Showing 6001 words to 9000 words out of 69765 words

Chapter 3 - MATAR AURE BOOK COMPLETE PDF.txt

Advertisement

a tattare dake,duk da mijinki ya shedaman cewa kinyi jinya amma baidace ace jinyar da kikai tasaki wannan ramar ba,Husnah duk cikin yarana kinfi kowa jiki mai kyau, kinfi kowa ƙiba da, amma yanzu duk kin zube,ni mahaifinkine baki da tamkarni arayuwarki,shin kina da matsalane koko kina da wani abun da kike bukata.


Kuka ta fara sosai zuciyarta na ingizata datafadama Abba irin zaman da suke.


A'hankali ta bude bakinta tace .
"Abbah dan Allah ka mayar dani gida wajen Umma nah, ina kewarsu kuma banajin...


Bummm aka turo kofar da kargi Wanda suduka saida suka furgita.


Sadam ne ya shigo a gigice ko ina na jikinshi rawa yake.


Abba ya mike azabure yana fadin" lafiya Sadam?.


Wayar shi ƙarama daya lallaba ya ajiye ƙasan kujera bayan ya kira da babbar tashi yayi picking call ya kallah dan anan yakejin duk maganarsu Mafarin shigowar shi aguje kenan karta tonamai Asiri.


Wallahi abbah sauri nike nason kunsha yunwa shiyasa duk ba cikin natsuwata nike ba yakarasa yana kallon Husnaty datayi kasa da kanta..




Wani kallo ahbah yamai kamar na rashin yarda kamin yace


"Shikenan ai da baka wahalar da kankaba saidia ita Hajja ya kamata ta Taso taci abinci maza Husnah kirawota.


Mikewa tayi cikin tafitarta mai sanyi ta haura sama, bakin kofar dakinshi taga Hajja zube azabure ta isa inda take ga jikinta sai zarnin fitsari yake dan da alamama wani takara.


Abbah!!!


Taita kwalama Abbah kira .


Abbah ya kalli sadam yace lafiya naji kiran matar ka.


Da sauri ya mike ya haura sama Zuciyarshi na bugawa fatanshi allah yasanya ba Zuma suka gani ba.


Turuss yaja ya tsaya ganin Hajja zube ka bako alamar numfashi.


A Gigice yamatsa yana fadin minene miyafaru da ita?


Cikin kuka tace haka na ganta dan Allah Hajja ki tashi karki tafi kibarni daga zuwa kawomin ziyara , Hajjah tah dan Allah kitashi.


Abbah dakejin hayaniyar su ya hauro saman saboda Sadam tamkar Ɗa yake a wajenshi ba wata kunyar surukuta a tsakaninshi dashi .


Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un yace yana fadin samomun ruwa.


Ruwa aka samomai yamata yan dubarunsu na manyan likitoci saigata ta warsake tana sauke ajiyar zuciya tare da fadin "Lukman muyi mubar gidan nan dan Allah,Wallahi akwai Aljana A gidan nan, Dan Allah mutafi nafasa baccin nan da wankan m,tashiga basu labari saida ta gama kuma ta zabura tana fadin wallahi tace kar in fadama kowa dan Allah mubar gidan nan.


Zuma kau duk abinda ke faruwa tanaji kuma tana ganinsu hakan yasa ta tattara komi nata ta shige wadrob tayi luff abinta tana Dariya ƙasa ƙasa.


Gaban sadam na bugawa yace .
"A ina Hajjah? gaskiya sai dai in idonki gizo yakemaki, Ya mike tsaye yana ɗan leka dakin shi da waiwayowa dan karwani ya biyoshi,ganin ba kowa ya shiga toilet nan ma babu kowa.


Yace Abbah dan Allah shigo kagani tsoratane kawai Hajja tayi , Amma ta ina wani zaizo gidan nan.


Abbah yace A'a Nasani Sadam wallahi..


Husnah kau tsaf ta fahimci komi amma bata da bakin magana sai gefe data koma ta buga tagumi.


Kama Hajja sukayi itada sadam har dakin Husnah suka kaita toilet tayi wanka ta fito ta kwanta bisa gadon Husnah tana sauke numfashi.


Husnah ta shiga ta wanke mata kayanta tass ta zagaya baya ta shanyasu.


Bayan ta dawo sadam ya shigo hannushi ɗauke da take away da flat ya juye fride rice din daya siyomusu da kazar datasha gashi sai kamshi take.


Nan Hajjah ta warware ta bigi dadinta kamin ta buga gyatsa sai bacci.




Husnah ya kallah ganin yanda tayi kasa da kanta batama koson ganinshi cikin kasa da murya yace.


" Wallahi billahi kika fadama wani wani abu saina ɓatar dake daga doran ƙasa,dan kinson zan iya fiye da hakan, zan iya kasheki in binneki babu ubanda ya sani tashi muje.


Jiki na rawa ta mike tabishi suka sakko kasa inda Abbah ke zaune yana waya da abokinshi Alhaji Bilal.


Ganin sun sakkone yasashi mikewa yace Husnah babu wata damuwa ko?.


Tace eh Abbah babu.


Yace masha Allah bari ni zan wuce zuwa anjima zandawo in dauketa mukoma.


Kai ta dagamai alamar gamsuwa tanamai Allah yakiyaye hanya.


Sadam yace .


Abbah dan Allah kazauna kaci Abincin nan, Abbah abincin fa Ƴaƴan kane.


Murmushi yayi yace karka damu My son wata rana ai zanci , Yanzu sauri nike yana fadin haka ya fita cikin kamala ya bishi yamai rakiya Yayin da ita kuma ta zame ta zauna kasa tana auna maganganunsa a mizanin tinaninta, shin tsorata ta yakeso yayi koko da gaske zai iya kasheta kamar yanda yace?.


Husnah yakira sunan ta yana zama kusa da ita.


Akwai wani sirri mai girma tsakanina dake wanda yake ɓoye kuma nikadai nason sirrin, Dan haka karki wani damu da duk yanayin da muke ciki ni natsara abina, kuma nikeso mu tafi a haka ina fatan kinfahimceni,inkika bini yanda nikeso wallahi zamu zauna zama mai dadi,abinda nikeso dake kawai ki kawar da idonko akan duk abinda zakigani,ki dauka cewa ke baiwace kudina na bada na siyoki,dan haka yazama wajibi duk kan abinda nikeso inyi agabanki batare da kin tankaba,ki kawar da kanki,ki rufe ganinki,ki toshe jinki inafatan kingane?.


Kai ta dagamai kawai .


Yace good karki manta gobene zaki fara zuwa makaranta.


Kai ta dagamai alamar gamsuwa.


A'hankali ya mike ya doshi dakinshi ya mayar ya rufe , Cikin kasa da murya yace ina kike ne?.


Zuma da jikinta yayi lakaɓ da gumi ta fito tana zare ido, garin ta fito kanta ya daki wani akwati take ya fado takardun ciki suka zame suka fadi.


Kwanciyarshi yayi akan gado tare da fadin" ki kwashesu kimayar muhallinsu, inaso ne kimin tausa dan duk nagaji ba karamin fargaba nashigaba da ganin wayan nan bayin Allah,kana taya akai kikai sakacin da har Hajjah ta ganki?


Zuma kau gabaki daya idonta nakan wata farar takarda jikinta har rawa yake ta dauka ta saƙeta ga safar dake kafan ta.


Bakijinane ya fada yana mikewa ya zubamata ido.


Au sorry wallahi inajin kaina ne kamar babu daɗi sakamon dukan da akwatin nan yamun, mikace ne tace tana kallonshi?.


Kamar bai yarda da irin yanayin taba amma ya koma ya kwanta yana mai sake Maimaitamata abinda yafada.


Da sauri ta mayar kana tabashi labari sukai dariya tace" bari in rage marata inzo ta fada tana fadawa Toilet, ta kara gyara gashin dokin ta kana ta fiddo takarda ,ta Duba sosai tasaki murmushi tare da fadin" kazo hannu Yaro,Zanyi amfani da wannan damar wajen juyaka kamar waina A tanda..




Tsaf ta mayar da ita tafin kafarta kana ta fito anan ta fada kanshi daganan yanayin nasu ya sauya salo.


Wayarshi daya bari tashiga ring.


Ahankali Husnah takai hannu ta ɗauka ta duba, ganin ansa meerah sugar yasa ta ajiye wayar tana mai lumshe idonta daganan bacci yayi gaba da ita.


Sai karfe hudu saura kwata Hajjo ta mike ta sauka tana salati ,kana ta banka toilet tayi wanka tayi alwallah ta zauna ta buga tagumi tana tinanin abinda ya faru dazu ,Tsoro ya kamata sosai hakan yasa ta fito da sauri, dai-dai kofar dakin sadam ta dingajin nishinsu da kuma sukuwar da sukeyi wanda hakan ya tabbatar mata da aljannune sukeso su cafkota aguje tayi kasa tana haki,Gudunta ya tada Husnah ta mike takamata tace lafiya Hajja,?


Tace Husnah maza bani sitirata insanya aljannun gidan ku basu maraba dani wallahi, dan Allah bani.


Zagayawa tayi baya ta dakkomata tabata anan palon ta sanya Abinta tayi sallah cikin rashin natsuwa tana gamawa ta zaro wayarta tace ungo kiraman ubanki , zakiga ansa Baban Sadam.


Karɓa tayi tana gilgiza kai ta kirashi yana dauka tamikama Hajjah .


Hallo Lukman kataho kuwa?


eh Hajja nakusa isowa, na tsaya saima jikanyar taki wayane gani nan kusa insha Allah ki shirya.


Ai a shirye nike tafada tana kashe wayar tare da fadin ina Sadan Husnah.


Tace yana sama.


Cikin mamaki tace waiku lafiya kalau kuke zaune ne bakwajin iskancin aljannun da ni nikeji.


Murmushi tayi tace Hajjah bari inkiramikishi ta tashi ta haura sama ta kwankwasa kofar shi.


Jin shuru ga Hajjah na kiranta yasata tura kofar ta shiga, dai-dai lokacin da yake juyema Zuma madararsa saman marar ta ,bakaramin razana yayiba ganin Husnah tsaye ta juya kai.


Cikin tsawa yace miye minene kika shigoman daki kamar goɗiya babu izini.


Hajja na jiranka ta fada tana juyawa da gudu ta fita ta shige dakinta ta fashe da kuka kana ta wanke fuska ta fito, dai-dai lokacin da hajjaj tasanya kafa da niyyar barin gidan tana fada akan sunyi banza da ita daga kiranshi yaran yanzu basu da kunya.


Husnah tace Hajjah.


Tsayawa tayi tana fadin nidai yau wlh gabaki daya na kasa natsuwa da gidan nan dakuma kanku wallahi, inama amfani jibi idonki ,tinda mukazo kike kuka,shin Husnah in kina da damuwa kina da wanda ya flmune,kidu ba tafiyayya da mukai daga jigawa har katsina danke, amma ace munkoma zuciya babu dadi.


Kiyi hakuri Hajjaju tinda ta ganki ta cika da rauni yanzu haka kuka takeman saita biku na bata hakuri, nason batada cikakkiyar lafiya da zata iya zama cikin mota tsawon tafiyar kusan awa ukku , Dan Allah hajjah kiyi hakuri kiyi zamanki kema damu sadam Ya fada yana kallon Husna da fuskar tausayi.


Hajjah ta gwalo ido tace" A'a Allah ya kiyayeni kudai aka amincema zama ni kunga tafiyana tafada tana fita suka biyota dan mata rakiya, Husnah ta ɗauki Hijjob inta tafito danyin bankwana da Baban ta, itama Hajja tsayawa tayi suna magana data shafesu wadda duk nasihace game da zaman takewar aure dakuma hakuri da rukon amana da takeso yama Husnah.
Yace ya amince Insha Allah zai kara akan wanda yakeyi.


Abbah kau gidan gaba ya bude mata yace tashigo ba musu ta shiga tana kakalo Murmushi.


Yace Husnaty azahirin gaskiya ban amince da yanayinki ba,amma bazan tilastakiba watakil sirrin gidan kine, saidai ki sani shi aure yana tattare da kalu balen rayuwa.


Dan haka dan Allah ki kara biyayya dakike awajen mijinki kinji ko,kudi yazaro mai yawa 200k ya mikamata yace karɓa ki boye abinki banaso kizama layin matan dake da yawan bani bani awajen miji , Dan hakan ma yana taka rawa lalacewar zaman AURE sosai,wannan kuma ya mikamata wata ƙatuwar leda yace kayan ciye ciyene gasunan dai yanzu abokina yabanisu in kawomiki Alhaji Bilal mai canji mutumin kirkine mun hadu dashine last year danaje Umara bayan bikin ki , To shiyasa yau na kawomai ziyara Tinda nashigo gari.




Wannan kuma wayace,gatanan mai kyau ta zamani na siyomiki duk da bansaniba ko ra'ayin mijinkine bayaso ,nadai maku katsalanda inaso kisamu natsuwa kikuma sami abinda zai debe miki kewa kinjiko.


Wani irin farin ciki taji tashiga yima mahaifin nata Godiya , Babu abinda takeso arayuwarta sama da waya dan tason abune mai ɗebe kewa.


Ahankali tace Abbah dan Allah ka sanar mai da kai kabani banaso ne yaganta karyace na roke ka.


Kai ya jinjina tare dajin babu dadi aranshi hakan ya tabbatar mai da sadam kenan bai ra'ayi tarike kila shiyasa bai siyamata ba.




Hajjah ta karaso wajen motar tace mutafi ko Karmuyi dare.


Abbah ya fito yana mikama sadam hannu yace "my son nama karanbani duba da yanayin da take ciki na kadaici yasa yanzu na ɗan siyamata waya dan allah ayi hakuri inba damuwa ta samu abinda zata gaisa da yan uwanta.


Wata irin kunya ta rufeshi Hajjah kau Fada ta rufeshi dashi na rashin kyauta da yayi na hanata rike waya.


Dakyal ya bude baki yace wallahi Hajjah ni gani nike damuwa zata shiga in tana waya da yan gidan,kamar zatai ta ƙagara zuwa gida, bayan ga yanda kikace.


Tace'' magana banza da Tinanin kifaye kenan, agidan ubanwa zataji daɗi..


Hakuri Abbah yabasu kana suka dauki hanya suna masu Allah ya kiyaye.


Suna tafiya sadam yace to ga waya nan anbaki amma wallahi kika zabi tonaman asari ƙudirina akanki ba fashi. .


Kai ta ɗagamai cikin farin ciki tace insha Allah nagode yah Sadam.


Kallonta yayi ganin duk ta rude da Murna ,ita abu kadan sai Taita murna har mamaki take bashi, baki ya tabe kana ya haura sama Ɗakin shi ..


❤️ *MATAR AURE* ❤️
*NA*
*UMMY AYSHA*
7️⃣&8️⃣
""Kwance yasame Zuma hakan yasashi janta jikinshi bacci ya kwashe su cikin jin daɗi.


Husnah kam tana shiga ta daka tsalle ta faɗa kan gado, Taba warware wayar Tata data kasance Android Infinix Smart 5 sabuwa ƙar abinta.


Hannu ta ɗaga sama tace yah Allah yasanya Abba nah Aljanna, yanda ya faranta Mun Allah ya faranta Masa, Allah kasanya in Rikeki da Alkhairi.


Charge ta sanya kana ta buɗe ledojin taga kayan ciye ciyene na Yan gayu, cake, biscuits, chocolate, sweet, Da sauran su.
Cake ɗin taci kaɗan ta ajiye kana tama kudinta muhalli mai kyau ta adanasu ta dawo ta rungume wayar ta abinta tanajin farin ciki.


Washe gari karfe Biyu ta kammala aikin gidan baki ɗaya kamar yanda ta saba, zuwa 2: 30 tayi wanka ta shafa mai tare da sanya kwalli kadan ta sanya lips stick ko powder bata shafaba ta dakko kayan nata da suka kasance maroum ta sanya rigar da hijjob din da bai kai mata kasa ba.


Kallon kanta tayi A madubi tanajin wani nishadi da farin ciki har cikin ranta, gabaki daya ta manta da damuwar wani Sadam, ga wayarta ga kudinta batada wani abu yanzu sai butun ganinta aji.


Cikin natsuwa ta fito Ɗakin tana zagayawa cen bayan kofar Ɗakin Sadam, inda daganan kana iya hango benen makaranta da farfajiyar wajen ta cikin glass ɗin wurin.


Murmushi tayi tace .
"Yau ina nan iso wa Insha Allah.


Ke mikike anan ko sai kin'makarane Sadam yafada yana rike da hannun Zuma daketa narkemai.


"Aa Yah kaidama nikejiran kafito zan wuce tace tana kallon gefe .




"Wai Sweety baka koyama yarin ya nan girmama nagaba da itaba ko batason matsayina a wajenka ba.


Kamin ma yace komi Husna tace" Ina kwana, tana fadin haka ta shafasu ta wuce suka bita da kallo.


Ahankali take sauka daga step ɗin ta sauka kasa ta ɗauki wayarta da form din data cike kana ta fita zuciyar ta fess.


Security suka bita da kallo suna gaisheta cikin mutunci da kuma tausayawa.


Fuskarta a washe ta mayar masu da gaisuwa kana ta fita.


Mai gadin ya kalli wani dakeken Kato dake kusa dashi yace.


" Gaskiya Yarinya nan akwai hakuri Dumba,jibi yanda ake shigomata da yan iska amma bata ko damuwa.


Ita taso yafada yana rufe get din ya koma cen baya ya zauna.


Husnah kam tinda ta fito ta shaki wani ni'imtaccen iska mai daɗi da ta daɗe bataji irin shiba.


Hannu damarta ta kallah taga gida hude ne tsakaninsu da makaranta.


Cikin natsuwa tacigaba da tafiya har ta karaso ta shiga da sallama.


Bata samu kowaba sai wata Dattijuwa tana share Share, Ashekaru bazata wuce 55.


Inna ina wuni ta fada Cikin siririyar muryar ta.


A'hankali matar ta ɗago kai .
Wai masha Allah nace dan ganinta kyakyawa duk da ta fara tsufa amma wannan dagani Yan matancin ta anyi kyakyawar budurwa.


Fuskar ta cike da murmushi tana bude fararan hakoranta wanda suka kasance fess Babu alamar goro aciki tace.


" Sannu da zuwa yau ke kadai kika fara zuwa ko ukku fa bata idaba...


Kai ta ɗagama ta kana tace .
"Ni ai yau na fara zuwa,kawo Tsintsiyar na tayaki.


Haɓa takama tana faɗin" A'a wallahi kibarshi Allah ya miki albarka,nima inayin wannan aikin ne dan kar jikina ya mutu inshiga ukku in lalace ɓarin jikina ya shanye barni in motsa jiki Tinda babu Abinda nike na karfi.


Cikin tausayinta Husnah tace.
" Inna miyasa kikeson wannan aikin bayan lokacin hutun kine yanzu? ya kamata kibar Duƙiya kodan bayan ki.


Dariya tayi tana gyara zaman Tsintsiyarta tace .


" Akwai jikana shine malamin ku anan ajin, Yayi Yayi in daina nikuma nakiya saboda inason in samu lada, Babban malamin makaranta duka har 3k yakebani duk wata nace bazan karɓaba ,HABIBIEEE ya tsayawamun akan komi wallahi...




Husnah tace" to Allah yabaki ladar.


Ameen tace tana kwashe sauran sharar kan ta juye cikin babban durom din da ake jiya sharar tana gamawa ta wanke kafarta kana ta kalli Husnah Da Murmushi tace" jikata zantafi gida kinga dai har yanzu babu wanda yazo ko, HABIBIEEE ma bacci yake bai tashiba yanzu zan koma in tashesa yaje yayi wanka ya taho, kibari kidingayin baccinki sai 4 ki fito,ko banan unguwar kike ba?


Husnah tace nan nike na matsu inzo ne Inna..


Dariya tayi tace.
" To shikenan nima gidana na jingine da makaranta nan.


Da sauri Husnah ta mike tace muje ingani sai inyi sallah nah a cen.


Tsintsiyar ta ajiye tace.


" Yau nayi Jika ni Maryamu, to muje .


Tare suka fita daga makaranta,gidanta shine karami mai ɗauke da baranda daga waje ga shago karami na provition .




Da sallama suka shiga tabi gidan da kallo, karamine sosai , Ɗaki biyune tall,sai ɗan kiching da kuma Toilet suna kallon juna .




Shigo Ɗiyata Inna tace tana bude dakinta dake shafe tass ba komi ciki sai tabarma da filo da kuma redio,sai jikkar dake nuni da kayanta amma gidan fess ko ina tsaf ba kazanta.


Kinga ɗan muhallin namu ko jikata tace tana kallon Husnah dakebin karamin dakin da kallo.




Murmushi tayi tace "
Ni tinda aka kawoni Inna banfitoba shiyasa yau danazo komi yazamemun sabo kiyi Hakuri.
. Cikin mamaki tace ko kece amarya gidan SHIKAƊAI?


Cikin mamaki tace "waye SHIKAƊAI?


Innah ta ce ga gidanan daga nan gidan gida ukkune tsakanin mu wani Babban gida,wallahi koni nasha zuwa dan mugaisa da matar gidan amatsayin mu na makwabta, amma sai yasanya wayan nan kattin su koroni,nikuma ina ganin nice Babba a cikin layin nan namu yakamata in jawoku jiki,nidai bani da kowa sai HABIBIEEE shiyasa nikeson yara amma baya barin kowa ya shiga gidan sa shiyasama ya Ajiye Wannan kattin bamuson nufinsaba,kila bayaso kinayin mu'amullah da Talakawa ta karasa tana Murmushi.




Wata irin kunya da takaici suka kama Husnah tace.
" Yanzu dama haka aka samai suna,kiyi hakuri Innah zan dinga shigowa ni ina ganin ki daga yau, kiyi hakuri Dan Allah.


Da naji dadi kau tace, daganan suka shiga fira Inna ta tashi ta fita tashiga wancen dakin ta fito kana ta kawo masu ɗan wake, Husnah ba kyamata bakomi dan bataga abin gudu daga Inna ba, akwano daya sukaci suka koshi Tana santin Ɗan waken Tsohuwar,,karfe huɗu saura tayi sallah Innah ta mike ta ce muje in kaiki to.


A tare suka fito suka shiga makaranta dai-dai lokacin ɗalibbai yara nata shigowa Yan tahfix kaɗai, kai tsaye wani aji dake gefe tanufa da ita tace.


" Shiga ki zauna har yanzu dai basuzoba sai yaran aka fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login