Showing 18001 words to 21000 words out of 69765 words

Chapter 7 - MATAR AURE BOOK COMPLETE PDF.txt

Advertisement

zaije ya dawo.


Husnah kau tana fita daga gidan kai tsaye gidan Inna tayi da sallama .


Inna ta fito tana amsawa cikin fara'a tare da mata sannu da zuwa .


Har kasa ta durkusa ta gaida Inna, kamin ta tashi ta fara share mata gidan .
Inna sai cewa take tabari.


Cikin sanyi jiki ta ajiye Tsintsiyar tace" Inna in kina mun haka sai inga kamar baki Ɗaukeni jikar da kike cewa ba, kamar baki haɗa matsayina dana Malami na ba,minene dan namiki shara? Ina ci gidanki, ina sha,ina samun natsuwa,amma ace dan zan'miki shara sai kin dakatar dani,shikenan Inna Nagode ta fada tana kwasar jikkar ta da littafinta zata fita.


Yah Shekh da duk abinda ke faruwa yana kallo, Tun shigowarta ya zabura ya mike daga zaune da yake ya zubamata ido ta window,Ganin zata fita yasashi fitowa da sauri tare da tareta ya fara jujjuyamata kanshi,wanda shikan shi baison miyasa ya kasa hana zuciyarshi tinkarar taba kai tsaye da son dakatar da ita.


Cikin sanyi da ko Inna batajinshi dan tinda taga Husnah na kokarin fita takirata amma bata juyoba taga Habib ya tsayar da ita ta shiga ɗaki tana hawaye tason zai lalasomata ita insha Allah..


"Dan Allah kiyi hakuri karki tafi, Dan Allah ki tausayamun,karkimin haka,kinkasance mai debema Kakata kewa, Dan Allah karki barta,Kuskurene tayi bazata sake ba,kana Inna wallahi batason anamata abu shiyasa kikaga duk aikin dazatai nike komawa gefe in zauna, Dan Allah Mamana karkiyi fushi ki guji zukatan da suka aminta dake ,Tare da baki amanar kansu kinji?.


Wani kuka ya kufcema Husnah cikin wani irin sassarfa tayo kanshi bata tsaya komiba ta fada jikinshi ta kankameshi kana ta saki kuka tace "Malami na Inna uwata ce,, Yayin da kai nike ɗaukarka ubana, Danmi duk abinda zanma Inna zata hanani?Atinani na munyi shakuwar da yakamata ace Inna zatama jirani inzo inmata aikin komi koda kau zan kwashe awanni banzo ba,Yarda daku yasa na fadamaku sirrin da wayanda suka kawoni duniya basu sani ba, Ina barin komi inyo wajenku dan kun zamemun katanga abin jingina,Yazan dinga tusa kaina inda aka kasa Aminta dani,Wallahi kwana nike ina Tinanin ku,Na Aminta daku ta Yanda baki bazai iya furtawa ba Yah Sheikh .




Wani irin kuna da zafi yakeji acikin zuciyar shi,inama yana da damar da zaiyi kuka koya samu saukin da zai ragemai azabar dake cinshi,zuciyarsa batai mai halacci ba, Data dasamai abinda yayi nisa a gareshi, SO da kaunarta ke fuzgarsa,yama rasa da minene zai misilta yanda yakejin Husnah a cikin zuciyarshi.


*Matar Aure cefa*


Wata zuciyar ta tinatar dashi.


Da sauri har yana neman faduwa ya zameta daga jikinshi kamin yayi baya ya jingina da bango,kamin A'hankali ya fara zamewa yayi kasa yanajin kamar yafasa katon kuka ko yasamu sukunin zuciya,Rawa sosai jikinshi keyi idonshi yayi jawur kamar zai yi aman wuta.


"Am sorry Yah Shekh,Ban faɗaba dan bata ranka amma kamin afuwa kaji? .


Husnah ta fada tana zamewa ta zauna gefen shi ta fara rera sabon kuka .


Jin shuru yasa Inna dake hawaye fitowa tace" Husnah, Dan Allah kiyi hakuri, kana kimin kyakyawar fahimta,wallahi ba nufina bane in katsemiki farin ciki A'a ,kawai gani nike baidace da kinzo kihau aikiba,baccin ga matsala gidanki uwa uba ga halin da kike ciki har yanzu idonki akwai jini aciki, Baidace ace kina aikin duƙiya ba,amma kiyi hakuri Ɗiyata daga yau bazan sake cewa karkimin komi ba,zanma dinga ajiye Miki aikin har kizo kiyi koda zankai goma na dare,Naji daɗi nagode Allah daya bani diya mai tarbiya da natsuwa ,ina rokon Allah yaba HABIBIEEE nah mata mai natsuwa da hankali kamar ki,nason zata soshi koda kau bashi da ko sisi,zatamai biyayya duk da halin da yake ciki,kema Allah yagyara zaman auranki, ya daidaita tsakanin ki da mijinki,inkuma babu Alkhairi a cigaba da zaman ku Allah yayi gaggawar raba tsakanin ku.


Cikin kuzari Husnah tayi kanta ta rungume tashiga godiya kamar an aikota,Kamin ta saki Inna ta naɗe Hijjob inta ta fara sharar gidan tass ,Tana gamawa ta kunna pampo dan daga makaranta ana basu ruwa,Ta wanke simintin gidan tass ,tare dayin wanke wanke kana ta mike tana murmushi tace Inna "zantafi saina dawo.


Hararata tayi tace" zonan kici ɗumame kamin ki wuce.


Zama tayi taci lafiyayyen tuwan masara dayasha miyar kuka mai wake yayi cakwai kamar an'zuba nama.


Rayuwar su Inna na matukar burgeta,gabaki daya basu sama ransu cewa sai kana da dukiya zakai farin ciki ba, A'a ako wane yanayi kake indai kana da rai da lafiya to ka kasance mai am'baton Alhamdulillah,Sun son cewa da wanda zaici naman kaji ya kwanta da wanda zaici tuwo yakwanta duka ɗaya suke, Dan zasu haɗu wurin shan ruwa.


Saida tagama tass kana ta fito,cikin mamaki ta kalki Yah SHEKH dake zaune bakin kofa yayi shuru.


Matsawa tayi wajenshi tace" mike faruwa Yah Sheikh,dana Allah mike damunka?.


Kai ya jijjigamata yana sakin murmushin yake yace "bakomi kitafi ganinan zuwa.


Cikin sanyi ta mike har takai bakin kofa ta juyo suka haɗa ido dan ita yake kallo.


Idonta ta lumshe kamin ta daga hannuwanta tanamai bye bye.


Shima idon ya lumshe sosai girar idon tayi wani shar da ita ,kamin ya bude rikitattun idon nasa ya sauke su akanta, kamin ya fara ɗagamata fararan yatsan sa guda biyu.


Murmushi tamai kamin tace "Nagode malamina tayi waje tanajin zuciyarta wasai.


Cikin farin ciki ya tashi ya shiga wanka ya fito yaci tuwo, kana ya sanya jallabiyar sa fara sol ya ɗauko tiraran sa na cikin kwalba ya murza a hannusa kamin ya murje jikinshi, take ya fara kamshi kota ina,Rawanin sa daya kasance fari da ja ya ɗakko ya ɗaurashi kamar yanda ya saba,Silifas dinshi ya sanya yace" Inna natafi.


Adawo lafiya tamai kamin ta kwanta dan tayi bacci.


Fita yayi yajamata gidan.


Yana shiga ajin ya iske Husnah da hafsah sai labari suke suna dariya.


Gaishe shi sukai ya amsa kamin yadan saci kallon Husnah yakuma dauke kai .


Hafsah tace "YAH Sheikh kwana biyu lafiya daiko,bama ganin ka.


Affuwan dan Allah,kumin uzuri.
Yace a gajarce Dan bai son mizai ceba kuma karya ba ɗabia'arsa bace


Tace shikenan dama fatan mudai ace lafiya Kake.


Aranshi yace ga damuwatanan kusa dake,Amma azahiri sai cewa Yayi Alhamdulillah.


Aranar dai yayi dauriya sosai dan shine ya yini dasu , Sai karfe daya saura suka tashi,Kai tsaye Husnah gida ta wuce dan tabar Inna ta huta.


Sadam .


Irin dukan da Dumba yamai ko kwatar shi Yaran Zuma basumai ba,yakai awa biyu kamin yatashi amma bai iya komi,dakyal ya kira maigadinshi ya shigo anan yake fadamai abinda Dumba yayi mai.


Hankalin mai gadin yatashi .


Yace maza ka kiramun likita dan Allah mutuwa zanyi kar jinin Hancina ya kare dan Ubanka.


Bakin Unguwar tasu yake inda keda wani Nursing daya bude shago,anan ya dakkoshi yazo gida ya Duddubashi yasamai karin ruwa leda biyu.


Saida akayi Sallah azahar aka kwance,yasamu yaji kwarin jikinshi, tashi yayi ya isa wajen mirro yafara karema kanshi kallo,gabaki daya sun'mai walmakalufatu, suncanzamai kamanni.


Ranshi ya baci sosai da har lokacin Husnah batazo dubashi ba Tsabar iskanci kamar ba mijinta ba.


Tinowa da makaranta yasashi fadin" zaki dawo yau dani dakene wallahi saina zaneki.


Yana ganin 12:50 ya fito palo tare da laɓewa cikin labule.


Cikin sanda ta shigo tana leka palon dan taga ko yana nan..


Shigowa tayi tana maida kofar A'hankali ta rufe dankar yaji motsi Ya fito.


Wuyanta taji an damka tare da rufemata baki.


Arazane ta fara ƙoƙarin waiwayowa amma ya shaketa sosai...




UMSAD MAKENTOSH


*Makentosh*
*Makentosh*
*Makentosh*


Ina macen da ta isa takejin takai Hajiyar gayu.


*HMMM DA SAURANKI HAJIYATA INDAI BAKYA AMFANI DA MAKENTOSH*


Matso kiji hajiyata


Kamar yanda kuka sani UMSAD INCENSE ta sake zomuki da wani sabo sahihi mai suna MAKENTOSH


MAKENTOSH wani sirrine nasu na mutan Maiduguri,yana da masifar kyau yana hade mace gam koda haihuwa goma tayi,ina uwargida ina amarya ina budurwa ina zawara duka dai gudun'muwace daga mai kishinku har kullum UMSAD INCENSE.


Ina baku shawara da ku nemeta dan magance matsalolin da suke faruwa damu tsakaninmu da mazajenmu dan gyara shinfiɗarmu kai tsaye.


Ni Ummy Aysha shiyasa na kasance shalele awajen mai gidana saboda gabaki ɗaya sirrin gyaran jikina yana Tattare da gudun muwar UMSAD INCENSE shiyasa koda yaushe muke cikin walwala da farin ciki da mai gidana🥰.




Dan neman farin ciki akoda yaushe tsakanin ki da mijinki ki tuntuɓeta a wannan layin






Sayen nagari maida kudi


UMSAD INCENSE 080 288 27241


Data service available
1gb 250
2gb 500
3gb 750
4gb 1000
6gb 1500
8gb 2000
Account number 1479603206
BANK name ......
BANK account jaiz bank
Phone number 09064260199


❤️ *MATAR AURE*❤️
*NA*
❤️ *UMMY AYSHA* ❤️
1️⃣7️⃣&1️⃣8️⃣


""Jin zata mutu yasata Daddagewa ta danna mai cizo.


Azaba yasashi sakinta tare da rike gashinta ta saman Hijjob ɗinta dan karta kufce.


Ido hudu sukai dakyal ta iya ganeshi ganin yanda halittatshi ta sauya.


"Ke jakar inace,Tin'jiya da kikaga baki ganni ba danmi bazakiyi jajena ba?Duk Matar Arziki Tana kulawa da mijinta amma bandake da yake duniyar Dabbobi aka Haifiki shiyasa baki da Kyakyawan Tinani,Bakison hakkina dake kanki ba ko? Dan kinga na ɗaga maki kafa tsawon shekara ɗaya da wata ɗaya?


"Ka sakeni dan Allah zaka ciremun kai tafada cikin tashin hankali jin yanda yake jan Gashinta..


"Wani bahagon mari ya saukemata tass tare da cewa "Kimin shuru kamin in'maki illah,Dami zanji? Bakiga jikina ba bazaki nuna alhininki akan halin da nike ciki ba.


Wata irin zuciya da batason tana da itaba ta tasomata,gabaki daya karfinta tasa ta tureshi .


Rashin kwarin jiki yasashi tafiya ya fadi kwaraf Yana mai zaman Dirshan.


Hawaye sun ƙafe daga idonta, Tsoro ya gushe, hakan yasata nunashi da yatsa cikin jin zafi tace.
" Wallahi billahi daga rana mai kama ta yau, ka sake taɓa koda tafin kafatane to katabbata sai nama lahani,Kai jakin inane,kataɓa ganin Duhu da haske a lokaci ɗaya, Koko kataba ganin inda Ruwa da wuta suka haɗu,Bahagon mahaukacin inane kai sadam ?Ya za'ayi ina mai tsarki ace zan kasance da fasiki Ƙazani,Kasani tsoronka ya gushe araina wallahi, Duk duniyata kaine mutum na farko kuma na karshe danaji na tsana, BAZAN taba kaunar kaba har abada,Haba ! haba!! Abin nan yayi yawa,kai ba ɗan halak bane wallahi,som baka kyautaci kyautatawa daga mahaifina ba, Yau da ubana yason zalincin da kakemun ina kyalewa ina da tabbacin bazai taba yafema ba,Taya za'ayi nazama gangarka akoda yaushe nice abin duka awajenka,Ada baka duka amma yanzu kana neman mayar dani jaka Abu kaɗan Duka, To kasani wallahi ka sake ɗaga hannu ka dakeni sai na rama,Jaki jahili ka koma makaranta kaje kaji yanda ake kula da mace,ka tsaya hauka cikin gida da Dukan mace, Girman kan asara ya hanaka gane miye Aure,Kamin na kyale ayanzu ina mai tabbatar ma da cewa ɗan zaki ya girma,kana barazanaka ta banza wallahi ,karkaga ina tsoron kace zaka ɓatar dani ko ka kasheni nason duk abinda yafaru daga abinda kake fada to bakai kayi ba, Ya zone a kundin kaddarata,Kana miye ruwana da Raunin jikinka,Wallahi A irin tsanar da nikema Ko gani nayi an kawo gawar ka gabana ba isata zakai kallo ba, sai naji ka isheni da Wari zansa a kawar dakai,Bana sonka,bana ganin girman ka, Nagaji da abinda kakemun,kana na kusa ɗaukar mataki wallahi kwana kusa ka zuba ido kagani..


Wani tsoro da fargabane suka kaimai ziyara,Har Yaushe yayi lalacewar da Husnah ke gayamai magana haka,Aiko zata gane bata da wayo,wai miyasa ranar nan tazomai ahaka ne?.


Itakam ganin baya da tacewa yasata haurawa sama cikin natsuwa take tafiya har ta shiga Ɗakinta ta zauna,gabaki daya ya Ƙeƙasarmata da zuciya,Tanajin Hakurin ta yazo ƙarshe,Ya dace ace Tayi amfani da Damar ta Tabar masa gidan, Wato Dama ganin yanamata tana sharewa tana kuka yasa yake ganin duk kazantar da ya kwaso akanta zai juye ,Aiko zasu Daura dammara daga rana mai kama ta yau yagama cutamata ta kyaleshi Alkawari ne ta ɗaukar ma kanta, A'hankali ta kishingiɗa Akan gado dan ba sallah zatai ba,Ta ɗauki wayar ta tarr da shiga camera,akaro na farko ta fara ɗaukar Fuskar ta Awayar,dan wajibine ta samu shedar tinkarar iyayenta kai tsaye,Gabaki ɗaya raunin dakw fuskar ya fito tass,Har marin daya mata da wajen yayi jawur.


Bayan tagama ta ɗauki wayar ta fara karatun wani novel na Oum Aysha mai suna Zaman Tasha,Sosai take dariya Jin diramar Modibbo da Inna,Gabaki ɗaya ta duƙufa baji ba gani, fatan ta taga yanda za'ayi,Shin Irfanu zai Auri Moopy koya?


*Yah Sheikh*


Suna tashi makaranta Alwallah kawai yayi yashiga masallaci , Yana gama sallah yayi Addu'a yafito,Sauri sauri ya fada gidan Inna, Fatan shi kawai yaga Husnah koya samu sukunin zuciya..


Inna ta tarbeshi tare da cewa" Yanzu nike cewa shuru Husnah bata shigo ba,ko baku tashi da wuri ba.


Cikin mamaki yace "bata zonan ba? To ina taje dan yama manta da Aure gareta.


Cikin mamaki tace "Yo inafa zataje in'ba gidan taba.


Hakane yace a sanyaye yana shiga dakin shi ya dakko key yacemata zai fita shago.


Fatan Sa'a tamai tare da fadin in'tagama abinci zata mikomai.


Kai kawai ya dagamata kana ya fita.


Shagonsa ya buɗe wanda babu wasu kaya masu yawa ya zauna akan Carpet din sallah ya fara karatun Alkur'ani cikin sanyin muryar sa, Yana fatan zai gusar mai da Damuwar sa.


Sadam kau baidawo natsuwar shiba har sai sadda yaji wayarshi na Ring.


Dakyal ya mike yashiga Ɗakin daya kwana ya dakko wayar .


Zama yayi akan gado tare da Natsuwa ganin mai gidanshi ne yayi Sallama, Tare da sanya wayar speaker dan bazai
Iya kangata ba, gabaki daya kunnansa sun jimai rauni.


Daga cen bangaran akace "Sadam ka yini lafiya? sakon dana baka jiya nayi Waya da Alh Bilan yace baka kaiba inacewa lafiya?.


Dam!!! gaban sadam ya buga, a kiɗime ya mike yana fadin "Yallabai banajinka bari in sake kira.


Aguje yama manta da raunin jikinsa ya fita yana kwalama mai gadinsa kira.


Da sauri ya fito daga toilet yana gyara zariyar sa yace" gani mai gida.


Kai budeman motar nan maza fiddoman akwatin dake ciki ka shigoman dashi palo.


Cikin mamaki yace" Aiko wallahi naga Dumba ya dauki akwatin nan yace kai ka aikeshi dashi .


Gabaki daya idonshi ya zaro yana ɗora hannu aka ya fasa ihu yace" Kai kana da hankali kuwa Rabe?,Biliyoyin kuɗaɗe ne fa aciki,Kana nufin ya fita da akwatin nan, in'kau hakane Dumba ya kasheni wallahii, Ya gama dani , Ya koma ciki da gudu tare da zaro wayar shi ya kira Mai gidan sa.


Yana dauka Sadam ya fashe da kuka yace.


" Yallabai jiya a hanyata ta dawowa Gida Wallahi ɓarayi suka tareni sukamun shegen duka daga karshe suka tafi da kudin ka gafaraceni Yallabai.


Wani irin dariya yaji mai gidan nasa yayi kamin yace .


"Yaro man kaza, Munyi irinku bila adadin masu irin wannan bakin naka,,To bari kaji, Wallahii Wallahi saika nemomun kudina CifCif, Dan ni ba jahili bane,A dauke kuɗi amma wayarka gata gaban ka ba adaukaba?,To kafi kowa sanin nawane aciki dan haka maza maza nabaka awa ashirin da hudu ka nemo kudin nan, in'ba haka ba zakaga abinda zai faru ya kashe wayar shi...


Tashin hankali wanda ba'asamasa rana Sadam yace yanajin duniyar na juyamai.


Dumba Dan Allah ka bani ba nawabane yace cikin tashin Hankali kamar yana gabansa.


Akiɗime kuma ya ɗauki wayarshi ya shiga kiran Dumba.


Cikin Sa'a ta shiga yakumaji an ɗauka.


Wasu ajiyar zuciya yashiga saukewa tare dayin sallama yace .


"Baba Dumba dan zatin Allah ka jikaina ka tuno Alkhairi dana ma ka kawar da sharrin da sheɗan yasani ma ka maidomun akwatin kudina, wlallahi ba nawabane , Zan iya rasa komi nawa dana mallaka akan kudin nan dan Allah.


What?.
"Wai kai Ɗan agwagwa kana nufin akwatin danakai a ajiyemun kudi ne? Hahahahahaha Cass.
Bye shege nagode daka faɗamun ya kashe wayar cikin jin daɗi, Dan
baitaba kawoma ranshi ba cewar kudi ne ciki ba shiyasa ko buɗawa baiba.


Kuka sadam yasa kamin ya mike ya Ɓalli magungunanshi yasha kami dakyal ya fito yanajin jiri.


Kai tsaye motar shi ya fada yafita daga gidan da gudu.


Gidan Mai GIDAN nasa yayi amma duk yanda Yayi tamai waya akan yazo yaga zahiri kiyawa yayi, Daga karshema sawa yayi aka korashi daga gidan.


Rana zafi inuwa kuna,Dakyal ya iya tafiya office dinsa,koda yaje Yaran dake kasanshi kallon shi suke ,Da yawansu daɗi sukeji dan yana balain basu wahala,ko kadan baison daraja dan adam ba shi amatsayinsa na mai arziki,Ko jaje basumai ba sundai tabbatar haɗari Yayi dan dagashi sai Vest tai kaca kaca da jini ga jikinshi duk ya kumbura.


Gaidashi sukai ya amsa a wulakance yana hararasu tare da fadin.


" Dan uban Inna ku bakuson Kuga mutum cikin yanayi ku gaisheshi da jiki ba?.


Duk kasa sukai da kansu kamin daya daga cikin su yace .


"Sorry Sar, Allah ya kyauta gaba.


Tsaki yayi kana yace" in Ameer yana kusa a turoman shi office yayi gaba.


Da kallo suka bishi daya daga ciki yace .


"Allah nagodema,ubangiji kasanya a karamasa lahani fiye da wannan,Natsani mutumin nan Wallahi, bashi da mutunci,ko Abokifa bashi dashi gani yake yafi karfin kowa, ɗan iska kai kamar shekar ungulu.


Nan sukaita tsogwami har Ameer din yazo suka koramai bayani .


Cikin tafiya irin ta Yan daba ya haura sama, yana zuwa yashiga yace.


" Barka dai Sir! Ya jiki jiki? sosai Allah koro affuwa.


Ameen yace yana hararashi.


"Waikai miyasa baka wanka kasa turare sai tsami kake Ameer? cewar sadam cikon isa?.


Kallon kanshi yayi yana sanye da kananunn kaya riga da wando wankama ya fito amma wannan dan iskan zai wulakantashi.


"Haba mai gida kallani dakyau kagani,Ni wallahi niyadace ince haka, Dan tinda nashigo zarni nikeji da warin Jini.


Shuru sadam yayi kamin yace.


"" Ameer taimako nike nema,naga kana da malammai ko,na tabajin kana firar dasu Haruna,Dan Allah ka samu acigitamun kudina,dan wlh rashinsu akwai matsala.


Ameer najin haka ya gyara tsayuwar shi kamin kuma ya saki murmushin mugunta yace.
" Aiko faɗuwa tazo daidai da zama, Dan Babana mashahurin malamin zaure ne,kai kai tsaye ma zan iya Cema Mushriki ne, Dan yason tuggu kala kala amma fa shi kawai aikin kudine yakeyi,In zaka saki kudi zakaga kayan aiki.


Ba matsala yace yana mikewa dagashi sai vest din dake jikin shi suka fita,, Kai tsaye hanya suka dauka har wani ɗan kauye dake jihar Katsina.


Cikin wasu Bukkoki suka tsaya bayan bishiyoyin da suka keta kamin su iso.


Ka tsayanan ina zuwa Ameer yace yana shiga wata bukka.


Tsaye yayi yana fadin" Allah ka taimakeni narasa aikin nan ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login