Showing 36001 words to 39000 words out of 69765 words
tsaka Allah yabani kuma in'kasa farin ciki? wallahi zan iya zaman Shekara ɗaya ina jiranta,Tinda dai an riga an ɗaura.
Gabaki daya suka jinjinamai da irin son da yakema Husnah,Tare da yabama ƙoƙarin shi dan ba kowa zai iya jurewaba,Amma shi da ya saɓama Allah kwara ya mutu bai furta ba.
Waya Sheikh ya dingama mutanen daya aani yana sanar dasu daurin auranshi 4:30, Gabaki ɗaya sunyi mamaki amma sukamai alƙawarin halatta.
Karfe 3:30 suka gama shirin su.
Mai karatu zanso ka hararo kyan da Ɗan Balaraben Husnah zayyi acikin manyan kaya farare.
Gabaki daya rudewa sukai sadda ya buga shadda nan ya dasa hula,sumar nan tashi tayi dass cikin hula,sajen shi kau sai sheki yake gashi ya zagaye kyakyawar fuskarshi yayi wani fresh daka gani dai kason an'gone.
Turaruka suka ɗauka suka dingamai ɓarin shi kana suka fesa suma suka fito komi nasu iri daya gwanin tsari.
Ahmed ya kalli yanda mutane ke kallon su yace" shaggu gabaki ɗaya batamu sukeba tadan Balarabe suke yasin.
Dariya sosai Sheikh yasanya wacce rabon da yayi irinta harya manta ,Cak suka tsaya da tafiyar suka dasamai ido ganin kwarjini da zatin da Allah yamasa, Fararen jerarrun hakoran sa kar masu kyau da tsari tamkar masara.
Cak ya tsaya yana zubamasu harara.
Ahmed yace masha Allah tabarakallah,hakika dole Husnah ta kasa musawa da samun irinka, wallahii banyi tinanin amincewar Taba,kaima ka burgeni da kaki kula wannan Ausharin daya dinga zaginka.
Murmushi shekh yayi yace muje *TAMMAL WAƘAT*.
suna bisa hanya Abbah yakira Ahmed yace suyi sauri suma sun shigo kwanar ga mutane sun taru.
Ganin 4 tayi suka tsaya wani masallaci sukayi Sallah kana suka wuce.
Suna shiga kwanar gaban Shekh yayi wata fitinanniyar faduwa, lokaci ɗaya ya dafe zuciyar sa yace.
*Allahumma Ajirni fi masibati ,Wa akhlifni khairan minha,Rabbi inni lima an'zalta ilayya min khairin fikir*.
Sunyi mamakin ganin yanda mutane suka halacci ɗaurin auran da aka shirya yinsa cikin awanni huɗu, Amma dubban jama'a kai kace shekara akai ana sanarwa.
Koda suka isa sukaji ta cikin speaker ana faɗin." An ɗaura auran Habibillahi da Amaryar sa Husnahhh, akan sadaki mafi kankanta da Albarka Naira 500k Lakadan ba ajalan ba.
Ido Shekh ya lumshe Tare da furta Alhamdulillahi lathi bi'ni'imatihi Tattimussalihat.
Halawa da dabino aka fara rabawa Yayin da mutane sukaita tururuwa zuwa yimasa Allah yasa Alkhairi ,su Ahmed sai amsawa suke shikau murmushi kawia yake yana hada hannayensa yana masu godiya da amsawa a zuci.
Abbah ne ya yafito Ahmed da hannu akan yaje.
Bayan yaje yace kirawoman Habib.
Zuwa yayi ya sanar masa kana suka doshi wurin zuciyar Sheikh nata tsinkewa.
Zama sukai cikin masallacin Abbah ya dafa gwiwar Sheikh,yace Alhamdulillah Habib Husnah tazama taka,Ngode dakaman wannan taimakon,banda matsala dakai saboda nason kana da iliminka da sanin hakkin aure, Allah yamaka albarka.
Alhaji Bilal ga Sirikin naka Abbah yace yana zubama abokin shi dake amsa waya ido.
Kashewa yayi ya juyo yana mayar da wayar aljihu tare da fadin Masha Allah..
Azabure suka mike shida Yah Sheikh lokacin da suka haɗa ido.
Wani irin rawa jikin yah Sheikh ya fara cikin tashin Hankali yake murza idonshi yana fadin Dadd..Da.
UMSAD MAKENTOSH
*Makentosh*
*Makentosh*
*Makentosh*
Ina macen da ta isa takejin takai Hajiyar gayu.
*HMMM DA SAURANKI HAJIYATA INDAI BAKYA AMFANI DA MAKENTOSH*
Matso kiji hajiyata
Kamar yanda kuka sani UMSAD INCENSE ta sake zomuki da wani sabo sahihi mai suna MAKENTOSH
MAKENTOSH wani sirrine nasu na mutan Maiduguri,yana da masifar kyau yana hade mace gam koda haihuwa goma tayi,ina uwargida ina amarya ina budurwa ina zawara duka dai gudun'muwace daga mai kishinku har kullum UMSAD INCENSE.
Ina baku shawara da ku nemeta dan magance matsalolin da suke faruwa damu tsakaninmu da mazajenmu dan gyara shinfiɗarmu kai tsaye.
Ni Ummy Aysha shiyasa na kasance shalele awajen mai gidana saboda gabaki ɗaya sirrin gyaran jikina yana Tattare da gudun muwar UMSAD INCENSE shiyasa koda yaushe muke cikin walwala da farin ciki da mai gidana🥰.
Dan neman farin ciki akoda yaushe tsakanin ki da mijinki ki tuntuɓeta a wannan layin
Sayen nagari maida kudi
UMSAD INCENSE 080 288 27241
3️⃣1️⃣&3️⃣2️⃣
Domin mallaka naki kai Tsaye turo kuɗin ki ta wannan account ɗin 300 kacal.
ƊAHIRU AMINA, Zenith Acc. is 2860983400.Domin neman karin bayani Tuntuɓarni a wannan Number 07038423451
"Daddy!.
"HABIBIEEE" Alh Bilal yace da ƙarfi ,lokaci ɗaya suka rungume juna a tare suka saki kuka,Abbah mah dasu Umar da Ahmed hawaye suka share, dan ko baafadamaba kai kason cewa jini ɗaya ke yawo a jikinsu, duba da tsananin kamar su dan dai Abbah yawan shekaru kawai yafi Sheikh.
Abba ne ya tashi yana kama hannun Abokin nashi ya zaunar dashi tare da fadin zauna" Ɗan uwa.
Zama sukai shikau Sheikh har lokacin hawaye ke sakkomai,yama rasa mizaice, duk sadda ya kasance da Husnah sai wani Alkhairi ya ɓulloma sa,Mahaifin sa daya fidda rai da gani yau gashi gabanshi,idonshi ya sake murzawa da ƙarfi yana sake waresu fess akan Daddy dake mikomai hannu akan ya zauna.
Cikin rawar murya Daddy yace" ka..kka.zauna HABIBIEEE dan Allah karka barni , Ina mahaifiyata ?
Zama yayi su Ahmed ma suka zauna kai kawai ya jinjina alamar tana nan dan inya bude baki zayyi kuka mai sauti.
Liman ne ya tashi ya kalli mutanan dake matsallacin dake tsaitsaye suna kallon au yace" kumuje inaga akwai wani abu na sirri da zasu Tattauna daya shafesu.
Abbah ne ya kalle shi yace" hakane amma suma akwai bukatar su son wani abu tinda yawanci akwai abokan karatun shi shekh ɗin, Da kuma mutan unguwa Abokan arziki, Tinda babu wanda yason wani abu akansu andaigan su suna rayuwa.
Daddy dake ruke da hannu Sheikh ya mike suka fito waje inda sukaga Cincirindon mutane magulmata ana fadin ga mahaifin Sheikh, Yau an'gano yan uwan Sheikh ashe yana da dangi.
Abbah ya kalli Daddy da duk baya cikin natsuwarsa Inna kawai yakeso yagani.
Mutane suka fara tururuwa sunayowa wajen su, suna masu Allah yasa Alkhairi, Gabaki ɗaya kasa magana sukai sai Abbah dasu Ahmed ke am'sawa..
Daddy ya matsa hannu Shekh ya kalleshi tare da goge idonshi yace" ina Inna?.
Da hannu ya gwadai gidan nasu .
Cikin mamaki Daddy yabi ɗan Kurkukun gidan da Mahaifiyarshi , Da Yaranshi mafi soyuwa azuciyar sa da kallo.
Abbah yace da mutane suyi hakuri suna zuwa,dyakyal suke kutsa mutane suka samu suka doshi gidan Inna , Anan sukaga su A'isha sun zage sunata girki da manyan tukane kai kace an shekara da sanya bikin wanda duk Wani hidima cefane Abba ne ya kawo dan ayi abama makwafta da Al'majirai Sadaka.
Da sallama suka shiga su duka, dai-dai sadda Inna ta fito ɗaki jikinta duk A sanyaye ,Tin bayan dawowarta gidan Sadam takejin bugun zuciya..
"Sannun k...
Kasa ƙarasawa tayi jikinta ya ɗauki rawa lokaci daya tai baya zata fadi Husnah dake tsaye ta window tafito ta tarota ta fada jikin ta amma ta suma.
Daddy kau da Shekh Aguje sukai kanta Daddy na gilgizata yana fashewa da kuka yace "ki gafarceni mahaifiyata ki yafeni,Banbar ki anan ba dan bana nemanki,
Ko ƙasƙanciba,Aa ikon Allah ne kawai bai hadamuba muna gari ɗaya sai yanzu, Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un dan Allah kitashi Inna, yanzu nike da buƙatar jin dumin jikinki mahaifiyata kitashi karki barni , Bayan tsawon shekarun da kika kwashe muna kewar juna dan Allah .
Husnah kau kuka take sosai tana jijjiga Inna.
Shekh kau zamewa yayi gefe yana dafe kanshi dake barazana fashewa,shin kuka zayyi ko dariya,farin ciki biyu arana ɗaya Yah Allah.
Aysha ce ta fiddo ruwa cikin madaidaicin fridge din Inna, Tare da jika karamin Rawanin Shekh ta ba Husnah ta shafamata ga fuska da jiki saiga Inna ta kawo ajiyar zuciya, A'hankali take bude ido,cikin low Voice tace" Ma'u mafalki nike ko,Mafalki nike da ɗana ko kamar yanda na saba, Dan Allah karki tasheni tace tana sake matse ido.
Inna ba mafalki kikeba nine dai azahiri gani gabanki da jikan ki HABIBIEEE mu,ki buɗe idonki mahaifiyata, ki kalleni,kimin kallo irin naso da kauna da kika sabaman matsayinki na uwa, Inna i miss You so much wallahi ,i miss you sosai Yaƙarasa yana share hawaye.
Abbah ma juyawa yayi yana share hawaye,harga Allah tinda yaga Shekh yakasa natsuwa da kin yarda da babu wata alaƙa tsakaninshi da Abokin sa, Yana bala'in kama da Abokin nashi sosai,, Duk da baitaɓa bashi labarin rayuwar shiba amma kamar tayi yawan da har ta ɓaci, ashe kau AURAN Husnah Alkhairi zai haɗa tinda har ya haɗa zukatan da suka fitar da ran sake ganin junan su..
Ido Inna ta buɗe tarr tare da zubama Daddy su bata ko kyaftawa..
Lokaci ɗaya kuma ta buɗe hannu ta Alamar yazo gareta.
A'hankali yaja gwiwar sa har inda take kana ya ɗora kanshi akan Gwiyagunsa cikin mugun kewa .
Inna kau bata tsaya komi ba ta rungume abinta tana sunbatar goshinsa da Samasa Albarka.
Cikin farin ciki tana share hawaye tace " Nasha fada inaji ajikina yarona na nan,inaji ajikina baka mutu ba,inaji ajikina kana kusa dani lokacine kawai bai hadamuba,ko yanzu Allah ya dauki raina naji dadi naga Ɗana , Ga HABIBIEEE nah ya angwan ce, Ya samu irin matar da yake so Alhamdulillah.
Daddy yace'' Insha Allah yanzu zaki fara sabuwar Rayuwa cikin Family naki, Inna ya bayan saduwa? Taya akai kuka dawo KATSINA,Taya akai kuka Fito daga hannun Azzaluman nan Ya karasa hawaye na zubomai.
Murmushi tayi tace" Sai Alkhairi,Ina Kulu ? Ina Sameer,Ina Imran? Da Takwara Maryama?
Daddy Yace Suna lfiya yafaɗa yana zaro waya Ya kanga akunne.
Bayan an ɗauka yace.
" Sweetheart kisa Imran ko Sameer ya kawoku nan gidan Bikin nan Da nike fadamaku,Anan yamata kwatance ya kashe wayar tare da bin gidan da kallo yace* Inna anan kuke rayuwa tsawon wannan Shekarun.
Kai ta ɗagamai tana Murmushi tare da nunamai Husnah da har lokacin ta kasa kwakwaran motsi tace ga "Yarka nan kuma sirikar ka m
Matar Habib.
Kallon ta yayi yana faɗin" Masha Allah tabarakallah, Yanzu wannan Matar Habib ce, Alhamdulillah,Naji daɗin kasancewar wannan auran da Abokina ya ɗaura ba tare da kyamatar ko damuwa da Rashin ganin wani jigo namiji daga family na Habib, Ina rokon Allah yasama auran ku Albarka, ya kuma baku zuria dayyiba,Wannn aure Alkhairi ne tinda ta sanadi shi Muka hadu,Bayan ina da tabbacin gabaki dayan mu muna cike da zullumi da Damuwa na Rashin sanin inda ko wannan mu yake,Amma yanzu Alhamdulillah.
Komi yazo karshe.
Sai Alokacin Shekh ya iya bude baki cikin wata fitinanniyar murya yace.
" Ameen . Tare da kallon Husnah da kanta ke ƙasa, ganin bazata juyoba ya kawar da kanshi gefe shi yama kasa gane wane yanayi zaice yake ciki, Gabaki daya zazzabi yakeji da masifaffan ciwon kai.
A'hankali ta ɗago ta gaida Daddy tare da mikewa ta shige dakin Inna cikin Kunya.
Su Aysha ma gaishe shi sukai suka maramata baya.
Suna shiga Aysha ta ɗanamata duka tace .
" Wow Husnaty Abbah ina tayaki murna samun balaraben mutum kamar shek kuttt,Kinga masifaffan kyan da Yayi kuwa?,Daganinsa dama kaga jinin azziki da natsuwa,wallahi bantaɓa yarda cewa Sheikh talakabane dama.
Husnah kau wani irin kuka tasaki tana Zamewa kasa ta zauna tace" Aunty taya zaisoni,Wallahi banyi tinanin dagaske za'ayi auran ba, nayi tinanin duk dan a ɓatama sadam raine, Aunty Shekh yafi karfina,Aunty yazan iya dashi dan Allah, Ni wallahi tsoron maza nike dan Allah ki sanar dashi wannan auran namu na wasane ya warware duka yaushe na fita uƙubar wani zan kumayi wani.
Wani irin huci Aysha tafara tana niyyar kaima Husnah duka meenah ta riketa tana bata hakuri.
Afusace tace" Dakin cika jaka dakikayi in:kikayi kuskuran rabuwa da sardidin saurayi kamar wanna,jakar inace ke,Ai'ni ganin farko danamasa nafahimci balain son dayakemaki wallahi,Ke ai'yanzu zakici Ɗammara zaman AURE,yanzu zakison kinyi AURE da namiki,Yanzu zakison kin auri wanda ya cancanta da rayuwarki mai Addini masani wanda bazaiyimiki komiba akan zalinci, Yanzu yakamata kijawo Sheikh jikin ki kishayar dashi Madara kauna,Amma tsabar wawanci kina nufin tsoransa zakiji ko abinda Sadam ke maki kikeganin zai maki? Aiko dakin cuceshi wallahi, Saboda a zaman da kikai dashi kinson baida aibu baida kuna niyyar Zalinci a rayuwar da zakuyi, Tinda duk abinda akafaɗamai akan ki yaji yagani kinga kenan dan Allah yake sonki, Ni bama wannan ba ɗazu miyasa kikace Sadam ya ciyar dake da haram yasaki kallon haram,mikenan ? Ko kina nufin kuntaɓa wani abu koya?
Cikin tsoro Husnah ta waro ido tace'' mikenan.
Rai ɓace Aysha tace "ke ba yarinya bace, ina nufin yataɓa saduwa dake dakikace ya cuceki koya?
"Laaa'haula wala kuwati illah billah Husnah tace azabure tare da buɗe baki tace "Na rantse da Allah babu binda yashiga tsakanina dashi ,kawai dai saboda Vidio danamasa,kuma shima ban kallesaba sai kuma lokutta da in'yana abinsa nike kamasa shiyasa kikaji na fadi haka..
Gabaki ɗayan su ajiyar zuciya suka sauke tare da furta "Alhamdulillahi>
Murmushi Aysha tayi tace gabaki daya Shekh dasu Abbah dama mukan mu munyi tinanin cewa akwai abinda ya shiga tsaki,in hakane kau zaki shayar da SHEKH mamaki aduk ranar daya kasan ce dake,na tabbata kimarki da darajarki zata linka wanda yake ganinki dasu a yanzu,ke akwai dai magana dole ayi tarewar nan kwana kusa, Yanzu dai inaso musan su waye shi tukun.
Kafin nan tashi kije kisake kaya wannan duk kin batasu da Ƙasa.
Aunty meenah tace "aini gabaki daya jikina yayi sanyi , Husnah naso gaban kowa ki fadi abinda yafaru amma kika rikice kikama kasa Sanin halin da ake ciki, Ga magana da akemiki amma kika bada wata Bauɗaɗiyar amsa.
Aysha tace aikwara datayi shuru wannan ma wani suprise ne ga Habibin ta na mussamman.
Fatan ki cire kunya kija mijinki jiki dan Allah,karki zama Daɗi mina liki Husnah,Kar Tsoron Sadam da kika tashi dashi yasa ki jahilci mijinki ki kasa bashi farin cikin da daga gareki kawai zai samu.
Shiru kawai tayi amma gabaki ɗaya abinda suke fada ta haddace, Dan ita kanta aganin farko tana son Shekh, dan-dai tayi yaki da abin ne sanin cewa ita MATAR AURE ce.
Tashi tayi ta sanya wata atamfa da Abba ya kawomatasu Doguwar riga, meenah tamata simple kwalliya ta zubamata dauri tare da daukar mayafi tasamata ta fesheta da turare .
Suna a' haka sukaji sallama .
Su meenah ne suka fito Yayin da ita kuma tayi tsaye tana hango wayanda zasu shigo.
Da sallama wata farar mata tashigo gidan tana sanye da Hijjob Jalbab Sak balarabiya ,kana ganinta basai an'fadama jinin larabawa bace ,bayanta wasu zaratan samarine masu balain kama da Shekh, sai budurwa da batafi tsarar Husnah ba tana sanye Da Abaya mai duwatsu.
Da sallama suka shiga,Lokaci daya kuma sukayi Turuss ! sukaja suka tsaya ganin abinda basuyi tinaniba ko amafalki.
SHEIKH kau jin murya da baizai taɓa mantawaba yasa azabure ya mike ya rungume mahaifiyar tashi,kukan da yake dannewa ne yafara sosai gwanin tausayi.
Ita'kau matar gabaki daya ta rikice sai shashshafa shi take a tsorace kamar zaa kwace mata shi,cikin wani murya mai masifar Daɗi irin ta Sheikh tace.
" HABIBIEEE.
"Na'am Oum Habib".
Shekh yafada cikin kuka .
Atare suka dago kai tafara kissing dinshi tana kuka a rikice tare da duba jikinshi ta shashaf har wajen kwantaccen sajensa taganshi lafiya kalau a rikice tace .
"Man aina ummi Abiha?.
Da Hannusa ya gwadamata Inna da samarin nan duk sukayi kanta suka rungume suka fara sabon kuka, Su Abbah kau sai kallon ikon Allah suke, Allah kadai yason miyafaru da wannan family dake cike da kaunar junan su,.
Da sassarfa tayi wajen Inna ta mikar da yaran ta fada kanta tafara kissing nata kota ina kamin ta rungumeta tace "nayi kewarki Ummu nah, nayi kewarki,ina kuka shiga tsawon wanna shekaru.
Inna ta shafa Fuskanta tace Kulu,Kina nan,Ashe zamu sake ganin juna Jidda? Hmm ai Abin da tsayi Hauwa'u , Ga Ɗakin HABIBIEEE nan muje nan yayi kaɗan.
Shekh kau Kannan nasa da suka taddosa ya rungume daya bayan daya kamin ya mikama Maryam hannu sukayi musabaha ,Ko cikin bacci zai iya gane kanwar tasa duk da lokcin daya barta batafi Shekara 11 ba gashi yanzu tazama cikakkiyar budurwa.
Hajja da tin sadda Inna ke kukan ganin Daddy tafara kuka cike da tausayi bata sake motsiba saida kowa ya mike kana ta fita waje ta samo Almajirai akan su kwashe Abincin a fita dashi Tinda an kammala,Nan suka biyota ta sanya manya cikinsu suka fara kwasa a boket suna fita dashi zuciyar su fess.
Ɗakin Habib ta isa inda ta iske kowa yayi shuru ana jiranta.
Shekh kau Kanshi ya dago da jajayen idanuwan shi yabi kowa da kallo , ganin baiga Husnah ba ya mike yana faɗin" ina zuwa.
Da kallo suka bishi harya fita.
Kai tsaye ɗakin Inna ya shiga da karama sallama abakin sa.
Husnah dake kuka sosai ganin yanda Shekh dinta ke kuka ta dago kai .
Cikin mamaki da kaduwa yabita da ido, Tare da zamewa ya zauna kusa da ita jikinshi har gogan nata yake akaro na farko su duka saida sukaji wani irin yarrr tindaga tafin kafa har saman kai.
Miya samu Matar Habib bayan yau ranar kice Amarya nah.
"Dago kanta tayi ta kalleshi kana ta turo baki cikin shagwaɓa da batason ta iyaba tace" Bakai neba kaketa kuka shiyasa nima nayi..
Jikin shi ya jawota cikin natsuwa ya rungumeta tsam yana sauke numfashi.
Jikin Husnahhh kau mugun rawa ya ɗauka jin namiji shaɓe shaɓe Akanta.
A'Hankali yafara shafa bayanta yana sauke Ajiyar zuciya,Sunkai 5mn kamin yafara magana cikin sanyin muryar sa.
UMSAD MAKENTOSH
*Makentosh*
*Makentosh*
*Makentosh*
Ina macen da ta isa takejin takai Hajiyar gayu.
*HMMM DA SAURANKI HAJIYATA INDAI BAKYA AMFANI DA MAKENTOSH*
Matso kiji hajiyata
Kamar yanda kuka sani UMSAD INCENSE ta sake zomuki da wani sabo sahihi mai suna MAKENTOSH
MAKENTOSH wani sirrine nasu na mutan Maiduguri,yana da masifar kyau yana hade mace gam koda haihuwa goma tayi,ina uwargida ina amarya ina budurwa ina zawara duka dai gudun'muwace daga mai kishinku har kullum UMSAD INCENSE.
Ina baku shawara da ku nemeta dan magance matsalolin da suke faruwa damu tsakaninmu da mazajenmu dan gyara shinfiɗarmu kai tsaye.
Ni Ummy Aysha shiyasa na kasance shalele awajen mai gidana saboda gabaki ɗaya sirrin gyaran jikina yana Tattare da gudun muwar UMSAD INCENSE shiyasa koda yaushe muke cikin walwala da farin ciki da mai gidana🥰.
Dan neman farin ciki akoda yaushe tsakanin ki da mijinki ki tuntuɓeta a wannan layin
Sayen nagari maida kudi
UMSAD INCENSE 080 288 27241
😂
3️⃣3️⃣&3️⃣4️⃣
"Ke Alkhairi ce a tattare dani Oum Habib,ke din ta musamman ce arayuwar Habib,kin kafa wani tarihi da bazaitaɓa goguwaba,Sanadinki naga iyayena dana fitar da ran sake gani,Husnah I love You so much my wife, Wallahi ina sonki so mai tsanani,ki daure kibama Habib farin ciki koya yake,Wallahi Husnahhh ina son akula dani ina son a nunamun tsantsar so,Dan Allah karkisa Alkunya a zaman takewar da zamuyi kinga sunna zamu raya,idan kau