala,nace ae haka yace me gidan can Shima nan zamu dawo,Mami tayi murmushi tace so kike ta rainaki ko kina tsokanarta kema.
Auta yana koshi yace na koshi a goge min bakina,Salma tasa tissue ta goge masa,yace zan kwanta a kaini kan gadona,harara ta watsa masa tace tashi ta rike shi har da yin tangal tangal zai fadi, tayi sauri ta ruko kafadunsa tare da Mika masa sandunansa suka tafi.
Masu Audio kar a juya littafi Babu izinina na siyar da shi,
Domin Karanta cigaban wannan labari ku danna bulun dake kasa ko kuma Hoton 👇👇👇
https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/yar-aikin-karuwai-book-2-page-106-110-by-asma-baffa
Masu sharhi Ina godiya aci gaba Dan Allah
AsmaBaffa
08061929616🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2🌼
MATAFIYA
BOOK 2
61-62
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN
*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
Page naki ne
MOM KHALISAT
Auta bai dade ba ya warke ras da shi ya fara zuwa makarantarsa shi kadai,Mami ce ta bugawa Baso waya tace naga kamar Salma tayi laushi haka duk tsiyar nan ta daina,Baso yace Ina ai bata daina ba ni nasan halin kayata,Mami tace to a canja mata gate gaskiya da wahala,Baso yace bafa ta jin magana yarinyar nan amma shike nan ku Maida ta sharar tsakar gida duk uban girmansa ta share sannan taci gaba da girkinta komai tayiwa Auta karku daga mata kafa,Mami ce ta Kira Salma daga bakin gate ta taho da sauri ta bata waya,tasan Baso ne yace kina ji na? tace ae yace an canja miki aiki kin koma share compound ko Ina da Ina na gidan nan,Sannan an canja miki yiwa Auta wanki ki masa girki sannan ki gyara masa daki duk abinda yace kiyi Idan ba haka ba nazo garin nan na lahira sai ya fiki jin Dadi,sannan Zaki koma Makaranta,ita dai Salma hawaye take,suna gama waya Mami tace kuka kike Salma? Kai ta girgiza da sauri,tace gidan nan na hango girmansa gari guda Mami Dan Allah ni marainiya ce ku tausaya min,Mami tace ai baki duba maraiciinki ba Salma,zanyi duk ko mene wlh bazan sake masa rashin kunya ba ni ba ruwana ma da shi inshallah bazan sake masa magana ba,Mami tace to ashe Zaki ci gaba da shara kuwa,tace dauki tsintsiya kawai,Mami taji tausayinta sosai bata son wahalar nan amma Salma bata jin magana ana barinta Idan ta mike kafa sai tsiya wasu gata da jin dadi hauka yake sasu.
Washe gari Salma da sassafe ta fito yin shararta tana yi tana hutawa har tazo garden bayanta ya kage,Auta yana ta Exercise yana motsa jiki yana kallonta tsugunawa tayi a wajen ta fashe da kuka, dariya ta kama Auta ya danne,tausayi ta bashi ya tako har inda take da kayan gym dinsa bakake,tsintsiyar ya karba a hannunta ta dago a hankali ta kalle shi,sharar ya duka ya fara mata ya karasa mata yana tattarewa tazo tace bani kar azo a ganni na Saka Dan Gold aiki ka jawo min a Kira Baso,fuska ya daure tace na gode to,Auta ne ya shiga Palon Mami ya sameta yace Mami tace Ina jinka,yace please ku kyaleta haka duk sai ta lalace tayi duhu,Mami tace oh ashe? yace ae Baso fa Dan kwaya ne ba dai dai yake da mutane ba,Mami tace ji nake nan kace ka tsaneta,to Dan na tsaneta shike nan sai a wahalar da ita,Mami tace shike nan Auta Kai da Salma ba ruwanmu.
Salma ciki ta shugo ta hada zufa ta sha shara ta shiga dakin Auta hannu ta Kai saman bed din zata gyara taji an rike mata hannu tasan Auta ne,yace jeki, ta furta nifa bance maka komai ba ka kyaleni nayi aikina,yace daga yau kin daina to shike nan? Kai ta girgiza tace kawai gwara nayi,Salma taci gaba da aikinta ba ji ba gani,ta fito ta dora girki tayi me Dadi kuwa tunda ta iya tazo ta shirya a dining.
Wanka taje tayi ta fito ko abincin bata ci ba ta tattaro kayanta Dana Auta Dana Mami ta fito taje part din Wise tace a bani kayan wanki,Wise bata San dalili ba ta kwaso nata ta bata ta zaci ita kadai zata yiwa,ta fito ta fada bangaren Iyamami tace kawo kayan wankinki zan Miki,Iyamami ta washe baki tace Allah ke,irinku ake so ba irin surukaina ba gasu nan basu da mutunci,ai ni dama nafi son wankin hannu yafi kyau,Iyamami ta kwaso kaya ta bawa Salma tace Sabreen kawo wankinki muna ganin yarinya kamar marar kunya ashe itace ta kirki,Sabreen ta tattaro ta Miko itama,Salma ta karba ta taho tana cewa Allah yasa wahala ta kashe ni kowa ya huta ,tayi zuciya yanzu a zuciye ta fita can fanfom garden ta zauna da uban wanki ta wani tare shi na kowa daban daban kamar me kashin dankali.
Dana Auta ta fara,Auta ne ya fito yana waya ya ganta da tarin wanki, na mutane daban daban,baki ya bude yana kallon ikon Allah,ga hadari ya hado sosai amma Salma ko a jikinta wankinta take yi,Auta ne yayi magana yace wai meke damunki ne,aiki fa ake so nayi wahala ake so na sha ba shikenan ba,kin ma yi breakfast? tace a'a, sanye take cikin Riga me siririn hannu da skert,tana wanki gaba daya wuyan rigar ya zazzago dukiyar fulanin ta rabi a waje,Auta ya kalleta ya dauke Kai yayi tafiyarsa ya kyaleta.
Sai da ta gama wankin tas Allah yasa ruwan Bai sakko ba,jikinta har rawa yake sabo da yunwa ta shiga kitchen ta hado tea me kauri ta shanye da bread.
Baso ne ya kirata a waya ta daga,yace ga matata ku gaisa
Auta yana Palo yana kallon Salma a dining,Salma taji muryar mace kuwa tana cewa Kanwata kina nan lafiya? Salma hawaye ya zubo mata ta daure tace lafiya Alhmdllh,Baso ya zaci ya kashe wayar bayan sun gaisa da Salma taji yana bawa macen labari yanda ya siyar da ita,yace Million Daya aka siyi Salma ai tayi tsada ban zaci zata Kai haka ba,yaron nan Auta Dan mutunci wlh ya aureta yanzu ji Alkhairi da yayi min ta tsaya tana shashanci a kaina,Salma tashi tayi ta shige bedroom dinta ta dinga kuka,a fili tace na tsaneka Baso ba ni ba kai yanzu da wani mugun ya bawa ni fa,ranar Salma Sam bata samu sukuni ba,washe gari ma sukuku ta fito zasu tafi school tana tsaye Auta ya gama karyawa ya mike yace muje ta Yaya Baso yana Shan ruwa,harara ta watsa masa ka daina hadani da wannan marar mutuncin ni ba Yayana bane,Auta ya zaro idanuwa yace Bason? tace ae shi din tana kumbura baki,suka fito tace da Auta ka Bude min mota,ya zaga ya Bude mata ta shiga ya rufe yace shike nan? tace ae,ya shiga yayi driving suka tafi, mota a hanya ta shiga security ta kulle kanta da kyar Auta ya gangare kasa yayi parking yace ta mutu fa,Salma tace Kai dai baka iya mota ba kawai,murmushi yayi kawai ya fita tare da Bude gaban motar ya tattaba ya dawo ya mata key taki tashi ya fita ya rufe yace bari na Kira me gyara ya duba ta,waya ya Kira me gyara yace gashi nan su inda yake an fara ruwan sama sai ya tsagaita,ruwa ne ya sakko me karfin gaske kafin Auta ya shigo mota har ya jika shi Salma tace baza ka shugo