Showing 51001 words to 54000 words out of 69765 words

Chapter 18 - MATAR AURE BOOK COMPLETE PDF.txt

girkin tarbar su Ahmed da suka gama komi suka dakko hanya da iyayensu da yan uwa na jigawa dan zuwa gagarumar walima da aka haɗa.


Cikin kamala da girmamawa tace "Aunty Aisha akwai wacce zatama kawata ƙunshi ko na kira mai lallena.


Cikin sauri tace" eh Dan Allah Maman Ameer kirawota dama so nike mu rage aiki mune nema, muma an muna dan baza'a barmu abayaba kp Mimido tace da Amina.


Tace wannan haka yake muma yau Amare muke a wajen mazajen mu.


Dariya tayi ta fita ta koma dakin Husnahhh ,kallon ta tayi sosai tace" Husnah wallahi har mamaki kike bani, wannan sihirtaccen kyau da kikayi cikin kwana kaɗan,Lallai kinci wahala gidan sadam wazaice kece....


Dariya sosai tayi tace" wallahi nikuma bana gani, kawai abinda nike gani nayi kiba, kana kadan kadan abinda ake bani yana sani ciwon mara gashi kema kin karamun wani ya zanyine cikina na mun ciwo Sosai Hafsah bakiji ba Wallahi,Abindama kika bani ya sake tayarmun da ciwo na.


. Dariya Hafsah ta kwashe dashi tace yaro man kaza, gobe kinwarke ai..


Fuska Husnah ta kwaɓe kamar zatayi kuka Hafsat tace .


"Nidai zo intina baya akanki, zo namiki kitso Tinda ba haka zaki da kankiba kwara a kitse shi,.


Da sauri Husnah tayi kanta ta rungume tace'' wallahi Hafsah kaina yafi shekara babu kitso, saidai in wanka in gyara Shikenan.


Murmushi tayi tace yau kau zakiyi .
Waya Hafsat ta ɗauka ta kira mai mata lalle tamata kwatancen gidan su Husnah kana ta kashe wayar.
Ta fara tsarama Husnah wasu kananun kitso kai kayi tinanin da Allura akeyinsa, Yanda ya tsaru yayi sharr dashi gata da sauri.


Lokacin dasu Aysha suka shigo turus sukaja suka tsaya ganin yanda aka yarfama Husnah kitso mai shegen kyau.


Anan duk suka rikice suka kwance ɗauri tare da fadin "sai tamasu tana Faɗin bazataiba kawarta kawai zataimawa.


Dakyal suka shawo kanta akan suma a
Amarene tace zata masu amma bazaikai na Husnah ba sukace sun amince.


Sai Azahar sukaci abinci sukai Sallah kana mai lallan tazo, Hafsat tacigaba da idamata.


Nanfa aka farama Husnah laillai na hannu ja mai masifar kyau dayasha kayan Hadi na sirrin Amare daya dace da farar fatar ta.


Karfe huɗu aka gama zana mata bakin lallan da ja kitson Ma lokacin aka gamashi, Alokacin aka fara yarfama Aunty Aisha ,Awa ɗaya aka gama mata Har lallanta dan ba mai yawa akaimataba kuma bakine tayi wanka ta cakare cikin riga da sket, meenah ma awa ɗaya itama tayi wanka sukayo shiga cikin wata dakekiya atamfa mai kyau da Abbah ya masu su ukku, Kai kace yan ukkune gabaki ɗayan su sunfito Hafsah sai photo take su,Sai mangariba ta fito ita da mai lallan suka shiga motar ta suka tafi da niyyar sai washe gari zatazo da wuri..


Yah Sheikh kuwa yana gama murnar tashi ya fada Ɗakin shi yazuba wani uban wanka cikin dakekiyar shaddarsa mai tsananin kyau sky blue ya tausa hula kana ya fito yana zuba kamshi.

A harabar gidan yaga su Imran suncika gidan da Abokan su sunfi 30 .


Suna ganin shi suka sanya Wata siririya Guɗa da yasanya Shekh murmushi,gabaki ɗaya Abokan su Imran suka hau rungume shi cikin farin ciki da soyayya hadi da tayashi murnar dawowarsa cikin Ah'lin sa.


Zamewa yayi ya zauna tare da am'samasu cikin fara'a sosai yana mika masu godiya.


Imran yace" Yah Habib wayan nan duk abokan mune,mungayyato sune dan tayamu murna,so zamuyini dakai yau,munson gobe ba ranar mubace,Naso Daddy yabani damar hada gagarumin party amma ina yakiya.


Kanshi ya shafa yace" masha' Allah daya Hana,Nagode sosai dan banason bidia,Amma zan fita naje unguwar da muka bari na kaiwa Abokaina malam mai katin waleema nah.


Sameer yace duk munhutar dakai munje Daga cenma muka dakkosu muka zo.


Fuska ya dan yamutsa yace "to zan shiga gidan Abba .


Baki suka hada wajen fadin" mizakayi Agidan da Duk mata ke akwai?.


Kanshi ya sosa yana Turo baki yace matata zangani kai haba.


Gaba-daya suka sanya dariya shikuma yayi murmushi ya ɗauki wayarshi yama Husnah text, Tare da mayar da Attention dinsa kansu suka fara fira, baya samasu baki sai dai kadan kadan ya duba waya amma har lokacin baiga reply ɗintaba duk yaji ya damu..


Sai bayan mangariba suka rabu da Abokan su sameer.


Bayan ya fito masallaci Isha yakasa dauriya kai tsaye ya nufi gidan a Bahrain yana tafiyar sa dai-dai cikin natsuwa.


A harabar gidan ya iske motoci cike da alama yan bikin ne suka kara so.


Wani iri yaji harya juya zai koma gidan su yaji ance .


*Ɗan balarabe*.


Da zafinsa ya juyo suka hada ido dasu Ahmed da suka fito daga Palo.


Wani irin farin ciki marar misultawa yaji ya dirar masa, Da sassarfa ya isa inda suke ya hade su duka ya rungume yace .


"Nayi kewarku yan uwana sosai,bana da Aboki ko daya sai wayan cen yaran da basuson daraja aure ba, Tinɗazu inaso naje ga matana amma sun'hanani,nason tinda kunzo zakumin jagora na ganta,yau kwanana biyar bansata idoba yakarasa yana langwabar da kanshi kamar zai kuka.


Cikin tausayinsa Ahmed yace" Ayyah Aboki yau zakaga matarka Insha Allah yan uwanla sunzo zamu shigema gaba.


Umar yace Allah nima yau da tawa zan kwana harma na kama muna daki bazan iyaba gaskiya kwana takwas fa ba awa takwas bane..


Ahmed yace Irin abinda kake bankamuna ai dole ka kama ɗaki,kai kenan ma soja, abu yama karfi inaga ni,Gana Abokina nan na ragomasa ya karasa yana bude bayan boot ya fiddo wasu ledoji dake cike da magunguna ya damkama Shekh yace karba ga tsaraba da na yoma.


Murmushi yayi yace na miye.


Ahmed na bubbudawa kamar in'garma yace" kai dai gashi,in'kasha ka fadamun,kason bazan baka gubaba,ga wannan shinike bukatar ka farasha zuwa gobe ka tsumu da akaika kasa kwara ka kai , Ya ware wani katon leda yabude yaba Shekh.


BISSIMILLAHI yayi ya sha yana ɓata fuska ,saida ya gama yace gaskiya Ahmed bayan karkace wani abu da sai nace banji daɗin wannan kyautar ba,gabaki daya ka batamun baki nida zanje wajen matana, Dole na koma gida nayi sabon brush kartace bakina na wari.


Dariya suka Saki Umar ya gilgiza kai yana fadin wannan haka yake yakau batama baki gobe kaima ka ɓata gado, Amma Ahmed kayi gaggawar bashi Maimakon kabari sai gobe,kaifa kana da abinda zaka rage shifa?


Ahmed yace shima wallahi yana dashi mutum da matar sa.


Shuru SHEKH yayi lokacin daya gane inda suka dosa,Take ya farajin canji ga jikinsa yana mai jin tsigar jikinshi na tashi.


Gabaki daya suka kalleshi shima ya ɗago suka hada ido dariya suka kwashe da ita ganin yanda yake lumshe nashi kamar zai bacci.


Rigar shi ya ɗan gyara yana zubamasu harara tare da cewa ɗan kiramin ita ni kunya nikeji Ahmed bazan iya shiga ba.


Ahmed yace niga rasa kuny beran tanka ko? Sirikanka ne nima nawane bazanjeba,kamata waya mana ta fito.


Bata ɗauki yace cikin damuwa.


Ahmed yace wallahi palon babu mutane duk suna sama dakin Umma,Amma naji ihunsu Aysha kasa kosu basu som munzoba na tabbata tana tare dasu.


Da suari yace" Allah"..


Kai ya dagamai Alamar tabbatar wa.


Sheikh ya gyara jikin shi Umar ya cillamai wani magic chingum ya sanya ga baki kana ya nufi kofa.


Ahmed Yace" wait !tsaya nima inzo in'dakko tawa wallahi , Umar ma binsu yayi suka shiga su ukku, Cikin Sa'a babu kowa palon hakan yasa kai tsaye sukayi kofar wajen, Umar ya dan kwankwa Sa.


Aysha da sukagama turara jikinsu da turaran UMSAD INCENSE su duka , cikin tako da kwalliyar da sukasha ta bude kofar tana ta sakin makirin kamshi.


Wani irin suman tsaye Umar yayi lokacin da ya hada ido da ita gabaki daya ta canzama ganin sa.


Gabaki daya ya rikice hakan yasashi manta inda yake,gabaki daya ya jawota jikinshi yana fadin.
" i miss u so much my A'ish, nayi kewarki sosai..


Ido Aysha tashiga rabawa lokacin dataga su shwkaru sunyi kasa da kansu wani bala'in kunya ya kamata.


Ahmed kau da ba ruwanshi yace dallah Malam kafita ka tsaremuna matan mu ciki ka barmu waje kamar kwandon shara.


Shekh kau gabaki daya ida rikitashi sukai da abinda yaga sunayi ga tsikar jikinshi sai tashi take, bakaramin daɗin maganarshi Ahmed yajiba kwara su tafi..


Da Sauri Umar ya kama hannuta yace zo muje kirakani wani wuri yana jan Hannuta.


Tace Baby mayafina? Yace bashshi ina da jaket a mota kyasanya.


Ahmed ma tashi ya cafko suma suka shiga mota sukayi gaba .


Shekh kau Saida Ya daidai ta kanshi cikin natsuwa kana yayi sallama yashiga Ɗakin ya rufe.


A razane Husnahhh dake karanta message din daya mata ta ɗago tana kallon shi .


Tsaye yayi jikin kofar ya jingina tare da zubamata narkakkun idanuwansa da suka canza kala.


Cikin rawar murya ta amsa tare da mikewa tayo inda yake da murmushi a fuskarta tace" Yah shekh! Sannu kaine,kaji sauki ka fara fitowa.?.


Kasa magana yayi dan wani masifaffan kyau yaga tayi ga farar fatarta datasha lalle tayi yalo shar sai glowing take na dilka, kitsonta kau ya fito tass ta gaban ɗaurin kallabin data kafa mai kama da gwargwaro ta saki sauran jela ta sakiya sai lilo take.


Hannuwansa ya bude mata alamar tazo gare shi.


Kanta a kasa ta fada jikinshi cikin kunya ya mayar da hannusa ya rufe ruff yana lumshe ido dajin wani feeling saboda kamshi jikinta daya dake shi.


Sun daɗe a haka kamin ta zame daga gare shi ta koma gefen gado ta zauna tayi ƙasa da kanta tare da faɗin" Sannu da zuwa ina wuni.


shiru yayi na dan lokaci kamin ya amsa yace ina wayarki namiki text shuru ba reply,miyasa kika gujeni bana ganin ki,hope badai laifi na mikiba?.


Fuska ta yamutsa jin cikinta na murɗawa kana tace'' Aa Babu abinda kamin , kawai Ammun lalle ne so bangani ba sai yanzu.


Cikin kula da yanayin yanda take ta matsa cikin ta yace" mike damun cikin ko har yanzu bakigama period dinba?


Kai ta gilgiza mai kamin cikin sanyi tace "cikina kemin ciwo kwana biyu.


Ido ya zaro kamin da sauri yazo inda take ya kama hannuta cikin kulawa ya zame kasa yace "mike damunki Oum Habib ko kinci wani Abune?.


Cikin shagwaɓa tace banci komi ba, kullum ciwo yakemun nakusa sati Fa amma yau yafi.zafeee.


"A ina"?.
yace cikin Damuwa tare da kafe cikin nata da ido.


Rau rau tayi da ido tare da nunamai saitin Mararta dayamata wani kumburi ya cika sosai .


Cikin damuwa ya tashi tsaye tare da cire kallabinta ya tsurama kyakywan kitsonta ido , Lokaci daya kuma ya shafa kanta tare da furtaa Masha Allah kinyi kyau Ƙurratu ainun, duk kwalliyar kasancewa da HABIBIEEE kine gobe?.


Hannu tasa ta rufe fuskanta tana turomai baki.


Ɗan murmushi yayi kana Cikin natsuwa ya kwantar da ita plat, tare da sanya hannusa yafara ƙoƙarin yin sama da rigarta


Da Sauri ta damke hannusa tana kadamai kai hawaye har sun fara zubomata tace'' ka daina yah shekh akwai zafifa.


"Husnah babu abinda zan miki karki manta a cikin gidan sirikaina nike,inaso in duba lafiyanki ne fa Sheikh ya fada yana kafeta da ido.


Shuru tayi tana lumshe ido yayin da yayi sama da rigar ta,Ya tsurama lafaffan cikinta ido,Babu wanda ya isa yace akwai ɗan da yataba kwanciya a cikin sa, dan a shafe yake luff( karku manta yaji labarin ɓarin da tayi wajen Hajja da sadam ya mata karya).


A'Hankali kamar bayaso yake dan tattausa wajen amma baiga ta nuna alamar zafiba,Kasan cibiyar ta ya ɗan farabi ya sanya manyan yatsunsa guda biyu ya ɗan Danna.


Ashhh tace da karfi tana rike hannusa gam.


Nan ne ke miki ciki yace cikin wata narkakiya murya?


Eh nan ne tace.


Shafa wajen yafarayi yana dan murzawa tare da lailayawa.
Kaɗan kaɗan.


Ajiyar zuciya ta dinga saukewa, wata zufa mai ƙarfi na Tsatsafomata.


Ya ɗau tsawom 10mnt yanamata haka kamin ya Daina ya kalleta yace" Husnah mikikaci,Hala wani abu aka bankamiki dayafi ƙarfin ki ko, bakya tausayina bakiga yarobane ni?,bakya gudun kimin rauni,dan Allah in anbaki abu kibarci ko kuma ki dinga sammun.


Cikin rashin fahimta tace mikake Nufi?.


Ido ɗaya ya kashemata tare da cije lips dinsa yace''" Kinci Kayan daɗi dan kinson zaki bada Daɗi, to ki ciyar da mai bakin Daɗin shima yaci ku taru kusha gamsashen daɗi mana.


Kamar an bugamata giduma taji kalamansa ,Sai yanzu taji haushin kanta data fadamai abinda ke damunta gashi har ya fassarata Hmm.


Dariya Sosai yayi ganin yanda tayi wuƙi wuki da ido yace" ko in ɗakko mota mubi su Ahmed muma?

Aguje ta tashi ta faɗa Toilet ya fashe da dariya .


Wayar shi yaji tana ring hakan yasashi dubawa, Ganin Daddy ne yasashi tashi yafita daga ɗakin Yayi gida,Sai wajen goma ya koma dakin shi zuciyar shi fal nishaɗi.


Adaran Ranar Shekh kasa bacci yayi idan ya tino irin taushi da santsin fatar ta daya dinga murzawa,Ahaka yayita juyi sai gab Asuba bacci ya sace shi.


Washe gari aka tashi da hidima kota ina ba kama hannun yara.


Zugar kawayen Amal guda data yan uwa da Abokan arziki duk sun cika Dakin Husnah .


Karfe ukku Husnah tayi wankan ta lafiyayye da turaruka aka kirawomata mai make up ta hau Tsantsara mata kwalliya ta kece raini.


Hudu da rabi aka fiddota cikin shiga ta Alfarma sai wani masifaffan kamshi take kamar kamfanin Turare aka juyemata.


Sanye take cikin wani dakeken material silver colour mai masifar kyau da tsada,daga sama kuma aka samu wata kyakywar Alkyabba mai shara shara aka rufamata.


Wani sihirtaccen kyau tayi kamar jinin sarauta.


Aunty Halima ce ta shigo tana sakin kamshi tasha jallabiya baka mai duwatsu sai sheki take.


Bayan sun gaisa dasu Umma tashiga ɗakin Husnah ta kamo hannuta tace kowa ya fito ana jira


Nan kowa yafito itama ta fito da Husnah ta buɗe wata kyakyawar farar mota sabuwa kall ta sanyata baya.


Wani sassanya kamshi Husnah taji lokaci daya kuma taji Ajiyar zuciyar shi tare da furta "Alhamdulillahi Masha Allah"..


*Gamai bukatar book din MATAR AURE yamun magana ta wannan layin 07038423451*




UMSAD MAKENTOSH


*Makentosh*
*Makentosh*
*Makentosh*


Ina macen da ta isa takejin takai Hajiyar gayu.


*HMMM DA SAURANKI HAJIYATA INDAI BAKYA AMFANI DA MAKENTOSH*


Matso kiji hajiyata


Kamar yanda kuka sani UMSAD INCENSE ta sake zomuki da wani sabo sahihi mai suna MAKENTOSH


MAKENTOSH wani sirrine nasu na mutan Maiduguri,yana da masifar kyau yana hade mace gam koda haihuwa goma tayi,ina uwargida ina amarya ina budurwa ina zawara duka dai gudun'muwace daga mai kishinku har kullum UMSAD INCENSE.


Ina baku shawara da ku nemeta dan magance matsalolin da suke faruwa damu tsakaninmu da mazajenmu dan gyara shinfiɗarmu kai tsaye.


Ni Ummy Aysha shiyasa na kasance shalele awajen mai gidana saboda gabaki ɗaya sirrin gyaran jikina yana Tattare da gudun muwar UMSAD INCENSE shiyasa koda yaushe muke cikin walwala da farin ciki da mai gidana🥰.




Dan neman farin ciki akoda yaushe tsakanin ki da mijinki ki tuntuɓeta a wannan layin






Sayen nagari maida kudi


UMSAD INCENSE 080 288 27241


4️⃣5️⃣&4️⃣6️⃣


"""Ƙasa ta sakeyi da kanta tanajin yanda zuciyarta keta tsinkewa.


SHEIKH kau dake sanye da Ash din shadda mai masifar kyau yayi wani irin sharr ,daka ganshi kaga ango, Sajen nan nashi yasha wani irin haɗaddan gyara yayi luf luf ga farar fatar shi,kyawawan idanuwanshi ya ɗan lumshe kaɗan kan ya buɗesu ya zubamata su, Kaɗan ya ɗan sunkuyo kanta tare da sanya hannusa ya dan ɗago haɓar ta.


Cikin natsuwa ta ɗan kalleshi cikin wani sabon salon data koya wajen su Aysha tace" Ina wuni Yah SHEKH.


Laɓɓansa har rawa suke wajen am'sawa,Gabaki ɗaya hankalin sa na wajen kallon Tsantsar kyan da tayi .


Cikin wani low voice yana kasheta da narkakkun idon sa yace.
* Ahaka zakije?.


Kallon shi tayi ta juyamai ido alamar kamar ya?


Jikin sa ya jata tayi luff akan faffadan jikin shi tana shakar lafiyayyan kamshin dake fita daga jikinsa yace.
" Husnah banƙi nayi gidana dake ba a yanzu,ina ma sai bayan biki aka sanya wannan walima,ina kishin aganemin adon ki my wife.


"Ɗan kallan shi tayi tana wasa da aikin gaban rigarsa tace "Wazai kalleni bayan ni takace Yah Sheikh Duniyama ta sheda da haka,waya kaika da zai ɗauki hankalina,kana fa tare dani karka manta kai din garkuwana ne, babu wanda zai kawomin hari bayan gaka kusa dani,na tabbata duk namijin da zaiganka ya kalli kansa sai ya rainama iyawar sa, Kai din daban kake a ko ina Malamina kajiiii.


Kai ya jinjina cikin samun natsuwa da kalamanta kana yace *i love You Oum Habib*.


Mee too my life tace tana lumshe Ido.


A kunnan ta yace.


"Ya daina ciwon yanzu?


Baki ta ɗan turo tana tashi daga kanshi ta juya kai .


Murmushi yayi yace. Hakuri kika basa my Husnah?


Nan ma shuru tayi hakan yabashi dariya yajata jikinshi yana lumshe ido da shakar kamshinta mai samai natsuwa kota ina.


Ahmed ne ya buɗe motar ya shigo yana fadin "mun'makara ko?.


Shuru SHEKH yayi dan gabaki ɗaya hankalinsa naga abincin ruhinsa, baimason da shigowar saba.


Ganin haka yasa Ahmad tada motar suka tafi.


Katafariyar harabar katsina motal suka shiga inda suka iske lafiyayyan motoci,gabaki ɗaya kowa ya hallara bakajin komi sai Qira'a Sheikh AbdulRahman Sudais cikin suratul Amfal, Gabaki ɗaya wajen yayi tsit karatu na ratsa zukatan Al'umma da samar masu da natsuwa.


Bayan sun iso Dai dai get din Ahmed ya buɗe masu mota SHEKH ya fito ya zagayo ya budemata ta sako da kafarta daya,Kana ta ida fitowa kanta a kasa.


Hannuta ya kama suka shiga ciki inda ke cike da jama'a.


Bayan sun zauna Shekh Abdallah Abokin Yah Shekh ya buɗe taro da Addu'a, Tare da taya abokin shi murna bayyana iyayen sa dakuma Angon cewar da yayi .


Bayan gabatar da Addu'a ya nemi ganin su Daddy a cikin fili dan bayyana farin cikin da suke Ciki da wannan rana mai Albarka..


Masha Allah nace lokacin da su Abbah suka taso cikin shigar su ta alfarma ,suna sanye da fararan shaddodi da sukasha Aikin gold brown masu masifar kyau da tsada, hula da takalmansu duk Gold Brown, shigar ta haska su duk tsiyarka bazakace ba jini dayabane su dan Sunfito kamar Yaya da kane..


Speaker Daddy ya karba yama baƙin sa sannu da zuwa da mika godiya ga Allah da ya nunamai wannan Babba rana ta Aurar da ɗanshi , Bayan shekara sha biyu daya kwashe batare da suba, Atakaice ya ɗanyi jawabin daya dace ya mikama Abba.


Shima Abbah godiya yayi ga jama'a su kana ya sama auran su Albarka .


Bayan sun mikama Shekh Abdallah yace.
" muna buƙatar ganin Ango a tsakiyar wajen nan dan gabatar da kansa wa Abokan mahaifinsa da kuma nuna farin cikin da yake ciki a wannan Babba Rana.


Cikin Kamaala Yah Shekh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login